Free chapter · Read without an account

2

by Azizat Hamza · CHEF ZEEY (Love in the Kitchen)

CHEF ZEEY
*Love In The Kitchen*

Topnotch season 4
©AzizatHamza2025
ArewaBooks @Azizat Hamza

                       ZEEY

2

Ina jin Lecturer ɗinmu yana cewa kowa ya dena rubutu na ja wata siririyar tsaki a zuciyata. Haba Jama'a! Ta ya mutum zai iya amsa Questions uku masu 'ya'ya a minti shabiyar. Shima dai wannan Malamin ba so ya ke mu ci course ɗinsa ba. Allah na gani Question ɗaya na amsa da ƙyar. Kwata-kwata ba inda na karanta mutumin nan ya fitar ba.

"Zeey, me kika rubuta? Ni fa babu abinda na sani, Ban rubuta komai ba" Bestie na Faty ta faɗa gaba ɗaya ta rikice. Course ɗin da muka gama rubuta test ɗinsa 3 credit unit ne, kuma mutumin ba shi da mutunci.

"Nima an gaya miki na rubuta wani abun kirki ne. Ke dai kawai Allah ya taimakemu ya bamu Assignment mu ɗan samu wani abu a nan in ba haka ba CA ɗin Dr Farouq zero za mu samu"

"Ni kinga gaba ɗaya wannan bikin da aka yanka mini ya bi ya hana ni karatu.  Sai da na cewa Baby ya bar bikin nan sai na gama Makaranta"

"Tabɗi! Abeg! Gara da aka sa mana shi nan kusa, kinga next year idan za mu yi graduation kina nan da cute Baby girl ko Baby boy" Faty ta kai min duka na sa mata dariya.

Fatima Jibril, ita ce Bestie na a gaba ɗaya duniya nan. Idan aka ce in kira sunan ƙawa guda ɗaya da zan so mu yi ƙawance har tsufa, to Faty zan fara kira. Faty mutum ce, Faty na da mutunci overrrr. Ba a iya shaidar mutum 100% saboda ɗan Adam ajizi ne, but gaskiya zan bawa Faty 99.9% cewa mutuniyar kirki ce.
Za ku ɗauka mun jima tare da ita but a wajen registration muka haɗu lokacin muna Level One. Right from day one muka clicking and tun daga lokacin Faty ta zame mun ƙawar arziƙi. Ko lokacin da matsalar soyayya ta sakani a gaba Faty was there for me. Lokacin da abubuwa suka mana zafi ni da Kaka Faty ta bani taimakon da ba zan taɓa iya biyanta ba. Lokacin dana fara ɗan posting video a FaceBook sama-sama haka, Faty ce ta bani ƙarfin gwiwa ta ce na cigaba watarana page ɗina zai yi girma har na fara samun kuɗi. Ita ta sa na fara posting a Instagram saboda ni lokacin ina ma na samu kuɗin datar da zan shiga IG. Faty za ta mini sub ɗin data ta ce Zeey ki dinga Posting a Instagram ɗinnan watarana za ki blow. Faty ce ta bani shawarar na je culinary school a Kaduna na koyi girki Professionally.
Kada kuce na cika ku da labarin Faty, gaskiyar shine, without Faty wataƙila da babu Chef Zeey.

Ƙarfe uku muka baro cikin school. Kasuwa muka wuce saboda Faty ta ce za ta duba wasu kaya. Bikinta saura sati shida yanzu. Mun jima a kasuwa. Bamu muka dawo ba sai ana kiran Magariba. Na riga na kira Kaka na faɗa mata ina gidan su Faty dan haka bani da matsala.

Ba wani kayan arziƙi muka siya ba duk yawace-yawacen da muka sha a cikin kasuwa. Sai da muka ci abincin dare kafin ta rakani har titi na hau Keke na taho gida.

Ina zuwa ƙofar gidanmu na samu su Baffa Lawalli da Baffa Zakari da wasu maƙotanmu akan tabarma suna cin tuwo.  Na haɗe fiska zan shige ba tareda na gaishe su ba Baffa Lawalli ya kira sunana. Na waske na ɗan risina na gaishe su.

"Daga ina haka?"

"Gidan su ƙawata Faty, na rakata kasuwa ne siyayyan biki"

"To a kula, banda yawon dare"

Har na shiga zaure ban dena jin haushin maganarsa ba, wai "banda yawon dare". Ƙarfe takwas ne fa yanzun. Kumama in ba neman magana ba ai ya san su waye masu yawon dare a gidan. 'Ya'yansa ne ba na kowa ba.

A ƙofar ɗaki na tarar da Kaka tana zaune akan tabarma ta kunna radio tana ji. Wasu jikokinta kusan su biyar suna gefe ta zuba musu tuwo a tray suna ci. Kullum abin kenan. Babu mai bawa Kaka naira biyar a gidan nan, amma da zaran ta yi girku sai su sako zugan 'ya'yansu su zo su cinye mata abinci.

"Kin dawo?"

"Kaks, Na dawo" na faɗa ina rataye gyalena a kan igiyar shanya. Wata ƙaramar kujerar katako na jawo na zauna na ce "Kaks, kin ci abinci kuwa?"

"Dama na ce in jiraki ko za ki ci tuwon idan kin dawo mu ci tare"

"Kai Kaka! Kin san dai dole zan ci abinci a gidansu Faty"

"Garin na da kyau kuwa, Tuwon yayi danƙo sosai, barin zubo mana kema ki taɓa"

"Ki zubo to, amma kaɗan zan ci"

"Kaka Altine a ƙara mana miya" wata daga cikin yaran da suke cin abinci ta faɗa tana turo tray ɗin gaban Kaka da ta tashi za ta zubo mana tuwo.

"Wallahi sai kun cinye gayan tuwon nan tas! Babu miyan da za a zuba muku. Oya ɗauki tuwon nan ki ajiye muku ku cinye" na daka mata tsawa

"Adda Ziiyaa, dan Allahhhh"

"Barin saka musu kaɗan"

"Kaks ba za a ƙara musu komai ba. Nan gaba za su koyi yadda ake managing miya, ko kuma suje balbalin iyayensu a basu miyar a can"

Wayata ce ta fara ringing a jaka na ciro sai na ga sunan Alhaji Nafi'u. Na ja tsaki ina mayar da wayar jakata.

Lokacin da Kaka ta zubo mana tuwo na wanke hannuna na fara ci. As usual tuwon ya yi daɗi. Girkin Altine mai tuwo ne fa. Kakata ta kaina.

Altine mai Tuwo ake kiranta, sama da shekara hamsin tana sana'ar sai da Tuwo. Tun kan ta yi aure ta ke taya mahaifiyarta sana'ar sai da Tuwo a Kano. Da ta yi aure a nan Zaria kuma, tun tana Amarya da ta fara sana'ar bata dena ba har sai da iftila'in jinya da tsufa ya hanata. Da sana'ar Tuwo ta gina kanta, da shi ta aurar da 'ya'yanta, da shi ta siyawa kanta daraja a wajen kishiyarta. Na ta so na ga Kaka tana siyar da Tuwo dan haka da kuɗin Tuwo Kaka ta reneni ta sakani a Makaranta.

So, idan na ce muku tuwon Kaka daɗinsa daban ne, to ku yarda kawai.

Ni dana ce kaɗan zan ci tuwon, sai ga shi da ni aka cinye shi tas. Dana gama ci na tattare wajen sai na je na ɗaura ruwan wanka a 3kg gas dana siya mana kwanaki. Da ruwan ya ɗan yi lum-lum sai na juye na kai banɗaki na yi wanka.

Lokacin dana fito daga wanka sai Kaka ta ce min wai Baffa Lawalli yana nemana. Tsaki na ja dan na san maganar ba zai wuce aron kuɗi ba.
Kayan baccina riga da gajeren wando na saka sannan na ɗau ƙaton hijabi na sa a kai sannan na wuce ɓangarensu.

Mutum shi ba wata sana'ar kirki ba ya je ya zauna ya tara mata uku shi kaɗai, ga yara kullum haihuwarsu ake.
Allah dai kawai ya shirya.

Ɗakinsa na shiga bayan na gaishe da Uwargidansa Maman Suwaiba da ta ke tatar kamu a ƙofar ɗakinta, wajen duk ya yi caɓal-caɓal da ruwa babu kyan gani.

"Baba, Barka da dare" na gaishe shi bayan na tsugunna.

"Barka da dare Ziyadatu, ya Makaranta?"

"Lafiya, Baba"

"Kin kusa gamawa ko?"

"Eh, daga mun gama wannan semestern za mu shiga ajin ƙarshe"

"Allah ya taimaka"
Na amsa da Amin.

"Ɗan ƙara mini gudun fankan nan"
Ina tashi zan je na ƙara gudun fankar Nepa 'yan tsiya suka ɗauke wuta.

" 'yan iska, Yaushe ma suka kawo wutan har sun ɗauke" Baffa Lawalli ya faɗa da ƙarfi kamar a ofishin NEPA na ke aiki.

Na dawo na zauna ina Allah-Allah ya yi ya sallameni.

Ina gani ya fara neme-nemen mafifici bai samu ba.

"Jummai, Jummai, ina mafificinkun nan ne?" Ya ƙwalawa matarsa kira. Itace matarsa ta biyu. Ina ga yau girkinta ne. Matansa duka uku gatan ɗaki ɗaɗɗaya suka samu da su da 'ya'yansu, duk wacce ta ke da girki ita ce za ta shigo ɗakinsa ta kwana. Manyan yaransu Maza kuma na kwana a ɗakin Zaure.

Har yau idan rikicin gidan ya tashi aka fara faɗan gado za ka ji matar Baffa Zakari tana mitar ai Baffa Lawalli shi kaɗai ya cinye gidan, ɗakuna huɗu ya take shi kaɗai.
Ni bana tunanin an shatawa Babana fili a gidan da sunan gado. Ina ga tun da ya rasu suka haɗu suka laƙume filinsa da ke gidan. Shi ya sa fa nake son na samu kuɗin kaina. Bana so ko kaɗan na shiga maganar gado. Wanda ya ga zai ci ya ci, ai Allah ne ya ce a bayar idan suka cinye  za su je su haɗu da Ubangijin da ya ce a raba gado.

Ina tsugunne duk ƙafafuwana sun yi tsami Anty Jummai ta shigo ta duba masa mafificin a saman ƙaramin tsohon TV da ke ɗakin. Ta miƙa masa mafificin ta fita.

Ina nan sai haɗa gumi nake cikin hijabi shi kuma ya dage sai fiffita ya ke bai ce da ni komai ba.

Sai can ya ce mini "Yawwa! Ziyada ban sani ba ko akwai kuɗi a wajenki ki bani aron dubu hamsin"

Na zaro ido cike da mamakin yadda ya kira dubu hamsin ɗin kaman ya taɓa bani ajiya.

"Baba, gaskiya babu kuɗi a wajena. Kwanaki na biya kuɗin Makaranta da su"

"To, to, ko dubu ishirin ba za a samu ba?"

Na haɗe fiska na ce "babu"

"To shikenan, je ki"

Na miƙe ina lissafin maƙudan kuɗaɗen da na ke binsa bashi har yau babu ranan biya. Ni Ziyada na sake bashi aron dubu hamsin. Allah ya kiyaye...

Har zan fita sai ya ce " Wancan Alhajin da ya ke zuwa wajenki har yanzu kuna tare ko?"

"Baba na sallameshi" na faɗa da ɗan ƙarfi dan bana son ya sa rai da Alhaji Nafi'u.

"Kin Sallameshi saboda me?. Mutumin arziƙi Azumin da ta wuce rabin buhun sugar da katan ɗin taliya fa ya kawo mana"

"Ni dai na sallameshi" na sake jaddada masa dan kar ya sa rai da kwaɗayin kuɗin Alhaji Nafi'u

Bai ce min komai ba nima na fita.

Ina zuwa sashenmu na cire Hijabi na hau gado na kwanta na shiga CapCut na fara editing videon da zan ɗaura gobe. Saboda school yawanci a weekend na ke yin shooting ɗin video idan na samu time sai na editing na ɗaura. Sau biyu a sati na ke ɗaura recipe amma wani lokaci na kan ɗan ɗaura random vidoes na wasu abubuwan ko kuma idan Kaka tana wani abu sai na ɗauketa na ɗaura.

Letter Z ne ya popping a saman notification bar ɗina. Ina ganin Z  zuciyata yai wani ras. Ko ban duba wa ya turo min ba, na san mutum ɗaya ne ke chatting ɗina da suna haka.

Ban buɗe ba na cigaba da editing da nake yi sai ga wani saƙon ya shigo

"Na san ba ki yi bacci ba, zan kira, plzzz ki ɗauka"

Ko gama processing kalmomin ban yi ba kiransa ya shigo. Na bi screen ɗin da kallo har yau ban chanja sunan dana saving contact ɗinsa da shi ba My Ameen❤

Sai da ta kusa yankewa sannan na ɗauka amma na yi shiru...

***

JAYKAY

A gajiye ya shigo gidan. Today was super hectic. Amma Alhamdulillahi akwai positive response daga investors ɗin da suka zo. Idan har sun gama shawara there's possibility sati mai zuwa za su turo Lawyers ɗinsu a zo a yi yarjejeniya.

Lokacin da ya shigo gidan main parlour ɗin babu kowa dan haka sai ya shiga ɗakin Hajiya ya sameta tana sallar Magariba, bai jirata ba sai ya wuce nasa part ɗin dan ya yi wanka ya chanja kaya. Da ya fito daga banɗaki sai ya buɗe closet ɗinsa zai ɗau kaya, tsayawa ya yi cak yana kallon wajen, wasu kayan bacci guda biyu da aka jera kusa da pyjamas ɗinsa ne ya tuna masa da cewa yana da MATA. Matar da ke wata duniyar bata da niyyar rayuwa da shi a inda ya ke. Shekaransa biyu kenan da dawowa Nigeria permanently da zama. A cikin shekara biyun da yai a Nigeria Cassandra ta zo masa Nigeria ne sau biyu. A shekarar farko ta zo ne lokacin Christmas ta tafi bayan New Year. Kwanaki 15 ta yi a Nigeria kullum sai ta tuna masa da hakan. A shekara na biyu kuma ta masa kwana 10. Wannan shekaran ma ya sani bata da niyyar zuwa sai ƙarshen shekara kamar yadda ta saba.
Yana tura mata ɗansu Junior London ya je ya mata vacation idan aka yi hutun Makaranta. Yanzu kamma kamar yadda bata damu da yaron nasu ba shima yaron ya fara jin daɗin Nigeria, bai damu da rashin mahaifiyarsa kusa da shi ba. Idan ba an yi hutu ba baya ma maganar zai je London.

Wai shikenan, a haka za a cigaba da auren?.

Ba zai iya abandoning Kamfanin da mahaifinsu ya kafa ya koma London ba. Balle ma bashi da wani identity yanzu a can. Idan ya je baƙin cikin abinda ya rasa ne zai hana shi sukuni. Gara yana nan Nigeria kusa da Hajiya, kusa da ƙanwarsa ɗaya da ta rage masa. Kusa da 'yan'uwa da abokan arziƙi...

Wani baƙin comfy shirt mai laushi ya ciro ya saka ya haɗa da wata baƙar wando. Da alwalarsa dama ya fito saboda idan ya gaida Hajiya sai  ya wuce Masallaci ya je ya yi sallar Isha.

Lokacin da ya shiga ɗakin Hajiya sai ya samu ta idar da sallah tana jan carbi.
Ya gaisheta, ta amsa masa sannan ya ce mata zai je ya yi sallar Isha.

Ta ce da shi "Muhammad yana ɗakinsa sai ka ɗaukeshi ku tafi tare". Ya miƙe ba tareda ya ce komai ba ya fita.
Ɗakin Junior ya shiga ya kira yaron suka fito za su je Masallaci tare.

Suna saukowa falo sai ga Janan ta shigo gidan tana maƙale da waya a kunnenta sai masifa ta ke yi.

"Ya Jalal Barka da dare" ta faɗa za ta haura sama ya ce mata
"Kin je office yau?"

"Na je manaaa" ta faɗa sannan ta haura sama tana cigaba da wayarta.

JayKay ya riƙe hannun ɗansa Junior suka wuce Masallaci...

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.