Free chapter · Read without an account

MAKIRIN IKO

by Aisha abbas Bidami · MAKIRIN IKO

☠️☠️ MAKIRIN IKO ☠️☠️

The hunted house 🩸

Jarumai writers association 📚📚📚🖋️🤩

MALLAKIN

MRS ISHAM

6&7

“Malam Yusuf shin a ina ne zamu samu ragowar ahalin Attajiri Taheer ?”

“Gaskiya se de in tuntubi Alhaji turaki saboda Alhaji musa Tahir abokinsa ne”

Kiran Alhaji turaki yayi a waya ya sanar masa da abinda yake faruwa tare da rokansa in ba damuwa ya zo tare da jikan Attajiri Tahir .bayan ya amsa da in sha Allah zasu zo ne ya katse kiran tare da gyara zaman jiran isowar su,ita kuwa Siyama tana zaune kan ta na kallon ƙasa ba ta kuma motsawa ba,kowa yayi jigum ana jiran su. Basu suka zo ba se karfe sha daya da minti ashirin.

Gaisawa suka yi cikin mutuntawa nan Alhaji musa Tahir ya soma magana

“Tabbas na ji abinda yake faruwa kuma a madadin kakanmu da baya wannan duniyar da kuma madadin ahalina mu na be ba ku. hakuri domin kun tsinci kan ku a mawuyancin hali. Hakikanin gaskiya nayi tunanin tunda an rusa gidan an yi sabon gini komai ze zo karshe a she ba haka bane. Ku gafarce mu dan Allah. Ni jika ne a wajen Attajiri Tahir wanda ban san sa a fuska ba balle hoto,domin ko hoton sa babu a wajen mu. Kakarmu ita ce uwar gidan Attajiri Tahir ita ce nan ta ba mu labarin sa da komai tun kafin ya aure ta da kuma bayan aurenta da yayi da abubuwan da suka dinga faruwa. Itama Allah ya mata rasuwa shekara biyar da suka wuce”

“Muna me yi maka ta'aziyar rashin kakar ka,sannan mu na so da ka bamu tarihin wannan Attajiri Tahir din domin neman mafita” cewar baba,gyara zama Alhaji Musa Tahir yayi ya soma basu labari kamar yanda kakarsa ta basu.

“Shekaru aru-aru da suka wuce,an yi wani matashi da ya kasance maraya ne kuma almajiri a wata tsangaya dake kauyen zanbar sunan sa Tahir. matashi ne me hazaka tare da neman na kansa se de duk yanda Tahir yake neman kudi abu ya gagara domin baya iya biyawa kansa bukatu duk kuwa kalolin sana’ar da yake yi. yana dako,yana noman ciyawa,yana farautar dabbobin daji ya siyar,yana zubar da shara. Amma duk da haka wayannan kudaden da yake samu basa isanshi yin abubuwan da yake so saboda shi mutum ne me buri yana son yayı duk abinda wayanda suka fi sa suke yi. Ana haka malamin su ya basa yar sa me suna Rashida sure.bayan an yi auren ne suka tare a wata yar karamar gidan laka da ke ɗauke da daki daya se bangida da kuma ƙaramar zaure. Tunda Tahir yayi aure nauyi da dawainiya ya taro ya masa yawa musamman da matar sa Rashida ta haihu. Rashida macece me hakuri sosai da riƙo da addini abin duniya sam be rufe mata ido ba. Duk sanda Tahir ya dawo gida ba kudi ba cafane haka zata zauna ta yi ta tausansa tare da faɗa masa in sha Allah komai ze zo karshe Allah be manta dasu ba,wannan nutsuwa da daɗaɗan kalamai ne yasa Tahir yake ƙara sonta. Talauci se ƙara ƙaruwa yake wata rana haka suke kwana basu ci komai ba gaba daya Tahir ya shiga damuwa gani yake ya gaza a matsayin miji da kuma uba talauci ya masa kamun kazan kuku.komai ya fi karfinsu ba ci mai kyau,ba sha mai kyau,babu suturan arziki.

Wata rana Tahir ya yanke hukuncin shiga daji farauta,fitowa yayi da Kayan farautarsa a cikin gida ya samu Rashida da ɗan su me shekara biyar salisu sallama ya mata ya fita. ko da ya shiga dajin dakyar ya iya kama gafiya har yazo fita ya hango wani tsoho mutumin ya tsufa sosai yana sanye da fararen kaya hannunsa riƙe da sanda dayan hannun kuma na riƙe da kwarya, da kamar baze karasa gun tsohon ba amma se ya yi tunanin ko tsohon na neman wani taimako ne.

“Barka baba shin akwai wani taimako da za'a maka ne?”

Tsohon ne yace “yaro ƙishi nake ji kuma na gagara samun ruwan sha,da zaka taimaka min da na ji dadi”

ƙarban kwaryar yayi ya tafi rafin dake dajin ya ɗibowa tsohon ruwa ya kawo masa karɓa yayi ya sha kafin ya ce

“Nagode sosai tabbas kai din me sa'a ne da har Allah ya baka ikon gani na yau domin se bayan karshen duk shekara nake zuwa wannan dajin domin taimakon wanda yake cikin wani hali. Lallai kai dan sa'a ne”

Cikin rashin fahimta Tahir ya ce “baba se de ban fahimce ka ba”

Murmushi wannan tsohon yayi ya ce “nasan halin da kake ciki na matsanancin talauci,sunan ka Tahir almajiri kuma maraya da ya ta so cikin ukuban rayuwa da gwagwarmaya. Kana da mata da yaro daya”

Sake baki Tahir yayi yana kallon tsohon nan a gefe daya kuma tsoro ya kamasa domin yanda wannan tsoho ke zazzago da bayanan sa kamar dama can ya masa farın sani

“Kar ka tsorata dani ni din ban zo gare ka da niyar cutarwa ba,nazo ne da niyan taimakon ka,ka faɗa min menene ka ke buri a rayuwarka ni kuma zan taimaka maka domin ka mallakesa “

Cikin tsoro-tsoro yace “Ina son in yi kudi yanda duniya zata san da ni”

“Aikin gama ya gama ka sa a ranka ka zama Attajiri Tahir daga yau”tsohon ya faɗa yana fito da wata yar ƙaramar littafi ya miƙa masa. karɓa Tahir yayi yana kallon tsohon domin neman ƙarin bayani

“Wannan littafi da ka ke gani shine ze taimaka maka domin cikar burinka. Yana ɗauke ne da makirin iko kala-kala duk wani burinka da abinda ka ke bukata in ka karanta wannan littafi a yanda ya kamata zaka same sa”

“Da…dagaske? Yanzu in na karanta littafin nan zan zama shahararren me kudi? zan fi karfin duk wani nau’in abinci?kayan sawa ni da matata da yaro na zamu dinga sa kaya ko wani iri?” Ya faɗa da al’ajabi akan fuskarsa

Gyada kai tsohon yayi “Kwarai kuwa. Laƙanin wannan aiki shine idan dare ya raba kowa na bacci ka yi wanka da ruwan buta sannan ka sanya fararen kaya kafita ka je can daji,in da babu wanda ze gan ka ko da kuwa dabbane me kaho. Ka samu hanya da ya rabu kashi biyu ka zauna a tsakiyan hanyar sannan ka fara karanta wannan littafin. Wani aljani ze bayyana a gabanka da suffa me ban tsoro,wanda matukar ka tsorata to tabbas zaka mutu ko kuma de ka haukace,in kuma baka tsorata ba wannan aljanin ze tambayeka me ka ke da bukata. Duk abinda ka ke so a wannan duniyar ka faɗa masa shi kuma ze cika maka. Tahir ka tabbatar da zaka iya?”

Da sauri ya ce “tabbas zan iya matukar zan fita a cikin wannan talauci da nake ciki zan iya”

“Zaka iya tafiya “cike da farin ciki Tahir ya bar wannan dajin batare da ya ɗauki gafiyan da ya ajiye ba. yana komawa gida yaje ya ɗaga buhun kayansa ya ajiye littafin ya boye,ita de Rashida kallon sa kawai take saboda ta jima rabon da ta ga me gidan na ta a irin wannan yanayı na farin ciki hakan yasa ta ce

“Ni kam me gida wannan farin cikin da ka ke ciki yau menene silar sa ko de ka samu aiki ne?”

Murmushi yayı yana “Rashidata kenan..yoo ko aiki na samu bazan yi wannan farin cikin ba,kawai de mun kusa fita daga cikin wannan ƙangin rayuwa da muke ciki in sha Allah “

“Allah ya amsa”

Dare na yi Tahir ya tafi majalisa shi da abokan sa suna ta hira bayan majalisa ya fara watsewa ne ya samu abokinsa Audu ya nemi rancen kudi ko da Abokin ya basa kudin,nama ya siya musu da Kayan abinci ya tafi gida suka ci suka yi hanikan sannan suka kwanta.

Dare na yi ya tashi ya dubi matar sa da ke bacci da ɗan su,ɗaukan littafin yayi ya fito zaure ya ɗiba ruwa cikin buta yayı wanka sannan ya sanya fararen kayan sa da suka kode.

Babu tsoro ko ɗigo daya a zuciyar sa ya fita ya shiga daji ya samu hanya da ya kasu gıda biyu ya zauna ya soma karanta wannan littafin. Guguwa me karfi ne ya taso yana rikiɗewa ya koma wani ƙaton dodo me ban tsoro da firgitarwa

“Ya kai bil adama!menene bukatar ka da yasa ka kirawa ni?”

Batare da ya ɗaga kai ya kalle sa ba yace “ kudi!kudi nake so”

Dariya wannan dodon ya sanya yana faɗin

“Ka ɗaga kai ka kalle ni ido da ido”

Hakan kuwa yayi ya ɗaga kai ya kalle sa duk yanda wannan aljanin ya zo masa a fuska mafi ban tsoro amma Tahir sam be tsorata ba,ko dar be ji ba.

“Menene burinka,wani bukata ka ke so in biya maka?”

Ya sake tambayan sa a karo na biyu

“Ina son in yi kudin da zan kere kowa a wannan kauye na mu,in zama Attajiri duniya ta san dani,sunana ya shahara a duniya ko Ina a san da zaman Attajiri Tahir”

“An gama in de wannan ne ka nema kuma ka samu,ga wannan zoben ka sanya sa a hannunka,duk sanda ka ke son gani na ka murza shi. Sannan kuma ka koma gıda zaka farka ne a cikin kudi dumu-dumu. Ƙa!idan wannan kudi kuma bazaka taɓa taimako da shi ba ko da mutum na kokarin mutuwa ne ya zo neman taimako to kar ka yi kuskuren taimaka masa saboda kana yin hakan zaka samu karayar arziki. Maza ka tafiiiii iya kacin kai ne da iyalanka zaku more wannan dukiya hahahhahahahahha” ya ƙare maganar da muguwar dariya da gudu Tahir ya bar wannan dajin ya koma gıda ya shiga dakin su cikin sanɗa ya kwanta a haka bacci ya ɗauke sa.

Washe gari ya farka amma be ga kudi a cike da dakin ba haka ya dinga neme-neme amma be ga komai ba hakan yasa yayi wanka da niyar zuwa neman musu kudin da zasu yi abincin rana.

Buhun kayansa ya nufa nan ya ga buhun a cike tab a kumbure da mamaki yake kallon buhun inda ya isa a hankali ya taɓa sa yaji babu alaamun kaya. hakan yasa jiki na rawa ya buɗe yana buɗewa yaga makudan kudade ne cike a cikinsa,ihun farin cikin da ya hau kwarmawa ne ya jawo hankalin Rashida da take cikin gida da gudu ta shigo a tunanin ta wani abun ne ya faru dashi se cin karo ta yi da abinda bata yi tsammani ba domin ganin sa tayi ya zazzage buhun kudin a tsakiyar daki ya kwanta a ciki yana ta dariya tsabar murna.

Tambayar sa tayi wannan kudin fa daga Ina yace mata Allah ne ya basu yanzu lokaci ne yayı da suma zasu fita a wanann kangin. ita de hankalinta be kwnata ba hakan yasa ta yi ta masa nasiha akan cin haram da kuma take dokokin Allah amma se ya nu na mata wannan kudi da ta gani Allah ne yayı zasu same sa dan haka ta saki jiki su ci arziki.

Tundaga wannan ranan Tahir ya fara walwala da kudi sannan ya fara manyan kasuwanci ba iya kauyen su ba har kauyukan dake makwabtaka dasu se da ya buɗe manyan shaguna a can. cikin kankanin lokaci sunan sa ya kewaye ko ina nan take ya zama Attajiri mai danasha da kudi mutanen da suka renasa suka fara girmama sa sama da ƙasa.bangaren rayuwar Matar sa Rashida da ɗan su kuwa komai na tafiya musu dede domin ko daga nesa ka hango su zaka fahimci suna cikin daula.can bayan garı ya je ya siya fili me girman gaske aka soma masa gidaje manya manya masu dauke da manyan part ana gama wa kuwa Rashida ta koma bangare mafi kyau da girma cikinsa sun dawo sabon gıda da kwana biyu kenan Attajiri Tahir ya auri kyawawan yan mata guda biyu a rana daya. Sosai Rashida ta yi kuka amma a fuska sam ba ta nu na masa komai ba. Amma son da yake mata yasa ya je ya dinga bata hakuri ta ce mai ba komai. Haka ya ci amarcinsa. Haka rayuwa ya ci gaba a yayinda Attajiri Tahir dukiyoyinsu suke ci gaba da haɓaka sannan kuma duk macen da ya aura daga zaran sun haihu daya da ita yake sakin ta ya auro wata a haka cikin shekaru da basu wuce takwas ba Attajiri Tahir ya tara yara sama da goma sha biyar banda yayan Rashida da suka kasance guda uku mace daya se kuma maza biyu. Ita de ta zuba masa ido ganin yanda yake ta auri saki.

Wata rana daya daga cikin yaransa na kasuwa suka zo da gudu cikin tashin hankali suka sanar dashi shagunan sa guda hudu da suke kasuwa sun yi gobara sun kone kumurus. sannan garken shanunsa ma an samu gawan shanaye ashirin,tabbas wannan rana hankalin Attajiri Tahir ya matukar tashi inda tun daga wannan ranan mugayen alkaba’i suka dinga binsa.duk wasu kasuwancinsa suka dinga rushewa gaba daya hankalinsa yana a tashe. ya rasa me ke masa dadi,matan da yake aure a yanzu da suka ga babu dukiya kawai suka nemi saki sannan suka tafi Rashida ce kaɗai ke tare dashi da kuma yaransa goma sha takwasa

Wata rana ya yanke hukunci ya shiga can turakarsa ya murza zoben da wanann Aljani ya basa nan take dakin ya koma baki aljanin ya bayyana

“Barkanka da wanann lokaci Attajiri me lokaci”

Fuska a haɗe Attajiri Tahir cikin fushi ya ce

“In har ka san za ka bani dukiya kuma ka kwace abunka meyasa ka bani?ai hakan bayi da amfani,gaba daya kasuwancina ya durkushe na zama abin dariya a idon mutane. Duk dukiyar da nake tunkaho dasu sun ƙare a ɗan kankanin lokaci”

Dariyar mugunta aljanin ya bushe dashi

“Ai dama dole bayan wasu shekaru ka neme ni saboda dukiyar da na baka da kuma ɗaukaka yana da wa’adi. Matukar kana son dukiya da ɗaukakan da ka samu ya ɗaure har abada to dole zaka dinga bani cin hanci ka dinga faranta min se nima in faranta maka ta hanyoyin da baka yi tsammani ba”

“Faɗa min menene ka ke so in dinga yi maka ?”

Bushewa da dariya aljanin yayi a karo na biyu “sadaukarwa!sadaukarwan rayukan yara tare da mata masu ciki,matukar kana zubar da jinin bil adama agareni Ina sha to tabbas arzikinka baze taɓa yankewa ba har abada”

Shuru Attajiri Tahir yayi a karo na farko da ya ji jikinsa yayi sanyi dangane da biyan bukatarsa taya ze iya aikata kisan kai ta Ina ma ze fara aikata wannan katon zunubin? abubuwa da yawa suka dinga yawo a zuciyarsa

“Shin ko baka bukatan hakan ne in yi tafiyata?”

Dawuwa hayyacinsa yayi Firgit ya furta “shin lallai dole se jinin mutum me ze hana in dinga sadaukar maka da dabbobi?”

“Kai banzan bil adama bana son shashanci,na yi maka kama da wanda ze sha jinin dabba? Dolen dole se jinin bil adama saboda a yayinda ka min sadokarwa da jinin su kai kuma ruhinsu zaka tsafance shi a cikin sirintaccen akwati ka hana ruhin tserewa.. kuma daga lokacin da ka amince ba komawa baya dole ko da yaushe ka dinga sadaukarwa matukar kuma ka yi fashin hakan to tabbas zaka yi mutuwar wulakanci cikin kaskanci,sannan kuma ruhin wayanda ka kashe bazasu taɓa zuwa duniyar su ba har se an musu kyautar ruhi guda biyu… dan haka zaɓi ya rage gareka.”

Sosai gumi ke yanko masa ya rasa takamanmen wani irin amsa ze basa,tabbas baya kaunar dalilin da ze sa ya koma kangin talaucin da yake ciki da. Kuma haka zalika baya tunanin ze iya aikata kisa.amma kuma me ze faru idan yaƙi amincewa da bukatar wannan aljanin hakan yana nufin se yafi da talauci?mawuyacin hali da yunwa da rashin suturan da ya dinga fama dashi a rayuwar sa na baya ne kawai suke masa yawo a ido

Cikin tsoron komawa gidan jiya yasa cikin sauri ya furta”na…na amince zan yi duk abinda ka ce”

İn takaice muku tundaga wannan rana Attajiri Tahir ya fara sadaka a cikin gidansa duk yaran da suka zo to se ya sace yara biyu ko uku ya kai su bangarensa ya tsafesu sannan ya kashe su tare da sanya ruhinsu a cikin wannan akwatin glass da Siyama ta buɗe.

Haka zalika mata masu ciki ya buɗe asibiti a anguwarsa duk wacce tazo haihuwa to se an kirasa da sunan ya musu addua shi kuma se ya tsafesu daga nan zasu dena magana da komai su koma kamar gunki in dare yayi har cikin bangarensa suke kawo kansu cikin rashin sani shi kuma se ya kashe su tare da sanya ruhin su cikin akwatin sa na glass.

Tabbas mutuwan da ake yi a cikin kauyen zanbar ya soma yin yawa kafin daga karshe aka fara zarginsa daga nan ne fa mutane suka fara nisanta kan su dashi da duk wani abinda ya shafesa. kowa ya soma kyamatarsa da kuma gudunsa inda tun daga nan samun mutanen da ze yi sadaukarwa dasu ya masa wahala hakan yasa ya fara yi da yayan sa daya bayan daya suka fara mutuwa babu ciwo babu komai. Tabbas da da ake zarginsa sam Rashida ta musa tace mijinta sam ba haka yake ba amma da ta ga yanda yayana da take rena na matan da ya rabu dasu suke mutuwa tasha jinin jikinta. hakan yasa ta tsaya tsayin daka akan yayanta ba dare ba rana tana nema musu kariya a gurin ubangiji ko ishashen bacci ta dena yi ta na ganin in ta runtsa to ze zo ya kashe ta da yaran su.

Abun duniya ya yi wa Attajiri Tahir yawa hakan yasa ya shiga mawuyacin hali saboda ya rasa da su waye ze yi sadokarwa kowa ya gujesa hatta yara sun gujesa.

Lokacin sadokarwa da yayi be yi ba saboda be samu ba,daga nan ne ya fara jinya da kadan-kadan ya kwanta ya zamana komai se an masa kafansa yazo ya fara ciwo ba inda baa yi yawo dashi ba amma ba a samu maganin wannan ciwo ba. inda daga karshe kafa ya ruɓe ya fara wari,duk jinyan da yake yi Rashida ce akan sa da kuma ƴaƴanta tunda yaransa da ya haifa da sauran matan duk ya kashe su.

Ranan da Attajiri ze mutu wannan aljani ya kawo masa ziyara ya kwace zoben da ya basa. sannan kuma ya sanar dashi tabbas ruhin wayanda ya kashe bazasu taɓa samun ƴanci ba se an musu kyautan salihin ruhi in ba haka ba zasu fara cutarwa daga lokacin da suka kai shekara uku a cikin wannan akwatin.

Yana gama sanar dashi wannan bayanın kuwa Attajiri Tahir ya soma aman jini me guda-guda ko da Rashida da yaransu suka zo kansa kuka kawai suke ganin halin da yake ciki a nan ne ya bawa Rashida labarin kowai be boye mata ba yana gama sanar mata kuwa ya mutu. Sosai ta yi kuka jin abubuwan da mijinta ya aikata marasa kyau ga shi be tuba kafin barin wannan duniyar ba.

Tsaban yanda yake wari dakyar aka samu sirarun mutane da basu wuce goma ba aka sallacesa aka kai sa makabarta aka binne.

Ko da aka zo ana maganar rabon gado Rashida sanar da mahaifin ta yi wannan dukiya na Attajiri ba halattatun kudi bane duk kudin jini ne dana haram hakan yasa aka haɗa kudin aka konasu. A gidan tayi takaba sannan bayan takaba maza suka dinga fito mata da zumbar aure amma taƙi,domin ita so take yi ta tsaya akan yaranta taga rayuwar su ya inganta ba ta son su yi rayuwar kaskancin da uban su yayı hakan yasa ta soma sana'a daga gıda tana kulawa dasu.

Bayan shekara uku ne fa suka fara fuskantar mugayen abubuwa a cikin gidan inda daga karshe fatalwayen suka shiga jikin yar ta mace wacce ta kasance budurwa suka haukatata ta dinga jiwa kanta ciwo kamar de yanda siyama take illata kan ta daga karshe suka kasheta ta hanyar sanyata ta yi hanging din kanta a bishiya ta mutu sannan suka ɗauke ruhinta. Dama ruhi biyu suke bukata sun samu daya saura daya.

Daga nan ne fa Rashida ta sa aka haɗa komai na Attajiri Tahir aka kulle masa su a bangarensa da ƙaton kwaɗo sannan suka bar gidan suka bar kauyen. Basu sake waiwaya ba se bayan shekaru masu yawa inda Musa Tahir yake bukatar bunkasa kasuwancin sa da tunanin duk ma abinda yake gidan yanzu babu shi yasa ya siyar da gidan.

Wannan shine takaitaccen tarihin Attajiri Tahir da abinda ya aikata inda ya kashe rayukan ƙananan yara bila adadı haka zalika mata masu ciki,wannan dalilin yasa har yanzu suke cikin wannan gida tare da fatan wata rana zasu samu salihin ruhin da ze yi sanadiyyar zuwan su duniyar da ya kamace su”…

Sosai jikin kowa ya mutu bayan jin tarihin wannan bawan Allah da babu abinda ya sani sama da zalunci da son duniya,domin jin dadin sa ya raba rayuka da yawa da wannan duniyar gashi ta dalilinsa Siyama na kokarin rasa rayuwarta.baiwar Allah bata ji ba bata gani ba tana shan azaba.

“Kun ji irin zaluncin da aka yi mana?kuna tunanin saboda son ran mu muke aikata musu haka? Muna aikata musu hakan ne dan kawai mu samu salihin ruhin da zamu bar wannan duniyar mu bar kowa ya huta…muna so mu nesanta kan mu da duniyar bil adama. Bama son yanda aka zalincemu muma mu zama azzalumai,ruhi daya kawai muke bukata daga nan kuma mun tafi na har abada babu wanda ze kuma shan wahala ta dalilin mu. Mahmoud ka yafe mana mun san mun wahalar dakai da matar ka amma yanzu ma zamu sake aikata maka wani laifin zamu ɗauki rayuwar matar ka domin zuwa duniyar da ya dace damu “ cewar Siyama tana miƙewa tsaye idanunta na zubar da hawayen jini

Miƙewa kowa yayi,Mahmoud ya so ma matsowa kusa da ita yana girgiza kai a yayinda ita kuma take ja baya tana sakar masa murmushi.

“Ah ah na roke ku ku rabu dasu,Ina kyautar ruhi ku ke so? Ku ɗauki nawa dan Allah ku rabu min da matata” ya yi maganar hawaye na zarya a idanun sa da suka koma ja tsaban kukan da ya yi dazun.

Malam ne ya ce “Duk mun fahimce ku,kuma mun fahimci manufarku,amma ku tuna Siyama da ɗan cikin ta basu aikata muku laifin komai ba shin meyasa zaku rabasu da rayuwar su?”

“Hakan ya zama dole a gare mu,zalunci ne da Attajiri Tahir ya aikata mana da ya zama na dole se mun tafi mun bar wannan duniyar domin haɗuwa dashi a gaban wanda ya kawo mu wannan duniyar a yi mana hisabi”

Ta gama maganar tana sa hannu ta soma naushin cikinta da karfi.

Fashewa da kuka su mama suka yi dasu hajiya cikin tashin hankalin ganin da gaske kashe siyaman zasu yi kamar yanda suka faɗa.

“Innalillahi wainnailaihi rajuun,na shiga uku yanzu laifin da kakana ya aikata shekaru da suka gabata shine wayanda ko sanın mu ma basu yi ba suke karɓan hukunci? Tabbas in akwai wanda za ku ɗauka to ni. ne ku ɗauki ruhina domin ni ne jinin sa na roke ku ku Kyale wannan Matar da cikin ta” cewar Alhaji Musa Tahir yana kuka.

“Shin me ku ke tunani da muka ce dole se salihin ruhi muke so? Salihin ruhi shine ruhin ƙananan yara da kuma mace me ciki ko kuma budurwa. Ruhin da muke bukata kenan,ban da su kuma bama bukatar wani ruhin “

Tana gama fadin haka ta nufi upstairs da gudun gaske

Da wani irin speed Mahmoud ya bi bayanta yana kiran sunanta

“Siyamaaaaaaa” tana haurawa ta hau kan karfen ta tsaya tana sakar musu murmushi

İn banda ihun kiran sunan ta da kuka da suke yi babu abinda suke yi jikin su na rawa.

Ta daka tsalle zata faɗa kenan yayı dede da isowar Mahmoud ya cafke hannunta na hagu ya riƙe hannun gam a yayinda cikinta ya bugu da karfi a jikin karfen stairs din. jawo ta yi ya sauko da ita yana kwantar da ita a kasa ganin tana a sume. da gudu duk suka hauro ganin Mahmoud ya yi nasaran ceto ta,tsayawa suka yi akan su kafin a hankali suka lura da jinin dake bin kafafunta. Bakin hayaki ne ya fito daga jikinta ya koma suffan mace tana riƙe da farin haske me suffan ɗan ƙaramin jariri duk tsayawa suka yi suna kallon wannan matar.

A hankali ta buɗe idanunta ta sauke sa akan jaririn da ke hannun fatalwan

“Ya Mahmoud jaririn mu “ ta faɗa murya a kasalance tana fadan haka fatalwan ta yi murmushi ta re da ɓacewa ita kuma siyama ta kuma suma.

FIVE HOURS LATER

buɗe idanunta tayi hasken da ta ci karo dashi ne ya sa ta rufe su da sauri tana yamutsa fuska kafin a karo na biyu ta kuma buɗe idanunta. nan ta gan ta kwance a gadon asibiti hannunta na manne da cacular ana mata ƙarin ruwa da kuma jini. Slowly ta kai idanunta kan cikin ta

Dammm haka kirjinta ya buga lokacin da ta ga babu ciki a jikinta. Runtse idonta tayi ta kuma budewa domin gasgata abinda ta gani mafarki ne ko kuma zahiri tabbas yanzu bata ga cikin jikin ta ba. Cikin kiɗima ta soma sauka akan gadon jikinta na bari domin tana son karin bayanın ina cikinta ya shiga.

Wata nurse ce budurwa ta shigo dakin domin duba ta taga ta farka tana kokarin sauka kan gadon yasa ta yi saurin rikota tana

“Madam ki yi hakuri ki koma ki kwanta kina bukatar Hutu sosai saboda condition din ki”

Tsayawa tayi tana kallon nurse kafin ta ce

“Sis dan Allah ki faɗa min me yasa me ni na gan ni a asibiti?ina cikin jikina?ko na haihu ne?shin bakwaini na haifa an sa shi a kwalba ne”

Cikin tsananin tausayinta nurse ta ce

“Am so sorry madam ɗan cikin ki ya mutu an ciresa sannan an miki wankin ciki”

Kallon nurse din take in disbelief

“Kina so ki ce ɗan cikina ya mutu?”

“Kwarai madam am sorry for your loss “ a hankali ta sulale ta fadi a kasa tana fashewa da kuka tare da fadin

“Shikenan sun yi nasaran rabani da ɗana,sun yi nasara “ta fada da karfi cikin muryar kuka kafin ta sa hannu ta fiske karin ruwa da jinin da aka mata

“Me ki ke yi hakan kina bukatar ki nutsu saboda baki gama samun sauki ba”

“Shikenan na rasa jaririna,shikenan sun tafi dashi “ta fada tana sa hannu ta tarwatsa magungunan da alluran da suke kan table din gadon ta,kamar wasa ta burkice ta fara fashe fashe da kuma fis-fisge labulan dakin da shimfidan gadon ta da duk abin glass dake dakin tana yi tana kuka me tsumma zuciya tana cewa tana

“Sun raba ni da jariri na”

Da gudu nurse din ta bar dakin ganin abinda take yi tana fita ta tarar da su Mahmoud da kowa a waiting area ko kallon su bata yi ba taje ta kira doctor ganin yanda nurse da doctor ke rige-rigen shiga dakin da siyama take ne yasa suma suka rufa musu baya suna shiga suka ga yanda Siyama ta yi kaca-kaca da dakin.

Nufanta doctor yayi da alluran bacci a hannun sa da niyan yi mata amma se jifan shi take yi.

Da sauri Mahmoud ya raba gefen doctor yaje ya rungumeta

“Ya Mahmoud shikenan sun rabani da yaro na,bazan samu daman kallon ɗana ba? Ya Mahmoud meyasa se ni ?mena aikata musu suka zaɓi su kuntatawa rayuwata? Sun rusa min farin ciki na whyyy?” Ta faɗa tana fashewa da sabon kuka. shi kansa kukan yake son yi amma ya danne domin in ya fashe da kuka waye me lallashin wani.jikinsa ya mutu sosai ba shi kaɗai ba duk wanda ke dakin se da ya matukar tausayawa siyama

“Shissh…. Ki yi hakuri my siyama mu kuma wannan shine jarrabawan mu. Allah da ya bamu wannan shi ze ba mu wani. Ki yi hakuri my siyam “

Sosai take kuka tana kokarin kwace jikinta amma yaki sakinta

“Na so in dauki yarona a wannan hannayen nawa kamar yanda ko wace uwa take daukan jaririn ta se de ni nawa ya tafi batare da na samu dama ganin ko da fuskansa ba balle in ji duminsa”

Haka ta dinga sambatu kamar zautacciya duk yanda Mahmoud ya so ya rarrasheta ta ya gaza a wannan lokacin ya gagara danne hawayensa saboda shi kan shi rashin dan su ya jijigasu amma ya zasu yi Allah da ya basu shi ya fi su son shi.

Alama yayı wa doctor da ido batare da ta sani ba kawai ta ji an sikara mata allura kafin ta farga har ya mata a take bacci ya yi awon gaba da ita a jikinsa mayar da ita kan gadon yayi sannan doctor ya mayar mata da ruwa da jinin da ta cire.

A haka suka dibi har satı daya a asibiti. kullum suna tare da ita amma ita baa cewa komai ta dena magana abinci ma se an yi dakyar take yarda tacı nan ma ɗan kaɗan,ko sun zo haka zata lumshe idon ta kamar wacce ke bacci gaba daya ta lalace saboda damuwan da ta sanya aranta se da mama ta yi mata fada sosai ranan da zaa sallameta akan rashin tawakkali. Sosai ranan ta yi kuka har suka koma gıdan su wato gidan iyayen ta domin kuwa wannan gida na Attajiri Tahir Alhaji turaki da Alhaji Musa Tahir sun mayarwa da Mahmoud kudin sa tare da basa hakuri sosai akan abinda ya faru. Sannan kuma gidan aka rusa shi gaba daya aka gına katon masallaci a gurin.

Mahmoud kuwa gidan su na da,da suka baro yasa aka yi masa gyare -gyare aka sa komai sabo a gidan wai duk dan in siyama ta yi farin ciki in sun tare.

Kwana biyu ta yi a gidan su ta ɗan warware ba laifi ba kamar da ba amma bata gama recovery daga shock din rasa jaririnta ba abubuwan da suka faru har yanzu suna dawo mata.

Ranan da zasu koma gidan su Hajiya da familynta suka zo gidan su siyama bayan gaishe-gaishe ne suka dan soma hira suna zaune se ga Mahmoud da Bilal sun shigo da malam bude taro yayi da addua sannan ya soma yi musu nasiha

“Na yarda wannan abinda ya faru da Siyama da Mahmoud ya zama darasi a gare ku,damu baki daya. Abinda ya faru abu ne kamar a shirin wasa wanda babu wanda ya yi tsammanin faruwan sa amma idanun mu sun shaida mana komai. Abubuwan da ake yi a wannan duniyar domin neman abin duniya da ɗaukaka suna da yawa,mu na iya Attajiri Tahir mu ka sani,akwai wayanda suke aikata fiye da abinda ya aikata.akwai wayanda suke zuwa makabarta dan su tono gawar mace su aikata alfasha da ita,akwai wayanda suke tona kabari su binne laya,akwai wayanda suke zina da mahaukata dan kawai neman abin duniya. Duniya ta zama abin tsoro yanzu muna rayuwa ne tare da mutane masu son zuciya kuma masu bujirewa ubangiji. Muna mantawa zamu mutu,zamu je gaban mahaliccinmu mu tsaya ,muna mantawa da duk abinda mu ke yi yana kallon mu,muna mantawa da kwanciyar kabari da azabarsa,muna mantawa da azaban wutar jahannama. Sannan wannan duniyar da muke faɗa da aikata mugayen abubuwa akan sa mun manta da cewa wata rana zamu bar sa ko mun shirya tafiya ko bamu shirya ba.

Allah ka tsare mu da aikata sabonka,ka kare daga aika shirka.

Se kuma batu akan bin iyaye,kun ga iyaye?ba abin wasa bane mutum in de ya fika ya fika wannan dalilin yasa hausawa suke cewa abinda babba ya hango yaro ko da ace tsauni ze hau baze taɓa hangowa ba. Daga lokacin da iyayen ka suka ce bari ka bari saboda su sun fi ka shekaru da hangen nesa. Duk da wannan abinda ya faru daku Allah ya kaddara amma yanada nasaba da rashin biyayyan da baka yi wa mahaifiyar ka ba,saboda ta nu na maka ran ta baya so amma ka bujire mata ka yi son ranka.

Sa’anan ana son duk ma’aurata su kasance masu so da kaunar junan su kuma hakan ba ze yu ba har se sun kasance sun yarda da junan su in babu yarda to tabbas babu soyayyah. Duk abinda abokin zamanka yace maka gashi-gashi yana da kyau a tsaya a yi bincike sosai domin gudun abinda ba a fata.

Allah yasa mu dace.

Siyama” ya kira sunan ta bayan ya gama jawabinsa,jiki a sanyaye ta ɗago ta dubesa sannan ta kuma sunkuyar da kai

“Siyama kiyI hakuri,kiyi hakuri siyama tabbas kin shiga cikin jarabawa kin fuskanci kalubale matuka,in da har yakai ki da rasa rayuwar ɗan ki….kiyi hakuri ki manta da komai Allah ya rigada ya rubuta hakan a kaddaran ki se ya faru,Allah kuma ya ba ki ikon cinye sa,ɗan da ki ka rasa kuma in sha Allah,Allah ze azurta ki da wasu yayan masu albarka. Ki yi hakuri kin ji in sha Allah komai ya kare wancan gidan kun da kaina naje aika yi sauka a gidan Allah ze kare ku da kariyarsa“

Murya a sanyaye ta ce “ameen ya Allah an gode sosai malam”

Murmushi ya yi yace “Masha Allah “ sosai ya sake mu su wani nasihan akan rayuwa kafin ya musu sallama ya tafi su kuma suka raka Siyama izuwa gidan su.

Bayan kowa ya watse dare ya yi ne ta fito daga wanka ta samu Mahmoud yana zaune fuskansa ɗauke da murmushi,mayar masa da martanin murmushin itama ta yi kafin ta ce

“Ya Mahmoud wani abun alkairin ne ya faru?”

“Yes my Siyam in ba ki manta ba da bikinmu na miki alkawarin zuwa honeymoon amma Allah be yi ba saboda visa ki da ya makale yau Ina fita office aka kirani aka ce min ya fito dan haka ki shirya zamu tafi India cin amarcin bayan biki”sosai hakan ya mata dadı at least in suka bar kasan na wani lokaci zata manta da sorrows din ta. Rungumesa tayi cikin farin ciki.

A cikin kankanin lokaci suka gama shirin tafiya India ranan tafiya kuwa yan uwa da abokan arziki aka musu rakıya izuwa airport.

Sosaima suke shan yawo gurare daban-daban a ƙasar India suna buɗe ido,ba laifi ta ji dadin ƙasan sosai domin yanzu ta koma Siyamar ta na da wacce murmushi baya gushewa akan fuskanta.sannan Mahmoud yana kulawa da ita sosai watan su biyar a can sun baje suna shan soyayyah kamar bazasu dawo Nigeria ba,Mahmoud kuwa daga inda yake yana business din sa online komai na tafiya dede kullum se sun yi waya da yan gida.

Kwatsam Siyama ta fara laulayi da kuma fever me zafi sosai Mahmoud ya shiga damuwa ya ɗauketa suka tafi asibiti suna zuwa kuwa gwajin farko aka shaida musu tana da cikin wata uku sosai suka yi farin ciki tare da kukan jin dadi. Suna dawuwa gida Mahmoud ya Kira yan uwa yana shaida musu sosai kowa ya yi farin ciki dajin wannan daddadan labarin.

“Ya Mahmoud ban taɓa tsammanin zan samu ciki nan kusa ba,Allah na gode maka da ka nu na min wannan rana cikin karamin lokaci tabbas Allah shine me yin yanda ya so a duk lokacin da ya so. Allah ya raya min abinda ke cikina”

“Ameen summa ameen my Siyam. Ko da yaushe in na yi sallah dare Ina me rokon ubangiji da ya azurta mu da wani dan dan kawai in ga kyakyawan murmushin ki da na jima ban gani ba se ga shi yau Allah ya cika min burina a gaskiya na yi murna. Sannan anan zamu reni cikin mu ya girma mu haifesa anan shima ya zama ɗan India ko ya ki ka ce my baby?”ya tambayeta yana dariya,dariya itama ta sanya jin abinda ya faɗa wai jaririn su ya zama ɗan India gyara kwanciyarta tayi a jikinsa

“Ina matukar son ka sosai ya Mahmoud dina Allah yabar mu tare har abada”

“Ameen ameen nima Ina son ki sosai”

TO ALHAMDULILLAH!, ALHAMDULILLAH ALA KULLI HALIN,a nan nakawo karshen wannan littafin nawa me suna MAKIRIN IKO (the hunted house) wanda ya kasance gajeran labari ne akan wasu ma’aurata da suka haɗu da jarabawan rayuwa suka afka cikin wani gıda me ɗauke da shedanu batare da sanın su ba.

Sai mun haɗu daku acikin sabon book dina,Allah ya nuna mana lokacin da rai da lafiya

Don’t forget to comment on this last page and share fisabilillah 🥰🥰

Sonso daga Mrs Isham 🫶🏻❤️❤️☺️🥰🤗🤝

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol