Free chapter · Read without an account
9
KURURUWA A KUNNEN KURMA 🥀 🥀
A 2025NOVEL
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
AMEENA IBRAHEEM
(OUM AMEER)
Wattpad:@ Ummu-Ameer
Arewabooks: @Aminatuibrahimbawa
From d experience writer of:
Zaytoonah
Abarwa rai
Gudun wuce sa'a
Kibiyar so
Kulsum
Bahiyya
Nuudarr
& Now Kururuwa a kunnen kurma
Littafin kuɗi ne. #500 kacal, zaki iya turawa ta wannan asusun 3132703269 Ibrahim Amina Bawa, sai ki tura shaidar biya ta wannan Layin ***. 🙏🙏
FREE PAGE 9
"Xuhra babu ɗa ɗaya da zan yi wa auren dole a ko wane irin hali, matuƙar bai amince ba ba zan masa dole ba, a nan ma babu tilas Xuhra idan kin amince ne za'a yi idan baki amince ba kuma babu zancen dole kuma ba zan ga laifin ki ba...."
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Ita ce kyakkyawar kalmar da Xuhra ta shiga furtawa a zuciyar ta, a ranta tana faɗin 'lallai yau Baba ka sanya ni a tsaka mai wuya ni Xuhra, ka kai ni ƙarshen babban bango ka datse ni Baba! Xunnurain? Ex ɗin Safnah fa? Mutumin da ya gurza min rashin mutunci... Ko da yake zan iya cewa muka gurzawa juna haɗuwa biyu kacal da muka taɓa yi a rayuwa, mutumin da ban san shi ba bai san ni ba, rayuwata daban rayuwar shi daban, yana duniyar sa ina duniya ta ta ina zamu haɗu, samarin da ma na amincewa na ke kula su ya na iya da su ballantana wani mutum daga sama? Ta ina zan fara ni Xuhra? Tsari na da Xunnurain sam bai zo ɗaya ba,na tsane sa! Na tsane sa, mutumin da yana kallo jini na fita daga jikina amma ko ɗigon alamar tausayi na babu a fuskar sa! Idan na aure sa binne ni zai yi da raina, Yah Allah!.........'
Ganin kalar reaction ɗinta shi ya sanyayawa Baba guiwa murya a raunane ya ce.
"Na fahimce ki Xuhra...."
Duk da irin tsananin ruɗanin da zuciyar ta da ƙwaƙwalwarta suka shiga, hakan bai hana ma ta aron jarumta da ƙwarin guiwa ba ta ce.
"Baba! Mu ɗin nan fa 'ƴa'ƴa ne, Allah ya ce mu yi muku biyayya matuƙar muna so mu shiga Aljanna kuma mu samu haske a rayuwar mu muddin abin nan ba na saɓa masa ba ne,Yardar Allah tana tare da yardar iyaye, haka ma fushin Allah akan mu yana tare da fushin iyaye matuƙar muka bijire, Safnah ta juya baya, idan nima na ce a'a kuma sam abun ba zai kawo kallo ba, tunda har ka amince da shi wallahi ni ma na amince na karɓe shi da zuciya ɗaya (a cikin ranta kuma da sauri ta ce 'astagfirullah', Tunda har tasan cewa idan Daddy yayi mata umarni ba zata taɓa iya tsallakewa ba, to haka shima a wurin Baba ba zata iya musanta mi shi ba, kuma tun tashin ta bai taɓa neman alfarma a wurin ta ba sai yanxu saboda haka akwai matuƙar kunya idan ta ce wai ta juya mi shi baya, she will accept the marriage for now, but daga baya dole zata nemarwa kanta mafita saboda wallahi tallahi ba ta son Xunnurain kai ko kusa da ita bata so ma ya zo ballantana wai a ɗaura musu aure) "
Cikin tsananin farin ciki ya washe haƙora yayi ta zunduma mata godiya yana sanya mata albarka, daga ƙarshe ya ce.
" Xuhra haƙiƙa kin yi min 'ƴa, kuma in sha Allah zaki yi alfahari da hakan wata rana, ta shi ki je, zamuyi magana da mahaifiyarki "
Daga haka ta tashi jiki ba ƙwari tamkar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki ta miƙe bata tsaya ko ina ba sai master bedroom ɗin Mummynta ta faɗa kan gado tana mai fasgewa da wani irin mugun kuka, daman side ɗin na su ba kowa duk ana ɓangaren hajiya Shafa. Bayan ta darji kuka ta fahimci dai babu wata mafita yasa ta ɗauki wayar ta ta kira Yah Umar, Yah Umar shi ne mutum ɗaya da suke da kyakkyawar fahimta da juna shiyasa kowa ke cewa don halin su ya zo ɗaya ne shiyasa suke aminta.
Shi kuma Umar ɗin yana can zaune suna tattaunar Maganar da Baba bayan ya koma yana yi musu bayanin cewa ta amince kwatsam ya ga kiranta, yana ganin kiran shi kan shi sai da ya ji zuciyar sa ta buga domin yasan halin Xuhra ciki da bai, manyan mutane 'ƴa'ƴan masu kuɗi masu manyan muƙamai da tarin dukiya, wa su ma masu neman ta most of them ba a ƙasar nan suke zaune ba but ko ɗaya ba ta baiwa space ba ina ga Xunnurain wanda ta ke ganin ba kowa ba ne?..... Ganin yanda ta ke ta kiransa miss call bayan miss call yasa ya miƙe kai tsaye ya ɗauki excuse ya fice.
Xuhra kuwa, Sautin kukan ta ne ya ƙaru ganin tayi ta kiran Yah Umar bai yi picking ba, it means ke nan ya na bayan Baba shi ma, hakan sai yasa ta ji ranta ya ƙara gashewa sosai, kai tsaye ta kamo numbern Jawad wato ɗaya daga cikin samarin ta ta tura mishi text da cewa an ce ta gabatar da wanda zata aura saboda haka ya yi maza ya shirya ya zo kada ya taushe hannu. Komawa tayi ta kwanta lamo! Akan gadon tana nazari,idan har plan ɗinta ya tafi yanda take so, idan suka fahimci bata son Xunnurain ɗin ran Daddy zai yi ɓaci ya ce ta kawo wani idan har tace bata son Usman ɗin, to da zaran yace haka kawai sai ta gabatar mu su da Jawad.
Gefen Usman kuwa,waje ya suka koma shi da Baba Lirwanu tamkar zai fashe masa da kuka, amma ganin cewa Baba Lirwanun ya goya baya akan zancen auren yasa dole ya baiwa kansa lafiya but wallahi akwai damuwa.
Gefe ya koma ya ciro waya kawai ya turawa Bilal text Kamar haka.
'To yanzu ai sai ka ta so ka zo za'a ɗaura min auren dole'
Ai kuwa cikin mintunan da ba su gaza talatin ba sai ga shi ya iso hankali ta she.
Ɗakin Umar ya same shi ya yi shiru abu ya ishe sa ya sha masa kai.
"Usman wai mi ka ce??"
Ya jefa masa tambayar yana mai ƙure sa da kallo tamkar yau ne ya fara ganin sa.
Ajiyar zuciya ya sauke murya a raunane ya ba shi labarin duk abinda ya faru. Cike da mamaki Bilal ya ce.
"To miye wani abun ɗaga hankali a nan? Shi ke nan kai da Safnah anyi one-one, ta ƙi ka taso tayi maka baƙin ciki but sai Allah yayi maka wata ni'ima da ba ta za ta ba, but tsaya ko kuma dai yarinyar ce baka so? Ko ka san ta ne tun asali? Ko bata cikin tsarin ka ?"
Girgiza kai yayi yana mai jin wani irin abu mai nauyi wanda ya taso ya danne masa zuciya, da ƙyar ya buɗe bakin sa tamkar ana masa dole ya ce.
"Haɗuwar mu ta farko a gusau ne, by then ba mu wani jima da haɗuwa da Safnah ba, na zo ƙofar gidan su Safnah da Mashin ɗina ita kuma ta zo da mota tayi ta horn a baya na wanda ban san cewa gidan ta ke so ta shiga ba, kawai yarinyar nan ta fito ta tsaya a gabana ta fara bragging tana faɗin.
"Are you mad! Ko kuma kai kurma ne da baka jin horn a kunnen ka, kazo ka wani tare ƙofa kamar ta gidanku....."
Cike da mamaki Bilal ya ce.
"And kai kuma sai ka yi yaya?"
"You know me Bilal, kallo ɗaya na yi mata na ɗauke kai, idan mashin ɗina ya amsa mata to nima na amsa mata, tana nan tana ta ihu kwatsam sai ga Safnah ta fito,nan fa ta tare ta tana tambayar mi yafaru, wai sai ta kalleni ta ce wai ta tambayeni mi ya faru, shi ne fa Safnah ta ce min mi ya faru, ni kuma na ce ai ban fahimci ma abinda take faɗi ba ta dai tambaye ta ita taji, shi ne abinda ya fi ƙona mata rai sosai ta ci gaba da faɗa tana ta zagi turanci da Hausa ni dai ranar haka na tsaya na zuba ido ina kallonta wanda da ƙyar Safnah ta yi nasarar lallaɓa ta ta shige gida ita kuma ta karɓi mukullin motar akan cewa zata shigar mata da ita daga baya, bayan ta wuce ɗin ne ita Safnah ta ke faɗamin wai in yi haƙuri, cousin sister ɗinta ce daga Sokoto suka zo Sallah, sannan ita ɗin ba a nan ƙasar ta ke ba waye waye.. Daga ƙarshe da naji rai na ya ɓaci haka na buga Mashin ɗina na tafiya ta"
Jinjina kai Bilal yayi sannan ya ce.
"Kai! Yau ake yinta ko...."
"Bilal sai da aka shekara biyu kuma wanda har ga Allah ni har na manta da ita a rayuwa ta, na zo Sokoto domin in duba Mahaifin su da ya samu accident shi ma sai ga shi ƙaddara ta sa ke haɗamu, na gama duba shi na fito ita kuma ta kawo ƙofa da tray a hannun ta muka yi karo gaba ɗaya glass cups suka zubo da babban jug ɗin suka tarwatse wanda sai da kwalba ta faɗa a saman ƙafarta ta yanke ta har sai da jini ya fita, Bilal yarinyar nan da ƙarfin hali duk da irin yanda kwalbar nan ta caki saman ƙafarta ga jini a ko ina hakan bai hana ta yi min rashin kunya ba, da taga na raɓata ko kallonta ban yi ba zan wuce shi ne fa ta fasa kuka har tana ɗaga murya, dole na ja tunga na tsaya a lokacin kuma sai ga Miqdad ya fito, nan ya ke tambayarta mi ya faru ta ce wai da gangan na saka hannu na ture tray ɗin da ke hannun ta saboda ina jin haushin ta akan tun abin da ya haɗamu a lokacin da ta zo gusau, Allah yasa Miqdad ya fahimce ni kawai murmushi yayi ya ce in yi tafiyata wanda har yanxu ni ban san yanda suka ƙara ta ba "
Ba Xunnurain ba hatta shi kansa Bilal ɗin sai da yaji zuciyar sa ta buga. Sai dai dole ya ɓoye damuwar sa domin ya samu ya ƙwarara masa guiwa, hakan yasa ya yi murmushi a hankali ya dafa shoulder ɗin sa ya ce.
" Usman! Sometimes mukan ƙi abu ƙiyayya mafi girma daga baya ya zo ya zame mana alheri, while sometimes kuma mukan so abu ƙololuwar so ya zama ba alheri ba ne a gare mu, Alhaji Hayatuddeen ba zai taɓa cutar da kai ba nayi imani da wannan, sannan game da Mata kafi kowa sanin irin halin su, kayi haƙuri ka amshi auren ta da zuciya ɗaya in sha Allah.... "
Girgiza kai yayi yace.
" Bilal Hajiya ni ke ji, kasan halin ta sai rai, yanxu jin abubuwan nan da suka faru a bayan idon ta sai ya sa ta kwana tana kuka kuma duk wanda yazo sai ta faɗa masa"
"Haba Usman, wannan ai duk mai sauƙi ne daga zaran an yi mata bayani zata fahimta, Hajiyar ka kuma ita daman bata da matsala, sabida haka ni dai gaskiya ina bayan su Baba Lirwanu domin wannan karamci da aka yi maka bai kamata a ce ka juya baya ba, sannan gida a shirye yake kawai a ba su mukulli duk sanda suka shirya su je su jera mata kayanta, sannan a bayanin ka ba wanda yacce dole dole yau sai ka tafi da ita gidan ka, su kan su nasan cewa sai sun shirya sannan, in sha Allah lafiya ƙalau za'a yi komai ka manta da ita kawai daga zaran an ɗaura auren dole ta bada kai bori ya hau... "
"Hhmm! Bilal ni fa ina hango abinda baka hangowa..."
"Common cheer up Angon Xuhra, bari na yi sauri na gayyato friends ɗin mu na nan garin...."
Miƙewa yayi yana mai sakin wani murmushin takaici ya ce.
"Wallahi Kada ma ka fara kaji na faɗa maka, auren da ba zai je ko ina ba miye amfanin gayyatar mutane"
Da sauri Bilal ya fice yana faɗin.
"Malam ango jira ni zan je na dawo yanxun nan, kuma kayi ƙoƙari ka sanarwa su Siddeeq kafin a ɗaure ku"
Da harara ya bisa har sai da ya ɓacewa ganin sa, daga ƙarshe ya sake faɗawa kan gadon ya dafe kansa wanda ke masa ciwo tunɗazu, Bilal ya ɗauki zancen nan wasan yara wanda shi a gare shi babban tashin hankali ne da ƙalubale, Safnah taga cewa bata cancance shi ba ita ma da Level ɗinta ke ƙasan na Xuhra ina ga ita Xuhra ɗin? Tsaki ya ja marar sauti sannan ya miƙe zaune ya ɗauki wayar sa ya bi duk en uwansa ya tura musu da saƙo but sai da ya jawa Siddeeq kunne akan kada a sanarwa Hajiya Sa'a su bar shi sai ya dawo da kan shi zai yi mata bayani.
🪐🪐🪐
Umar kuwa ya na fita ya je ya kira Hajiya Saratu wato mahaifiyar Xuhra suka zauna tiryan tiryan ya shaida ma ta duk abinda ake ciki. Hajiya Saratu tafi Hajiya Hindou sauƙin kai abinda kowa ya sani ne a family ɗin. Wannan yana daga cikin dalilin da yasa Baba ya zaɓi Xuhra domin yasan cewa ita da mahaifiyarta ba su da matsala, duk da cewa Aydah an yi mata engagement ko da ace ba'a yi mata matsayi ba bai isa ya ce zai aura mata Usman ba domin mahaifiyarta ba zata amince ba, shiyasa hatta Umar wanda ita ce ta haife shi ya fi bada go ahead akan Xuhra fiye da Aydah da ke zaman ƙanwar sa wadda suka fito ciki ɗaya.
Ajiyar zuciya hajiya Saratu ta sauke a hankali sannan ta kalli Yah Umar ta ce.
"Umar! Ba auren Usman ɗin ni ke ji ba, Xuhra ni ke tunani, Usman bai da matsala har cikin zuciya ta bana haufin aura masa 'ƴata amma kuma albasa ba tayi halin ruwa ba kai ka sani, al'amarin Xuhra na ɗaga min hankali"
Murmushi yayi sannan ya ce.
"Hajiya ka da ki damu in sha Allah lafiya ƙalau za ta zauna ba abinda zai faru, khairan in sha Allah"
"Tau yayi Umar, Allah yasa alheri yasa mijin ta ne har mutuwa"
"Amin amin Hajiya nagode sosai da fahimta,yanxu bari na je gunta na ga tana ta kirana tun ɗaxu"
"To shi kenan, bari nima na taso na je na kira en uwana na sanar musu abin da ake ciki"
Daga haka ya miƙe ya wuce can ɗakin da Xuhra ta ke ita kuma Mummy Saratu ta je ta ɗauki wayar ta ta fara kiran danginta tana shaida musu.
Umar na shiga ya tsaya bakin ƙofar ɗakin a hankali ya ce.
"Xuhra!"
Da gudu ta taso ta faɗa jikin sa tare da sake fashewa da kuka ta ce.
"Yah Umar!"
Bai hana ta kukan ta ba, sai da don kanta ta janye jikin ta ta kalle shi ido cike da hawaye ta ce.
"Yah Umar bana son sa! Wallahi ni bana ƙaunar sa, Miyasa Baba sai ni? Auren Usman is gonna ruined my life for ever.."
Jinjina kai yayi cikin taushin murya ya ce.
"I know......"
"Please Yah Umar bana son Baba ya ga kamar na yi disobeying na sa please kasan yanda zaka yi cikin hikima ka hana a yi min wannan AUREN dan Allah na roƙeka, Safnah ce fa ta guje shi da kanta ita da suka shafe shekaru kusan biyar a tare, kayi duk yanda zaka yi dan Allah Yah Umar ka taimake ni but kada ka bari yasan cewa ni ce bana so..."
OUM AMEER