Free chapter 路 Read without an account

003

by BIL-SAN 路 IDO A DUHU

IDO A DUHU

NA

BILLY S FARI 馃拵

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

                            3.

Rai a 蓳ace ganin yadda aka maida mata da 蓷a ta dawo gida tayi parking 蓷in motarta ta kashe ta fito ta fara tafiya tamkar wacce 茩wai ya fashewa aciki, a yanayin da take ciki idan ka kalleta zakayi tsammanin itama dukan tasha saboda yadda gaba daya jikinta ya mutu, sashenta ta nufa da gudu yar tata ta rugo ta rungumeta tana yimata oyoyo, bata iya tanka mata ba sai ma janyeta da tayi daga jikinta ta wuce 蓷aki abinta, tamkar yarinyar za tayi kuka tabi mahaifiyar tata da kallo, tasan halinta idan tace zata je ta sameta 蓷akinta yanzu nan zata maido duka fushin da take ciki a kanta, don haka sai kawai tabar sashen gaba蓷aya ta nufi na matan babanta ta shige cikin yan uwanta, dama tafi samun natsuwa da farin ciki idan tana tare dasu sama da mahaifiyarta dake nunawa kamar ba ita ta haifeta ba.

Saman gado ta jefa mayafinta da jakarta ta zauna gefensa tasa gaba蓷aya hannayenta ta tallabe fuskarta dasu. Ya Allah! Ta ina zan fara? Ta tambayi kanta cikin matsananciyar damuwa tana jin baza ta iya zuba idanuwa ba a raba 蓷anta da rayuwarsa, koma meye tasan dole ya zama bisa kuskure da tsautsayi yafaru, minti biyu tayi a haka ta mi茩e ta shiga toilet ta dauro arwala tayi sallah, tana idarwa bayan tayi addu'a ta mi茩e ta shiga kitchen, abinci ta shirya da kanta sanin duk wanda zai girka abinci a gidan idan ba ita ba yaronta baya ci saboda tun yana 茩arami ta sabar masa da haka, bayan ta kammala tafito ta 蓷auki wayarta ta kira 茩anenta, bugu 蓷aya ya 蓷aga ta fa蓷a masa yazo tana son ganinsa, ba'a jima ba ya iso gidan ya gaisheta sannan suka zauna ta sanar dashi halin da ake ciki, tausayin ta ne ya kama shi duk da koma meye ita ta jawo saboda yadda take nunawa yaron so abun ba'a magana, jajanta mata ya yi kafin ta 蓷auko abincin ta bashi tana cewa, "Ka kai mashi abinci kuma ka 茩o茩arta ya samu yaci, akwai magani dana saka aciki ka bashi yasha kafin gobe nasan abinda zan yi don wallahi bazan iya zuba idanuwa ba 蓷ana na kulle a hannun 'yan sanda suna gana masa azaba, bazan iya ba wallahi". "Shikenan amma kibi komai a hankali kuma kiyi addu'a Allah yayi masa mafita, saboda case 蓷in kisa ba abu bane 茩arami". "Koma dai meye ina bu茩atar yarona gida akusa dani". "Allah ya kyauta". Ya fa蓷a sannan ya mi茩e ya dauki abincin ya tafi.

Kasancewar yau ita keda girki har goma ta wuce bai gane ta ba yasa ya 蓷aga waya ya kirata, kamar bazata 蓷aga ba sai kuma tayi wani tunani da sauri ta 蓷aga wayar kafin ta katse ta kai a kunnenta ba tare data ce uffan ba, jin tayi shiru yasa shi cewa. "Ina jiran ki?" Kafin tace wani abu ya katse kiran, haushi ne ya kamata don so tayi ta dan茩ara masa maganar da zata hanasa bacci yau kamar yadda ita da 蓷anta suma baza su runtsa ba, sai gashi ya katse kiran, kwafa tayi ha蓷e da yaye duvet 蓷in data lullu蓳a dashi ta sauko saman gadon don tuni ita ta kwanta tana faman karanta wasikar jaki don baccin bai iya 蓷aukarta ba, babban hijabi ta saka kasancewar kayan bacci ne ajikinta sannan ta nufi sashen maigidan nasu, tura kofa tayi ta shiga sannan ta mayar ta rufe ta jingina aijkin 茩ofar ta na蓷e hannayenta a kirji fuskar nan babu 蓷igon walwala ko 茩ire a tattare da ita. "茦araso daga ciki mana". Ya fa蓷a yana 茩o茩arin canza channel a tv 蓷in dake jikin bango a gefen gadon. Sai da ta taushi zuciyarta sosai sannan ta iya cewa. "Kafadi abinda kake son fa蓷a ina so na kwanta". Hankalinsa ya maido kanta yana 茩are mata kallo kafin yace, "Kizo ki kwanta anan mana". "Bana bu茩atar hakan domin babu natsuwa atattare dani". "Ban gane ba?" Ya fa蓷a yana kafeta da idanuwa, tsananin takaicin yadda yake magana tamkar bai san abinda ke faruwa ba da halin da take ciki ya sata fashewa da kuka tana cewa, "Dole zaka fa蓷i hakan tunda kai hankalinka a kwance yake kama manta da halin da 蓷ana yake ciki saboda baka son sa baka 茩aunarsa". Takaici ne ya rufe sa shima cikin zafin rai yace, "Indai akan wannan maganar ce eh 蓷in mu barshi a bana sonsa tunda ba jinina bane! Wai me yake damunki ne? Ya kike so nayi shi 蓷in ai ba yaro bane, abinda ya aikata yana sane da cewa kuskure ne zai iya jefasa awannan halin da yake ciki amma yaje ya aikata sai kace shi yafi kowa ba茩ar zuciya, Yanzun nan muka gama waya da d.p.o ya kirani ya fa蓷a mani sunyi sunyi ya bu蓷e baki yayi magana ko report ne a dauka yadda za'a iya bada belinsa amma ya茩i, ke da kika je ma ya tabbatar mani da cewa bai tanka maki ba to me kike so ayi masa? Ko zamu zo mu sanya bakin cikinsa ne a zuciya mu mutu?". "Ba haka nake nufi ba, gaba-daya fa ka nuna tamkar ba kai ka haifesa ba, ka nuna kamar ba 蓷anka bane shi, ka kuma 茩i 蓷aukar wani mataki don taimakonsa, bayan ina da tabbaci akan waya 蓷aya idan za kayi za'a sako mani yarona, gaba蓷aya tunda na dawo zuciyata ke faman tsuke mani waje 蓷aya takeyi idan na tuna yadda suka bubbuge mani fuskar yaro, sun sauyawa masa kamanni ko tafiya baya iyayi da kansa". "Haka ya za蓳a don haka wlh bazan ta蓳a sa a fito dashi ba, ai zama a cell ko gidan kaso, gyara hali ne, don haka yaje tunda mu mun gaza a matsayin mu na iyayensa su sai su gyara mana halinsa, lauya 蓷aya bazan 蓷aukar masa ba sannan kuma bazan nemi abada belinsa ba don sunce idan har yakai gobe bai ce komai ba to jibi zasu mi茩a sa kotu". "Abun da zaka fa蓷a kenan? To wallahi bazata yiyu ba kuma idan ka 茩i 蓷aukar masa lauya ai ni mahaifiyarsa ina da rai kuma kasan zan iya yin komai, idan nace komai to fa ina nufin komai ciki har da abinda baka yi tsammani ba". Tana gama fa蓷ar haka ta juya ta bar 蓷akin. Ji yai gaba蓷aya kallon ya fice masa arai sai kawai ya kashe tv 蓷in ya shiga kai da kawo a tsakiyar 蓷akin, ba wai baya jin damuwa bane shima akan halin da 蓷an nasu ke ciki ba ne, kawai baya so ya nuna mata ne saboda ta gano kuskure da girman laifin da take aikatawa na nuna ma yaron son da daya wuce wuri. Da haka ya nemi waje ya kwanta ko zai samu bacci ya 蓷aukesa.

A police station

Duk wani duka da horo da ake yiwa mai laifi don ya bu蓷e baki yayi magana ko ya amsa laifinsa anyi masa amma ya茩i furta ko da kalma 蓷aya ce, tsabar dukan daya sha gaba-daya idanuwansa basa bu蓷uwa, tsanin tausayinsa ne ya rufe 茩anen mahaifiyar tasa daya kawo masa abinci, cikin sigar lallashi ya fara yi masa magana, "Bana tunanin a wannan ga蓳ar taurin kan rashin bu蓷e baki kafadi gaskiyar magana zai amfaneka, idan kuskure ne ko tsautsayi yakamata kafa蓷a don anemi hanyar da zaka iya samun sassauci, kasan irin shakuwar dake tsakaninka da mahaifiyata baza ta iya jurewa ganinka cikin wannan yanayin ba, gashi acikin da茩i茩u yan ka蓷an da kamaka duka ta fita hayyacinta, don Allah ka fa蓷a masu abinda ke faruwa ko belinka ne mu samu bayar kafin agama bincike". Nan ma dai kansa na sunkuye 茩asa bai bu蓷e baki ya yi magana ba har 茩anen mahaifiyar tasa ya gama maganarsa, haka ma abincin daya kawo masa yayi juyin duniya dashi ya samu yaci ko da ka蓷an ne yasha magani amma ya茩i kar蓳a, a dole haka ya mi茩e yabar police station 蓷in da abincin ba tare da ko kallon abincin yai ba, sanin halin yayar tasa idan tasan bai ci komai ba zata tashi hankalinta yasa ya samu almajiri akan hanyarsa ta komawa ya rabar masu da abincin..

******

Duk wanda yasan 茩auna da soyayyar dake tsakaninsu da 蓷ansu dole ya tausaya masu halin da suka shiga ciki bayan tabbatar da cewa lallai sun rasa shi rasawa ta har abada, dukkansu sun shiga cikin matsanancin tashin hankali daya haifar masu da matsananciyar rashin lafiya musamman mahaifin yaron, wanda hakan yasa har akayi komai na mutuwar yaron aka rufesa bai san inda kansa yake ba, ya koma tamkar mutum mutumi yake yi don ya kasa gasgata faruwar lamarin. A 蓳angar 蓷aya zuciyarsa ta cika da son 蓷aukar fansa ta hanyar ganin yasa shima wancan saurayin an kashewa kamar yadda ya kashe masa 蓷a, Mahaifiyar yaron ita ta koma lallashinsa tare da bashi baki wanda ita kanta karfin haline kawai takeyi.

A 蓳angaren bincike sau biyu yan sanda na zuwa ganawa da wannan matashiyar budurwar, sai dai yanayin data shiga ciki na zazza蓳i mai nauyi yasa basa samun damar yi mata tambayoyin da suka dace sai 蓷an abinda baka rasa ba dangane da ita da ala茩ar dake tsakaninta da ahalin gidan, wanda yayanta ne ke rakata ayi komai a gama su dawo gida, yau kwana na uku kenan da faruwar lamarin ranar da ake tunanin washe gari za'a tura case 蓷in zuwa kotu, zaune take tayi zuru-zuru yayan nata da mahaifiyarta sun tasata agaba ganin ta samu sau茩i, yayan nata yace. "Wai ni abinda ke damuna kuma nake son sani shine, shin meye ala茩ar wanda aka kashe dashi wanda ya yi kisan? Shin kinsan shi ne koko a gidan da kika taddashi kika fara ganinsa?" 茒ago kai tayi tace. "Eh Yaya nasan shi". Zaro idanuwa yai ha蓷e da cewa. "Makashin? Taya?". "Lalle kam tambaye mana ita don ni nafara wani tunani akan lamarin nan, a ina kika san shi?" Sai data share 茩wallah sannan ta fara basu labari....

ALLAH KA JIKAN IYAYENMU 馃憦

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol