Free chapter · Read without an account

14

by Rasheedat S Director · FEERYAL

🌺🌺 FEERYAL 🌺🌺

NA

RASHEEDAT S DIRECTOR

( Book 1)

~Free page~

Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta ***

____________________________________

🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼

🇦SSOCIATION🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***

domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan👇🏻

***

____________________________________

Bismillahirrahmanurrahim

🅿️14

Side d'in Daddy ta nufa ta kofar baya, dan tasan ta ainahin kofar kam cike yake tam da mutane.

ai ko hakan take har cikin babban parlour'n sa ba'i ne maza ciki a ciki.

D'akin kwanan sa direct ta wuce, tana shiga ta kirasa a waya.

ganin mai kiran nasa yasashi mike acikin jama'a ya nufi bedroom d'in sa, domin amsa kiran.

ya tura kofar yana kokarin kuma maida kiran dan ya yanke,

sai ganin ta ya yi tsaye cikin d'akin.

ido ya bud'e da kyau ya kura mata su, itako murmushi take sakar masa.

a hankali ya tako ya iso in da take.

hannu ta mika ta sakalo wuyan sa, tana cigaba da aika masa murmushi.

cikin sanyin muryar ta mai kara masa kaunar ta.

ta ce

"Daddy tun d'azu nake son ganin ka mutane sun min fin karfi."

ta karasa maganar da kashe masa ido.

wani numfashi ya sauke, sai kawai ya rungume ta ya na fad'in

"Godiya ya tabbata ga Ubangijin daya mallakamin wannan kyakkyawar tsuffar."

ya d'ago ya manna mata kiss a goshi.

d'an zame jikin ta tayi tana fad'in

"Daddy ka fara tsufa fa."

"Ina da ke ai ita ma tsufar bata isa ta dumfaro ni ba, sai dai ta tsaya a iya shekaru."

dariya ta yi ta ce

"Yau fa ka aurar da 'ya tsufa ya dad'a bayyana ga furfuran ka sun karu."

ta karashe maganar da muryar dariya.

kumatun ta yaja ya ce

"To kar ki bari tsufar tai mana tasiri, ki san yadda zakiyi ki yake sa tun kafin a fara kiran mijin ki da tsoho, shi ke nan ke ma kin tsufa."

dariya duk sukayi wa junan su.

Ya matsa can jikin bedside drower ya danna ma dannin bud'e sa, gilashin jiki ya zuge, yad'auko d'aya daga cikin makullan motocin da suke ciki.

ya zo ya mika mata.

ta karb'a tana bin key'n da ido sannan ta ce

"Na mene ne wannan?."

ya ce "Naki ne tukuicin wannan kwalliyar."

wani lallausar murmushi ta sake ta rungume shi tana fad'in

"Godiya marar adadi, naji dad'i dad'in da bazai fad'u ba."

murmushi ya bita dashi, yana matukar jin dad'i ya yi mata kyauta yaga tana nuna yabawa da jin dad'in kyautar da ya yi mata.

yana daga cikin abin da yake dad'a kara girman fadarta a cikin birnin zuciyarsa.

Bata jin kanta ita wata ce dan mahaifinta yana da dukiya, ko min kankancin kyauta takan nuna jin dad'in ta mara misaltuwa.

akasin sauran matansa da iyayensu ba koman komai ba sai fad'in ran tsiya.

Da sauri Miemie ta shige side d'in Aunty, ta haura sama da sauri tashige d'akin Feeryal.

tana zaune sunata wasa da kawayen ta, wan da ita take ganin su.

Miemie ta ce

"Feeryal taso muje ayi mana kwalliya ga mai kwalli tana kan yi wa su Ameerah, a side d'in Hajiya,

muje gurin walima ke bazaki je bane?."

"Ni bazan je ba Ammie na ta ce nazauna nayi wasa na a nan kije kawai abinki."

"Dan Allah taso muje gasu Umaima'n Dubai ma sun zo zo muje ki gansu."

ta janyo hannunta suka fita.

tun kafin su karasa sauka daga stairs hankalin 'yan cikin parlour'n ya dawo kansu.

wad'an da dama sunsan Feeryal d'in tun tana jaririya,

suna ta mamakin girman ta da yanayin tsarin zubin halittarta.

wad'an da kuma basu santa ba suna binta da kallon rashin sani, kallon itama daga cikin ba'in da suka zo daga kasashen turai suke mata.

Har sun zo shiga parlour'n Hajiya,

Feeryal tayi baya da sauri a matukar tsorace.

Miemie ta ce

"Hajiya bazata miki komai ba zo muje, kar a gamawa Ameerah a kama yi ma wani."

hannu Feeryal ta d'aga baki na rawa ta ce

"Ga mage can ni dai bazan je ba."

"Baya komai fa ki zo mu shiga."

"A'a ni bazan shiga ba!."

tayi maganar tana ja da baya a mugun tsorace, tamkar zata shid'e.

"Ke Miemie me kike yi a nan ana can anayi wa su Ameerah kwalliya ke kina nan, gashi har an watse an tafi gurin walima, kiyi maza kije a yi miki."

cewar Hajiya data fito zata gurin walimar tana gyara zaman mayafin ta.

ido ta gwalalo kan Feeryal dake ja da baya da baya.

"Me zan gani haka me ya kawo wannan aljanar nan?

ke Miemie kifita idona na rufe, ban rabaki da wancan yarinyar mai kamata faran mayu ba,

kin d'auko ta zaki kaita cikin jikoki na ta lashe su da maita ko ta shige jikinsu,

kar ki sake ki shiga min b'angare mayyar banza mayyar hofi ko na had'a ki da karnuka su yayyaga min namarki anan."

Ai da gudu Feeryal ta juya tayi waje.

Uwar amarya Mommy ta fito da ka kawayen ta zasu gurin walima, ta cab'a kwalliya cikin wani arnen lashi mai tsadar gaske tasha d'inkin manyan mata,

matan masu nera.

Umma Karima ita ma da nata kawayen kusan shiga iri d'aya sukayi da Mommy sai dai kalar leshin ta daban ne amma mai tsadar ce ita ma.

Motar Hajiya Luba ne ya kunno kansa cikin gidan.

bayan ta nunawa security pas d'in gayyatar ta,

suka bud'e mata get ta shigo.

Mommy suka tsaya suna zaman jiranta su karaso dan ta gane motar ta.

a babban parking lot d'in gidan in da motoci ke cike tam nagidan dana jama'ar da suka sami halarta bikin ke tare.

direban ta ya dai-dai parking.

Hajiya Luba suka fito ita da wata budurwar yarinya.

suka karasa in da su Mommy ke tsaye.

suka rungumi juna da Mommy,

Hajiya Luba ta saki Mommy tana fad'in

"Kaga uwar gida a gidan Alhaji Abubakar Fiya, Allah dai yasa bamu makara a walimar ba."

"Kun dai kusan makara dan har an fara, na ce gajiyar jiya ce ta hanaki isowa da wuri, to ya gajiyar jiyan."

"Wlh ke kam dai ingaya miki bawai gajiya bace ta zaunar da ni, d'iyarki ce gata nan Kuraiba ta b'ata min lokaci, kin san shirin 'yammata sai a hankali, a fenta nan a fenta can,

ke Kuraiba ga Mommyn ku nan ki gaida surukan ki."

Budurwar da aka kira da Kuraiba ta ce

Ina yini."

ta fad'a a takaice.

Mommy tayi murmushi tana amsawa da

"Lafiya lau Kuraiba ya school."

ta ce "Alhmdulillah."

"Kuraiba fa an girma nakai 1y rabon da na ganta,

har tafi Farida a tsaye."

cewar Mommy, tana dubanta da murmushi.

Hajiya Luba ta ce

"Ni da nayi zaton ma lokaci guda za'a had'a bikinsu a wuce gurin."

"A'a dai adai bi d'aya bayan d'aya, ayi shi daban-daban ai zaifi dad'i, surukar tawa ko ba laifi."

cewar Mommy tana duban Kuraiba.

"Da dai mun karasa kar a gama muna tsaye muna wata maganar muyi wacce take gaban mu, abar wannan da ba'a san yuwuwarsa ba tukun."

cewar Umma Karima da tun farin maganar ta had'e rai da alama dai akwai wata a kasa,d'ayan biyu ko bata son faruwan lamarin da suke magana a kai ko kuma akasin haka.

Hajiya Luba ta ce

"Ai Insha'allahu Kuraiba ita ce surukar Alhaji Abubakar Fiya na farko, mudai karasa wanda ake cikin yanzu dai kawai, kafin zuwan nasu lokacin."

FEERYAL data fito daga side d'in Hajiya da sauri, sukayi kicib'us da su zasu wuce.

Mommy ta bita da harara tana fad'in

"Ke kutumar uban ki bakya gani ne zaki bige mutane yarinyar banza kawai."

Umma Karima ta kai mata zunguri a goshi tana cewa

"Tsintacciyar mage bata mage wuce ki je in da aka gayyace ki."

"Wace ce wannan d'in?."

cewar Hajiya Kuba tana nuna ta.

tsaki Mommy taja ta ce

"Yarinyar da Hajiya Fatimah ta tsinto mana."

"Wai ita ce haka anya ba sato musu yarinyar mutane tayi ba a asibitin wata kasa ba kuwa?

bata shiga US after 2 mon before kawo yarinyar gidan nan ba."

Mommy ta ce

"Hm zata iya ai dan rashin haihuwa babu abun da bazai iya sata ba, an gama yawon gurin malamai niman maganin haihuwa an rasa ai dole ta b'ullo ta wata hanyar."

"Amma dai tayi asara, taraba yarinya da danginta dubi kyakkyawar yarinya fa dan Allah."

cewar sauran kawayen nasu.

Feeryal bakin get na side d'in Aunty ta tsaya har saida su Mommy suka wuce kafin ta dawo ta d'au hularta da ya fad'i lokacin da Umma Karima ta zungure ta.

Ta sunkuya ta d'au hularta tana mikewa, ta saki murmushi ganin wad'an da suke kusa da ita ta ce

"Laa Chuchu Chulu baku tafi ba da man?."

"Babu tafi ba muma mun tsaya jin wa'azin ne mu je gurin walimar dan anyi nisa da farawa kar a gama babu je ba."

"Ni dai bazan je ba, akwai su Mommy a gurin zasu kore ni ko su duke ne."

"Baza suyi miki ko mai ba zo muje, bazamu zauna ma a kusa da su ba."

yatsa ta saka a hab'arta ta ce

"Kun tabbata."

"Mun tabbata."

suka had'a baki wajen fad'a.

Suka sakata a tsakiya suna tafe a hankali suka nufi gurin da ake gudanar da walimar.

har suka dumfaro filin gadan-gadan babu wanda ya lura da su.

malamar da take gudanar da walimar ita ta fara lura da su.

zumbur ta mike tsaye tana fad'in

"Yaaaku jama'a ko shin kuna ganin abin da nake gani kuwa!?."

Gabakid'aya jama'ar gurin sukabi inda take nunawa da hannu.

nan da nan gurin ya kace da hayaniya had'e da kururuwan mata suna fad'in

"Wayyo ga zakuna zakuna sun shigo gida."

tuni mata suka fara hargitsewa suna niman mafaka domin ceton rayuwar su.

zo kaga mata in da suke zubewa kan kujeru suna karya kujeru.

Mommy da aka tureta a kan kujera ta zube kasa shirim, ta kasa ko da iya motsawa tsabar tsoro tana baje a kasa jikinta na rawa.

idanunta a kan Feeryal da manya-manyan zakunan da suka sakata a tsakiya.

suna cigaba da dumfaro gurin gadan-gadan.

Hajiya kuwa da rarrafe take tafiya ta tafi bayan wasu kujeru can ta b'oye, ta rufe idanunta gam-gam.

tana karanto addu'ar ta da ta saba

"Wasayyahu wasayyahu wasayyahuuuuu yasin me manjaga li'eelafi kafa bakwai yasin kafa dubu lakadija'akum kafa d'ari ba d'aya."

Mata sai karo da juna ake ana zubewa kasa, sai ihu da niman agaji.

Ganin haka yasa Feeryal taja ta tsaya.

tana bin jama'ar da kallo.

tsoro taji ganin idon Mommy a kanta sai ta juya da sauri ta gudu, tana gudun kada Mommy'n ta taso ta bige ta, dan a zaton ta, zuwan gurin su da tayi ne yasa ran Mommy b'aci, kuma ta rigada ta san cewa ta hanata zuwa in da suke.

Side d'in su ta koma ta haye upstair tana hango yadda mata ke gudu suna fad'uwa suna karya kujeru.

Dariya ta tuntsure da shi hango wata katuwar mata ta zube kasa timm , mata sai zubewa a kanta suke sai ihu take kurmawa takasa tashi.

tana ta juya katon d'uwawu a kasa.

"Ke Feeryal."

da sauri ta juyo jin maganar Aunty a bayanta.

Aunty ta ruko kunnen ta ta ce

"Ke ce ko, ke ce kika sa duk wancan ko?."

kai ta girgiza tana kunshe dariya ta ce

"Auchii Ammie zafi."

"Me yasa kika yi haka Feeryal su d'in sa'annin ki ne, ko abokan wasanki."

d'an karamin bakinta ta cuno

"Ba ni bace fa Ammie babu ruwana Chuchu da Chulu ne, suke razanin su."

fuska Aunty ta had'e ta ce

"To ki ce dasu su daina su saida abinda sukeyi haka, ya isa!."

Duk da tazaran da ke sakanin su wan da ko ihu mai tsananin karfi tayi daga in da take zuwa gurin walimar nan baza'a jitaba,

amma sai gashi ta kira sunan su sun waigo, ta ce

"Ammie na ta ce ku dai na razanin su."

aiko nan take suka juya su na girgiza gashin jikin su, da suka rikid'a suka koma manyan zakuna masu matukar ban tsoro.

suka fice a filin taron.

Sai a lokacin hankalin security yakai kan jama'ar da ke ta ihu,

suka shigo ciki da sauri.

mutane kuwa ganin juyawar zakunan nan yasa wad'anda suka fad'i mikewa tsaye suna kuma niman mafaka.

Ganin security yasa wasu dawowa cikin hayyacin su.

Hajiya ta fito daga mab'oyar ta tana ciccire ido da fad'in

"Kun harbe su kun kashe su ko ya?."

security suka ce

"Su wa suka shigo Hajiya?

babu wanda suka shigo kai tsaye batare da shaidar izinin shiga gidan nan ba."

Hajiya ta ce

"Injiwa ai wad'annan basa bukatar niman izini,

ko ku suka samu loma d'aya zasuyi da ku a bakin get babu wanda ya sani,

ku bisu ku harbe su in baku kashe su ba karsu kuma dawo mana nan, zakuna ne suka b'allo suka shigo mana gida."

Sai a lokacin Mommy da ta sha tumurmusan mutane ta mike da kyar tana kad'e jikinta.

sai matse ido take kafa tayi tsami.

Umma Karima kuwa bakin nan mud'uss ya mutu itama ansha birgima gaye ya b'aci.

Farida amarya ma ta tumurmusu ba kad'an ba ita da kawayen ta.

Su dai jami'an tsaron basuga wani bakon halittar daya shigo gidan ba bayan duk jinsin mutane ne babu na dabbobi.

kofar baya ma a kulle take ko mutum bazai iya bud'e shi ba bare kuma dabba, in ta sama ne ma bazasu iya hayewa su shigo ba, babu wata hanyar da zasu iya shigowa sai dai in ta ainihin kofar gidan.

suka juya da sauri suka soma bincikar gidan rike da bindigogin su, lungu da sako.

amma babu wani halittar da suka gani face mutane wad'an da suka ziyarci bikin.

Haka nan taron walima ya watse, da yawan mutane kuwa kowa ya kama gabansa.

Da karfe 6 na yamma 'yan d'aukar amarya suka zo, aka d'auki amarya a kaita tsarenren gidan ta na gani na fad'a.

Sai da aka nutsu aka fara maida zance.

uwar amarya Mommy kam ana zaune ana jinyar kafa dan ko kafa tayi tsami.

Hajiya'n Dubai da ita bata je gurin walimar ba tana sashin Hajiya lokacin da abin ya faru, ta ce

"Wai kuma kun ganta da idon ku tazo da zaki, a ina ta sami zaki? kai gaskiya da sake wannan 'yar ban yarda da ita ba."

Hajiya ta ce

"Wlh idona idon ta da jibga-jibgan zakuna,

'yar nan ta girma a maitanci duk jinin mu taso sha kurwar mu ya mata d'aci, shiyasa ta kyale mu,

ku kira min Abubakar yau za'ayi ta ta kare,

ke Bishira kirawo min matar tasa itama 'yar gol d'in tasa ba, da mayayyar yarinyar duk suzo nan."

Batare da b'ata lokaci ba Daddy ya amsa kiran da Hajiya ta masa.

Daddy na shiga Aunty da Feeryal suka shigo.

da kaga Aunty jikinta a matukar sanyaye yake,

dan tasan irin wannan kiran Hajiya'r ba alkhairi ba ne.

tun kafin su zauna

Hajiya ta dira a kan Daddy masifa take kamar zata ari baki,

"Abubakar yau sai ka zab'a ko ni ko mayyar yarinyar can, wlh yau bana kuma kwana gidan ka,

ka nuna min iyakata ka gwada min mata ta fini."

Hajiya ta kawo kuka ta saka tana fad'in

"Fatimah zaki raba ni da d'ana, Abubakar nagama d'awainiya da kai ka nuna min mata ta fini,

to ka zauna kai da matarka, kuyi shaida idan na taka kafata na bar gidan nan nabarka har abada ke nan, kada ka kuma min kallon uwa a gare ka,

ka rike mata ta zamo uwarka da ubanka, kai har ma da danginka,

dan babu wani wan da zai kuma zuwa gidan ka ba kana da kud'i ba,

su sayo maka dan gi da iyaye tun da gashi nan ai ka siyo mata da shi."

Hajiya ta mike tana sharb'e hawaye.

da sauri Daddy ya rike kafafun ta

"Hajiya dan Allah kiyi hakuri ki yafe ni,

Feeryal zata bar gidan nan yanzu -yanzu ba sai anjima ba."

"Kyale ni na tafi, tsawon sheka nawa tayi a gidan nan kullum haka kake fad'a,

tun da kazab'e su a kaina babu ruwanka da ni rabu da ni nayi tafiya ta,

ke kuma Fatimah ki zuba ruwa a kasa ki sha yau zan bar muku gidan,

ki cigaba da maida Abubakar d'anki dama baki da shi, ita rashin haihuwa ai ba hauka bace da zaki je ki jijjib'o mana annoba ki kawo mana gida,

tun da ke juya ce bazaki haihu ba sai aka ce kije kirika kalen 'ya'yan mayu dana aljanu, kice dole sai sun zamu naki,

shifa haihuwa wanda kayi nakudar sa da kanka ka ji zafin haifosa duniya shine naka,

d'an wani bazai tab'a zamowa naka ba."

Aunty ta rumtse idanunta tana jin matsananciyar zafi cikin zuciyarta.

tun da take a gidan bata tab'a jin zafin gorin haihuwa irin wanda Hajiya ta mata yanzu ba,

duk da ba yau ne karo na farko, da ta fara yi mata gori akan haihuwa ba,

amma sai taji zafin na yau yafiye mata na kullum.

ko su

Mommy da Umma Karima dasunsha yi mata gori a kan haihuwa, amma bata tab'a jin zafin nasu kamar irin na Hajiya na yau ba,

dan tasan nasu bakin kishi had'e da jahilci ne ke sasu yin sa.

Ta had'iye wani miyau mai d'aci kana ta ce

"Kiyi hakuri Hajiya bana fatan ace ta sanadiyya ta uwa ta rabu da d'an ta,

idan hakan ta kasance kuwa bazan tab'a yafewa kaina ba."

ta mike tsaye ta kamo hannun Feeryal ta na fad'in

"Bazaki bar gidan nan ba Hajiya sai dai ita ta barshi."

Ta janyo Feeryal sukayi waje.

Suna shiga side d'in ta bedroom d'in Feeryal ta shige rike da ita.

ta saki hannunta da sauri taje ta d'au katon akwati ta bud'e wardrobe tashiga kwashe kayanta ta na zubawa cikin akwatin da sauri-sauri.

Feeryal da hawaye ya cika idon ta tana duban Aunty.

Aunty ta kawar da kanta gefe tana maida hawayen da ke shirin zubo mata.

akwatin nacikawa ta rufe, bawai dan kayan cikin wardrobe d'in sun kare ba.

Ta janyo akwatin zuwa bedroom d'inta.

Feeryal ta biyo ta.

kayan Feeryal dake cikin d'akin nata ta d'au babban akwati shima ta cika shi,

ta rufe tana sauke ajiyar zuciya dan tuni ta kece da kukan zuci.

"Ammie ina zamuje tafiya zamuyi?."

ta waigo tana duban Feeryal da kyar tayi karfin halin cewa

"Ke zaki tafi Feeryal, dole zakiyi nesa da gidan nan, domin samun farincikin masu gidan, ki tafi kiyi nesa da nan."

Kuka ta fashe da shi ta taho da gudu ta rungume Aunty, tana wani irin kuka cikin muryar kuka sosai take fad'in

"Ni dai bazan tafi ba Ammie kice Hajiya tayi hakuri bani so natafi na barki sai dai mu tafi tare."

hawayen da Aunty take ta dannewa ne suka zubo, ta rungume ta tsam tana wani irin gunjin kuka.

"Feeryal bazan iya rabuwa da ke ba, abin da suka kasa ganewa ke d'in tamkar jinina na ce,

ji nake kamar ni ce nayi nakudar ki,

bazan iya rabuwa da ke ba d'iya ta."

Jin karar bud'e kofa ya sanya Aunty duban kofar,

Daddy ne ya shigo yana dubansu cikin matukar tausayawa.

tabbas yasan abune mai matukar wuya rabuwar Aunty da Feeryal, yasan so da kauna da shakuwar da ke sakanin su irin na uwa da d'anta ne.

shi kansa rabuwa da yarinyar tamkar rabuwa ne da d'iyar daya haifa.

a hankali yataka zuwa inda suke ya dube su cikin raunin murya ya ce..........!

Mommyn Twins ce

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol