Free chapter 路 Read without an account

Pregnancy

by Ramlat Abdulrahman Manga 路 ROYAL POLITICS 2

ROYAL POLITICS 馃敟
_An yanka ta tashi_
    Ramlat A Manga
       Mai_Dambu
TOP-NOTCH SEASON 4
  Sadaukarwa ga Auntyna RUKAYYA GOMBE 馃グ 馃ぉ 馃槏

06
#Pregnancy

Rintsa idanunsa yayi ya bude da karfi, yana huci idan ya kyale Malam Junaid ya zalinci kansa da kansa, kallon yarinyar yayi ya ce mata. "Zaki iya tafiya!" A daddafe ta shiga ban蓷aki cikin ruwan zafi ta shiga tana haki. Sai da ta gasa takashinta sannan ta fito ya bata wasu magunguna, kafin ya bude wata jakar kudi ya mika mata shi jakar baki蓷aya a dan razane ta ja baya tana fa蓷in. "Alhaji kana son a kama ni ne?" Dariya yayi domin yadda tayi maganar ya bashi dariya don ta fitar da yarintarta ya ce mata. "Ba ni account dinki na banki, sannan sunanki." "Amnah suna na!" Ta fada tana me karanto mishi number wayarta. Janyota yayi jikinshi yana shinshina wuyarta ya ce mata. "Ganinmu a haka ya kara tayar min da hankali, ki bari muyi sau daya." Cikinta ne ya dauri ruwa  ta ce mishi. "Amma ba ta baya ba ko?" Girgiza kai yayi ya ce mata. "Rijiyarki zan shiga na dibo ruwan dad'i!" Ajiyar zuciya ta sauke, daga nan suka sake fadawa sabon masha'arsu wanda yafi na da, bata ta蓳a sanin cewa akwai maza masu shekaru da jarumta ba sai Alhaji Nafi'u, wanda aka hada ta da shi ta sanadin kawarta Nusaiba ta shigo da ita wannan duniyar me cike da jin dad'i. Alhaji Nafi'u ya saba niman mata musamman matan aure, wanda yasan kome na rayuwarsu a boye yake. Zai matu茩ar wahala matar aure ta tona maka asiri, amma budurwa ko a wurin kawayenta kowa zai sani, sannan wannan harkan su kansu matan auren 茩ungiya suke da shi wanda suke gudanar da kome, kafin a kawo mishi ita hatta tests na cututtukan zamani sai da aka mata shima kuma an san nashi lafiyar. A wannan kungiyar duk matar da tace zata fita tow kuwa hukuncinta daidai yake da mutuwa, shi yasa basu fita har gara idan asirinka ya tuno zaka iya barin gari ka gudu amma inda ka je ba zaka zauna a banza ba. Zaka cigaba da yiwa kungiya hidima da aiki domin ta haka ne za a tabbatar da kai din na musamman ne.

A da can an san karuwai yan mata ne da suka bar gida gaban iyayensu, ko sanadin auren dole ko sanadin abin kunyar da suka yi, amma yau an wayi gari matar aure a dakin Mijinta ne take bin maza tana rayuwar da take so ana zuba mata kudi ta zama jaka, kuma ana gani an san abinda ake yi babu kyau amma an mai da shi normal kowa ma zai iya aikatawa, ba tare da an tuhume shi ba.
    Yadda Alhaji Nafi'u yake gurnani akanta yana surutai ya kara saka mata jin dad'i, domin ita bata san wannan abin ba, wai namiji yana tarayya da kai yana sumbatu ita mijinta gyara kawai yake ce mata ya shiga yayi yadda yake so, yana gamawa zai sauka koda ace ita bata gamsu ba , amma yau gashi ana gaya mata tafi kowace mace dad'in mu'amala.  Sai da ya jikata sosai sannan ya janye jikinshi ya zube a gefe yana numfashi. A tare suka yi wanka tana fitowa ta rikice domin taji nononta har wani zogi yake Babynta yana kuka, da sauri sauri ta saka kaya ya mika mata jakar ya ce mata. "Na tura miki ta account 蓷inki, sauran kuma ki yi amfani da shi. Naji dadinki Amirah zan so na kara miki wasu kyautar amma dole ki san yadda zaki na takunki." "In sha Allah Alhaji!"

  ***
Salmanu Faris
Mai da file din yayi gefe, sannan ya cigaba da aikinsa. "Baby ba kace kome ba?" Ta kuma tambayarshi, a da can baya lokacin da suke kasar waje be tab'a yunkurin hanata yin yadda take so ba, amma tunda suka dawo wannan shegen zuri'arsa kullum sai ya saka mata idanu, kai hatta motsi bata isa tayi me kyau ba, sai ya ce forsake of the family. "Babe!" Ta kuma kiran sunanshi a hankali, tana shafa kunnensa. D'ago fararen idanunsa yayi ya zuba a kirjinta. A hankali ya kai kanshi yana mirginawa gyara zama yayi a dest 蓷in.."Baby!" "Ban amince ba!" Kamar diran aradu haka ta ji sautin muryanshi. Da wani irin sauri ta janye shi daga jikinta. "Prince me kace?" Jan kujeransa yayi baya yana kallonta kafin yayi mata wani irin kallo me cike da tuhuma. "Me yasa?" Ta kuma tambayarshi. "Ban gamsu da agender din kungiyar ba ne!" Daga haka ya mike zai bar wurin. Ta sha gabanshi cikin huci, "Me yasa kake min abinda baka min da? Me yasa yanzu ban isa na kawo bukatata gare ka ba? Ka kasan asarar da zan yi?" A matu茩ar gajiye ya ce janyo ta jikinshi tare da rungume ta. "Ban san asarar da zaki yi ba!" "Tow ka bar ni nayi yadda nake so, na gaji da fitilar nan kullum cikin gasa min gyad'a a hannu wannan project din yau kwana biyu kenan da na kawo maka amma baka ce kome ba." Shiru yayi kafin ya nufi wurin kujera ya ajiye ta a kai. Karamin firji din da yake dakin ya bude ya ciro ruwa ya bata. Ture ruwan tayi tana fa蓷in. "Bana bukatarshi." Murmushi yayi ya ce mata. "Idan har zaki amince, ki hakura da project din domin babu alkhairi a cikinsa, akwai project din da nake nima miki, saura ka蓷an a cimma nasara zaki samu ku蓷in da." "Ni zaka gayawa zan samu ku蓷i? Ni zaka gayawa yadda zan saita rayuwata? Kada ka manta da rayuwata ka same ni, don haka abinda na saka kaina shi zan yi ko kayi approved ko kada ka yi na rigada na saka a raina zan yi kome domin kaina."
      Daga haka ta mike tana me 茩o茩arin barin dakin, kallonta yake ya ma rasa me zai ce mata, maganar gaskiya bata jin maganarshi. "Na fito daga cikin bloodlines na Royal family ne, don haka ba zaki yi ba."   Ya fada mata a hankali, juyawa tayi murmushi kafin ta juya ta fita.

The next.
Ya shirya cikin ya nufi asibiti, yana shiga office ya dauko face mask ya saka sannan ya nufi ward na mahaukata mata, bin gadonsu yake yana duba files dinsu, yana tambayar Nurses din da suke gaya  mishi cigaban da aka samu, gaban gadon wata mata suka zo, tana barci ne sakamakon alluran da suka mata. Duk da an daure ta amma idan da zata farka sai su ga sarkan da suka daureta da shi a warware su baki蓷aya don haka sai sun sake mata allura. "Wannan yaushe?" "Yau kwana biyu kenan Dr Bashir ya amshi case dinta, ana tunanin za a mai da ta gida ma don case din ba ta asibiti ba ce." "Yarima Salmanu Faris Attahiru Shehu Yayari." Kallon matar yayi ya ce mata. "Na'am!" "Akwai yarinyar da aka haifa da jinin nasara da sa'a, wacce ita ce mafarin raba kan amana hu蓷u, ka nimo yarinyar ka mallaketa, koda wasa ba zaka tab'a faduwa ba,.akwai yan baiwa da yawa da suke kasancewa haka, kayi sauri kada ka rasa wannan damar. Wancan tana can tana faffutkar fadawa wata rayuwa. A hankali zaka fahimta domin an juya kome! Daga sama zuwa kasa."

    A hankali ta koma ta barcinta, murmushi yayi yana me rubutu. "Dr Faris, dama kai ne  Royal Prince din da yake aiki a cikin asibiti?" Hannu ya kai bakinshi. "Shiii!" Daga haka suka kama dariya, "but why doctor, babu amfanin." "I want to live like some ordinary people. Don haka ayi shiru a bar maganar anan!"

    Sai da suka gama ganin marasa lafiya mata, kafin suka koma wurin sauran marasa lafiya maza yan iska na asibitin mahaukata. Musamman wadanda suka samu matsala ta hanyar shan kwayoyi. "Likita yau ma kazo? Jiya da na ce mata zan baka miliyoyin Naira ina baka dawo ba, ni zan baka gangaliyo trillion tare da zillion na naira." Kallon Nurse din yayi ya ce musu. "Kuje zan zo yanzu!" Sannan ya nufi kan mutumin kama kunnensa yayi ya murd'a. "Gaya min waye ke sayar muku da kayan maye?" Yadda ya murd'a kunnen sai da mutumin ya sake fitsari. "Khalifa da Ahmad Rilwani Yayari." Murmushi yayi sannan ya ce mishi. "Good Boy!" Ya fita daga ward din, kiran wayarshi aka yi. "Sir everyone is ready, muna jiran ranar ne!"
      D'ago kai yayi yana kallon hasken rana, "done!" Yana kashe wayar ya mai da cikin rigarshi. Office dinshi ya nufa a babban parlourn ya hadu da sauran likitocin. "Golden spoon!" Inji wani likita. Kwashewa da dariya suka yi. "Kai dai Dr Mikel kana da matsala." "Eh mana mu anan shekaru goma sha biyar muka dauka muna hada degree da master, Golden spoon kuwa shekaru goma zai dauka ya ha蓷a master da Phd, kaga kuwa skill is rather than degree." Wucewa yayi office dinsa bai ce musu kome ba, "ka lura kuwa ance a fadar sarki yake zaune maybe irin Yaran dangin nan ne!" Nurse Amina da Nurse Nana kallon juna suka yi, Nurse Nana ta ce musu. "Hmmm kuna abu a jahilce!" Rike mata hannu hannu Nurse Amina tayi mata tana girgiza mata mata kai. "Kada ki ce kome."
          Basu kara magana ba, kiranshi aka yi  ana nimanshi. Can kamar minti goma sai ga Dr Bashir, office din ya nufa ya kalle shi. "Dr ka yi hakuri, kiran gaggawa ce." "Haba Yallabai, akwai abinda zaka nima na gaza maka, yau ina tsaye ne a matsayin likita ta sanadin Mahaifinka, don Allah ka je ni zan kula da su." Mikewa yayi zai magana Faruq ya turo kofar. "Mutumin ashe kana nan?" Dr Bashir ya mikawa Faruq hannu. "Ina nan aiki ne baya kawo ni nan!" Inji Faruq yana mika mishi hannu, bayan sun gaisa ya dauki jakar Prince ya fito sai da Salmanu Faris ya fito shima rufa mishi baya tare da Dr Bashir, sai godiya yake yi yana jin dad'i. Har Addu'a yake Salmanu Faris ya kira shi ya rike mishi aikinsa wannan ai babban abin farin ciki ne, sannan idan wata yayi wani irin mahaukatan kudi ake zura mishi, tunda Salman ya fara aiki a asibitin har yau bai san.iya adadin kudin da ake bashi domin yayi wani abu da za a ga laifin Salmanu din ba, amma ya kasa domin shi mutum ne mai amana, bayan ya dawo daga raka su Dr Mikel ya ce mishi. "Loyalty dog!" "Duk abinda ka gadama kace, amma ka sani wannan asibitin mallakarshi ce." Mikewa Dr Mikel yayi "what!" "Yes aikin da kake yi a karkashinsa kake yi, wanda ka gani rike da jakanshi shine mataimakinsa idan ya saka jan biro akanka tow takare maka,  albashin da ake bamu asibitin gwamnati bai kai allowens din da muke samu anan ba, ka sani kowani mutum yana da abin da yake so ko yake ki, shi 茩wa茩walwar mutane ita ce abinda yake so idan har ka sake ya juya gare ka tow ba makawa zaka sha mamaki."

***
Cikin gida
Kai tsaye bangaren Mai Babbar daki ya nufa, anan ya samu Hajiya Kilishi wato Hajiya Balkisu wacce take bin Mai Babbar daki,da Hajiya Turaki, wato Hajiya Hadiza wacce take bin Hajiya Kilishi. Sai iyayen Nady sai Nady da take zaune. Sai Alhaji Rilwanu Abubakar Yayari da Baba waziri Alhaji Mamman Abba yayari sarki mai rikon kwarya, sai Alhaji Kabiru Hamud Yayari. Zama yayi a 茩asa kanshi a sunkuye, a rayuwar zamansu ba a tab'a mishi abinda Nadiya tai ba. Da addu'o'i aka bude taron. Kafin Mahaifin Nadiyyah ya ce musu. "Naso da kun kira Imam Junaid Gobir domin shi na bawa amanar Nadiyyah, lokacin da Mai Martaba yasan Faris ya auri Nadiyyah, and akan me zai na cutar da ita? My daughter ta tashi cikin aminci da nutsuwa taya za a kawo ta cikin inda bata tab'a mafarkin rayuwa ba ace tayi abinda ake so? Haka zai faru ne? Ai haka ba zai taba yiwuwa ba, shi yasa idan don arziki ne Faris bai isa ya kai kafarshi inda Nadiyyah take, amma ya zauna yana juya ta."
         "Kayi hakuri, amma mu Royal family muna da limit dinmu da muke tsayawa, sannan shi yasan dalilin da yake dakatar da ita ko Son!" Ciwon lips dinsa yayi tare da dunkule hannunsa. Kanshi a sunkuye ranshi yayi bala'in b'aci. "Idan har dai haka ne gaskiya tow zan tafi da Yarinyata, domin ba zan iya ganinta a wulakance ba, kafin ya aure ta ai har yarjejeniya suka yi babu batun rabuwa amma yanzu zan dauke ta idan ya bukaci tayi yadda take so fine sai ta dawo." "Kayi hakuri duk da mai martaba baya nan amma ina mai baka hakuri da abin da ya faru, baa kyauta mata ba sannan, shima za mu mishi fa蓷a."
"Hajiya Maryam bai da ce a yanke hukunci bangare daya ba, domin idan aka yi haka babu adalci a cikinsa. " "Alhaji Mamman wannan shine adalci, tayi hakuri." "And akwai wani labari da yake yawo na cewa ana son Salmanu Faris ya kara aure?" Tabbas Mai Babbar daki ta fadi haka. "Tow amma ku sani idan har aure zai yi ina ga lokaci yayi da zai sawwake mata." Shiru duk wurin ya dauka still dai ita mai Babbar dakin ta ce mishi. "In sha Allah ba za a mata kishiya ba, Alhaji  kayi hakuri."mikewa yayi zai bar parlourn. "Ina zaka ka bawa surukinka hakuri!" Juyawa yayi yana kallon Mahaifiyarsa. "Ummina ai kin bashi hakuri idan sun rena naki shi kenan su yi duk abinda suke so!" Ya saka kai ya fita, "Ummi ba sai ya basu hakuri ba, Dad ai ka hakura ni dama kawai a samu masalaha shine bukatata!" Ta fada tana bin bayansa, "ai kun ga irinta mata da miji kenan haka suke gashi zasu daidaita kansu."
                 Alhaji Rilwanu Abubakar Yayari bai so haka ba, idan har da Salman ya yi zuciya ya ce zai rabu da Nadiyyah tow shi zai nimawa kanshi Nadiyyah, zuwa yanzu da ake hasashen Alhaji Jamil Chiroma zai iya zama next shugaban kasa haka zai bashi dama da ikon biyan bu茩atarshi. Kyaututtukan da aka yi ta shigo musu ne, wasu irin manya kwati ne kowa da na shi kudi ne na fitar hankali mazan kenan, matan kuwa kayan kawwa ce danginsu zinari musamman Mai Babbar daki da taji babu zancen yiwa Nadiyyah kishi matukar tana raye. Da aka suka watse suma suka koma garin Jos dama a can suke da zama.
Da dare da ya shiga mata sai da safe nan ya samu sabon nasiha har da mishi iyaka da wata mace, matu茩ar ya ce zai yi aure sai ta mishi Allah ya isa.  Wannan abin ya tsaya mishi a rai.
  Dalilin Mai Babbar daki kuwa Mahaifin Nadiyyah yana da karfi, zai iya amfani da karfin domin karawa da kowa a bawa Salmanu Faris kujeransa. Haka yasa dole su hakura da Nadiyyah.

Koda ya koma da wasu kayan barci ya same ta, ajiye mishi file din tayi ya dauka ya saka mata hannu sannan ya wuce dakinsa,domin mai Babbar daki ta gaya mishi Nadiyyah da iyayenta sune damarsu ta karshe don Allah kada ya ce zai yi wani abu da zai shiga tsakaninsu yana rabuwa da Nadiyyah kamar mulkinsu ya rasa.
Abinda Mai Bauchi ya fada yasa ta fusata yana fa蓷in. "Tow idan Nadiyyah ta mutu fa Ubanta zai cigaba bawa Yaya goyan baya ne?" Dakuwa tayi mishi tana hararansa..

Washi gari, sai da Nadiyyah ta zo ta gaishe ta sannan ta ajiye mata damin kudi ta ce. "Ummi a rabawa masu tayaki hira." "Bakya gajiya ne?" "A'a Ummina dama nace idan ba zan takura Aneesa ba ita da Dawla zan biya muku umara sai ku tafi ku yi ibada tare da yiwa mai Martaba addu'a." "Ikon Allah, Nadiyyah!" "Ummi albarka zaki saka min kawai!" "Tow Allah ya miki albarka."

Fita tana jin dad'i, Babanta yayi gaskiya da ya ce mata, suna da ikon ja da kowa amma Salman ba zai tab'a musu biyayya kamar yadda suke gani a wurin kowa ba, idan suka janyo danginsa suna kashe musu kudi da da musu hidima zai batar tayi yadda take so domin ko bar ta ba, danginsa ba zasu tab'a barinsa ba.
***
Friday

Ikhlas Junaid Gobir
Tun da Hajja tazo kullum sai Abba ya raba Fada a tsakanin Hajja da Iram.
"Junaidu nazo gidanka ne bakin ciki ya kashe shi?  Yarinyar nan Irak kaga yadda take min kallon banza, wallahi ba zan yarda ni da gidan d'ana ana min kallon uku saura kwata."
"Iram me yasa baki jin magana ne?" "Abba!" "Munafuka yi min shiru." Inji Hajja. "Ni dai gaskiya ba za a saka min Ya a gaba ana cutar da ita a banza ba, ka jawa Hajja kunne ko a ji mu da ku."
    Murmushi Hajja tayi ta ce mishi. "Ai dama nasan mara kunya sai kin yi magana, tunda nayi magana. Yarinyar nan shiru-shirunta na munafunci ne." Fisgar hannun Iram tayi tana fa蓷in.."Allah ka蓷ai yasan karatun kurma." Daga haka ta wuce.  Irin wannan rigimar bata karewa a gidanmu..
        Shigowa Hajja tayi tana fa蓷in. "Kilas baki ga sauyi a tattare da yarinyar nan Irak ba?" Girgiza kai nayi nace mata. "Ban ga kome ba Hajja!" Na fa蓷a ina hada kaya zuwa office. Wayata ce tayi 茩ara na 蓷auka ina sakawa a kunne. "Yeemar!" "An gaya miki labarin yau garin kamar za a samu wani karamin crisis?"
"A'a gani ina shirin fitowa ne?" "Gaskiya kada ki fito, domin ana tsammanin ba lafiya jiya an samu gawarwaaki wasu mutanen da ba sani ba. And an saka Curfew." "Curfew? Gaskiya zan fito kada ki damu na samu damar yin wani bincike ne. " "Ikhlas kada ki fito fa!"
"Sai kiyi! Na kashe wayar, na dauki jakata. "Ke kilas baki ga sauyi a tattare da yar uwarki ba?"  Juyawa nayi na kalleta kafin na ce mata. "Hajja don Allah ana zaman lafiya a gidan nan, kada ki rusa mana zaman lafiyar da muke yi Please!" "Tow shi kenan amma ni nasan abinda na gani yar nan!" "Ke iya idanunki ka蓷ai zai ni mu kuma abinda zuciyarmu yake dauke da shi zamu gani." "Ina zargin tana da juna biyu...

Bononza bononza matan kwarai masoya gyaran sunan kunada lbr sallah promo kuwa wanda mayan mata  wada sukashahara  tawajen bada magani  tazomuku d promo datakeyi duk shekara nakayan dahu hjy kisaya kihada dakanki  inamasuso cicibin da nakayan cikin dana tsuka yanka 9  dana bindi saniya to gamagani kisaya  kihuwa kema kiji me akeji ne 馃 lahiya yazo kemakizama  tauraruwa agidanki 馃グ  dakudinki kalilan promo 1 cicibin magani  promo 5k ,,7k
2 bindin saniya 8k 10k
3 natsuka yanka 9 3500 2500
4 nakayan ciki 3k 2k
5 nakaza  4k noml 6k
7 nasoya koyi 1000 2k
8 nasawa kowani kalan cukudin magani shikuma 3500  yadaukan abudayauwa  ummu rayan inagodiya  m zee 馃
Kar ayibake don sallah akayi wanan saukin

Top_notch season 4 ROYAL POLITICS is not free, pay N500 to get a complete access to the book.

Marubutan TopNotch Writers sun sake zuwa muku da sabon labarai masu 茩ayatarwa a tafiyarsu ta Season Four:

MAI_DAMBU kuwa ta faso muku ne da labarin da ya ha蓷a da Sarauta, Siyasa da kuma Soyayya, duka a littafin ROYAL POLITICS: An yanka ta tashi.

AZIZAT kuma ta tattaro muku rikitacciyar soyayya ne da ya hawo jirgin JayKay ya dira a Kitchen 蓷in Ziyada. CHEF ZEEY: Love in the Kitchen

Account Details:
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*

POSTING
*茒aya: 500*
*Biyu: 1000*
*Uku: 1500*

DOCUMENT (da zaran an gama posting zai koma)
*茒aya: 1k*
*Biyu: 2k*
*Uku: 3k*

domin tura shaidar biya ko 茦arin bayani, ku tuntu蓳i:
*****
Ko
*****
Ko kuma
*****

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol