Free chapter · Read without an account

ƳAR KARUWA Chapter 23

by Aysha Ɗansabo · ƳAR KARUWA PART 1

Arewabook@ayshadansabo

Paid book

***

©️ Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻

Chapter 23

Yana komawa ɗakinsa yakai zaune bisa sofa ya dafe kansa da ya fara masa ciwo sakamakon faɗan da Momy ta dinga ɗaga murya tana yi masa,zazzafar huci ya fitar yana sake jin yadda zauciyarsa ke sake matsewa da wani irin yanayin da bazai iya misaltawa ba.Wayarsa dake aje saman mirrow ne ya fara kukan neman ɗauki,ya mike a nutse ya isa wajen ya ɗauki wayar idanunsa na sauka akan sunan Abbah.A nutse yayi receiving call ɗin tare da saka wayar a handsfree ya koma wajen sofar ya zauna,gaida Abbah yayi cike da ladabi muryarsa a matuƙar sanyaye.Hakan yasa Abbah fahimtar cewa Ammar Chiroma na cikin damuwa,domin yafi kowa karantar halayyarsa kakaf."Ammar what's wrong with you?" Abbah ya tambaya cikin harshen nasara yana sauraran jin amsar da Ammar Chiroma zai bashi.Tamkar bazai ce komi ba sai kuma ya buɗe baki yace,"Abbah Mamie." Abbah ya saki murmushi tamkar Ammar na gabansa kafin ya furta,"Me Mamie tayi ma Yaron Abbah?" Ammar Chiroma ya saki murmushin da iya fatar bakinsa kaɗai ya tsaya yana jin sanyi na sauka a cikin zuciyarsa domin ya sani Abbah yafi kowa iya karantarsa da yadda yake bi dashi,cike da narke murya yace,"Abbah na ƙosa su koma 9ja,bana son wannan ziyarar tunda ba ita kaɗai ta taho ba,please Abbah call her kace su koma wallahi kullum cikin yimin faɗa take akan wancan Yarinyar." Ya dakata da kalamansa kansa na sake masa ciwo domin ya tsani yawan magana shiyasa bai iya doguwar hira a waya sosai ba,idan har bada Abbah bane ko Hajiya Inna da suka fi kowa sanin lagonsa da suke jan ra'ayinsa har yayi surutun da bai shirya yi musu ba.Yana jiyo yadda Abbah ke dariya sosai kafin ya tsaida dariyar yace,"Son meyasa za ka ƙosa su dawo alhali ta kawo maka ɗiyar Barirah ne ku fahimci juna,inace kaida bakinka kace ka amince da Labibar yanzu ko?" Ammar kamar zai saki kuka haka yake ji,cikin raunin murya yace,"Abbah bani da zaɓin daya wuce yin hakan ne,but still i don't like her Abbah,don Allah su taho hakanan ni ko auren za a yi bazan taho ba." Abbah yace cikin sauri,"Ai kuma baka isa ba Ammar,dole ka zo ayi biki na al'adah tare dana ƴan ƙannenka,abinda yasa na kira ma shine Jannat keso a kwashi ribar data samu na wannan shekarar cikin dukiyar gadonta a gina masallaci wa Marigayi Kabeeru domin ladan ya dinga cin masa,Ammar na jima banga Yarinya mai hankali da nutsuwar Mamana ba,na daɗe banga Yarinya mai ƙarancin shekaru da ƙuruciya wacce take da zurfin tunani da hangen nesa irin Mamana ba,a yau ta sake birgeni har sai dana share hawayen farin ciki da yin alfaharin samun ɗiya kamarta,kadai ga ko saninsa batai ba,bata tashi tare da shi tasan daɗinsa ba,amma har tayi zurfin tunanin data ga yakamata a ɗibi wani abu cikin dukiyar da yabar mata a gina masa ɗakin Allah,tabbas wannan abin farin ciki da yin alfahari ne,tabbas Kabeeru yabar ɗiya ta gari wacce bazai gushe yana alfahari da ita ba yana kwance a ƙarƙashin ƙasa,yanzu abinda nake so shine ka zauna kayi mana zane mai kyau daya amsa sunansa zane,zane irin wanda idan aka ginashi a tsaye zai zama abin kallo da kwatance,ni kuma zan zuba dukiyarta na haɗa da nawa kason wajen tabbatar da cewa an gina shi a yadda yake ba tare da jin ƙwanjin nawa za a kashe ba." Abbah ya ƙare maganar yana jin sautin ajiyar zuciyar da Ammar Chiroma ya sauke.Shuru ya ratsa a tsakaninsu tamkar Ammar baya bisa line ɗin,zuwa can yace cikin sanyin murya,"Zan yi Abbah In Sha Allah! But a ina ne za a gina Masjid ɗin?"Abbah yace kai tsaye a wani ƙauye ne kafin a shigo cikin garin Jos,suna da buƙatar a gina musu babban masallaci har ma dasu Bohol." Ammar yace kansa tsaye,"Abbah nima zan saka nawa kason,sannan a duba sauran masallatan da suke da buƙatar gyara a cikin gari a faɗa mini zan aiko kuɗi duk ayi wannan aikin." Abbah yace cike da farin ciki,"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Na gode da samun ɗiya kamar Jannat data zamo silar fargar da ɗan uwanta irin ayyukan alkhairan da suka kamata ace kana yi ba tara kadarorin da za mu tafi mubar su ba,tabbas naji daɗi Ammar Allah yayi muku albarka." Ammar Chiroma ya haɗiye wani abu kafin yace cikin low voice ɗinsa,"Ameen Abbah thank you." Daga haka suka cigaba da tattauna wasu mihimman lamura kafin suyi sallama da juna.Ammar ya aje wayarsa yana mai jingina jikinsa da jikin sofar tare da lumshe idanunsa,ya rasa me yake ji a cikin zuciyarsa game da wannan labarin da Abbah ya kawo masa.Sake lumshe idanunsa yayi yana hasko Yarinyar da kuma ƙarancin shekarunta yana tuno fuskar Mahaifinta wanda ya nuna masa ƙauna tamkar shine ya kawosa duniya,wani abu mai nauyi ya sake danne zuciyarsa domin duk lokacin dazai tuno da Abbah Kabeeru sai ya ji ɗacin mutuwarsa ya sake mamaye zuciyarsa."Good gal!" Ya furta cikin wani irin zuzzurfar sauti ba tare da yasan cewa a fili ya furta kalamansa ba.Daga can ƙasan zuciyarsa ya dinga tambayar kansa dama akwai mata masu ƙaranci shekaru kamar su Arfah dake da irin wannan hangen nesan da zurfi tunani irin haka? Tabbas maganar da Abbah yayi ya doki zuciyarsa domin abu ne da ya kamata shine ya fara yin irin wannan tunanin nayin wani abin alkhairin da zai iya sadaukar dashi zuwa ga Abban domin lada ya riƙa kai masa sai gashi ƙaramar Yarinya ta fishi tunani da hangen nesa.Wani irin abu mai kama da jin zafi da kishi ya soki zuciyarsa a lokaci guda,yaja ƙaramin tsaki yana sake jin yadda sam baya son tuna koda face ɗinta sabida ko kaɗan baya son duk wani abu daya raɓi Nuratu.Ya jima yana kokawa da zuciyarsa akan lamura da dama kafin ya tashi ya nufi toilet domin ɗauro alwala,koda ya fito wajen sallaya ya nufi domin gabatar da shafa'i da wutri da baya yinsu sai yazo kwanciya bacci.Yana idarwa ya kashe hasken ɗakin ya nufi saman bed,bed side lamp ya kunna ya ɗakko kyakkyawar zanensa yana shafawa tamkar mai shafa jikin ɗiya macen da yake tsananin buƙatar kasancewa tare da ita.Idanunsa suka lumshe yana jin yadda wani irin feeling ke sake cika zuciyarsa,cikin wani irin sanyi ya kai bakinsa ya sumbaci fuskar zanen yana sake jin wani irin zazzafar yanayi na sake bin jinin jikinsa.Ya jima sosai rungume da frame ɗin bisa ƙirjinsa har bacci ya fara fisgar idanunsa,hakan ya sanya shi tashi a nutse ya maida frame ɗin ya aje a wajen zamansa bayan yakai baki ya sake sumbatar hoton.

Koda ya koma ya kwanta bai jima ba bacci yayi nasarar sacesa,bai kuma farka ba sai ƙarfe shida na safe agogon can.A gaggauce ya nufi toilet ya ɗauro alwala ya gabatar da sallar asuba,koda ya idar ya jima a zaune yana azkar kafin ya rufe da karatun Qur'ani.Tashi yayi ya koma bakin bed ɗinsa tare da ɗaukar wayarsa ya duba wasu saƙwanni,aje wayar yayi ya nufi wajen laptop ɗinsa da yake aiki da ita a gida.Nan bakin gadon ya dawo ya zauna yana mai aje laptop ɗin bisa saman bed ɗin,buɗeta yayi ya fara ƙoƙarin saita komi domin tsara yanayin yadda zanen ginin masallacin da sukai zancen da Abbah yake son farawa kafin ya fita office.Sai da time ya buga 7:30am sannan ya tashi ya nufi toilet domin yin wanka,ya fito sanye da rigar wanka kalar sky blue daya haske dark skin ɗinsa.A cikin nutsuwarsa ya gama shafa mansa yayi shirin fita office cikin wasu haɗaɗɗun suite brown colour,yayi kyau har ya gaji ga wani irin kwarjini dake haskawa a saman face ɗinsa mai matuƙar dukan zuciya.Wayoyinsa ya kwasa ya fito daga ɗakinsa yana kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa dake buga ƙarfe 8:30am na safiya,shuru yaji babu alamun motsin kowa daga cikin su Mamie.Ba ƙaramin daɗi hakan yayi masa ba domin bayi ƙaunar ganin gilmawar Yarinyar a cikin idanunsa,ATM card ɗinsa da zai basu suyi amfani dashi ya aje musu saman center table dake tsakiyar falon yadda idanunsu zai fi saurin kaiwa nan,ya juya ya fito daga gidan yana ƙoƙarin saka kiran Nawaf domin ya sanar dashi cewa zaizo ya fita dasu Mamie yawon buɗe idanu da yin shopping.Nawaf asalinsa ɗan Nigeria ne,ya fito ne daga jihar Maiduguri karatu ne ya fara kawosa ƙasar Turkey sai kuma yana haɗawa da yin wasu jobs ɗin domin samun kuɗin rufawa kai asiri kasancewar Iyayensa masu ƙaramin ƙarfi ne.Karatun ma wani maƙwafcinsu ne acan gida Maiduguri yayi masa hanya ya samu scorlarship ya taho,shiyasa ko bayan daya kammala degree ɗinsa ya koma gida yayi service sai ya sake neman hanyar da yayi ya dawo ƙasar ya samu aikin da yake yi yana samun kuɗin ɗaukar ɗawainiyar Iyayensa.Ya taɓa yiwa Ammar Chiroma aikin gyaran gida dayi masa aike zuwa kasuwa da sauran hidimar gida yana biyansa,daga baya ne bayan kammala karatunsa ya koma gida Maiduguri suka rabu.Lokacin daya dawo ma Ammar ɗin shine yayi hanyar daya samu aiki a wani ƙaramin company na sarrafa takalma ya fara aiki dasu,aikin ba full time yake yi ba yana zuwa ne sau uku kawai a sati.Shiyasa yake da time ɗin gudanar da wasu jobs ɗin da ake iya biyansa a yini ko sati,ya danganta da lokacin daya zaɓa a biya shi hakkinsa dai.Sun saba da A.Chiroma sosai domin a mafiya yawan lokuta shike zuwa ya fita dashi wasu wuraren a ranakun weekend idan baya jin yin driving,shiyasa a yanzu dasu Mamie ke da buƙatar mai zagawa dasu ya zaɓi ya haɗasu da Nawaf ɗin wanda babu wani wajen buɗe ido Ko shopping malls dabai sani a ciki da wajen INSTANBUL ɗin ba.Bugu biyu ya samu Nawaf ɗin ya ɗaga wayarsa ya sanar dashi buƙatarsa tare da tambayarsa ko yana da aiki yau ɗin? Nawaf ɗin ne ya bashi tabbacin yau yana free zai samu damar fita dasu a yau zuwa jibi domin gobe akwai jobs ɗin da yake dashi bazai sama time ba.Godiya sosai Ammar yayi masa kafin ya kashe wayarsa ya nufi wajen motarsa,a nutse cike da ƙwarewa a iya driving ya murza kan motarsa ya fice daga gidan zuwa wajen aikinsa.A can yayi breakfast ɗinsa domin yayi sabo da hakan baya iya tsayawa yayi ma kansa abin kari kafin ya fita office,sai yazo office ɗin yake yin breakfast a mafiya yawan lokuta.

Su Mamie kuwa ya fita baifi da mintuna talatin ba suka tashi daga bacci,itace ta fara tashi kafin ta tashi Labibah.Wanka Mamie ta fara yi ta kintsa kanta kafin Labibah ta iya barin bed ɗin ta nufi toilet,wankan ta sallo itama ta fito sanye da rigar wanka pink da kalar ya haske farar fatarta sosai.Wajen dresser ta nufa tayi shafa kafin ta wadata jikinta da ƙamshi,wajen kayansu ta nufa ta zaro straight english gown ta saka.Sosai rigar tayi mata kyau tare da zama a jikinta,shape ɗinta ya fita sosai kasancewar yadda rigar tabi jikinta sosai.Jelunan kitson Calaba da aka mata yasha ƙarin gashi su ta kame ta ɗauresu da babban ribbon,ta ɗauki wani ƙaramin veil daya shiga da kalar red straight gown ɗin jikinta ta naɗa wani irin ɗauri irin nasu na ƴan matan zamani da suka san kan gayu.Sake bin jikinta tayi da turarenta mai sanyin ƙamshi,ta isa wajen data aje wayarta ta ɗauka tayo falo.

Kitchen ta nufa direct don tasan Mamie nacan tana ƙoƙarin haɗa abinda za su yi breakfast,duk idan tazo ƙasar bata yadda da siyan abinci ba matuƙar ba fita sukai yawon shaƙawa su tsaya suci a waje ba.Amma kamar dai abincin breakfast zuwa dinner tafi gane tayi musu da kanta,sai dai idan da Abbah suka zo sukai masauki a hotel shine kaɗai suke ordering abinci har su bar ƙasar.Custard ta dama musu ta soya dankali da egg,sai ta ɗebi catfish ɗin Ammar dake cikin freezer ta ragargazu tayi musu veggies sauce dashi.Duk kitchen ɗin ƙamshi ya ɗauka hakan yasa time ɗin da Labibah ta shigo har wani lumshe idanu tayi tana yaba iya girkin Mamie,domin tasan tafi Momynta nesa ba kusa ba indai a fagen ɗaura sanwa ne."Mamie sannu da aiki aida kin jira nazo na dama custard ɗin ma." Mamie ta saki murmushi tana duban shigar dake jikin Labibah daya bayyana shape ɗinta ƙarara,tace cike da kulawa,"Ai babu yawa aikin daughter,oya tayani dai da ɗaukar kulas ɗin zuwa dining." Labibah ta kwashe kulolin da Mamie ta shirya a saman babban tray ta fito ta nufi ɓangaren dining,aje wa tayi ƙamshin chips sauce ɗin na sake bugun hancinta.Mamie bata fito daga kitchen ɗin ba saida ta gyara komi tsaf don tafi kowa sanin halin Ammar Chiroma baya shiri da ƙazanta ko rashin gyaran muhalli,koda ta isa dining area ɗin ta tadda har Labibah tayi serving kanta ta fara ci."Miƙo min wayata na kira Ammar daughter,dama haka yake fita baiyi breakfast ba akan me?"Cewar Mamie kenan tana miƙawa Labibah hannu alamun ta bata wayarta dake aje kusa da Labibah sosai.Labibah ta miƙa mata wayar tana faɗin,"May be yaga ya kusa yin late ne Mamie." Mamie taja tsaki tana saka kiran nasa domin ita gaba ɗaya bata so ya fita bata ganshi bane,bugu biyu ya ɗaga wayar cikin wannan cool voice ɗin nasa ya fara gaida Mamie.Ta amsa a gajarce tana zarcewa da faɗin,"Duk sabida gujema zama kayi breakfast tare damu yasa za ka fita baka karya ba Ammar?Meyasa baka tadani kafin ka wuce na sama maka abinda za ka yi breakfast dashi ba?Sannan ina card ɗin da muka rabu za ka bani sabida fita shopping?" Duk ta jerawa Ammar Chiroma tarin tambayoyin tana sauraron amsar da zai bata.Shi kuwa cikin sake ƙasa da muryarsa yace,"Mamie karki damu yanzu na gama yin breakfast dana taho nan,maganan ATM card kuwa yana saman table dake falo,Nawaf zai zo da zaran kun kammala shirin fitan,so just call me idan kun shirya Mamie ni kuma zan turosa." Mamie ta ja tsaki tace,"Okey ka kyauta,zan kira idan mun kammala,sannan idan ka tashi daga office ɗin saura kace ka sake wucewa hotel kaga yadda zan ɓata maka rai tunda naga rainin wayon naka ya fara yawa Ammar,ina so ka kaini gidan Malaminka domin bana ji zamu wuce 3 days nan gaba bamu koma inda muka fito ba tunda sam baka yi farin ciki da wannan ziyarar dana kawo maka ba." Mamie ta ƙare maganar cike da mita tana jin zafin yadda Ammar Chiroma ko kaɗan ya nuna baiyi farin ciki da tahowarta tare da Labibah ba,haƙuri kawai Ammar ke baiwa Mamie domin shi ya rasama ina zai sanya kansa sabida rigimar Mamien.

Kashe wayarta tayi tana jan ƙaramin tsaki tare da aje ganinta akan Labibah data gama jin wayar da sukai domin a handsfree Mamie ta sanya wayar,"Labibah idan kin Kammala karin ina ga sai muyi shirin fita ɗin ko?" Labibah ta saki murmushi tace,"Okey Mamie aini na kammala shiri bag kawai zan ɗauka na saka shoe mu wuce idan Nawaf ɗin ya zo."Mamie ta sake duban shigar dake jikin Labibah tace,"Amma daughter ai ko kimono kya ɗaura akan wannan shigar ki rufe surarki,gaskiya Ammar ba zai ji daɗi ba idan muka dawo muka tadda shi a gida yaga cewa da wannan rigar kika fita kuma babu ko mayafi,at least ki saka kimono ko ki sauya kayan marasa nauyi daga ciki sai kiyi shigar Abaya hakan ma zaifi."Mamie ta ƙare maganar cike da tsare gida domin itama ta fara jin haushin kalolin shigar rashin mutunci da Labibah keyi tunda suka taho ƙasar, sabida babu kaya kala ɗaya data ga alamar ta taho dasu na shigar mutunci sai ƙananun kaya na fitsara da bayyana sura.Hatta da kayan baccin da take sakawa tasan cewa basu dace ba,domin sunfi dacewa da kayan bacci na masu aure bawai budurwa mara miji ba."Mamie kimonon dai domin ban taho da Abaya ko ɗaya ba." Cewar Labibah tana faman ɓata face.Cike da takaici Mamie tace,"Aiko yau za ki sayesu indai Abayas ne ai ƙasarsu kika zo domin akwai shagunan saidasu burjik haɗaɗɗu kuma na gaske." Labibah baki kawai ta taɓe ba tare data sake cewa komi ba ta mike tsam tabar wajen domin ta gama cinye chips ɗin tas da Custard ɗin data zuba.Bayanta Mamie tabi da kallo tana sake ganin yadda shape ɗin mazaunanta suka bayyana har ana ganin shatin pant ɗin dake jikinta sabida yadda rigar tabi jikinta sosai ta lafe,ta ja ƙaramin tsaki tana saka kiran Ammar Chiroma ta sanar dashi cewa sun gama ya turo Nawaf ɗin kawai su fita.

*******

KADUNA

Ƙarfe goma da mintuna sha biyar Jannat ta isa skull cikin motar Feenah,ita kaɗai keda lacture yau Feenah bata da class sai gobe.

A nutse ta fito daga cikin motar bayan ta kammala yin parking ta kashe motar,sanye take da dogon hijab daya rufe jikinta ruf ya ɓoye shigar dake jikinta na pitted gown daya kama jikinta.

Niƙab ɗinta ta sake shi ya rufe face ɗinta ta rufe motar bayan ta nufi hanyar isa lacture hall ɗin,ta samu har Lacturer ɗin nasu ya iso Allah yasa kusan a tare suka shiga cikin ɗakin karatun da bazai taɓa bari ta shiga ba domin ba mutunci ne dashi ba.Kamar yadda ya sanar cewa test zaiyi hakan ne ya kasance,lacture ɗin awa guda yayi musu ya bada sanarwa cewa test zai yi a ragowar 1 hour ɗin daya yayi masa saura.Ko a jikin su Jannat domin su a shirye suke koda yaushe sabida indai brain ne Allah ya riga ya basu,shiyasa a nutse suke sosai basu da wata fargaba domin suna da tabbacin ko wani irin question ya yanka ba za su garara amsawa ba.Cikin mintuna sha biyar Jannat ta kammala ta zauna tana jiran a fara submitting test ɗin,yana bada dama kuwa ita ce farkon tashi tayi submitting tare da yin signing attendance ta fito daga hall ɗin.Agogon hannunta ta kalla domin duba time,ganin sha biyu har da rabi ya sanya ta nufi isa wajen motar Feenah domin wucewa gida.Har ta buɗe murfin motar za ta shiga su Aysha suka ƙariso suna mata tsiyar cewa saurin me take yi haka? Jannat ta ɗan narke face tana kai hannu ta cire niƙab ɗinta ta cillashi cikin motar tace,"Aysha kun manta Abuja zan wuce yau,train ɗin 2pm zan bi so ina so na koma gida na samu na ɗan huta kafin na nufi Train station ɗin." Aysha tace cikin sauri,"Oh! Wallahi na manta ne Besty,so Allah tsare ki gaida Sister Arfah ɗin da Amarya Allah ya sanya alkhairi." Kafin ma Jannat ta amsa addu'ar Muffy tace,"Saura kuma karki kawo mana tsaraban Abuja ehe!" Jannat ta maka mata harara tana faɗin,"Ni Hafsat me zan kawo miki tsaraba idan ba kayan zaƙi kike so nayi shopping ɗinsu na taho miki dasu ba." Muffy ta saki dariya tace,"Eh ina so." Jannat ta jinjina kanta tana shigewa cikin motar tace,"Okey,nidai zan wuce mutanena sai munyi waya okay." Daga haka sukai sallama da juna Jannat ta tashi motar tayi gaba suma suka juya domin komawa hostel tunda dama lacture ɗaya garesu yau ɗin.

Koda Jannat ta isa gida abinci taci bamai yawa sosai ba sabida kwaɗayin cin gasasshen fish kawai take ji,kuma gashi akan hanya take babu halin tace za ta yi taci.

Ƙarfe ɗaya nayi tayi sallama da Momy suka fito ita da Feenah dake janye mata da luggage ɗinta zuwa compound,ita kuma Jannat riƙe da hand bag ɗinta da kuma wata ƙaramar jaka dake ɗauke da takalmanta da kayan wanka suka nufi parking space da tuni Isa har ya fiddo motar Momy da zai kaita train station ɗin a ciki."To Besty Allah tsare ayi biki lafiya,ki gaida su Anty Khairy da Ummu idan ta iso."Cewar Feenah tana sake kallon yadda Jannat tayi mugun kyau cikin shigar after dress ɗin dake jikinta kalar Gray da yayi masifar haske brown skin ɗinta mai wani irin haske da glowing,tasha rolling da veil ɗin Abayar da ya rufe har saman ƙirjinta sabida veil ɗin yana da ɗan girma."Ameen Feenah za su ji In Sha Allah,har na fara missing ɗinki." Cewar Jannat a shagwaɓe tana kallon yadda Feenah ke mata dariya.Haka dai sukai sallama da juna Jannat ta shiga back seat,tuni isa ya saka Luggage ɗinta cikin boot hakan yasa tana shiga Feenah ta rufe murfin motar ya tashi motar suka nufi gate.Koda suka isa ya aje ta waya ta ɗaga ta kira Suraj,shi yazo har inda take ya sameta tare da ɗaukar mata Luggage ɗinta ya wuce mata dashi.

Ƙarfe biyu da wasu mintuna jirgin ƙasan ya ɗaga dasu Jannat dake zaune kusa da wani matashi,ganin irin kallon da yake binta dashi ya sanya ta janyo rolling ɗin data yi ta rufe face ɗinta,duk da hakan ta kasa daina jin tasirin idanunsa dake bibiyarta hakan kuma ba ƙaramin ɓata ranta yayi ba domin yawan kallo na cikin abinda ta tsana a rayuwarta musamman a wajen maza.....✍🏻

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.