Free chapter · Read without an account

8

by Azizat Hamza · CHEF ZEEY (Love in the Kitchen)


*CHEF ZEEY*
*Love In The Kitchen*

Topnotch season 4
©AzizatHamza2025
ArewaBooks @Azizat Hamza

8

                       ZEEY

Yau za mu ƙarƙare class ɗinmu da Hayfa. Sati uku muka yi maimakon sati huɗu da aka saka. Nima dama ina tunanin zan ɗau excuse saboda bikin Bestie na da za mu fara ranan Laraba sai kuma Hajiyar ta kirani da kanta ta ce tana so mu ƙare class ɗinmu a satin nan saboda ranan Tuesday ita da Hayfa za su je Dubai. Ai kuwa na ce ba matsala tunda nima zai zo min da sauƙi kenan, zan samu na sake a yi hidimar biki ba tareda wani abu ya riƙeni ba.

Jiya Saturday da na zo ban tafi ba har kusan ƙarfe tara na dare saboda mun yi tuwon Biski. Gaba ɗaya ilahirin gidan ya buɗe da ƙanshi. Lokacin da aka gama  hatta Hajiya Maryam sai da ta yaba da tuwon wai rabonta da cin tuwon Biski tun bata yi aure ba.
Hayfa kam ko a jikinta sai cewa ta ke ita bata da patient ɗin wannan ɗawainiyar. Na ce mata in har kuwa ba za ta yi haƙuri ba tuwon ba zai mata yadda ta ke so ba. Ta ce min oho dai tunda ba ita za ta ci ba. Duk da dai bata son tuwo amma yadda ƙanshin tuwon ya cika mata hanci sai da ta gutsiri kaɗan ta ci. Ta ce wai ƙanshin ya fi taste ɗin daɗi. Na ce ba ta san daɗi ba kuwa.

Alhajinsu na nan, kuma shima an zuba masa tuwon shi da wani abokinsa. Wallahi har da neman ƙari kuma babu saboda ba dayawa na yi ba. Nima na so na ajiye kaɗan in kaiwa Kaka amma duka komai ya ƙare. Da ke dama duk abincin da muke yi na class ɗin masu gadi da Direbobinsu ake bawa shi yasa komai nake kaɗan-kaɗan amma Tuwon Biskin da na yi sai ya yi Albarka tunda masu gidanma sun ci. Ina kitchen Hajiya Maryam ta zo wai Alhaji ya ce a kawo musu tuwon shi da baƙonsa wai ƙanshin tuwon ya hana su sakewa. Na yita murmushi ni kaɗai. Ashe dai masu kuɗi ma na son abincinmu na gargajiya.

Yau Sunday ba zan daɗe ba, dan Dambu kawai za mu yi, da shi zan ƙarƙare mata class ɗin. Tun da na ce Dambu zan yi Hajiya Maryam ta ce na yi dayawa wai ta jima ba ta ci shi ba. Ni abin ma sai yake bani mamaki, suna da kuɗi suna da mai aiki amma ba za su riƙa dafa irin waɗannan abincin ba. Koda ya ke mai aikin nasu ba Bahaushiya bace, intercontinental girki ta ke musu. To idan har suna son namu na gargajiya mi yasa ba za su ɗauko wacce za ta riƙa girka musu duk lokacin da suka buƙata ba?. Ko dai ni ce ban san ya masu kuɗi suke lamarinsu ba?. To ma ta ina zan sani ni dana taso gidan Talauci. Wallahi ko, ba dan Kaka ba, da a miskiniya zan taso bayan Babana ya rasu. Kuɗin Makarantana Kaka ce, kayan sawa da abincina duka Kaka ce. Allah Sarki lokacin da ta ke sana'a Wallahi ko nawa ne za ta cire ta yi mini hidima da shi. Jarrabawar WAEC ɗina na farko ita ta biya mini. Da zan gyara NECO dan da jarrabawar NECO nake amfani yanzu shine yaya Aminu ya biya mini.

Su fa mutanen gidanmu kowa ta kanshi ya ke yi. Ba dan na dage sai na yi Boko bama dan ta su ne kawai na je na yi aure. A gidanmu wanda ya damu da Boko shine Baffa Mamman, ya ɗan yi Diploma ya samu aiki a ABU as non Academic Staff, daga baya ya samu ya haɗa Degree a wajen. Ina ga ba zai wuce shekara uku bama da kammala Degree ɗinsa. Ya yi ta encouraging ɗina akan na yi karatu lokacin dana dage ina JAMB bana ci. Shi dai akwai bada shawara, amma sisinsa bai taɓa bani wai dan na yi hidimar karatuna da shi ba.

A cikin irin mutanen dana taso kenan. So ni ban san yadda masu kuɗi suke lamarinsu ba. Amma a ɗan zuwana gidan nan, na fara fahimtar wani abu daga irin rayuwarsu.

Yau ma kamar jiya, tun dana fara turara Dambu gidan ya buɗe da ƙanshin Gyaɗa da Zogale. Kun san abu da masu kuɗi Dambun namu ya ji hanta dumu-dumu. Ga extra veggies da zan sake zubawa idan ya kusa yi, na haɗa saboda komai ya tafi dai-dai da irin cimarsu.

Ina cikin kitchen ina danna waya Mai aiki ta shigo wai in je Hajiya na kirana. Dama tun ɗazu na ke jin voices kamar Hajiyar tana tareda baƙuwa.

Ajiye wayar na yi na fita daga kitchen ɗin na wuce falo. Hajiya Maryam ce da wata kyakykyawar mata, da ka ganta ka ga gogaggiyar 'yar Boko. Za ta iya kaiwa 50 koma 60 amma jikinta sam bai nuna tsufanta ba.

"Ita ce Chef Zeey ɗin?" Matar ta tambaya. Hajiya Maryam ta jefawa tambayar dan haka sai na ja na yi shiru ina ta blushing.

"Ita ce, Hajiya Layla. Ai jiya hatta Alhaji sai da yayi santin Tuwon Biskin da ta yi"

Sai a lokacin matar ta kalleni da kyau fiskarta a sake ta ce "Masha Allah, ai na kusan shekara ina following videos ɗinki a Instagram. Chef Zeey ina Kaks?"
Dariya na saka saboda bata manta yadda nake kiran Kaka a cikin videos ɗina ba. Shi yasa har a comment section idan ni na yi girki ba a ga hannun Kaka ba sai a riƙa tambayata ina Kaks ta shiga.
"Kin san Hajiya Maryam na jima ina cewa zan mata magana tunda a Zaria ta ke amma sai na basar ashe da rabon za mu haɗu ne" ta kalleni ta ce "gaskiya content ɗinki yana nishaɗantar dani, keep it up" murmushi ya suɓuce mini na fara yi mata godiya.

Yanzu wai wannan haɗaɗɗiyar matar ne ta ke cewa ina burgeta. Kai akwai daɗi fa wani da yake bibiyarka a social media ya nuna har a zahiri shi fan ɗinka ne. Musamman idan wanin babban mutum ne. Duk da ban san wacece matar ba, amma yanayinta kaɗai idan ka kalla za ka san babbar mata ce da duniya ta san da ita.

"Ai ina shigowa gidan nan da na ji ƙamshin Dambu ke na fara tunawa kwanaki na ga kin saka recipen a YouTube, shine ta ke ce min ai ke Chef Zeey ɗin ce a Kitchen. Gaskiya i'm happy to meet you. Gashi Hajiya Maryam ta ce yadda muke gani a video haka girkinki ke da daɗi a zahiri"

Hajiya Maryam ta ce "gaskiya ba laifi. In dai girkin gida ne ki bar wa Chef Zeey"

Har na koma kitchen ban dena blushing ba. Jina nake kamar wata celebrity. Ashe dai manyan mutane ma na kallon videos ɗina. Gaskiya dole na ƙara himma wataƙila na samu wanda zai min hanya Ɗangote ya bani tallen gishiri da Taliyarsa. Na sa dariya ni kaɗai.

"Wai abin nan ba zai yi bane. Tun awa nawa muke ta jira" Hayfa ta faɗa duk ta ƙagu a gama class ɗin da muke yau.

"Kar ki damu mun kusa gamawa" ta ɗan ja wani ƙaramar tsaki ta cigaba danna iPhone ɗinta. Jiya daɗewar da muka yi a kitchen ya dameta.

Ba zan yi wasa da damata wajen ƙara burge wannan Hajiya Laylar ba, dan haka dole na bi komai a hankali, babu rushing-rushing.

Lokacin da muka gama na serving Hajiya Layla da kaina na kai mata na tsaya a wajen ina jira ta taɓa ta ji ko ya yo daɗi. With Hajiya Maryam ban taɓa damuwa da yabawarta ba dan ba ci ta ke yi ba, ita damuwarta 'yarta ta koyi girkin ne. Jiya ne dai Tuwon Biskin da na yi ya tado musu sha'awar cin abincin gida.

Loma ɗaya Hajiya Layla ta kai ta ce "Masha Allah! Na jima ban ci Dambun da ya mini irin wannan ba"

Lokacin da ta kai loma na uku sai ta ce "Allah ya jiƙan Kakata Jamila, a wajenta na koyi cin Dambu"

Hajiya Maryam ta sa dariya nima na yi dariyar saboda gaskiya ba ƙaramin daɗi na ji ba jin cewa girkin da na yi ya tashi kanta.

Lokacin da Hajiya Layla za ta tafi sai ta ta bani kati da ke ɗauke da suna da numbarta. Mun yi maganar zan zo gidanta gobe nai mata Tuwon Biski itama. Ta ce min rabonta da cin tuwon ya fi shekara ishirin. Ban yi mamaki ba. Ina ruwan masu kuɗi da Tuwo, Tuwon ma na Biski.
Ta ce min idan na zo akwai maganar da za mu yi ɗanta yana son buɗe restaurant wataƙila zai iya ɗaukana aiki. Na ce mata nima ina da burin buɗe restaurant amma wanda za a riƙa yin abincin gargajiya zalla.

"I like the idea, Ziyadaah" ta ja ƙarshen sunan, sai hakan ya ƙarawa sunan daɗi. Karo na farko da ta kirani da sunana ba Chef Zeey ba tun haɗuwarmu da ita kenan.

Ina shiga kitchen na buɗe katin na karanta sunan da ke jiki LAYLA J. MAIYAƘI. Da sauri na kwafi numbar na saving a wayata.
Bayan na gama tattara kitchen ɗin sannan na fito na yiwa Hajiya Maryam sallama. Hayfa kam tuni ta koma ɗakinta dama a matse ta ke.

Da zan wuce sai Hajiya Maryam ta ce min idan na je wajen Hajiya Layla na yi mata tallen class ɗina tana da 'ya Janan wataƙila ta sakata yin class ɗin. Na yi mata godiya na fita. Kai anya ba zan ƙara kuɗin class ɗina ba kuwa, tunda dai sun ga aikina yana kyau.

Kai! ko Hajiya Layla ba ta ce za ta biyawa 'yarta Class ɗina ba zan iya koyawa 'yarta a kyauta. Matar ta burgeni ne. Ya jima ban haɗu da matar da lokaci guda ta shiga raina ba irin Hajiya Layla.

Dana isa gida na faɗawa Kaka abinda ya faru na ce mata Hajiyar ma na gaisheta ta ce tana amsawa. Da na ce ba zan sake yin aiki ba tunda satin bikin Bestie za a shiga amma gobe dole na je gidan Hajiya Layla, irin mutanen nan idan suna sonka za su iya buɗe maka ƙofa dan su ɗaga ka. Ga shi dai daga haɗuwa har tana cewa ko za a ɗaukeni aiki a restaurant ɗin da ɗanta zai buɗe.
Kafin na kwanta na shiga IG na searching sunanta, ai kuwa sai ga shi nan ta fito. Kamar yadda na yi hasashe babbar mata ce. Wikipedia na shiga a Google na karanta labarinta tsaf. A Zaria aka haifeta, bayan aurenta da Alhaji Kabeer Maiyaƙi sai ta koma London da zama, a nan ta yi karatu har matakin Phd. Lokacin da mijinta ya dawo Nigeria da zama gaba ɗaya shine ta ke shuffling tsakanin London da Nigeria, amma bayan rasuwar mijinta sai ta yi retire ta dawo Nigeria da zama gaba ɗaya. An ce tana da 'ya'ya uku amma ɗaya ya rasu a hatsarin mota shekara uku da suka wuce.

Wani abin da ya bani dariya gameda ita shine, a wani videonta dana ke kallo ana hira da ita ta ce sunan Kakarta ta ci wato Jamila, ake kiranta da Layla amma tun tasowarta take ƙin suna Jamila saboda basa shiri da Kakar tata.

"Na yi ƙoƙarin maida sunana Layla kawai amma mijina Allah ya jiƙan rai har ya rasu Jamila ya ke kirana baya son Layla shi yasa na bari" a dai-dai wajen ta yi murmushi. Irin murmushin da ya fi kuka ciwo ɗinnan. Ni da nake gani a waya ma sai da idona ya ciko da ƙwalla.

"Saboda son sunan da ya ke, yaron dana fara haifa sunan Jamil ya saka masa, unfortunately ya rasu few weeks bayan haihuwarsa. Na zo na sake haihuwa ya saka masa Jalal, then Jamal, akan autata sai ya mayar mata da sunana Jamila" wannan karan dariyar da ta yi dariya ne har zuciyarta.

"Amma itama kamar ni, ta fi son a kirata da ɗayan sunanta ba Jamila ba"

Mai yin shirin ne ya katseta da cewa suna Jamila dai ya ƙi karɓuwa a gidan Alhaji Kabeer Maiyaƙi.

Cikin dariyar Hajiya Layla ta ce "ka san bayan rasuwarsa menene abu ɗaya da na fi missing?" idanunta ya ciko da ƙwalla "yadda yake kirana da JAMILAH"  hawaye ne ya gangaro mata, aka miƙa mata tissue ta fara gogewa, a dai-dai wajen videon ya yanke.

Nima sai ga shi ina goge hawayen. Dama ga ni da saurin kuka idan na ga abun tausayi.
A nawa ɓangaren, cikin abinda na missing bayan rasuwar Babana, shibe yadda idan ya kira sunan ZIYADA a kowanni lokaci fatan na yi tsawon rai ya ke mini.

"Husnan wa Ziyada'... daga nan aka ce ya ɗauko sunan. Babana ba Malami bane, a tafsiri ya ji ma'anar 'ZIYADA' kuma ya saka min saboda na yi tsawon rai, na samu alkhairi, na samu rayuwa mai kyau...

Haka dai na kwanta cike da tunanin labarin Hajiya Layla Maiyaƙi...

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol