Free chapter · Read without an account
Page 1
by Rahma Kabir · MIJIN ARO
MIJIN ARO
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 1.
Sarac Stars R Pen...✍️
Labari ne da wani ɓangare ya faru, wanda sai da na samu sahalewar rubutashi, wataƙila yayi iri ɗaya da labarinki ko wata 'yar uwarki to arashi ne, fatana in isar da saƙo da faɗakarwa a cikin nishaɗi.
Gargaɗi
Ban yarda a juya mini labari ba ko ayi afmani da wani ɓangare na labarin, ko a ɗaura min shi a wata kafa ta media ba tare da izini na ba, sannan ina gargaɗi ga masu cire sunana a cikin labarina su saka nasu tare da sakinsa a shafinsu, a barmin sunana tare da barin rubutuna a yadda yake, da fatan za a kiyaye
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
NURATU.
Sanye take cikin tsadadden leshi mai ruwan ƙasa fuskarta cike da annuri mai ɗauke da Madaidaiciyar kwalliya, a wuyanta sakar gwal ne mai haɗe da zobe da awarwaro, yanayinta ya nuna tana cikin tsantsar natsuwa da kwanciyar hankali tare da jin daɗi, dan a fatarta kawai hutu ya ratsa gata 'yar duma-duma da hasken fata mai kyau da sheƙi. Yinin sallah babba ne suka zo yi a gidan iyayenta wanda ya yi daidai da kwanan wata 18/6/2024, wato kwana biyu kenan da aka yi sallar idi babba, sun saba haɗuwa duk bayan kwana biyu da sallah dan sada zumunci a tsakanin alhalinsu. Nuratu tana zaune bisa katon dadduma wanda ya mamaye tsakiyar falon Ummansu ga kuma abinci kala kala da kayan ciye ciye da aka jerasu akai, ta saki murmushi lokacin da ƙanwarta Mubeena ta shigo wacce suke kira da Beena tana riƙe da kofin tangaras a hannunta tana cewa.
Anty Nuratu amma dai yau kwana zaki yi a nan, domin muji daɗin hirar zumunci na yaushe gamo?
Hmmm shi kuma Mahmood na yi yaya da shi? Sanin kanki ne bana wasa da al'amarin mijina, ba zan iya kwana anan ba in har yana gari.
Nuratu ta ambata tana saka cin-cin abakinta tare da sakin murmushi, guntun dariya Beena ta yi tana zama tare da fuskarta Nuratu.
Kwana ɗaya fa za kiyi, kinga gobe da gari ya waye zamu je gidan baba mai dabino ba sai mun tsaya jiran kin zo ba.
Na dai faɗa miki Mahmood bai yi lalacewar da zan yi masa riƙon sakainar kashi ba, har gobe wannan soyayyar da kika sani a tsakaninmu tana nan daram.
Hmmmm Beena ta faɗa tana taɓe baki tare da zuba ruwan kunun aya a kofi ta kurɓa, sai da sanyinsa ya jiƙa mata maƙoshi kafin ta aje kofin ta kalli Nuratu da kyau.
Anty Namiji fa ba ɗan goyo bane, domin akan Abdallah na sare da lamarinsu.
Me ya yi miki da kike yiwa masa kuɗin goro?
Raba mini kwana yake yi da matan banza...
Kai Mubeena anya kuwa? To ke a ina kika ji? bana son zance irin wannan, taya zaki jefi mijinki da mummunar magana irin haka.
Cewar Nuratu da ta tari numfashin Beena tun kafin ta kai aya, Beena ta ce cikin sanyin murya.
Wallahi babu sharri a cikin maganata domin da idona na ga irin mummunar charting ɗin da yake yi da 'yan mata, wanda bai tsaya anan ba har haɗuwa suke yi a guri mabanbanta suna sheƙe ayarsu.
Ta ƙare maganar cikin rawar murya idonta yana kawo ruwan hawaye, sai ta danne su bata bari sun zubo ba, sheƙeƙe Nuratu ta tsaya kallonta fuskarta ɗauke da maɗaukakin mamaki.
Wa ya aike ki duba masa waya? Mubeena ƙazantar daba ka gani ba tsafta ce, wayar namiji tamkar albasa ce kina dubawa kina hawaye, wanda gashi kin ga illar yin haka domin sirrin ciki sai hajji, duk abinda kika ga Allah ya rufe shi to hakan shine mafi alkhairi, dan haka wlh daga yau karki sake.
Ta faɗa tana nuna ta da yatsa manuniya alamun gargaɗi, Mubeena ta share guntun hawayen daya sauka a kuncinta, fuskarta a dame cike da tsantsar damuwa wanda ya kauda farin cikin da ta shigo falon da shi, ta danne wani ƙulli daya tokare mata maƙoshi tare da haɗiye miyau kwad da ƙarfi kana ta kalli Nuratu.
Anty ba zaki taɓa fahimtar halin da nake ciki ba, zama da mazinaci abu ne mai matuƙar wuya da nauyi, ni kaɗai na san ƙunar da zuciyata take ciki tare da ƙunsar bakin cikin da Abdallah yake tusa mini, kuma har gobe ƙaryata ni yake yi akan shi baya aikata komai dan ban nuna masa a wayarsa ne na gani ba.
Hmmm gwara da baki nuna ba dan kuwa da ba ƙaramin rikici hakan zai haifar ba, ki bar abinda Allah ya rufe shi Beena! Kuma dan girman Allah ki kiyayi wayarsa domin in baki daina ba to kinyi ban kwana da farin ciki kenan, abu mafi kyau a yanzu shine ki dage da addu'a kina nima masa fatan shiriya a gurin Ubangiji Sarkin da baya gyangyaɗi, mazan ne koda basu nima matan ba wlh matan suke bibiyarsu sai wanda Allah ya tsallake.
Hakane, Allah ya shirye su yasa mu dace, ya batun kwanan to?
Babu wannan zancen gidan mijina zan kwana, ko wannan labarin da kika bani ya isheni izina na ƙara zage damtse wajen kula da Abbansu Ashraf, duk da ba duka aka zama ɗaya ba ina yi masa kyakkyawar zato, kema kuma ki daina saka masa ido kina bin diddiginsa dan hakan ba shi ne zai sa ya daina ba, Addu'a shine makamin da zaki riƙe.
Nifa da na zo kenan ba shirin komawa, dan ba zan zauna da mazinaci ba.
Cewar Beena tana zumɓuro baki cike da jin haushi, wani harara Nuratu ta watsa mata wanda ta yunƙura zata yi magana sai wayarta ta soma ringing ta miƙa hannu ta ɗauko shi akan cushing da ta aje, sai taga Ƙawarta Zuhura ce ta kira, ta ɗaga kiran fuskarta ɗauke da fara'a.
Manya manya inji ƙanana, Zuhura matar Marigayi Alhaji Taju.
Ba kida kirki ƙawata, wannan sakin zance kamar Mahmood ya baki kyautar hajji.
Hmmmm Allah ya amshi bakinki, to ya sallar? anyi sallah lafiya? yasu mama da su Mimi.?
Duk suna lafiya, gani a gidanki zaune a falo mai gadi yace bakya nan amma ƙofa a buɗe take wai Mahmood bai yi nisa ba.
Shegiyar duniya, shine ba zaki kirani ki tambaye ni ko ina nan ba?
Ato sanin baki fiye fita ba matar kulle, na yi zaton kina gida, yanzu kina ina?
Ina gidan Ummanmu mun je yi mata yinin sallah, kinsan duk bayan kwana biyu da sallah muke zuwa jiya kuma gidansu Hajiyar Mahmood muka yini. In ba damuwa ki ƙaraso nan mana dan sai ɗan anjima zan dawo, kinga kuma yanzu aka yi la'asar.
A'a ni barci nake ji dan a gajiye nake, zan kwanta kafin ki dawo zuwa dare Masoyi Mus'ab zai zo ya ɗauke ni.
To ki shiga ɗakina ki kwanta, inna dawo za muyi magana akan wannan Mus'ab ɗin da ya kasa fitowa aurenki sai gantali kuke yi a titi gwanin takaici.
Hmmm Kyaji da shi, ni da Mus'ab dai nan gani nan bari.
Ta faɗa tana 'yar dariya tare da kashe wayar, Nuratu ta cire wayar daga kunnenta baki sake tana cewa.
Shiryayya ana buɗe mata ido tana runtsewa, aiko zamu hau sama mu faɗo dake akan wannan maganar, zan zo na same ki.
Ke da waye kuma Nuratu kike tada jijiyar wuya.?
Cewar Ummansu data shigo falon tana dubansu, nan Nuratu ta sanar da ita Zuhura ce har take faɗa mata tana gida tana jiranta, Umma ta samu guri ta zauna tana cewa.
Ai sai ki yi himma ki sameta dan bai dace ta zauna tana jiranki ba tunda gobe In Allah ya kaimu zaki dawo, dama na zo muyi zancen matar yayanku ne, tun ɗazu muna ta magana da Baffanku Sunusi a waya akan maganar, abu dai yaƙi ci yaƙi cinyewa.
Nifa Allah Umma in abun yaƙi kawai su rabu ya samu wata tunda ta zaɓi boko akan aurenta.
Cewar Beena da take taɓe baki, Nuratu ta kalle ta cike da hararar wasa.
Da yake ance kowa irin guntun tunaninki yake da shi ko, babu zancen rabuwa dole ne ya yi mata abinda take so tunda haka ya ɗaukarwa iyayenta alƙawari zata cigaba da karatu, dan haka tunda ya saka ƙafarsa wlh bai isa ya cire ba. Umma maganar gaskiya dole yaya Hafiz ya jurewa zama da Zulfa inya so tunda matsalarsa abinci ne da gyaran gida sai su nima 'yar aiki.
Ko kuma ya ƙara aure ba.
Cewar Jalila da ta shigo falon riƙe da 'yar Beena mai suna Halwa da suka fita yawon sallah tare, wani irin kallo Umma da Nuratu suka yi mata mai ɗauke da harara wanda Umma tace.
A'a yarona bai kai ya zama Mijin Aro ba, haka kawai su saka shi a tsakiya da masifar kishi, Hafizu ko zai ƙara aure ba yanzu ba, kuma kar na sake jin bakinki a wannan maganar.
Ta ƙare maganar tana karkaɗa yatsarta manuniya na hannun dama, sai hakan ya bawa su Nuratu dariya suka kwashe da shi, Umma ta saki baki tana kallonsu.
Au! Abin ma dariya ya baku? To maganar gaskiya kenan babu mai jona masa hawan jini da ƙuruciyarsa.
Nan ma dariya suka yi Nuratu tana cewa.
Umma ai auren zai kawo musu maslaha, duk da nima bazan zo ya ƙara aure a yanzu ba, amma dai shawarar dana bayar na a niman musu 'yar aiki shine kawai mafita a yanzu, In Sha Allah gobe in nazo zamu je muyi bikonta.
Allah ya kaimu kuma ki tashi ki tafi gida tunda ana jiranki, sai ki bar yaran a nan su kwana.
Dama sun zo kenan su kwana muku biyu ko na huta da bari bari.
Cewar Nuratu tana miƙewa, Umma tace cikin murmushi.
Ni kuma sai ki kawo min su suyi ta sakani magana ko? bayan na gama naku sannan nayi na 'ya'yanku, wanda kuma har yanzu ban daina bari bari ba dan ga Hafizu nan sai sakani magana yake yi.
Nan dai suka dinga mayar da hira wanda Nuratu ta saka Jalila ta ɗiba mata abinci da duk kayan ciye ciye ta haɗa komai a kwando kana ta ce.
Anty Nuratu in kai miki mota ne?
A'a riƙe mini zaki yi muje titi na samu napep dan motar anan zan barta, na gaji da tuƙi wlh duk kafaɗuna ciwo suke yi saboda ya haɗe mini da gajiyar aikin sallah.
To Jalila ta ce kana tayi gaba tana kwalwawa Yasmeen kira ɗiyar Nuratu ta biyu, ta zo da sauri sai Jalila ta miƙa mata kwandon tace su je bakin gate su jira Maminsu ta fito. Nuratu kuma ɗakin Umma ta shiga ta ɗauko gyalenta da ƙaramar jaka ta fito nan suka yi sallama tana mai kallon Beena data yi kwaɓo kwaɓo da fuska kamar wata ƙaramar yarinya, Nuratu ta taɓe baki tana ɗan murmushi.
Hakanan zaki rungumi sorry ni gidan Mijirille zan kwana, amma fa anjima za muyi chart karki wani ji kin damu.
In kika haɗu da Yaya Mahmood kuna wannan hirar taku tuni zaki mance da ni, ni dai sai da safe asha bidiri lafiya dan nasan yau akwai ƙara'i yara duk suna nan an baku guri.
Cewar Beena a hankali data biyo bayanta dan yi mata rakiya, dariya sosai Nuratu tayi kana tace.
Amma kince wani abu, to fashin sallah ma nake yi, ke kuma sai ki je ki rungumi filo ki kwana da kewar Abdallah.
Hmmm wannan da shi da babu duk ɗaya ne a gurina, dan ya gama sire mini a rai.
Haka nan zaki rungumeshi ki amsa ƙaddara ki dage da addu'a, kuma a daidai wannan lokacin ya kamata ki ƙara bashi kulawar da ta fi na da, domin ki ja shi a jiki tare da amfani da salo salon soyayya dan ki janye masa hankali ga matan wajen ki zama karuwar cikin gidanki, duk wani ɓarɓashin kunya ki aje shi.
Ta ƙare maganar tana tsura mata ido lokacin sun isa bakin gate, Beena tayi kwafa tace.
Aunty wanda yayi nisa baya jin kira, idonsu rufawa yake yi shaiɗan ya gama haska musu haram zuwa halal.
Beena duk abinda aka ce miki ibada ne to tabbas sai Allah ya sanya jarabawa a cikinsa domin ya gwada imaninmu. Sannan Ina so kisa a ranki duk abinda aure ya halasta shi koda baki iya ba to ki koya dan inganta zamantakewarku, duk in da mijinki ya juya kema sai ki sauya salon karkato da hankalinsa ta ko wani fuska matsawar ba zaki faɗawa haram ba.
Hmmmm Aunty shiyasa abu ne mai wuya Yaya Mahmood ya ƙara miki kishiya, Dan Allah gobe In Allah ya kaimu ki zo ki ɗaura mini karatu dan Wlh Ina buƙatar a sabunta mini komai dan Abdallah ya goge mini hadda.
Ta faɗa tana sosa kai cike da damuwa, Nuratu ta dafa kafaɗarta tana cewa.
Ko wace mace da iyawa aka santa, Dan haka kin san komai Beena ba sai na ɓata baki wajen faɗa miki ba, abinda kika sani ɗin nan shine zaki koma ki ƙara jaddada shi ki Kuma sabuntashi, sannan ki sa a ranki mijinki naki ne babu wata mace ta zata sha gabanki, duk wani sakaci da ƙika yi to ki gyara. Amma fa ki sani duk iya tattalinki da kafa-kafanki ba shine zai sa Allah ba zai jarabceki ba, Allah yafi jarabtarmu da abinda muka fi so domin ya gwada imaninmu, dan haka a wannan gaɓar dole ki ninka haƙurinki da juriya da kawar da ido, Idan ma aure zai ƙara ya kawo maslaha a tsakaninku, to ga fili ga mai doki! yafi biye biyen banzan da yake yi.
Anty kishiya fa?
Eh ita fa.
Haba-Haba! Umma bata zauna da kishiya ba sannan kema yaya Mahmood bai ƙara aure ba sai ni ce za a yiwa kishiya, tafɗijam da sake bindiga a ruwa.
Kaddarar Umma da ni da ke duk daban daban ce, Da yayi miki kishiya gwara ta waje ko Beena? ashe baki shirya yaƙi da matsalarsa ba, yanzu haka ma ƙila laifinki ne ya haddasa masa bin matan banza. Ni na tafi dan ina biye miki ba zan tafi ba akan lokaci.
Ni dai za muyi maganar amma banda shawarar ya mini kishiya wlh.
Ashe wanzami bai son jarfa, yanzu fa kika gama bada goyon baya yayanki ya yiwa matarsa Zulfa kishiya, to abinda kike sowa kanki ki sowa 'yar uwarki musulma.
Ta faɗa tana cire hannunta ɗaga kafaɗar Beena kana ta fice daga gate ɗin gidan, Beena da murmushi ta bita wanda na ciki yana ciki, dan har a zuciyarta bata jin zata risina Abdallah ya ƙara aure, zata dai cigaba da faɗawa Allah har ya karkato da hankakinsa ya daina, da wannan tunanin ta koma cikin gida jiki a sanyaye. Nuratu kuma basu daɗe ba ta samu abin hawa suka wuce, Jalila da Yasmeen suka koma gida.
*****
MAHMOOD.
A lokacin da Zuhura ta sauka a napep yana hangota saboda yana zaune a ƙofar shagon wani mai sayar da kayan masarufi dake cikin unguwarsu Sabon Kawo wanda yake ta ɓangaren unguwar dosa ta kan titin sheikh Jafar, sai da ya ɗan jima a gurin suna hira da mazajen unguwar da suka taru a ƙarƙashin bishiyar mangoro da aka jera kujeru suna zaune suna hira, da yake duk mazan sun samu hutun sallah daga ma'aikatan gomnati har 'yan kasuwa, shima Malam Ya'u mai shago gidansa yana jikin shagon ne shiyasa yake fitowa ya yi ciniki dan in bai buɗe ba har gidan ake sallama a ce ana son abu. Mahmood sallama ya yi musu ya nufi gidansa dan ya cakusa da Zuhura, saboda duk cikin ƙawayen Nuratu yafi sabawa da ita dan sosai suke wasa da hira tamkar shima ƙanwarsa ce, da yake itama Zuhura akwai surutu ba kanwar lasa ba ce, kuma ɗan zawarcin da take yi ya buɗe mata ido sosai, shiyasa take biye masa suke cakusawa ta fatar baki a gaban Nuratu ko a baya idonta.
Ko da ya shiga falo bai samu Zuhura ba sai kawai ya nufi ɗakin Nuratu dan ya san can ta yada zango, bai tsaya kwankwasa ƙofa ba ya murɗe handle ya shiga ya sameta kwance a rigingine tana charting, tana ganinsa ta tashi ta zauna tana cewa da murmushi.
Angon Nuratu ashe kana kusa?
Ina ganin saukarki a napep, daga ina kike sarkin yawo.?
Daga in da ka aike ni.
Tayi maganar cikin gatsali da murguɗa baki. Mahmood yayi guntun murmushi.
Ki dai ji tsoron Allah, wai sai yaushe za kiyi aure.?
To da tsoronka zanji, haka ɗazun matarka a waya ta soma yi mini ƙorafin aure sai kace akanku nake zaune.
Au kin yi waya da ita ne?
Eh, tace sai anjima zata dawo wai na yi barci na jirata.
Ok sai ki kwanta dama kin saba barci ke kaɗai, ina tausayinki yarinya miji ya rasu ya barki cikin kewa, ke kuma kin kasa aure.
To kayi maganin abun mana tunda akan ka nake zaune.
Cewar Zuhura data faɗa tana murguɗa masa baki cikin wasa. Mahmood ya ƙarasa shigowa cikin ɗakin dama tun ɗazu a jikin ƙofa ya tsaya, ya shiga nuna ta da yatsa ciki wasa.
Zanyi maganinki kuwa. Wai ina wannan Saurayinki mai kanne ido sai kace ɗan kwaya.?
Yana bayana ka laluba ka ganshi.
Cewar Zuhura tana gantsaro ƙirjinta, nan take Mahmood ya nufeta zai kai mata rankwashi sai ta goce ta diro daga gadon nan take wasan banza ya ɓarke a tsakaninsu, kuma abinda bai taɓa faruwa ba kenan ko dan yau ƙila suna da garanti ɗin ba kowa a gidan ne, daga haka kuma shaiɗan ya samu gurbin yaɗa manufarsa a zuƙatansu, da yake Zuhura 'yar duniya ce abin kunya gaba ta bashi ba baya ba haka ta dinga jansa suna mugun wasa, wanda shaiɗan ya gama kafa gomnatinsa da tsayar da ɗantakarar shugaban marasa lissafi, tunani da tsoron Allah Muhmood da kuma mataimakiyarsa Zuhura, nan ya fara kissing ɗinta tana mayar masa da zazzafar martani tamkar dama ta zo da shirinta, da yake kayan haram ba karamin daɗi yake da shi ba ga bayin shaiɗan, tuni lamarin ya soma zarcewa zuwa wani turba na daban wanda har ɗankwalin Zuhura ya faɗi suka yada zango akan gadon Nuratu cikin gushewar tunani dan tuni suka mance a inda suke.
Nuratu.
Rahma ce Matar MG.