Free chapter 路 Read without an account
001
by BIL-SAN 路 IDO A DUHU
IDO A DUHU
Written by
BILLY S FARI馃拵
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
RANAR FARAWA: Wednesday on 7th May 2025.
Wannan littafin ha茩茩in mallakata ne ban yarda a juya mani shi ba ta kowace irin fuska har sai da izinina! labarin dake ciki kuma 茩ir茩irarren labari ne, saboda haka idan ya zo dai-dai da labarin ki/ka ko kuma rayuwar ki/ka to akasi ne kawai
Bismillahirrahmanirrahim
1.
Wata irin 茩ara ce tun daga bakin gate suka jiyo data kara蓷e gidan, hakan yasa ko gate mai gadi bai gama budewa ba aka danno hancin motar aguje zuwa cikin gidan wanda ka蓷an ya rage a take mai gadi, ya yi wani irin tsalle tare da sakin gate 蓷in ya wuntsila gefe, a rikice matu茩in motar wanda da alama shine mamallakin gidan ya yi parking ha蓷e da fitowa hankali a tashe. Sauran wu蓷anda ke cikin motar kuma suka nufi cikin gidan a guje, a iya saninsu basu bar kowa cikin gidan ba kafin su tafi, to daga ina wannan 茩arar ke fitowa kuma wane aciki? Tambayar da dukkaninsu suke wa kansu kenan acikin zuciya kafin cike da ru蓷ewa ya nufi wajen mai gadi don shi ne wanda ya kamata ya amsa masa wannan tambayar. "Musa waye acikin gidan nan?" Ya fa蓷a yana wurga masa wani irin kallo cike da tuhuma, cikin rawar murya Musa ya shiga bashi amsa yana cewa, "Allah ya taimaki ranka shi da蓷e Wallahi ban sani ba". "what? Kamar ya baka sani ba to motar waye a kofar gidan? Ya akayi har wani ya shigo cikin gidan nan baka sani ba? To meye amfanin aikinka? Me yake faruwa ne acikin gid..?" Bai 茩arasa ba da gudu sai ga wata matashiyar budurwa ta fito tana fa蓷in, "Wayyo Allah sun kashesa, wallahi sun kashe sa, wayyo Allahna na shiga uku na lalace". Wata irin juyowa yai da 茩arfi cikin tashin hankali, gaba蓷aya ji yai ya kasa fahimtar inda maganganun nata suka dosa, to waye aka kashe? ya tambayi kansa, ji yai ya kasa motsawa tamkar an kafesa a wajen ko 茩afafuwansa ya kasa 蓷agawa sai binta yake da kallo, tamkar wanda aka tsikara yai firgigit tare da saurin ri茩ota ganin yadda gaba-daya ta fita hayyacinta itama saboda tsananin tsoro da tashin hankalin data gano, lumfashinta ta shiga yin sama da 茩asa dashi tana nuna masa hanyar shiga cikin palourn gidan tana sake cewa, "Sun kashesa!". jin haka ya sashi saurin sakinta ya nufi cikin gidan yana jin zuciyarsa na wani irin bugawa da karfi, abunda idanuwansa suka gane masa lokacin daya shigo cikin paloun ya haifar masa da wani irin ka蓷awar zuciya ya yi baya zai fa蓷i yai saurin dafe kujerar dake kusa dashi yana jin tamkar ana tsittsinka masa zuciya.
Idanuwansa ya 蓷ago ya zuba akan Kyakkyawan matashin dake tsaye acikin paloun ri茩e da wu茩a a hannunsa duk jini, fuskar nan tasa a ha蓷e babu alamun tsoro ko kuma shiga tashin hankali na riskarsa da akayi cikin wannan yanayi balle kuma nadama, a gefensa kuma wata budurwa ce du茩e tasa hannayenta ta toshe bakinta dasu tana kuka, kukan da gaba-daya kana kallon ta zaka fahimci yadda ya sauya mata kamanni ta hanyar sauya kalar fatar fuskarta izuwa ja, yayin da launin idanuwanta dake farare tas suka yi jajir suna cigaba da tsiyayar da 茩walla. A gaban su kuma babbar macece ta rungume wani matashi ajikinta dake kwance cikin jini ko motsi bayayi tana kuka tana girgiza sa ha蓷e da sabbatun ya tashi. Ganin da tayi tabbas bazai tashi ba ya sa ta mi茩ewa cikin wani irin fushi da zafin rai ta nufo wajen saurayin dake tsaye ri茩e da wu茩ar da kana gani kasan da ita akayi amfani wajen illata wanda ke kwance cikin jinin babu lumfashi a jikinsa, tana zuwa ta 蓷auke sa kyakkyawan mari har guda biyu saboda tabbacin da take dashi akan ko shakka babu shine ya yi wannan aika aikan, cikin zaro idanuwa da 茩araji take cewa "Kai 蓷an gidan uban waye? Me ye ya kawo ka cikin gidan nan? Waye ya aiko ka aikata masa haka? Me yarona ya yi maka ne?". Ta jero masa tambayoyin tana sha茩o wuyan rigar sa kafin ta fashe da wani irin kuka tana zubewa 茩asa, saurayin kuwa kasa amsa mata yayi sai ma 茩asa da ya yi da kansa don har lokacin babu alamun nadamar abinda ya faru ko tsoro a tattare dashi, banda zallar masifa da jin kai babu abinda ke cikin idanuwa da suka yi jajir tamkar an watsa barkono.
Kukan da matar keyi ya maido da mutumen cikin hayyacinsa yana fa蓷in. "Innalillahi wainna ilaihirrajiun". Kalmar daya iya fa蓷a kenan ha蓷e da ciro wayarsa, bugu 蓷aya ya yiwa wata lamba aka 蓷aga, cikin wata irin murya dake nuni da cike yake da damuwa yace. "Commissioner ina so ka turo mani da yaranka anan gidana, Please ranka shi da蓷e". A ta 蓷ayan 蓳angaren commissioner of Police ya amsa masa da, "Yanzun nan amma yalla蓳ai ina fatan dai lafiya ko?" "Ba lafiya ba.." nan ya kwashe duk abinda ke faruwa da suka isko ya sanar dashi yana jin idanuwansa na kokarin kawo 茩walla yana ji duniyar nayi masa wani irin juyi, gaba-daya ya gama ru蓷ewar da bai san me zai yi ba banda ya kira hukuma.
Bayan mintuna goma sha takwas da kiransa sai ga motar police har guda biyu ta iso gidan, Nan ya basu izinin shigowa tare da nuna masu wanda zasu yi arresting da suna shigowa su da kansu suka fahimci shine mai kaifin ganin wu茩a da jini a hannunsa, a take suka zagayesa tare da saita bindigogin su akansa saboda kar ya gudu, 蓷aya daga cikin yan sandan ne ya fiddo ankwa zai saka mashi a hannu da sauri matashiyar budurwar dake gefe tana kuka ta mi茩e tsaye ta nufo wajen, ganin zatayi magana saurayin ya nunata da wu茩a yana cewa. "Wlh kalma 蓷aya idan kika fa蓷a zan kasheki kema sannan na kashe kaina nim.." Bai 茩arasa ba ya ji saukar kan bindiga saman kansa ya saki wata irin 茩ara tare da zubewa akan guiwoyinsa saboda tsananin azabar da yaji, baya ta ja tana sake toshe bakinta saboda garga蓷in da yayi mata da take da tabbacin zai iya aikata abinda ya fa蓷a, "Inspector kuje dashi ayi bincike a gano waye ya turosa har cikin gida yazo ya aikata haka ga 蓷ana! Bana so ku sassauta masa har sai kun tabbatar daya fa蓷a maku gaskiya, ku gana masa azabar da zata sa da bakinsa ya fa蓷i ko waye ya aikosa, ni kuma zan ga wanda zai tsaya masa akaf fa蓷in 茩asar nan, sai naga wanda ya 蓷aure masa gindi da zai hana nayi Shai'a dashi ko da duka abinda na mallaka zai 茩are". Wani dukan suka sake kaiwa saurayin a karo na biyu a saman kafa蓷a bayan sun saka mashi ankwa kafin su 蓷aga shi suka nufi hanyar fita dashi, suna kaiwa bakin 茩ofa ya juyo yana ma yarinyar wani kallo mai cike da garga蓷i, 蓷an sandan dake ri茩e dashi ya hanka蓷asa yana tura 茩eyarsa waje yake cewa, "wuce muje, zakayi bayani". Suka turasa cikin motarsu ta yan sanda bayan sun fito tare da tayar da motar suka fice daga gidan, 蓷aya motar ta yan sanda kuma suka 蓷auki wanda ke kwance cikin jini aka nufi asibiti dashi, kallon yarinyar mutumen ya yi da sautin kukanta ya 茩aru yace, "Ya isa haka ki tashi ki tafi gida, idan ma ya hanaki magana yanzu lokaci zai zo da gaskiya zata bayyana idan aka zo bincike, ina fatan zaki fa蓷i abinda kika sani don bima yarima da jininsa hakkinsa". Jiki ba 茩wari ta mi茩e zata fita matar tace.
"Ki sani ke kadai ce zaki iya bada tabbacin abinda ya faru, idan har kika 蓳oye kuma bazan ta蓳a yafe maki ba". Bata iya cewa komai ba tana kuka ta fice daga gidan, yara yan mata biyu suka zo suka rungume matar suna kuka, shi kuma mutumen ya fice yabi bayan yan sandan zuciyarsa cike da damuwa, driven yake amma tunani yake yi yaushe 蓷ansa ya dawo 茩asar nan ba tare da saninsa ba? Me yakawo wancan saurayin acikin gidansa har hakan ta faru? Waye shi meye alakarsa da 蓷ansa da zai shigo har cikin gidansa yayi masa wannan mumunan aika-aika. Ji yai zuciyarsa ta bushe ta cika da wutar son 蓷aukarwa 蓷an nasa 茩waya tilo da yake matu茩ar 茩auna fansa, a take ya 蓷auki alwashin ko waye yaron kuma ko dan gidan waye shi sai an hukunta sa shima dai-dai da laifinsa don bazai yafe ba, bazai ta蓳a bari jinin 蓷ansa ya tafi a banza ba.
06:35pm
Zaune yake a farfajiyar cikin gidan nasa daga wajen gate can cikin wani 茩aramin waje da aka tanada don shan iska, a gefensa wata kyakkyawar mace ce bafulatana da shekarunta duka baza su haura shekaru arba'in da wani abu ba, Labari suke yi cike da kulawa, k'auna da kuma soyayyar juna, wanda kana gani kasan ba sai an fa蓷a maka su 蓷in miji da mata bane dake tsananin 茩aunar junansu. wayarsa dake ajiye agaban sa ce ta shiga yin 茩ara, hakan ya tilastasa dakatar da firar da suke yi da yake matu茩ar jin da蓷in ta, wayar ya fara 蓷agawa kafin yakai a kunnensa bakinsa 蓷auke da sallama, shiru ya yi na wasu yan sakanni kafin yai wata irin zabura yana mi茩ewa tsaye yake cewa. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, wace police station aka je dashi? Laifin kisa kuma? To shikenan commissioner, kar ku ji komai ku gudanar da duk binciken daya dace akansa, Nagode". Ya fa蓷a bayan gama sauraren dalilin kiran nasa da akayi yana cire wayar daga kunnensa. Nan take kyakkyawar fuskar matar nan dake tare dashi ta sauya kamar yadda tasa fuskar ta sauya daga sassau茩an mutum da 蓷azu a kallo 蓷aya zaka iya fahimtar hakan tare dashi zuwa wani mutum da bazaka ta蓳a cewa ya ta蓳a yin dariya ba, hannayensa duka ya zuba a baya ya shiga kai da komowa a tsakiyar wajen, kwarjininsa da kuma yanayin da nan take ya shiga ya sa matar duk yadda hankalinta ya tashi ta kasa furta masa kalma ko 蓷aya da nufin tambayar sa abinda ke faruwa, sai dai fa gaba-daya jikinta ya saki tsoro ya dabaibaye mata zuciya tare da yimata wani irin kullin goro daya sa fitar lumfashinta da wani irin 茩arfi, da茩yar ta iya tattaro 蓷an karfin daya rage mata cikin rawar murya tace.....
ALLAH KA JIKAN IYAYENMU馃憦