Free chapter · Read without an account

1

by Azizat Hamza · CHEF ZEEY (Love in the Kitchen)

CHEF ZEEY
*Love In The Kitchen*

Topnotch season 4
©AzizatHamza2025
ArewaBooks @Azizat Hamza

                       ZEEY

Sunana ZIYADA SADIQ HARUNA a.k.a CHEF ZEEY. Ofcourse na je culinary school, dan haka, I am a certified Chef. Certificate ɗina ma yana cikin folder a ƙasan gadon Kaka.
A hankali nake duba littafin da ke gabana, a lissafin dana gama yi kuɗin buɗe restaurant ɗina saura Naira Miliyan huɗu da dubu ɗari takwas da saba'in (#4,870,000) kacal.
Kenan na tara Naira dubu ɗari da talatin (#130,000) a cikin Miliyan biyar da nake nema. Classy Restaurant da za a riƙa siyar da abincin gargajiya zalla a garin Zaria na ke son buɗewa, at least daga yanzu zuwa ƙarshen shekarar nan na ke fatan haɗa kuɗin. Wannan shine babban burina.

Watanni shida da suka wuce account ɗina na Instagram ya tafi viral, wannan ya sa na fara samun 'yan chanji daga tallace-tallace da nake yiwa ƙananun 'yan kasuwa irin masu siyar da spices da kayan kitchen haka.
Duk wanda ya ga numbers ɗin social media accounts ɗina zai ɗauka na fara samun wasu maƙudan kuɗaɗe, irin na BLOW ɗinnan. Amma gaskiyar shine, ZIYADA SADIQ HARUNA a.k.a CHEF ZEEY bata blow ba. Followers ɗina dai sun ƙaru, amma kuɗin fa sai a hankali, musamman saboda masu kawo tallace-tallacen sun mugun rena ni. Dan kawai sun ga abincin gargajiya kaɗai na ke yi, kuma bani da fancy kitchen irin na manyan Food bloggers da suka yi fice sai suke ganin ko nawa suka bani kawai in karɓa in yi godiya.

Ba laifinsu bane, Instagram gidan aesthetic ne, gidan kwalliya, gidan gayu, gidan ƙarya, so babu wanda zai ɗauki maƙudan kuɗi ya bawa wata ƙaramar Chef da ke girki da murhun itace ta yi mata tallen kayanta. Sun fi son masu fancy kitchen. Chef Zeey bata da fancy kitchen. Ni da nake zaune da 'yar tsohuwata muna fama da kanmu ina na ga ta fancy kitchen. Amma Alhamdulillahi, ɗan abinda na ke samu yana rufa mana asiri, ba ga ni kaɗai ba, har da mutanen gidanmu.

"Adda Ziya, wai inji Mamana wai ki bata aron dubu ɗaya idan kina da shi"

A fusace na ɗaga idanuna na kalli yarinyar da ta shigo min ɗaki hanci duk majina tana sanye da wani babban zani babu ko riga a jikinta.

"Yanzu dan iskanci Atika kike ko waye..."

"Assima'u..." ta gyara min tana wani zazzare idanu.  Hannuna na kai na kwaɗa mata biron da nake rubutu da shi

"Ban hanaku shigo mana ɗaki babu sallama ba. Ana koya muku tarbiyan da zai gyara muku rayuwa amma sai shegen taurin kai"
Yarinyar ta wani  zuba mini idanu ko a jikinta.

"Koma ki je ki yi sallama!" Na daka mata tsawa. "Jibeta fiska duk majina, za a tashi da safe iyayenku ko fiska ba za su wanke muku ba"

"Salaama Aleekumm" ta faɗa da ƙarfi sannan ta shigo ɗakin

"Bakinki ne Salama Alekum ɗin ai. Wai waya aikoki nema? Eh?"

"Mamana"

Na kalli yarinyar da kyau ko zan gane daga wani balbali ta fito. Yaran da ke gidanmu sun yi yawan da ba iya ganesu nake ba, musamman ma ƙananan.

"Mamanki ita ce, Amaryar Baffa Zakari?"

Sai da ta ja hancinta ina ganin green ɗin majina da ya maƙale mata a ƙofar hancin ya koma sannan ta ce "eh"

"Zo zo zo ki wuce ni bana son ƙazanta" na jawo purse ɗina na cire gudan dubu ɗaya na miƙa mata. Na san idan dubu ɗayan nan ta fita ta fita kenan. Kaf matan gidan wacce ta ke da ɗan ƙoƙarin biyan bashi idan ta karɓi aron kuɗi a wajena Anty Hafsah ce,  amma duk sauran idan zan fara lissafin ɗari biyu yau, ɗari biyar gobe, dubu ɗaya jibi da suke karɓa aro ba sa biya, ina ga sai ya cika littafi.

A yanzu haka a FaceBook page ɗina ina da followers dubu saba'in (70k followers) FaceBook shi nafi samun followers saboda a nan na fara food content ɗina. Sai kuma Instagram da nake da followers dubu talatin da takwas (38k Followers). Kar ku sha mamaki idan na ce muku a cikin wata shida na tara followers dubu talatin ɗinnan. Na yi shekara biyu ina posting a Instagram, ina samun followers kaɗan-kaɗan da ƙyar na haɗa 8k followers. Then, Boom!, wani video dana posting ni da Kaka muna yin kwaɗon rama da zogale sai ya tafi viral. Ban san mutane na son abincin gargajiya ba sai a wannan videon. Shikenan Instagram ɗina daga 8k followers sai ga shi wai video guda ɗaya tak ya kawo min mutane dubu talatin, har yau ina mamakin abin nan.

Shi kuma YouTube na buɗe shi last year ne lokacin dana lura duk manyan food bloggers dana ke bibiya sun koma can kuma kowa na faɗin YouTube suna bada kuɗi sosai. Kai! YouTube ya bani wahala, sai na ɗaura video ya yi wata ban samu 1k views ba. A haka dai na yita gurgurawa har na samu 2k subscribers a shekarar amma kuma ban zama monetized ba saboda haka bana samun kuɗi. A YouTube dai videon dana yi na Alalen gwangwani shi ya jawo na samu 6k subscribers a wata shida, ya zamana ina da 8k subscribers kenan kuma na shiga YouTube Partner program amma har yanzu saboda bana samun views ban samu adadin kuɗin da za su fara biyana ba.

TikTok kuma gidan rikici ne, har kirana suke da 'yar Talakawa a comment section, ko su kirani da 'yar gargajiya. A can followers ɗina yanzu haka sun kai 52k followers. Tare na buɗe da YouTube amma shi gudu yake kamar me. Ya ma fi Instagram saurin samun followers. Amma taron yu-yu-yu ne a can, dan  wani lokaci har rufe comment nake saboda jarrabarsu. A TikTok har hashtag ɗin #ChefɗinTalakawa aka bani, da ka saka Chef ɗin Talakawa a TikTok videos ɗina zaka fara gani. Ban damu ba, dan ni ɗin Talaka ce, ni ɗin marainiya ce dana taso a hannun Kakata...

*
Ina cikin buga lissafi Kaka ta kwala min kira daga tsakar gida

"Ziyadatu, ba za ki fito ki wuce makaranta ba?"

"Kaks, Ina zuwa" na faɗa ina rufe littafin dana ke lissafin kuɗi a ciki. Can ƙasan akwati na saka saboda 'yan gulma da ɓarayin cikin gida. Idan kana zama a babban gida komai za ka yi sai kana taka-tsantsan. Idan aka san ina tara kuɗin restaurant ai labarina sai ya shiga kowani balbali a gidan nan, sannan masu karɓan aron kuɗi duk za su bi baya su zo su karɓe ɗan abin dana tara. Dama tunda aka ga na fara samun alkhairi a social media shikenan kowa ya saka mini ido.

Black handbag ɗina da ke rataye jikin ƙusar da ke kusa da window na ɗauko sannan na ciro handouts ɗina a ƙarƙashin pillow na sa a jakar. Jiya ina cikin karatu na yi bacci. Allah na gani ba zan iya tuno komai cikin abinda na karanta ba, komai ya gudu. Ƙarfe goma muke da test ɗin so na san dai ko a cikin Keke ne kafin na isa school zan ɗan yi bitar wasu abubuwan. Tunda na samu carryover biyu a shekarar farko na yi alƙawarin ba zan sake wasa da karatuna ba.

Jarrabawar soyayyar dana faɗa a lokacin ya sa na samu Carryover biyu a Level One, ban ma ɗauka zan cigaba da karatun ba saboda yadda na lalace a lokacin. Amma dana farfaɗo daga ciwon so sai na yiwa kaina karatun ta nitsu, babu ni babu soyayya har sai na cimma burina. Babban burina a rayuwa a yanzu shine: 1- na gyara shashin Kaka. 2- na buɗe restaurant. 3- na kammala Degree lafiya.

Sai dai at this point komai ma is proving to be difficult. Karatuna na shirin ƙwace mini, kuɗin restaurant ya ƙi haɗuwa, gyaran gida kuma... na gyara mana banɗaki daga pit zuwa water system, at least na ɗan yi wani abu ai...

Lokacin dana fito daga ɗaki sai na tarar Kaka tana tankaɗe garin Masara a tsakar gida.

"Kaks, Tuwo za ki mana ne yau?"

"Garin da Ladidi ta aiko tun kwanaki ne na ce barin yi tuwo da shi kar ya lalace"

"Kaks, lallai a gaishe ki, kusan wata huɗu fa kenan da Umma ta aiko miki garin nan"

"Lah! na manta inda na ajiye ne. Sai jiya da yamma na gani a cikin jan Fantekan da ke ƙasan gado"

Wani tsumma da ke saman igiyar shanya na jawo na ɗisa ruwa daga butan Kaka da ke bakin ƙofar ɗaki na fara goge baƙin flat shoe dana saka dan ya yi ƙura sosai.
Ina gama gogewa na yar da tsumman dan sai wani maiƙo-maiƙon datti ya ke min a hannu, ko uban me ma aka gobe da shi sai Allah. Na wanke hannuna da sauran ruwan da ke butan na yiwa Kaka sallama.

"Kaks na tafi" na faɗa ina ɗaga mata hannu.

"A dawo lafiya, Allah ya bada nasara ya kuma kaɗe fitina"

"Amin, Kaka" na amsa ina ficewa daga sashenmu...

***

JAY-KAY

A hankali ya ke saukowa daga matakalar da zai sadaka da babban falo. Meeting ya ke da shi da wasu investors ƙarfe tara na safe.

Hajiyarsu ce a falon ita kaɗai tana shan green tea.

"An fito" ta faɗa lokacin da ya gaisheta

"Yes"

Zama ya yi a kujera yana saka agogo yace "Ina Janan?"

"Ai ina ga bata tashi ba" Hajiya ta faɗa tana kurɓan tea ɗinta.

"Bata tashi ba?" ya duba agogon hannunsa, ƙarfe takwas ne na safe har da minti bakwai

"Kaima ka san halinta ai" Hajiya ta faɗa tana ajiye mug akan saucer.

Miƙewa yai zai tafi ta kira shi "Jamal"
Tsayawa yai cak ya kasa motsi yayinda ƙirjinsa ya fara cunkushewa yana masa wani suka.

"Afuwan! Jalal, maganar Plaza ɗinnan ne, na ce har yanzu ba a yi komai akai ba"

Sai da ya ɗau kusan sakan talatin yana ƙoƙarin saita nitsuwarsa kafin ya juyo ya kalleta ya ce "idan na dawo za mu yi maganar, ban manta da Plazar ba"

Hajiya ta sake ɗaukan mug ɗin da ta ajiye ta ce "to sai ka dawo ɗin"

Wucewa ya yi ba tareda ya sake cewa komai ba. Yana fita ya shiga mota Direba ya ja mota suka bar cikin gidan. Sai da suka yi nisa da gidan sannan ya saka hannunsa a ƙirji yana furzar da iska. A duk lokacin da Hajiya ta yi suɓutan baki ta kira shi da Jamal sai hakan ya tuno masa da wannan mummunan rana da komai na rayuwarsa ya chanja. Shekaru uku kenan amma kullum ya tuna da wannan mummunan rana sai zafin abun ya dawo masa sabo.

Duk sadda Hajiya ta kira shi da Jamal ji ya ke yi kamar gazawarsa ya sa ta ke auna shi da sunan ɗan'uwansa. Wataƙila hakan shi ya ke sanyaya mata zuciya.
Wataƙila idan ta kira shi da Jamal zai rikiɗa ya koma Jamal ɗin na gaskiya.

He was never her favourite.

Jamal shine perfect son. Ɗan Albarka. Wanda kowa ya ke alfahari da shi a family.

Ba zai taɓa mantawa da abinda ta faɗa masa ba ranan da ya ce mata zai auri Cassy.

"Jamal ba zai taɓa kawo min suruka wacce bata Sallah ba"  abinda ta faɗa kenan, and it breaks him.

Lokacin da aka saka bikin Jamal ta fi kowa farin ciki. As if a lokacin ne ɗanta zai fara aure.  She was all over the place tana ta shirye-shirye, yau Dubai, gobe India, jibi China, tana ta siyayyan biki.

Lokacin aurensa da Cassandra saboda ma kar a yi auren tana kusa barin London ta yi ta wuce Nigeria. Jamal da Daddy ne suka zo kotun da aka ɗaura aurensu.

Bayan auren Hajiya bata sake saka baki a maganar auren ba sai lokacin da Cassy ta haihu da ta zo ganin yaro. A lokacin ne ta maimaita masa abinda ta faɗa ranan da ya zo mata da maganan Cassy.

"Kai da baka zama ka san dai kwacokam tarbiyyansa yana hannun uwarsa ko" ta ƙare da faɗin "Allah ya bashi  hasken musulunci" tsabar sanyin jiki bai iya amsa addu'ar ba. Jamal ne ya amsa yana yiwa yaron wasa yana faɗin "Hajiya kar ki damu, Ni da hannuna zan riƙa tafiya da yaron nan Masallaci" yai maganar yana dariya.

Jamal kenan, Sarkin dariya. Har yanzu yana iya tuno sautin dariyar Jamal na ƙarshe a duniya.

"Yallaɓai mun iso" Direbansa ya faɗa ganin Ogan nasa bai fito daga motar ba minti biyu bayan ya yi parking a parking space na Kamfanin.

"Thank you, Abdullahi" Jalal ya faɗa bayan ya farfaɗo daga duniyar tunani da ya tafi.

Yana shiga Kamfanin mutane suka fara gaishe shi yana ɗaga musu hannu har ya shiga elevator ya wuce 7th Floor inda office ɗinsa ya ke.

Yana zuwa Sakatariyarsa ta gaishe shi ta ce masa baƙin da za su zo sun iso. Karɓan file ɗin hannunta ya yi ya shige cikin office ɗinsa.

Ƙaton Hoton da ya yi tozali da shi a office ɗinne ya sake tuno masa da rashin dacewarsa da wannan office ɗin. Kowa ya sani ba shi ya dace ya mallaki wannan office ɗin ba. Mamallakin Office ɗin Jamal ne. Shi yasa ya kasa cire hoton tun shekaru biyu da ya amshi ragamar tafiyar da kamfanin. Ji ya ke kamar idan ya cire hoton Jamal zai gani.  Sannan Hajiya ba za ta ji daɗi ba. Shi ya sa ya kasa cirewa. Amma a kullum ya shigo office ɗin ya kalli hoton sai gabansa ya yi ras!

Zama ya yi a kujera ya gyara tie ɗinsa sannan ya buɗe file ɗin da Sakatariyarsa ta bashi dan ya duba takardun kafin ya wuce ɗakin da zai gana da baƙi.
Haka ya gama duba takardun har ya kai wajen da aka rubuta sunansa JALAL KABEER MAIYAƘI.
A baya sunan Jamal ne a wajen ba nasa ba. A baya Jamal ne zai yi signing a wajen ba shi ba.

"JayKay" aka kira shi.
Ya ɗago idanunsa ya kalli ƙofar. Mr Munir ne abokin Jamal kuma CFO na kamfanin.

"Time" ya faɗa yana nuna masa agogon hannunsa.

"Oh, yes" yai saurin saka biro a wajen sunansa ya yi signing. Sannan ya miƙe hannunsa riƙe da file ɗin ya bi bayan Mr Munir suka fita.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol