Free chapter · Read without an account
15
KIWON KUBUBUWA
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
PAGE 15
Tartsatsatsaaa...! haka ƙaran fashewar plate me ɗauke da abinci ya sauƙa ƙasan tile ɗin babu zato ya samu fuskanta ya sharara mata mari cikin hantara da masifa kaman yadda ya saba treating nata ya soma zuba faɗa.
"Baƙar munafuka wato kin ji ina magana da kawu Labaran akan aurena shine kike so ki kasheni tun da kin gama morona ko? To wallahi ahir ɗinki kema kin san na fi karfinki a komai kawai kaddara ne ya hada mu har kika samu ake kiran ki matar Tahir banza kawai wacce bata da zuciya ke anya ba kare kika yar wa wannan zuciyar ya cinye ba? a yi mace bata san a gaya mata magana ranta ya baci ba? Toh Allah ya kyauta ya raba mu da irin wannan zuciyar aure kuma sai na yi sai dai ki faɗi ki mutu, zaki ga mace danya sharaf cikakkiya ba kaman ke ba da baki da maraba da kwalbar maltina... Sai ki shirya mutuwa"
Yana kai nan ya juya ya wuce fuuu.
ƙasa ta kai tana kuka sossai da sossai, tana zaune ne kawai gidan Tahir amma har ga Allah rayuwa da shi ya isheta gashi babu yadda ta iya iyayenta gani suke ita ke cin alfarmar Tahir ba shine yake cin alfarmarta ba kaman yadda shima yake ganin hakan, auren su da gaske na haɗi ne kuma na zumunci amma sai da suka nuna interest akan juna kan a haɗa su ɗin ba wai dole bane, babanta da mamanshi uwa ɗaya uba ɗaya suke.
Tashin farko ya nuna mata shi mai son rayuwa ne, yana son flexing da matarshi sossai sannan kuma baya daga cikin mazan da suke son haihuwa da wuri a akallah su mori juna tukuna kwatsam sai ga ciki, babu maganin da bai tula mata ba akan cikin ya bare shi bai shirya wani haihuwa yanzu ba cikin nan ya ƙi fita a karshe magungunan suka matuƙar illata yaron ta yadda ya fito babu lafiya sam kuma a kullum laifinta ne Tahir ke gani, ya daketa ya zage ta duk ba wani abu bane a wurinshi, planning ya yi mata amma sai da ta sake samun wani cikin gashi suna fama da jinyar babban ko tace tana fama don shi bayan kudin da yake basu ko kallon yaron baya yi wai baya son kazanta ga yaron ya iya dilalar da miyau, har sakin ta sai da yayi akan ciki na biyun nan don ta ƙi shan magani ya daka ya daka cikin ya ƙi barewa dole suka haife shi daga nan har waje ya fita da ita aka yi mata wannan planning da yake sanya mata rashin lafiya sossai, ya sa tayi ƙiba irin mai munin nan gashi dama bata da tsawo sai ta zama kaman kwalbar maltina ta bakinshi idan ya tashi zaginta, ta kai ƙara ita zai lauye maganar a ga laifinta a maimakon ya bata haƙuri sai ita ce zata dawo tana bashi haƙuri.
Hawayenta ta share ta miƙe ta fara tattare plates ɗin da ya fashe da abincin da tayi kuskure gishiri ya ɗan zarce, sam aurenshi bai dameta ba ai bulalar da aka daki uwargida da shi ake anfani wurin dukan amarya, ita a wurinta ma tunani take kila auren ya rage mata wasu wahalhalu tunda ba kullum ne zata ke ganinshi ba.
****
Kawu habu ne da isowarshi kenan ya kwaceta da kyar hannun Mama daga ita har maman kuka suke yi.
"Duka baya maganin taurin kai sai dai ya ƙara kangararwa kiyi hakuri a bi komai a sannu Maman Aliyu Don Allah".
Harara kawai take zabgawa Afnaan da ta rakube a gefe, sannu da zuwa ta mishi ta ɗauko taburma ta shimfida mishi a 'yar inuwarsu ta janyo kujera ta zauna tana bashi labarin abin da ta iske jiya gashi Aliyu tun da ya fita bata ganshi ba, ita tsoron ta kar ya shiga wani hali ta nuna mishi ko dole ne su yiwa Afnaan in ya so daga baya ta natsu ta dawo hayyacinta
"A'a Maman Aliyu ba za'a yi haka ba, kafin Yaya Bashir ya bar wannan duniya sai da ya bar min wasiyya kaman yadda yayi alƙawari dukkansu 'ya'yan shi ne da ba zai iya tauye ɗaya ya bar ɗaya ba ya kuma sa na mishi alkawarin ba zan taɓa yiwa ɗaya dole akan daya ba, na yi mishi alkawarin ba zan musu dole ba sai duk sun amince kan na ɗaura musu aure kinga kenan wannan magana bai taso ba, kaman yadda na faɗa miki jiya mu sake basu lokaci idan har ta nace lallai lallai shi wanchan ɗin take so a bata zaɓin ta"
"kawu ba zaka gane ba, bana tsoron halin da Aliyu zai shiga kaman yadda nake yi mata tsoron wanda zata shiga, wallahi ina yi mata tsoron haƙƙin Aliyu ina yi mata baƙin cikin hasarar soyayya ta gaskiya..."
Ta karashe hawaye na sake gangaro mata ta sa hannu ta share.
"Wani lokacin karatun duniya ya fi zama a kan bawa fiye da jawabin baki, Dukda akwai yaranta a lamarinta sai dai kuma son zuciya da butulci ya fi yawa duk babu matsala kowa ya ɗibo da zafi ai bakinshi".
Tana jin su daga ɗaki kuma hakan bai sa ta ji a ranta zata iya kin Tahir ta auri Aliyu ba, kaman yadda Jawahir ta ce wa zai ƙi daaɗi ya zaɓi wuya? Ai da tayi kuka a gaban murhun icce gwara tayi gaban gas.
"Aliyu me kake tunani haka da lokaci ɗaya jininka yayi hitting? Ga tarin damuwa da kuma stress a tattare da kai"
Likitan da yake duba file nashi ya faɗa, murmushi ya ɗan yi kawai wanda iyakarsa Fatan baki bai ce komai ba
"Zaka iya tafiya idan aka cire maka wannan ruwan amma gaskiya kana bukatar hutu sossai na kwakwalwa da na jiki don Allah ka kula"
"Na gode"
Abin da kawai ya faɗawa likitan kenan, tsabar ciwon kai jiya ko runtsawa bai yi ba da kyar ya iya yin sallahn asuba hakan ya sa ya nufi asibiti yana gama buɗe folder za'a kaishi Layin ganin likita ya yanki jiki ya fadi dole aka yi emergency dashi aka fara bashi taimakon gaggawa, bai farka ba sai yanzu misalin karfe huɗu na yamma drip leda uku ya kare a jikinshi duk bai sani ba.
Bai ƙira kowa ba bayan na jikinshi ya kare yaje ya biya bills ɗin shi ya fice daga asibitin jikinshi duk babu ƙarfi, sallolin da aka bi shi ya tsaya yayi kan ya nufo gida Dukda bakinshi babu appetite sai dai ya san yana bukatar abinci gashi shi ba iya cin abincin waje yayi ba sai in ya zamar mishi dole ba yadda ya iya sam bai san wainar da ake toyawa a gidan ba, ya dai samu kawu da wani mutumi kuma ya ga motan Tahir sai dai be ce musu komai ba ya wuce cikin parlorn Mama, ganinshi ya sa ta miƙe
"Aliyu tun safe ina ka shiga haka? Baka jin daaɗi ne?"
Kai ya girgiza
"lafiyana ƙalau Mama ina wurin Jabir ne"
Ya faɗa a hankali sam baya son daga mata hankali yanzu ma ya tabbatar aka duba jininta ba zai rasa hawa ba.
"Akwai abinci?"
Ya tambaya don kau da kallon da take mishi kaman bata yarda da magananshin ba.
"Eh bari na kawo maka"
Tana kai nan ta fice ta kawo mishi abincin jollof ne na shinkafa da wake na manja, ya ɗan ci kaɗan kan ya ɗan kwanta a wurin don har lokacin jiri yake gani kaɗan kaɗan, daga waje bayan kawu sun gama magana da kawun Tahir ya shigo parlorn ya zauna.
"Ashe chan safana ya fara zuwa aka ce mishi na zo nan shine suka biyo ni"
"uhmm"
Kawai mama tace
Kawu ya dubeta
"Mu yi wa yarinyar nan Fatan alkhairi don Allah dai Maman Aliyu duk wanda ta zaɓa cikin su Allah ya sa shine alkhairinta, na bashi nan da sati biyu na kuma amince dukkansu daga Aliyu har Tahir ɗin su zo zance wurinta bayan nan duk wanda ta zaɓa shi za'a aura mata"
Aliyu na sauraronsu sai dai bai ce komai ba har kawu ya gama magana, nan ya ce zai koma Aliyu ya miƙe ya raka shi a hanya ya dubi Aliyu
"Aliyu ina fata zaka iya juriya ga wannan lamari, ka zama namiji kaman yadda kake kuma kar a manta da Adu'a ayi ta addu'a babu wanda ya isa ya tsallake hukuncin Allah duk kuma abin da Kaga ya faru haka Allah ya tsaro mana shi tun fil azal"
Kai Aliyu ya gyaɗa mishi ya tare mishi machine ya shiga ya zaro dubu biyu ya bashi.
Hannunshi cikin aljihu ya shigo gidan yana tafiya a hankali irin na masu ciwo sai dai in baka sani ba zaka zaci kawai tsabar ɗaukan kai wani ne kaman yadda ake faɗin yana da girman kai da ɗaukan kanshi wani alhali takalan kayau ne.
Yana shirin shiga ɗakinshi ita kuma zata fita ya kira sunanta
"Afnaan"
"Na'am"
Ta amsa cikin sanyi ta ɗago tana kallonshi kaman yadda yake kallonta
"Ina zaki je?"
"Mama ce ta aikeni in karɓa mata gawayi"
"ohk in kin kawo ki zo ina son ganinki"
Ta gyaɗa kai ta wuce ya bita da kallo har Ranshi bai ji ko kusa ko alama soyayyarta ya ragu ba daga duk abubuwan da suke faruwa, sai ma tsananin tausayinta da tsoron kar ta jefa kanta inda zata cutu, ko bai aureta ba ba zai taɓa yi mata Fatan cutuwa ba kaman yadda ya faɗa ta riga ta zama jini dake yawo a jikinshi.
A hankali tayi sallama sai da ya amsa daga ciki kan ta shiga ta samu wuri ta zauna, zaune ya miƙe daga kwancen da yake ya tsura mata idanu har yau mamakin irin chanzawar da Afnaan tayi yake yi, ita kuwa hannunshi ta tsurawa idanu kan wani tabo me faɗi dake daga bayan hannun take ta kallo ya kai idanunshi wurin kan ya kai hannunshi ɗaya ya shafa
"Kin tuna?"
Ta ɗan yi murmushi kaɗan
"Karen gidan maman bright, ban taɓa sanin dabba na yiwa mutum farin sani ba sai a kan wannan shegen karen in ta tsokanarshi ashe dako na yake... Bana manta an aikeni markade ya ritsa ni tuni roban mama da kullun kosai yayi wurinshi nima nayi nawa wurin ba don ka zo ba da ni fa zai ciza ya kuma yakusha da ni ce da wannan tabon"
Lumshe idanu ya ɗan yi yana murmushi shima abubuwa dayawa irin hakan na dawo mishi Dukda bata da kiriniya ko tsokana sai dai duk wani abu zai sameta kaman an ajiye shi ne don bata kariya hakan ya sa a yanzu yake jin cewa tana buƙatar shi, tana buƙatar kariyarshi daga bala'in da take shirin jefa kanta.
"Afnaan ashe na jima da tashi daga bestienki?"
Da sauri ta girgiza kai
"Toh Meyasa Shigowar Tahir rayuwarki ya zama sirri a gareni har yayi miki illah ba tare da na farga ba?"
Ta ɗan kalleshi ta sauƙe idanu
"Saboda yana tsoron zaka hanani kula shi kuma wallahi mutumin kirki ne, ka duba taimakon da yayi magana a asibiti ba tare da ko sanin mu yayi ba"
"uhmm"
Ya faɗa kawai
"Afnaan yanzu nine bakya so ko?"
"A'a wallahi ina sonka matsayin ɗan uwana da bani da kamar shi sai dai ina jin Tahir tamkar rayuwata, Yaya baka so in je inda zan huta ne? Baka so in je inda zan dawo ina taimakon ku kaima ka samu ka huta da wahala?"
Lip ɗin shi ya ɗan haɗe kaɗan yana tuna yadda ƙarfi da yaji duk soyayyar shi da karatu ya haƙura saboda Afnaan tayi karatu amma a yanzu be ga bambancinta da wanda bai taɓa zaman aji ba, har tsoro yake anya ba asiri Tahir ɗin nan ya yi mata ba wani zuciyar na ce mishi samm kawai tana hangen abin duniya ne, idanunta na kan dukiyar da Tahir yake da shi tunanin ta na bata in dai ta bar gidan ta fita daga kangin talauci Alhali ya tabbatar basu daga cikin waenda za'a ƙira da Talakan ƙayau tunda yana da zuciya, suna ci su sha su saka tufafi kuma su kula da lafiyansu sannan tayi karatu ba a gomnati ba ma a private.
Shanye maganan yayi ya miƙe Tsam ya matso gangan ta ya ɗan duka
"Rayuwa tare da ke a kusa da mu sai ya fi daaɗi da kwanciyar hankali akan dukiyar da kike magana Afnaan, wallahi ba a kaina kaɗai kika ga na dage akan wannan maganan ba har zuciyata ina yi miki son da bana tunanin Mama da Baba da suka haifeki suna miki, ko menene zaki yi min ɗaukar shi nake a ajizanci irin na ɗan adam please Afnan Don't let any other man marry you, kar ki bari wani chan ya shiga rayuwarmu har ya kawo tangarɗa ga ingantacciya kuma tsaftatacciyar rayuwar da na tanadar mana for the second time ina roƙon ki ki ajiye batun Tahir a gefe mu gina rayuwar da zai anfani goben mu"
Hawaye ne ke sauƙo mata ina ma zata iya, ina ma zata iya fitar da Tahir a rayuwarta? Sai dai kaman yadda jawahir ta faɗa fitar da Tahir a rayuwarta kaman tayi kururuwa ne ta ɗauki wuka ta dabawa cikinta don ita zata yi asara, ta tabbatarwa kanta da tayi kuka a napep gwara ta yi a jirgin sama.
"Kayi haƙuri Ya Haidar wallahi bana yi maka son aure kuma ba zan taɓa iya yi maka hakan ba"
Idanunshi ya runtse sossai idan ta faɗi hakan yake jinshi har tsakiyar zuciyarshi.
"Afnaan wallahi Tahir baya miki kwatan ƙaunar da nake yi miki... Ki gane mana ke fa you are not just in my heart ke ce gabaɗaya zuciyar, Not just in my thought, you are the thought itself zaki cutar da ni ba ƙadan ba zaki illata rayuwata muddin kika halaka min kanki.."
Cikin wani irin sanyi da danne harshe yake maganan, sossai take jin wani irin abu a jiki da jininta sai dai kwakwalwanta ya ƙi bata haɗin kan aminta da Aliyu girgiza kai tayi kawai ta miƙe ta fice da gudu.
Turus ta ja ta tsaya ganin jabir daga wajen ɗakin yana yi mata wani irin kallo
"Meyasa Afnaan? Meyasa shaiɗan ke buga miki gangar son zuciya, butulci kuma kike taka masa rawa? Ashe zaki iya butulcewa Aliyu Afnaan? Ki samu soft spoken man ma irin Aliyu wanda he never raises his voice at you wanda he always treats you with respect even when he's upset wani rahama ne da ba zaki gane ba sai kin je kin ɓatawa wani namijin yayi miki dukan kawo wuƙa..."
"Wai dole ne yaya Jabir? Dolene sai kowa yayi min dole in auri Ya Aliyu alhali bana yi mishi soyayyar aure? Ku barni mana in samu nawa farin cikin dole sai da ya haidar zan yi farin ciki? Har fata kake yi min in auri miji me duka saboda kawai na ƙi a zalunce ni? In shaa Allahu ba haka Tahir yake ba kuma ba zan taɓa amincewa a zalunceni ba"
Tana kai ta wuce da gudu tana cigaba da kukanta.
A hankali jabir ya ɗago ya kalli Aliyu dake tsaye jikin kofan dafe da goshinshi...
🖤Gureenjoh🖤