Free chapter · Read without an account
Page 12
TURKEN GIDA.
Wattpad:Jamilaumar315
Arewabooks:Jamilaumarjanafty
SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)
🅿️12
Sulaiman Abubakar Yashe. Shi ne cikakken sunan Alhajinmu. Inkiyan Alhaji da ya samu ba yana nufin ya je ya sauke farali ba ne.
A zamanin baya in mutum ya baro ƙayensu zuwa garin Kano a matsayin jihar ta cibiyar kasuwanci sai a riƙa tunanin ai ka zama Alhaji ballatana in ka samu rufin asiri to mutane da yawa kan iya sakaya sunanka da Alhaji.
Sunan Alhaji ya bi sa har matansa da haka suke kiran shi har muma ƴaƴansa muka wayi gari da sunan a bakin mu.
Alhajinmu haifaffan ƙauyen Yashe ne. Ita kuma ƙauyen Yashe tana cikin ƙaramar hukumar kusada. Ita kuma ƙaramar hukumar kusada tana cikin yankin Jihar katsina ce. Garin kusada manoma ne da makiyaya shi ne sa'arsu da shi suka yi kuɗi har suka arzuta wasu ma. Mallam Abubakar ya kasance kafin rasuwarsa matan auransa biyu Halima(Hajiya Dubu) da Balkisu. Kuma ya rasu bayan Balkisu ta riga su gidan gaskiya. Sai ɗawaniya da nauyin komai ya koma kan Hajiya Dubu.
Kafin rasuwar Balkisu ƴa'ƴanta biyu ne kacal ta haifa sauran duk sun koma Sule da Hasiya. Sai riƙon su ya dawo hannun Hajiya Dubu da ta riƙe su tun suna kañana ba nuna bambamci. Ita Hajiya Dubu ƴaƴanta uku ne biyu maza mace ɗaya. Akwai Aminu sai Muhammad sani sai ƙaramar su Aina'u wacce ta yi aure sai ta rasu wajen haihuwa.
Sulaiman a cikin garin kusada ya gama sakandirinsa daga nan ya yi tunanin haurawa garin kano domin ya cigaba da karatunsa na boko. tun da ya samu na addinin har matsayin sauka. Lokacin ba kowa ke saka ɗan sa a karatun boko ba amman shi Sule da kansa ya kai kansa makaranta saboda ya na sha'awar karatun sosai. Ya tafi kano neman ilimi bayan ya saida gonar da ya gada a wajen mahaifiyarsu. Ashe dalilin haka Kano za ta zame masa mafaka da sillar zama abin da ya zama.
Diploma ya fara yi a can kano cikin ikon Allah kuma sai ya samu aiki a NEPA hukumar wutar lantarki na jihar Kano tun da lokacin ana iya ɗaukan masu takardan sakandiri aiki tun da tana da daraja. Samun aikin shi a wajen shi ya inganta masa rayuwa sannan gefe ɗaya ya na kiwo a gida ga Noma Aminu da Sani duk ba su yi karatu ba suna noma sannan suna kiwo. Ya auri matarsa ta farko Maimuna yar nan garin Yashe ne maƙota suke ma. Sun yi aure tun shekarunsa ba su rufe talatin ba itama ta ƴar yarinya a lokacin ta fara zama a yashe kafin ya kama mata haya a anguwa uku ya ɗauketa suka koma can suka fara gina rayuwarsu.
Farkon rayuwar ya fara ta ne da Maimuna(Gwaggo) sai dai kamar auran naTa ya zo masa da tarin buɗi. A shekarun biyun da suka yi aure ya yi noma kuma ya samu amfanin gona sannan ya saida kiwon shi ya siya wasu alherai sai bin sa suke yi da buɗe. Sannan ga albarka samun ƙaruwa ta ɗa Namiji wanda ya ci sunan kakanshi Abubakar. Bayan shi ba daɗewa ta sake haihuwan wani namiji aka sanya ma sa suna Hamza.
Maimuna na da cikin Aina'u Sulaiman ya ƙara aure da Rukayyatu yar kano ce. Sun haɗu kuma Allah ya haɗa zukatansu waje ɗaya. Ya aure ta kuma Maimuna ta karɓeta hannu bibbiyu a matsayin abokiyar zama ba kishiya ba. A ƴan'uwansa ba wanda ya yi mgana kan ƙarin auransa sai Ƙanwarsa Hasiya balle da ta ga tun bayan auran shi kenan abubuwa suka fara lalacewa ko Sulaiman ya yi noma baya samun komai sai kiwon sa da ɗaya da ɗaya suna ta kasawa wasu ma sai dai a tashi a ga gawa shi kenan Hasiya ta ce Rukayya ce da ya auro mai farar ƙafa sai da Hajiya Dubu ta tsawarta mata. Lokacin Hasiya ta yi aure anan garin Yashe amman dai Allah bai bata haihuwa da wuri ba. Ana ta raɗe raɗen wanda ta aura ne baya haihuwa kwata kwata sai da aka raba auran ta sake auran wani saurayi Hashimu shima dai kusan shekaru huɗu shuru ba wani labari.
Cikin wannan halin sai kuma a ka fara rasa wasu abubuwan na dukiya. Sai kuma aka yi ta samun ƙaruwa Gwaggo ta haifi Murja ita kuma Mama ta haifi namiji an saka masa suna Auwalu. Sai dai bai yi sati biyu ba Allah ya yi masa rasuwa.
Sun tashi daga gidansu na anguwa uku ya kama wani a gandun albasa. A can aka haifi Balki da ta ci sunan kakarmu. Sannan Mama ma ta sake haihuwan Namiji sai aka maida mishi sunan wanda ya rasu Auwal.
A yadda Gwaggo ta faɗa mana sun samu cikin mu a Gandun albasa ita da Mama amman kuma ba su haife mu a wannan gidan ba sai a gidan da Alhajinmu ya sake kama musu da ke Fagge shi ya fi girma ne sannan ga iyalai sun fara yawa. Kuma su Baba Aminu suna kawo masa ziyara ba shi da wajen safkarsu.
A yadda labari ya zo mana a bakin Gwaggo. Tsakani na da Rahila kwana arba'in ne. Rahila aka fara haifa, ni kuma sai ranar da Rahila ke cika kwana arba'in sannan aka haife ni. Ni na ci sunan Hajiya Dubu ita kuma Rahila ta ci sunan marigayiya mahaifiyar Gwaggo da ta rasu ba daɗewa a lokacin.
Tsakani na da Amina ko shekara biyu bai kai ba shekara ɗaya ne da wattani daga kuma kan Rahila Haihuwa ta tsaya ma Gwaggo. Amman Mama ta yo auta Abdulsalam ana kiran shi Datti.
A ƙiyasu mu goma ne cif a gidanmu. Ta bangaren Mama mu huɗu ne ta bangaren Gwaggo kuma su shidda ne sau zuwan Ma'u da muka zama mu goma sha ɗaya. Mun ta so cikin gata saboda Alhajinmu ya na ta samun ƙarin girma a wajen aiki sannan kuma har gobe bai daina noma da kiwo ba. A gidanmu kowa da halin shi misali kamar ni ina da tsiwa sannan ga taurin kai ina da nacin magana. Za ka ganni kamar ban san me na ke yi ba nan kuwa ina ankare da motsin kowa tun taso wata Allah ya yi ni da son jiki har suna Mama ta saka min Sadiya yar laushi. ina da sakin jiki amma ga ƴan'uwana ba ni da sakewa da mutane ba kuma tsoro ba ne kawai ni haka Allah ya halliceni ban cika son mutane ba sosai shi ya sa bayan Rahila da muka yi damben kuruciya tare ban taɓa wata ƙawa ba. Sabanin ita Rahila mai sanyi ce ga hakuri sannan tana da faram faram da mutane kuma kowa na ta ne shi ya sa in yara sun zo gidanmu tabbaci wajen Rahila suka zo ni ko mutm ya so mu saba ba na barin haka ta faru sai na janye jikina.
Kamar ta bangaren Yaya Abubakar da Yaya Hamza ne. Shi Yaya Abubakar ba shi da zafi shima dai akwai sakewa da mutane ga surutu saɓanin Yaya Hamza da bashi da wasa ƙwata ƙwata. kamar misalin Yaya Auwal ne shi kuma wannan ɗan i dont care ne. Abu goma za a yi a cikin gida bai ma san an yi ba shi fa rayuwarsa kawai yasani sai ko in ya ji yunwa ya ci abinci. Yaya Aina itama ba ruwanta ba ta da faɗa amman Yaya Murja ta fi kowa shegen shisshigi da shiga abin da ba ruwanta ga sa ido sannan ba ta da haƙuri kamar zawo ta ke. Shi ya sa ba mu taɓa shan inuwa ɗaya da ita ba ita faɗa ni kuma rashin kunya. In aka duba Amina da Datti. Gwara ma Datti ita Amina miskila ce irin Auwalu sha'ani ko an saka su aciki ma ɓata lokaci ne abu nawa zai faru a cikin gidan suna nan amman ba dai ka ji bakin su ba. Shi ya sa na ce a gidanmu kowa da irin halin da ubangiji ya yi masa dai dai gwargwado da zai zauna da mutane.
******
2000
Ɗorayi
Hajiya Dubu ce ta ƙure Radiyo ɗin ta a tsakar gida tana sauraran gidan radiyon jihar kano ana karanto labaran yammaci. Zaune take saman tabarma daga can ƙofar ɗakinta. Gwaggo na gefen ta suna jin labaran jefi jefi Mama ma dake can gefe tana tankaɗen garin masara a cikin farantani. Tana ɗan saka musu baki jefi jefi.
Ina kwance a kan gadon Hajiya Dubu har wani ƙara nitsewa ne ke yi. Ba wanda ya san ina ciki saboda gadon mai rumfa ne. Kuma san da na shigo har Hajiya Dubun ba ta sani ba. Yau alhamis ba islamiya kuma ni ce ke da girki gabaɗaya na gaji. Da rana alkubus ɗin alkama na yi gabaɗaya a gajiye na ke daman kun sani yar laushi ba na son aiki kawai ina kwance bayan na idar da sallar la'asar ina hutawa Mama ta leƙo ta ce min na fito na ɗora miya a lokacin tura baki na yi kafin na ce.
"Mama Tuwo kuma?
"E."
Haka ta faɗa tana kallona idanuwana har ya ciko da ƙwallah. Gaskiya dai na gaji kuma a ƙasa ƙasa sai da na ce na gaji Mama ta yi tsaki ta na sakin labule kafin ta ce"Ke daman ai ko kina kwance ne sai kin ce kin gaji. Malama ki taso kar dare ya yi kin kuma san Alhaji ya hana ku tuwon dare."
Na fi mintina talatin kafin na taso sai da Mama ta ƙara leƙowa tama faɗin za ta make ni. Ni kaɗai ne a ɗakin Amina ta bi su Rahila yau wata yar islamiyan mu na aure ni daman ba na zuwa biki ban je ba ina gida amman daga baya na fara nadama da na sani na bisu sai na ga wanda zai tsaya har a ce ya yi tuwon dare. Shekaru wajen biyu kenan Alhajinmu ya ce aikin gidan da ya dawo kanmu ni da Rahila da Ma'u tun da alokacin mu ne ƴan matan gidan muna cikin shekaru na sha tara ne kuma muna zangon karatu na ƙarshe a matakin babban sakandiri a makarantar GGSS ƘAWAJI dake kwanar dakata a jihar kano.
Yaya Balki ma ta yi aure shekaru wajen huɗu da suka gabata. Yanzu a gidan daga mu sai Datti da ke ajin ƙarshe a ƙaramar sakandiri sai Amina dake ƙokarin shiga matakin farko a babban sakandiri. Sai Yaya Muntari da ya dawo gidanmu da zama shekaru uku yana karatu anan FEC KANO. Sai Hajiya Dubu da Alhajinmu ya ɗauko ta bayan mun tare a sabon gidanmu dake Ɗorayi.
Domin Alhajinmu tuni likafa ta cigaba ya koma aiki da Hukumar KEDCO na jihar Kano.
Sai Yaya Abubakar da ke karatu a jami'ar Bayero yana karantar Vitnary ya na shekara ta uku ne. Sun ɗaɗe a gida shi da Yaya Hamza kafim su samu su ci jarabawar babbar sakandiri a lokacin samun jami'ar ba ta wahala cin jarabawar sakandiri ne mai wahala wajen sau uku suna sake rubutawa sannan suka ci. Shi sai ya zauna a gida nan kano shi kuma Yaya Hamza sai ya lula Sokoto Usman ɗanFodiyo University Udus. Acan ya ke karantar accounting shima yana shekara ta huɗu ne. Yaya Auwal kuma yana Nasara state University Keffi. A shekaran nan ya tafi shima.
Mun zama ƴan mata duk wani tantanin budurci ya gama bayyana mana. Alhajinmu yana da burin in mun gama sakandiri mu yi aure. Ban san dai tunanin sauran ba amman ni ba ni da burin aure yanzu sai na gama jami'a na samu aiki saboda a lokacin Alhajinmu ya samu ƙarin girma manaja ne a hukumar wutar lantarki ta jihar kaduna kuma ya samu daman ƙaro karatu tun a zamanin baya. Ni ma sai na ji ina sha'awar haka. Rahila dai na san cewa ba ta da ra'ayi mai zurfi kamar nawa, Ma'u kuma har gobe ba jituwa a tsakanimu shi ya sa ni ban san me take ciki ba. Amman shekarun sun tura da ya sa na ƙara aminta da zargina na cewa Tana son Yaya Hamza shi kuma ba ta gabansa duka ɗaya ya ke ɗaukan mu. Shi kuma Yaya Abubakar a yanayin yadda ya ke kafa kafa da Ma'u son ta yake yi ita kuma baya gabanta ni dai ina gefe ina kallon komai ina tunanin ta yadda Ma'u za ta ɓullo ma lamarin ƴan'uwa guda biyu. Amman na ci alwashin ba zan bari ta zo gidanmu ta raba mana kan yan'uwa ba na san halinta ba ta da kirki kanta kawai ta sani.
A yadda muka taso a haka muka girma. Ni da Rahila mune masu tsawon. Sai dai muna da bambamcin jiki ita Rahila ta fi ni kiɓa. Ma'u kuma muna da yanayin jiki bamu da kiɓa amman ita ba ta kai mu tsawo ba ta ɗauko tsawon mahaifiyarta ne Baaba dake can kura ta hayyaffa da wasu ƴaƴan bayan Ma'u. Amman kuma duk wanda ya ganmu ya san mu ɗin jini ɗaya ne. Ballatana ni ban cika yawo da Ma'u ba sai dai makaranta in ya zama dole a gida kuma ta shafa mini lafiya saboda ba na ƙyaleta. Sannan dawowar Hajiya Dubu gidanmu ya sa ba ma wanda ya isa ya taɓa ita da Yaya Abubakar sun sha artabu a kaina. Tun kuma da Hajiya ta dawo gidanmu na tattara kayana na koma ɗakin ta can na ke kwana sai in har na ga dama ne nake shiga ɗakin mu duk saboda kar na haɗu da Ma'u za mu kwana gida ɗaya mu tashi amman ba za mu yi ma juna mgana ba. In ko faɗa ya haɗa mu in na fara gaba da ita sai mu yi wata ba mu yi mgana ba sai in Rahila ta gaji ta kai ƙarar mu wajen Alhajinmu in ya yi mgana sai Ma'u ta ce in ta yi mini mgana ba na tanka ta. Sai a ɗora laifin a kaina amman thank god Hajiya na nan ita ce ke zama justice ɗina in dai akan Ma'u ne.
Bangaren Yaya Murja ma ba ta sauya zani ba. Ko bayan auran ta in dai za ta zo gidan da abun arziƙin da za ta kawo ma Ma'u da Rahila har da Amina ni kuma sai ta ce ba ni da kunya. Ni ma da na gane ko gidan zan iya kirga zuwana, na fi zuwa gidan Yaya Aina ko Yaya Balki in ma fitan ya kamani kenan. Har a lokacin ba ni da wata kawa da zan iya nunawa amman Rahila da Ma'u suna da ƙawayen su. Barin ma Ma'u ƙawarta din nan Shema'u har lokacin suna tare su Gwaggo duk sun santa ta na zuwa nan gida itama Ma'un ta na zuwa gidan su saboda su haɗu da Ma'u su yi ta munafunci har can dakata tare suke a makaranta. Ni dai kamar yadda ban son Ma'u itama Shema'u ban ƙaunarta domin gabaɗaya halin su ɗaya. Za mu haɗu sau goma a makaranta sannu ba ta haɗamu da Shema'u amman in ta zo gida tana mini fara'a kamar ta Allah. Na daɗe da yarda da mganar hausawa da suka ce sai hali yazo ɗaya ake abota. To akwai mugayen hallayar Shema'u da Ma'u da suke kamamceceniya.
****
Mama ta shiga madafi ta ga na ɗora miya tana tafasa ko ƙashin miyan ma da Muntari ya shigo da shi ban saka ba sannan ban ko ɗora tuwo ba. Ba ta yi mamaki ba sanin halina sai ta fito tana faɗin" Sadiya me take son zama ne ni Rukayya?
Gwaggo na zaune ta ce"Me ya faru hala?
Sai ta kaɗa kai tana nufar ɗakin mu kafin ta ce" Ba ta ko ɗora tuwo ba. Kuma miya na ta dahuwa ko ƙashin da muntari ya shigo da shi ba ta saka ba."
Lokacin ta ɗaga labulen ɗakin tana kwala min kira ina daga ɗakin Hajiya har na fara barci.
"Ba ta fa a ɗakin"
Hajiya hankalinta na wajen jin radiyonta ba ta ma jin su. Gwaggo ce ta leƙo dakin Hajiya ta na kiran sunana na ji har gyara kwanciya na yi. Ban ankara ba sai ji na yi an ɗaka mini duka a cinyata da sauri na miƙe ina sosa wajen sai na ga Mama tsaye a kaina tana huci.
Cikin tura baki na ce"Kai Mama a cinya fa kika dake ni."
"In ba ki tashi ba sai na mare ki a fuska yanzu."
Ina jin haka na yi saurin saukowa daga gadon saboda na san halinta tana da saurin hannu. Ina fitowa na ga har mangriba ta yi Gwaggo ta kalleni ta na faɗin" Sadiya ho. Ke ko koyi da ƴan'uwanki ba kya yi. Su in dai suna da aiki akan lokaci suke gamawa."
Haushin aikin dake gabana ya sa ban ko yi ma Gwaggo magana Hajiya ce ta kashe radiyon ta na faɗin" Me ya faru ne? Ke Dubu ina kallabin ki? Sai a lokacin na taɓa kaina ba ɗankwali ina tura baki na koma na ɗauko a saman gadonta da ya saɓule na ɗaura na fito dai dai Hajiya na faɗin" Dare ya yi ina su Asma'u ne? Su kama mata su yi girkin tare.'
Jin haka sai na washe baki amman sai Mama ta ce" ƙyalata ta Hajiya. In na su aikin ne tana ɗaki kwance kauda kara ba za yi musu ba. Sai su ne za a ce su yi mata na ta aikin? Sai murnata ta koma ciki sai dai Hajiya ta sake ƙwatana da ta ce"Ita ai ba yanayin su ɗaya ba. Tun da sun fita zafin nama ai ba a zauna a zama ɗaya ba."
Jin haka yasa na miƙe da karsashina saboda na san in su Rahila suka dawo sai Hajiya ta yi musu mgana sun tayani. Icce na haɗa na ɗora Tuwo Mama na ta faɗan in ina girki har jajjage ita ke yi mini kawai na fito na ɗora ina jin ƙyashi na duba har wanke wanke da sharan tsakar gida da Amina ce ke yi sai da ta yi kafin ta fita sai ni da in dai ina da aiki sai ran kowa ya ɓaci ina cikin madafi ina tura baki amman raina fes domin na samu raran kuɗin cefane Alhajimu 2k ya ba ni kayan Miya kawai na siya kashi daman yaya Muntari ya kan tura ma kuɗi in dai za a yi miya ya siyo. Kuɗin cefane ke saka ni farinciki in ranar aikina ya zagayo amman bayan haka yini na ke yi cikin baƙin ciki sai na ji gabaɗaya duk na gaji kamar mahaukaciya haka nake komawa a irin yanayin ana takata sai na yi sati ina gaba da mutum.
Ana kiran sallar mangariba su Rahila suka shigo. Gwaggo sai da ta yi musu faɗan da Alhaji ya shigo fa. Ma'u ce da yanayin mganarta ta ce" Mun taso da wuri Gwaggo rashin abun hawa ne."
Ina madafi ina talge da fitila a hannuna ba wuta. Na gama kenan na rufe na fito nepa suka kawo wuta. Miya ta isa kaɗi har na kwashe ƙashin ina fitowa Rahila ta kalleni yadda na yi kaca kaca kafin ta ce" Wai ke ba ki gama tuwon ba daman?
Wani kallon tara saura kwata na yi mata na wuce ta. Ba domin ta matsa ba sai na bangajeta. Ma'u wajen rijiya ta nufa bayan ta miƙa ma Amina Hijabinta ta kai mata cikin ɗaki wajen Hajiya na nufa ta miƙe tana kwashe tabarma tun da an kira mangariba raɗa na yi mata a kunne.
"Hajiya ga su Rahila nan."
Sai ta kalleni kafin ta juya ta na kallon Rahila wacce ke mgana da Ma'u.
"Rahila da Asma'u in kun yi sallah ku kama ma Dubu aikin nan ta gama kafin Sule ya shigo."
Rahila ta amsa da to amman Ma'u sai da ta kalleni nima na kalleta gwalo ta yi minibni kuma na ɗauke mata kai na koma kitchen. Gwara na kaɗa miyar da kaina na bar musu su ƙarisa tuwon. Sai da na kaɗa miyar na sauke sai na saka ruwan wanka ni kuma na je na yi alwala saboda ma ba na son mgana a ɗakin Hajiya na yi sallar mangariba na kuma yi zama na ƙarshenta dai Rahila da Ma'u suka ƙarisa tuwon Alhajinmu ya shigo gida bayan isha'i lokacin ina wanka a bayi daman ina ta Allah Allah na gama na fito kar ya dawo.
Ina fitowa yana tsakar gida an baza masa tabarma. Na so na yi saɗaf na shige ɗaki amman hakan bai samu ba sai da ya ganni.
"Dubu"
Dole na amsa ina kallon shi faɗa ya fara min na wankan dare wannan karon ma Hajiya ce ta fito ta ƙwace ni.
"Sule ka ƙyale yarinyar nan. Yau fa a tsaye ta yini tana aiki har daren nan gwara ta yi wanka ko ta ji daɗin barci."
Alhajinmu ya yi shuru amma Mama sai da ta ce" To ta riƙa yin aikin ta da wuri mana. Sadiya son jikinta har bani tsoro ya ke in ta yi aure ban san ya za ta yi ba "
Alhajinmu sai da ya yi dariya kafin ya ce" In ta ga ta samu ɗakin kanta za ta yi ne Rukayya. Nan saboda ta ga akwai su Asma'u ne in ba ta yi ba su za su yi."
Ni dai na samu na shige ɗakinmu tunda nan ya fi kusa ina shiga na ga Rahila da Ma'u ana ta hiran bikin da suka je. Na yi kamar ban gan su ba mai na ɗauka na shafa ina da sauran kaya a ɗakin na buɗe jakar Rahila na ɗauko wata rigata na saka kafar Ma'u na wajen da gangan na taka ta saboda na ga ita ba makauniya ba ce ta na ganina a wajen ba ta janye ba.
"Dutse kika taka hala?
A sakarce na kalleta kafin na ce"Wataƙila."
Ta yunƙuro za ta yi mgana Rahila ta hana ta da cewa" Kyale ta Ma'u. Ke kuma Sadiya don Allah ki koyi zaman lafiya."
Na kalli Rahila kafin na taɓe baki ina faɗin" Sannu yar koran gimbiya."
Haka na ke ce mata in na ga tana haƙiƙancewa akan lamarin Ma'u. Wani lokacin Rahila ba ta cika ban mamaki ba irin Yaya Abubakar bai ɗaukan lamarin Ma'u da sauƙi amman ina masa uzuri makauniyar soyayya ce ke damun shi.
Tun bayan dawowar Hajiya kano rabon mu da garin Yashe amman dai su Baba Aminu suna zuwa duba Hajiya in kuma wani sha'ani ya tashi ƙwansu da ƙwarƙwatan su. Ma'u dai ta manta da gidan tsoho ba zuwa take yi ba. Kuma ni dai ban taɓa ganin wani daga cikin dangin babanta ya zo nemanta ba. Amman tana zuwa kura wajen Baaba itama Baban na yawan zuwa kuma duk saboda Ma'un ne. In ta tashi zuwa tare da Rahila suke zuwa ni ko in yi zamana a gida ban taɓa marmarin zuwa ba. Tun da na fahimci Baaba ba ta ƙaunar uwata nima daga ita har yarta ba na som su tun ballatana da na fahimci Baaba na da son abin duniya.
Ko irin a makaranta ƙawaye an sha zama kowa na faɗin irin ra'ayin mijin da zai aura ni ba na mgana saboda ra'ayi na ya bambamta da na kowa. A lokacin maza ba sa gabana duk da an sha tare ni a hanya ban taɓa maida kai ba saboda har a lokacin ban sami irin zaɓina ba.
Rahila kuma daman na fara zargin suna soyayya da Yaya Muntari. Na daɗe ina mamakin shi so daman haka yake? Saboda Ya Muntari gajeren namiji ne kuma baki sannan yana da barkwanci ni dai ban ga abin so a wajen shi ba anawa tunanin kenan Ma'u ko an taɓa tare ta a hanya muna tare ta ce ita ta na da miji. Buɗe bakin Rahila tana dariya sai ta ce.
"Yaya Abubakar ba. Na sani kun dace kwarai Ma'u."
A lokacin Ma'u ta kasa yin gaddama amman yanayinta ya sauya ni kuma ina gefe ban ce komai ba a raina na ce maji ma gani an tura uwar amarya biko. Kuma gashi Ma'u da jinin masu kuɗi amman ba ta sauraran kowa ni dai masu cewa suna sona daga malaman islamiyamu sai na boko ita kuma Rahila gajerun maza kamar Yaya Muntari da ta sauya ma suna zuwa Yaya Muktar.
Shekara ɗaya ta shafe tuni har mun zana jarabawar fita babban sakandiri a ƙarshen shekaran 2000 sai dai dukkanmu ba wacce ta ci sai mu ka dawo zaman gida. Lokacin Yaya Abubakar da Yaya Hamza sun gama karatun su suna hidimar ƙasa. Shi Yaya Hamza can sokoto ya yi zamansa yana hidimar ƙasarsa. shi kuma Yaya Abubakar nan kano wani ƙaramin asibiti na dabbobi kuma ya gamawa suka riƙe shi duk da yana ta cewa zai ƙaro karatu shi kuma Yaya Hamza bai tsaya ba tuni ya nemi gurbin masters a University of Ibadan. Sai dai in ya zo gida hutu bai ma cika zuwa ba bai wuce a shekara sau uku haka ba.
Mun sake zana jarabawa a 2001 shima dai ba a dace ba. Ga shi su Baba Aminu sun fara mganar ya kamata Alhaji ya aurar damu. Tun da lokacin 15 16 ake aurarwa mu gamu sha tara muna shirin shi ga ta ashirin amman ba mgana ƙwaƙƙwara gwara ma Rahila mganarta da Ya Muntari ya kai gaban Alhajinmu kuma ya yi murna ƙwarai. Kowa kuma ya yaba da haɗin tunda su suka haɗa kansu. Ni ce dai haɗin ke ban dariya in ta yi ma Rahila dariya in na ga ta na rawan jiki akan Ya Muntari. To gwara shi ana son shi. Shi fa Yaya Abubakar yana yi ne amman kwata kwata kamar ba a son yana yi ba.
In da ma su Gwaggo suka fahimci yana son Ma'u bini bini sai ya je Kura gaida Baaba da ɗan siyayyan shi itama kuma ta fahimta. Magana dai ta yaɗu a tsakanimmu amman ba ta je wajen Alhaji ba. Su Yaya Murja kar a ji labari tana faɗin tuwona maina ne za'ayi ita ƙanwar ango sannan yayar Amarya. Ban taɓa tunanin Ma'u da Baaba za su iya tunanin abin da suka aikata ba. Domin Yaya Abubakar kafin ya kai mganar Ma'u wajen Alhaji ya yi magana da Gwaggo sai ta tambaye shi ko ita Ma'un tana son shi sai ya ce a'a bai bayyana mata ba sai ta ce ya nemi yardan Ma'u.
Abin da ya sa na san haka ya faru. Ranar wata asabar da daddare Yaya Abubakar ya kira Ma'u zuwa zaure na fito daga ɗakin Hajiya na gansu sun wuce shi ya sa na bi bayansu a lokacin ne na ji yana faɗa mata yana sonta ya faɗa ma Gwaggo ga abin da ta ce. Ma'u ba kunya ba tsoron Allah ta buɗe baki ta ce ma Yaya Abubakar ya yi haƙuri ita a matsayin yaya ta ɗauke shi ba da wani manufa ba tun da aka kawo ta gidan nan Yaya Hamza ta ke so. Ina laɓe ina ganin har duƙa mata ya yi amman Ma'u ta fara kukan munafunci sai ya ce shikenan saboda ita muguwa ce sai ta ce wai ya taimaka ya rufe mganar ba ta so Alhajinmu ya ji shi kuma ya ɗau alƙwarin ba wanda zai ji Gwaggo ma zai san abin da zai faɗa mata.
Kafin ta taho na shige ɗakin Hajiya ina maida numfashi ta na kwace sai da ta ce" Dubu lafiya?
Ina sauke numfashi na ce" Ba komai Hajiya."
Ranar ko barci ban yi ba ina tunanin mafita ko da ba shiri tsakanina da Yaya Abubakar jinina ne. Na ji tausayin shi da ya sa na fara tunanin yadda zan ɓullo ma lamarin. Washegari na je gaida Alhaji sai ga Ma'u bayan sun gaisa ta ce wai in Alhaji ya bar ta za ta je kura wajen Baaba.
Ina jin haka na ji a raina akan Yaya Abubakar ne. Saboda lokacin wayar hannu ba ta daɗe da shigowa ba sai wane da wane Alhajinmu kaɗai ya mallaketa. Ina jin sanda ya ce shikenan sai ta shirya cikin ni ko Rahila wata ta rakata ina jin haka na yi karaf na ce" Alhajinmu ni zan rakata."
Ba Ma'u ba har Alhajinmu sai da ya yi mamaki. Ma'u kam sake baki tayi kawai tana kallona.
"Lalle Hasiya na da babbar baƙuwa."
Haka Alhajinmu ya faɗa ni ai ban tsaya ba na koma ɗakin Hajiya ina haɗa kayana Hajiya ta ce lafiya na ke haɗa kayana.?
"Ma'u zan raka kura wajen Baaba."
Da mamaki Hajiya ta kalleni ba ta da wani karfi kwana biyun nan ba ta da lafiya ta na fama da zazzaɓi sai da aka kaita ma asibiti. Maida kanta ta yi ta kwanta lokaci ɗaya ta na faɗin" Yau kuma? To Allah ya tsare."
Kowa ya ji zan raka Ma'u sai ya yi mamaki har Rahila sai da ta ce"Allah ya sa Sadiya kin sauya kenan."
Ni ba na ta kanta ni na san abin da zai kai ni.
Ma'u ba ta da yarda za ta yi ta na ji ta na gani na shirya kayana Alhajinmu ya bamu kuɗin mota mun bar gidan ba ma mu haɗu da Yaya Abubakar bawan Allah shi kaɗai ya san abin da ke damunsa.
Har muka isa kura sannu ba ta haɗamu da Ma'u ba. Mun isa gidan Baaba ita kanta ta yi mamakin ganin mu tana da abokiyar zama. Zaman dai ba wani daɗi ita kanta ta yi mamakin ganina tare da Ma'u cikin mamaki ta ce" Yau kuma wannan ce ina Rahilan?
Ma'u ce ta amsa da cewa ni ce na rakota wannan karon.
Duk da ban samu tarban da ya kamata ba ban damu ba Zainab ce kawai ƙanwarta ta kulani duk da ta na ƙarana ne sai sauran ƙannenta maza. Bayan mun yi salla mun ci abinci Ma'u na son keɓewa da Baaba amman ba hali tun da na hana ina wajen. Sai daddare sun ɗauka na yi barci suka ƙule cikin ɗaki ba su san ina kwance laɓo ina dakon su ba. Ina ganin sun shige ciki nima na tashi saɗaf saɗaf na laɓe ta jikin labule a daga nan na ke jiyo muryan Baaba ƙasa ƙasa.
"Shi wai Abubakar ɗin ya ce ya na sonki?
Ma'u ta ɗaga kai cikin damuwa saboda ina hangosu ta jikin labulen ƙurwan ɗakin
Sai kawai Baaba tayi tsaki kafin ta ce" Shi ma dai da rigima ya ke. Ai ke matar manya ce duk da ban raina Abubakar ba. Sai dai tunda Hamza kike so shi ne zaɓina kuma ba kin ce yana can yana cigaba da karatu ba? Nan gaba Allah kaɗai ya san abin da zai zama."
Ma'u ta kalli Baaba kafin ya ce" Baaba ya zan yi? Har fa ya faɗa ma Gwaggo. Kuma su ma yan gidan sun fara gane yana so na ba na so Alhaji ya ji labari Yaya Abubakar ya yi min katanga da abin da na ke so.'
Baaba ta kama hannun ta lokaci ɗaya tana faɗin" Kwantar da hankalin ki. Gobe da safe ku koma gida ni kuma cikin satin nan zan shigo. Da ikon Allah ke rabon Hamza ce."
Sauri na yi na koma wajen kwanciya a falo a saman katifa na yi kamar mai barci sai can bayan wani lokaci Ma'u ta fito ta dawo ta kwanta a gefena. Ta kwana mutsu mutsu nima haka a cikin raina ina tunanin ta wata hanya zan hana Baaba aiwatar da kudirinta?
Har muka koma kano ban samu mafita ba. mun koma mun iske Yaya Abubakar na kwance ba lafiya daga ni sai Ma'u muka san dalilin ciwon shi. Zazzabi da ciwon kai har dai da Yaya Muntari ya raka shi asibiti ya ga likita. Na ɗauka Ma'u za ta tausaya masa amman sai na ga kamar ba ta da tausayi ban samu mafita ba har Baaba ta zo gida ta kuma tara su Alhajinmu ta kawo mganar Ma'u tana son Hamza tun tuni ganin abin na gida ne yasa ta zo da mganar Alhajinmu na jin haka ya fara murna ya ce kuma zai aurama Ma'u wanda ta ke so. Gwaggo ta na so ta yi mgana amman Baaba ta san me za ta ce sai ta datse ta. Bayan an gama zaman a ɗaki Hajiya Dubu ke faɗa mini abin da ke tafe da Baaba. Daman na san za a rina. Ma'u na so ta haɗa mana yaƙi a gida Yaya na sonta ita kuma tana son ƙani.
Cikin lokaci kawai na ji ana mganar haɗa auran Yaya Hamza da Ma'u da kuma Rahila da Muntari. Yaya Abubukar kuma Alhajinmu ya ce fito da matar aure. Ba shi da mafita illah ya amsa Gwaggo ta so ta yi magana sai na ji sa yana roƙonta ta bar mganar shi da Hamza duk abu ɗaya ne. Kowa ya ji ba Yaya Abubakar ba ne sai ya yi mamaki saboda shi dai Yaya Hamza kowa ya san halin shi. Shi kuma Umarni kawai Alhaji ya bashi, shi kuma bashi da mafita. Amman kwata kwata bai taɓa hasaso da ya auri Ma'u ba. Da farko da aka sanya lokaci na yarda makaman yaƙina ganin har Alhajinmu ya ba ma Yaya Hamza umarnin dawowa gida ya ga Ma'u ya kuma dawo sun gana Ma'u ta yi ta rawan jiki ita a dole burinta ya cika. Sai dai me Yaya Abubakar ya kasa ɗaukan takwallalin ya haƙura da Ma'u ya fara rama a tsaye ga yawan ciwo ina tsoro kar rashin tausayin Ma'u ya kashe min ɗan uwan na yi ta kulla yadda zan yi na rasa mafita.
A wannan halin an saka ranar auran su da zaran mun ƙara zana jarabawar sakandiri a karo na uku. Yaya Muntari ya samu aiki da wani kamfanin sarrafa leda. Shi kuma Yaya Hamza ya fara aiki da bankin first bank a can ibadan ɗin. Ni ba kaina na damu dashi ba saboda ban samu miji ba daman kuma ni burina sai na gama jami'a zan yi aure.
Muna gabda gama zana jarabawarmu kawai Yaya Abubakar ya fara wani ciwo har da kwanciya a gadon asibiti ganin haka yasa na ce ba zan bari Ma'u ta kashe mini ɗan'uwa.
Ni na je na samu Hajiya Dubu na faɗa mata duk abin da na sani. Ita kuma ta samu Alhajinmu ta faɗa masa abinda ke faruwa ni na ba da shaidar Gwaggo ma ta sani da aka kirata sai ta amsa amman ta ce Abubakar ɗin ya ce a bar mganar kar kowa ya sani kuma itama tana ta tabbacin ciwon nan saboda Ma'u ne. Alhajinmu bai yanke hukunci ba sai aka sallamo Yaya Abubakar daga asibiti Alhajinmu ya taramu a gaban kowa da kowa har da masu auran da Yaya Hamza da Alhaji ya sa ya dawo garin.
A gaban kowa da kowa ya tsitsiye Yaya Abubakar sai da ya faɗi gaskiyan yana son Ma'u duk yadda ta yi ta masa inkiya da ido kar ya faɗa. Har Baaba an kirata tana wajen jin haka shima Yaya Hamza ya ce ya bar ma ɗan uwansa shi daman baya sonta.
Hankalin Ma'u da Baba ya tashi saboda Alhajinmu ya ce an maida auran Ma'u akan Yaya Abubakar kuma ya yi ta faɗan cewa ba domin na zo na faɗa ba da an yi auren kuma azo ana neman mafita. Ban manta kallon da Ma'u ta yi mini a wannan lokacin ita da Baaba. A kuma nan take ta fashe da kuka ta ce ba ta son Yaya Abubakar Yaya Hamza take so shi kuma ya ce a ƙanwa ya ɗauketa. Alhaji ya rasa mafita yace zai yi mgana da sauran yan uwanshi. Har sai da su Baba Aminu su ka zo garin. A ɗakin Hajiya suka zazzauna suka tattauna Hajiya Dubu saboda samar da masahala sai ta kalli Alhaji kafin ta ce
"Sule a shawarata kar ka matsa ma Ma'u ko Hamza. Tun da Hamza ya ce baya so. Abubakar ma yace ya hakura da ita to mu fasa wannan al'amarin kowanensu ya nemo mata itama ta nemo nata mijin mu aura musu sai na ke ganin kamar in muka yi haka za a samu mafita."
Su Baba Aminu ma sun aminta da shawaran Hajiya kuma ita Alhaji ya ɗauka aka warware mganar auran Ma'u da Yaya Hamza har da Yaya Abubakar ɗin bayan an ce kowannen su ya zaɓo na shi matar daga waje. Wannan lamarin shi ya ƙara rura wutar kiyayya tsakani da Asma'u.
Kwana biyu da faruwan lamarin na samu salama saboda ko banza itama ba ta samu abin da take so ba. Sannan Yaya Abubakar ba zai ga laifin Yaya Hamza ba. Ina kwance a saman gadon Hajiya ba ta ɗakin tana makewayi Ma'u ta shigo har ɗakin ta tsaya a kaina.
"Lafiya Ma'u?
Idanuwanta jajir ta kalleni kafin ta fara mgana cikin zafi."
"Wallahi na tsane ki Sadiya. Na tsane ki."
Nima kai tsaye na ce" To ai nima ba sonki nake yi ba Ma'u."
Sai kawai ta nuna ni da yatsa kafin ta ce" Tun da kika zama silan rasa burina Sadiya ina so ki rubuta ki ijiye na rantse da sarkin da ke busamin numfashi sai na kuntata ma rayuwarki sai na saka ki a uku fiye da yadda kika sakani ko kin samu farinciki sai na yi sanadiyar lalatashi zuwa baƙin ciki. Kamar yadda na saba cin nasara akanki haka zan cigaba da nasara akanki har ƙarshen rayuwarki.".
Kai tsaye nima na kalleta kafin na ce"To in kin fasa. Ta Allah ba ta ki ba. Aniyar ki sai dai ta biki. Kuma ban yi nadaman abin da na yi ba. Da ki ɓata mana zuru'a gwara ke ki rasa na ki burin na zalunci."
Sai kawai ta yi kwafa ta fice a ƙofar ɗaki suka haɗu da Hajiya tana kiran sunanta ta yi banza ta wuce da ta shigo sai ta tambaye ni ko mun yi faɗa da Ma'u ne? Ina komawa na kwanta na ce" Ni ina ruwana da ita."
Hajiya na faɗin" Sai hakuri ki rika kyaleta yanzu kin san ga abin da ya faru.'
Ina jinta ban tanka ba.
Tun faruwan lamarin bayan wani lokaci Ma'u ta warware Yaya Abubakar ɗin ma da sauƙi. Ta nuna ma kowa ba komai amman ni nasan ba ta hakura ba. Tsakanina da ita sai ya ƙara lalacewa. Ko da yaushe in ta fakaici idon mutane sai ta gaya min mgana nima sai na rama haka dai muka yi rayu cikin bata sona nima bana sonta. Jarabawar mu ta fito cikin ikon Allah ni da Ma'u muka samu ban da Rahila ba ta damu ba tunda aure za ta yi ni kuma ina ta murna zan fara jami' a.
Alhajinmu ya so ya hana Yaya Hamza ya matsa masa aka nema min gurbin karatu a jami'ar bayero a shashen tsumi da tattalin kasa economics. Ma'u kuma ta ce bording za ta yi sai aka nema mata Federal University Minna ko na ce ita ta nuna tana bukatar can ɗin.
Saboda lamarin da ya faru bikin Rahila da Yaya Muntari ba a ma ƙara mganar shi ba sai zuwa gaba in zukata sun huta.
Yaya Auwal kuma yana can keffi sai salla sallah ma ya ke zuwa ganin gida wani abun ma sai dai ya ji labari bai san faruwan shi ba.
Na fara zuwa jami' a farkon shekaran 2002. Ma'u ma a shekaran ta tattara ta tafi Rahila kuma tana gida amman auran su da yaya Muntari ana tunanin karshen shekara tun da shima ya cigaba da karatunsa.
A kuma lokacin ne Allah ya yi ma Hajiya Dubu rasuwa. Rasuwan da ta gigitani matuka. Na yi kuka domin har daren da za ta rasu mun kusa raba dare muna hira sai dai mun wayi gari ba ta raye tabbas ni aka yi ma mutuwa. Rasuwar Hajiya dubu da wattani uku lokacin muna jarabawar semester farko a makaranta na haɗu da Yusuf Muhammad Inuwa(Tafida) kuma mun yi aure da shi a ƙarshen shekaran 2002 rana ɗaya aka yi bikin mu tare da Rahila da Yaya Muntari. Kuma ana saura kwana talatin da biyar auran mu Allah ya yi ma Mama rasuwa daga kwanciya barcu ciwon ciki dare zuwa asuba ta ce ga garin ku nan.
Janafty