Free chapter 路 Read without an account

Chapter 35&36

by Nanameera 路 IMARA

*IMARA 馃拫馃拫*

35&36.

***.

Mikiya writers asso...

Kai tsaye makarantar su ya nufa, har sannan kuma ruwa ake sosai. Shiga makarantar ya yi har office 蓷in director saidai bai same shi ba, dan ya fita, shiru Abaan ya yi sai kuma ya fito daga gate 蓷in makarantar. Mai saida man fetur ya gani ya 茩arasa wajensa ya yi sallama cike da girmamawa ya ce

"Baba dan Allah ba kaga wata yarinya ba?, yar fara haka"

Shiru ya yi sai kuma ya ce "to ina yawan ganin fararen yara suna fitowa daga makarantar nan, amma da zan ga koda hotonta zan iya shaidata"

Wayarsa ya ciro ya nuna masa wani hoton Imara wanda batasan ma an dauke shi ba. Saurin jinjina kai ya yi ya ce "Eh tabbas naganta. Yarinyar ta zo take tambayata hanyar da za ta yi ta kai ta Nassarawa G.R.A to na ce dai ta samu me Napep ya kai ta, kuma ina ganinta ta hau Napep" shiru Abaan ya yi sai kuma ya yi masa sallama ya koma motarsa. Indai har ta shiga motar zuwa Nassarawa to tabbas tana cikin unguwar kenan.

***Banda kuka babu abin da Nana ke yi ta takure waje guda, kallonta Mamah ta yi ta ce"za ki gane bakida wayo, saboda rashin hankali ki tawo ki barta acan bayan kinsan yarinyar ba yar nan ba ce. Duk abun da ya sameta ai mune a ciki tunda ba茩uwarmu ce"

"A'a Mamah maybe fa ko ganin yarinyar ne ba ta yi ba, kuma kinga an tashi daga makaranta ai mutum so yake ya dawo gida, ko Nana?"

Da sauri Nana ta 蓷aga kai tana kallon Jidda ta ce"A'a Aunty Jidda ba haka bane, na ganta fa, na ce mata ta taso mu tafi ta yimin banza, sau uku ina kiran sunanta ko kallona ba ta yi ba saboda lokacin tana tsaye da wani 蓷an ajin mu, daman ko a aji bata nuna ta sanni ba, shiyasa kawai na tawo na barta"

Ta 茩arashe maganar tana kuka, cikeda masifa Jidda ta ce"ni daman nasan wlh akwai saka hannun ta, saboda tun da naga yarinyar naga tanada rawar kai" tsaki Mamah ta yi ta ce"ba sai ki kira waya ki fa蓷a ba, ai idan aka yi mata magana za ta tawo ko?" Tashi Jadda ta yi ta kama hannun Nana tana cewa

"Karki wani ce za ki yiwa yarinya masifa, tun da ita waccen ce taga tafi 茩aunar zama a makaranta. Ke mu je ciki" daga haka ta ja Nana suka bar parlon, shidai Abbiey shiru ya yi bai ce komai ba yana kallonsu. Umaima kuwa girgiza kanta ta yi dan ta tabbatar Nana 茩arya take, babu yanda za'a yi Imara ta 茩i yarda ta dawo gida, tunda bata da inda ya fi nan.

***Wani burki ya ja ganin ya kusa karo da wata mota, ya yi tsaki sannan ya sake kunna motar, 茩in tashi ta yi ya gwada har sau uku taki koda motsi. Sauka ya yi lokacin ruwan ya daina zuba sai yayyafi, tayar motar ya kalla yaga ta yi faci ya ja tsaki. Kasancewar ya kusa gida yasa ya fara tafiya yana kalle kallen hanya ko zai hangota. Can gefe ya hangeta a tsugune fuskarta a rufe, babu ko haufi ya 茩arasa inda take ya dafata, a razane ta 蓷ago tana wani irin numfashi. Tsungunawa ya yi a gabanta ya shiga girgiza ta, fa蓷awa tayi jikinsa tana wata iriyar karkarwa, rungumeta ya yi tsam a jikinsa ya shiga shafa kanta cikin cool voice yake fa蓷in

"Sorry dear, I'm here, nutsu kinji"

Ko ka蓷an Imara ba ta jin abin da yake cewa, dan gaba蓷aya hankalinta baya jikinta. Tashi ya yi da ita a jikinsa ya yi mata 蓷aukan jarirai, bata da nauyi ko ka蓷an hakan yasa ya fara tafiya toward direction 蓷in gidan.

Har sannan suna zaune a parlon babu wanda ya tashi, da sauri Mamah ta 茩arasa inda yake tana kallonsa ta ce"lafiya?, meya sameta?" bai ce mata komai ba ya shige ciki da ita, ajiyar zuciya Mamah ta sauke tana dafe 茩irjinta, murmushi Umaima ta yi sai kuma ta shige ciki da gudu itama. Jidda da ba茩in ciki ya isheta taji 茩irjinta ya fara yi mata nauyi ta yi saurin fita daga apartment 蓷in, da idanu Abbiey ya bita sai kuma ya ce

"Alhamdulillahi"

Murmushin jin da蓷i Mamah ta yi ta ce"har naji da蓷i wlh" jinjina kai kawai ya yi sannan ya tashi ya bar parlon. Shi kuwa oga Khalil wani irin abu ne ya zo ya tokare masa zuciya, idan ya bu蓷e idanunsa babu abin da yake gani sai Imara kwance a jikin Abaan, takaici yasa ya bar falon without looking at anybody.

***Fitowarsa kenan daga wanka ya kalli inda take a kwance, har sannan bacci take, numfasawa ya yi sannan ya 茩arasa gaban mirror ya shiga gyara jikinsa. Saida ya shirya tsaf cikin wasu kananan kaya, riga armless milk colour sai wanda cargon 3-quater ba茩i, gashin kansa yasha gyara sai she茩i yake, ya feshe jikinsa da turaren roja. Fita ya yi daga 蓷akin ya zauna a parlon yana kallon Al-jazeera. Yana nan zaune har lokacin magrib ya 茩arato, kasancewar ruwan ya sake dawowa yasa basu fita masallaci ba kowa ya gabatar da sallah a gida.

A hankali ta shiga bu蓷e idanunta tana kallon inda take kwance, tashi zaune ta yi tana jin jikinta na wani irin ciwo, ga kuma zazza蓳i wanda har sannan bai saketa ba. A hankali take sauke numfashi saboda yanda 茩irjinta yake a cure, tuna abin da ya faru ta yi sai kuma ta fashe da kuka, wanda hakan ya yi daidai da shigowarsa. Kallo 蓷aya ya yi mata ya 茩arasa inda take ya kama hannunta ya zare drip 蓷in, bai kalleta ba ya juya zai fita.

"Ni ka mayar dani gida, wlh bazan sake zama anan gidan ba, banaso, bazan sake zuwa makarantar ba!"

Juyowa ya yi ya watsa mata wani shegen kallo wanda ya sanya ta sunkuyar da kanta ya juya ya fice ba tare da ya ce mata komai ba, sake rushewa tayi da wani sabon kukan na shareta da ya yi ta kwanta akan gadon tana burgima.

Sai wajen 茩arfe 8:30pm sannan ya dawo 蓷akin, lokacin ta yi shiru sai kalle kalle take a kwance, zama ya yi gefen gadon ya kalleta ya ce"ke tashi anan" tashi zaune ta yi ta tana kallonsa, cikin whiskey voice ya ce

"Koda wasa kar na sake jin kin ce wai ba za ki je makaranta ba, ko ke baki son makaranta, dole ne ki je makaranta, dole ne kiyi karatu, kuma dole ne ki zauna a gidan nan. Sannan irin haka banason ta sake faruwa ki tabbata kun dawo tare kullum, idan ita tanada baki ke bakida shi ne!?"

Yanda yake maganar babu wasa ya sanya ta sunkuyar da kanta tana hawaye kawai. Turo 茩ofar ta yi ta shigo tana sunkuyar da kanta, zama ta yi a 茩asa ya kalleta ya ce

"Khadijah!"

Cikin rawar murya ta ce "na'am Yaya"

"Nasan abin da kika fa蓷a ba shine abin da ya faru ba, kece kika tawo ki ka barta, koda ban je na tambaya ba nasan abin da za ki iya aikatawa, ita 蓷in ki 蓷auketa matsayin 拼ar uwarki kuma 茩awarki, ba zaku shige shekaru 蓷aya ba saboda haka banason jin tashin hankali, duk ranar da irin haka ya sake faruwa ko kuma kika yi mata gori zan tabbatar da cewa na hukuntaki kamar yanda na fa蓷a miki. Saboda haka ku zauna lafiya, ku je makaranta tare ku dawo tare, tashin hankali ba naku bane, banason fa蓷a banason ba茩ar magana kin ji ko?" Cikin rawar murya ta ce

"In sha Allah bazan sake ba, Imara dan Allah kiyi ha茩uri" ta fa蓷a tana kallonta, shiru Imara tayi tana kallonta ita ma

"Ba ki ji abin da ta ce ba?"

Murya can 茩asa ta ce"na ha茩ura, kema ki yi ha茩uri" tashi Nana tayi ta zo ta rungumeta, murmushi suka yi a tare ya kallesu ys ya ce "ku tashi ku je" jan hannunta Nana ta yi suka fice daga apartment 蓷in nasa. Akan idanun Khalil suka fito daga 蓷akin, kwafa kawai ya yi sannan ya bar wajen. 茒akin Nana suka shiga, ita dai Imara sai bin ta take da kallo, ganin ta tsaya yasa Nana ta ce"ki zauna mana, bari na kawo mana abinci" a gefen gadonta Imara ta zauna ita kuma ta fice daga 蓷akin.

***茒ago kanta ta yi tana share mata hawayen ta ce"Jidda, ki daina wannan kukan, kinsan dai ni a rayuwa banason naga abin da zai saka ki kuka, in dai Abaan ne ki daina damun kan ki" cikin shasshe茩ar kuka ta ce"wlh Mommy banason ganin yarinyar nan, ni kawai so nake na daina ganinta. Ko kuma Abaan ya daina ganinta, ko dai ta bar gidan ko kuma ni da Abaan mu bar gidan, kawai a dawo da maganar saka ranar auren nan dan Allah Mommy, ki fa蓷awa Abbiey, nagaji da jiransa, dan Allah Mommy wlh idan ba haka ba za'a samu matsala, zan iya kamuwa da ciwon zuciya" saurin rufe mata baki ta yi ta ce"kar na sake jin kin fadi irin wannan maganar, ki saka a ranki kamar an yi auren ki da Abaan an gama. Za ki aure shi nan da 蓷an lokaci wanda ko ke ba kiyi tunani ba"

Goge hawayen ta shiga yi ta ce"Nagode Mommy, nasan duk abin da nakeso za ki yimin" shafa kanta ta yi ta ce"zan yi komai saboda ke gudaliya ta"

Washegari da wuri suka shirya driver ya 蓷aukesu, tare duk suka tafi aka fara ajiye su sannan aka 茩arasa da Umaima, yau a waje 蓷aya suka zauna sa蓳anin ji da suka raba wajen zama. Kasancewar duk suna da kokari yasa suka iya karattunka su na ranar 茩arfe 4 suka fito daga lecture kamar jiya. Suna tafiya a second floor ya hangesu, 茩arasowa ya yi suka gaisheshi, murmushi ya yi ya ce"Imara ko?, ya kike ya gida?" cikin sakin fuska ta ce"Alhamdulillah sir" jinjina kai ya yi ya ce"ba dai gida za ki tafi ba?" gya蓷a masa kai tayi kawai ya ce"to mu je sai nayi dropping naku" kallon Nana tayi sai kuma ta girgiza kanta ta ce"a'a driver ya zo 蓷aukar mu yana 茩asa, Thank you" 蓷an murmushi ya yi ya ce"okay tom sai gobe" sallama suka yi masa sannan suka cigaba da tafiya. Saida suka sauka 茩asa Nana ta kalleta ta ce"wato daga zuwan ki makaranta har kin yi saurayi ko?, sai na fa蓷awa Uma" kwa蓳e fuska Imara tayi tana kallonta ta ce"mene haka dan Allah, kina gani fa malami ne, wane ya ce miki cewa ya yi yana sona?" Tuntsirewa da dariya Nana ta yi ta ce"ai idan kaga kare na shinshinar takalmi to 蓷auka zai yi, wlh ko kaffara bazan yi ba sonki yake, kinsan yanda yake ignoring mutane kuwa, ta蓳" turo baki Imara tayi ta ce"to nidai babu ruwana, dan ni ba yar iska ba ce, karatu nazo yi ba soyyaya ba" dafata Nana ta yi ta ce"kin ga Malama lokacin abu a yi shi, idan mun je gida ki cewa Yaya ko Abbiey a siya miki waya saboda assignment, kinga sai ku dinga gaisawa ko?" kallonta Imara kawai tayi sai kuma ta shige mota ba tare da ta bata amsa ba.

***Driver na yin parking ta bu蓷e motar ta fito tana ri茩e da takardun ta, a 茩ofar entrance 蓷in gidan ya ganta tana 茩o茩arin shiga

"Imara"

Juyowa ta yi sai kuma ta 茩ara inda yake zaune ta sunkuya ta gaida shi, murmushi Khalil ya yi ya ce"an dawo?" gya蓷a masa kai ta yi ya ce"sannu, fatan dai kina 茩o茩ari?" gya蓷a masa kai tayi tana murmushi, daidai nan Nana ta 茩araso wajen ta kalleshi ta ce"yawwa yaya dan Allah ka siya mata waya, ana bada assignment kuma batada ita" murmushi ya yi ya ce"to shikenan kuje ku huta, idan anyi magrib sai muje shopping right?" Tsalle Nana ta shiga yi ta ce"yawwa shiyasa nake sonka" ta janye hannun Imara suka shiga gidan.

Mamah ce zaune a parlon sai Jadda tana faman aikin bada labari, tana ganinsu ta ce"an dawo?" murmushi Nana ta yi ta ce"kuma yunwa muke ji Mamah"

"To acici ke wannan yarinya wanda ya aureki ya gamu da wahala, ba zaki bar masa abinci ya huta ba"

Kallon Jadda ta yi sai kuma ta murgu蓷a mata baki ta ce"to ai naga Abbiey ne dai ya siyo abincin" sakar baki Jadda tayi sai kuma ta ce"Muhammadu Rasulullahi, au gori za ki yimin, to ai ko shi uban naki da ban haifeshi ba bazai samu dukiyar da har kike ta茩ama da ita ba" 蓷aga kafada Nana tayi tana tafiya ta ce"ai ko baki haifeshi ba wata zata haifeshi" kwafa Jadda tayi ta ce"za ki zo har nan ki sameni" .

Kallon Imara tayi wacce ke tsaye ta ce"yawwa 拼ar albarka je ki 蓷akina ki daukon wata roba a kusada gadona ki zo na baki abin da蓷i" to Imara ta ce sannan tayi apartment 蓷in Jaddan, Murmushi kawai Mamah tayi tana binsu da kallo.

Around 7pm Umaima ta shigo tana kallon su ta ce "naga kun yi shiri ina za ku je?" Nana dake rolling mayafi ta ce "unguwa"

"Unguwa kuma?"

Umaima ta maimaita.

"Eh Yaya Khalil ne ya ce mu shirya zai kai mu shopping"

Turo 茩ofar 蓷akin ya yi ya shirya cikin wata shadda gezner blue colour sai zuba 茩amshi yake. Kallonsu ya yi ya ce"kun gama?"

"Eh Yaya mun gama"

Kallonsa Umaima ta yi ta ce"okay su ka蓷ai za ka kai shopping 蓷in kenan?" rankwashinta ya yi ya ce"sai na ce miki ki shirya" murmushi tayi sai kuma ta fita daga 蓷akin da sauri dan itama ta shiryo. Kallon Imara ya yi wacce take zaune gefen gadon, ba wata kwalliya ta yi ba dan atampa ce a jikinta ta sanya hijabi milk colour har 茩asa, murmushi ya yi sai kuma ya juya ya bar 蓷akin.

A compound 蓷in gidan suka sameshi yana tsaye jikin motarsa, 茩arasawa suka yi Ita dai Imara a hankali take tafiya, murmushi ya yi ya ce"wannan hijabin fa Imara?" kallon jikinta tayi sai kuma ta sunkuyar da kanta. Murmushi Umaima ta yi ta ce"Yaya ai kasan hijabin yafi mata kyau" jinjina kansa ya yi ya ce "to muje", gaban motar ya bu蓷e mata ta kalleshi sai kuma ta shiga a hankali. Shiga baya sukayi sannan shima ya zagaya ya shiga sannan suka bar gidan. Glasses 蓷in idanunsa ya zare ya tashi daga saman benan ya juya ya koma 蓷akinsa.

# *IMARA 馃拫*

# *Bestnovel*

# *Nanameera*

# *2025*.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol