Free chapter 路 Read without an account
Ajnabiyya page 5
AJNABIYYA...
NA
*HAJJA CE* 馃憟
Arewabook@Hajja22522
Wattpad@Hajjace
Facebook@Hajjace
Page 5
Gefen zaninta ta 蓷an kamo ta shiga share hawayenta, Ameerah kam dama bata san tuhuma ko a tsareta akan abu, indai kayi mata hakan nan da nan zuciyarta ke shiga kunci taji komai ya fice mata a rai. Ji tayi bama zata iya zuwa gidan Yaya Hannen ba, mood 蓷inta ya canza sosai. Tana 蓷akko kaya a cikin maadanin su tana tunanin yanzu me zata yi? Mama taji tana cewa.
"Idan kin gama ga kwa蓷an garin kwakinki can a cikin langa ta saman, idan kin 蓷auka ki rufewa Yayanki nashi yace yanzu zai dawo." Ameerah ta saki murmushi, yau ina ita ina cin abincin gidan nan? Kuma a rasa me za'a yi sai kwaki? Nooo! Bazata iya ba da uwar ku蓷i a hannunta. Sai da ta gama shiryawa tsab sannan ta fito sanye da hijab a jikinta. Kallanta Mama tayi da mamaki, sai dai bata ce da ita komai ba da alama jira ta ke taji ta bakinta. Ameerah ganin yadda Mama ta zuba mata ido yasa ta cewa.
"Mama bazan ci kwaki ba gaskiya. Tunda ga ku蓷i zanje shagon Ayuba na siyo wasu abubuwan." Cike da 蓷aurewar kai jin abinda Ameeran ke cewa yasa Mama yi mata kallan tsab tana cewa.
"Daga samun ku蓷in shine har zaki tattare ki fita siyayya dasu? Kin nunawa mahaifinki ne?" Ameerah tayi shiru tana jijjuya ku蓷in a hannunta. Cikin ranta kuma tana mamakin shin me Mama ke nufi? Wai bazata ta蓳a komai ba a cikin ku蓷in har sai Baba ya dawo an nuna masa? Idan ya kwace kuma fa? Hanata fitar nan yana nuni da cewa kwakin da ake nuna mata shi 蓷in zata ci kenan? Nan da nan zuciyarta ta shiga yi mata zafi, su kenan ba za'a yi wani abun arziki a gidan ba sai an maida shi abun tashi hankali?
"Dan Allah dan annabi Mama ki barni naje na siyo. Har sababbin pants nake so tunda kinga bani dasu."
"Ban hanaki siyo komai ba Ameerah. Cewa kawai nayi ki jira mahaifinki yazo a nuna masa idan yaso sai kiyi duk abinda kikaga dama." Ameerah ta juya ta koma 蓷aki da sauri, zuciyarta banda zafi da tafasa babu abinda ta keyi.
"Da na sani tun kafin na dawo gidan na kashe su wallahi. Yanzu idan Baba ya kar蓳a ya hanani fa?" Taji zuciyarta na gaya mata. Nan da nan kuka ya kwace mata ta dinga yi kamar wacca aka yiwa dukan tsiya.
"Kin fasa zuwa gidan Hannen ne?" Mama ta tambayeta tana 蓷age labulen 蓷akin. Hango Ameeran tayi ta ha蓷e kai da guiwa alamar kuka ta keyi tace mata.
"Laaah ha'ilahaaa illallahu, au! Wai kuka ma kike yi? Ehhh! Lallai ma. Iyeeee. Tohhhh baki fara ba tunda ke ba zaki iya jira Baban naki yazo ki nuna masa ba. Bari ma ya dawo ya tambayeki wane 蓷an gidan shafaffu da mai ne ya baki ku蓷in da har kike jin ba zaki iya jiran yazo ba. Sakarai kawai, idan zaki 蓷auki abincinki ki 蓷auka kici. Idan kuma kukan zaki ci sai kiyi ni dai na gama magana." Ameerah ta sake cusa kanta cikin guiwa jin ko lallashin ta ma ba za'a yi ba. Yanzu da a gidan 拼an gayu ne, yadda za'a dinga lalla蓳ata musamman da ta ke auta, Allah kawai ya san irin shi. Amma yanzu wai ita Mama ta hana fita siyo abinda zataci. Yanzu tsakani da Allah itama haka za'a yi mata? Irin na su Yaya Hanne? Bazata yadda ba ita kam, haka kawai tana da bu茩atu ta samu ku蓷i ace bazata amfana dasu ba.
"Mama ina Ameerah ne?" Yaya Ammani ya tambaya yana janyo kujera ya zauna.
"Tana 蓷aki." Mama ta fa蓷a tana ci gaba da aikin ta.
"Ameerah fito min da abinci na kin wani shige 蓷aki cikin wannan uban zafin. Kai Mama yau ko iska babu a garin nan 蓷if kike ji." Mama bata ce komai dan ita kam ba fiye yin magana ta ke ba. Ameerah dake 蓷aki ta tashi ta 蓷akko langar abincin Yayan nata ta fito kanta a sunkuye dan bata so ma yaga kukan da tayi. Yadda ta ke 蓳oye fuska ne yasa shi san kuma kallan ta. Juyawa tayi zata bar wajan ya ri茩o hannunta yana cewa.
"Meye ke kuma?"
"Ba komai Yaya."
"Ohh kukan jin da蓷i kike yi kenan?"
"Ku蓷i ne aka bata shine ta ke so na barta taje ta kashe su. Cewa nai mata ta bari Baban ku yazo ya gani muji mai zai ce, shine ta shiga 蓷aki tana kuka ita ga 拼ar gwal." Da sauri Ya Ammani ya saki dariya yana janyo ta kusa dashi yake cewa.
"Ahhh kice ta samu kenan? Nawa ne ku蓷in?" Ameerah na kallansa take cewa.
"Dubu goma ne, nayi amfani da dubu biyu da 蓷ari biyar a makaranta." Langar gabansa ya bu蓷e yana kallan kwakin da ke ciki yace.
"Yauwa 拼ar gari, jeki 蓷akko mana ko dubu biyu ne mu siyo kifi a 蓷ora a abincin nan zai fi wucewa." Ameerah ta sake ha蓷e rai jin abinda ya fa蓷a tace.
"Yaya amfani fa zanyi dasu." Ya daka mata tsawa jin zata hanashi yana fa蓷in.
"Dallah can jeki 蓷akko dan yau kinyi abin duniya shine zaki wani ce amfani zaki dasu?" Ta juya tana hawaye. 'Me yasa ta fa蓷i gaskiyar yawan ku蓷in bata rage ba?' Tun kafin ta gama shiga cikin 蓷akin taji yana sake cewa.
"Kiyi sauri malama yunwa nake ji." Ya fa蓷a yana rufe langar ya mai da ita gefe ya ajiye. Jiki babu kwari ta kawo masa dubu biyun ta bashi ya kar蓳a yana jujjuyawa yake fa蓷in.
"Biyun kuwa kika kawo min ko? Ni wallahi na zata ma duka zaki ban su."
"A'a bazai yiwu ba, wannan 蓷in ma idan Baban ku yai fa蓷a sai ka biya su." Ya Ammani ya mi茩e ya nufi hanyar fita yana dariya yake cewa.
"Haba dai na biya sai kace sata nayi." Ameerah kam ciki ta koma, gidan gaba 蓷aya ya mata zafi ji ta ke tamkar tayi tsintsuwa ta fice ko zata samu sassaucin zafin da zuciyarta keyi. Yadda ta ke ta jin kunci yasa Mama tayi ta aikin ta ita ka蓷ai bata kirata ta taya ta ba. Haka itama Ameeran bata ce zatayi komai ba. Babu jimawa kuwa Ya Ammani ya dawo gidan, tun daga 蓷aki Ameerah ta dinga jiyo 茩amshin kifin. Nan da nan yawun ta ya shiga tsinkewa, tana so ta fito tana gudun kar Ya Ammani ya sake cewa ta bashi ragowar ku蓷in dan tasan indai ya fa蓷a sai ta 蓷akko duk abinda Mama zata fa蓷a sai yasan yadda yai ya amshe su duka.
"Ameerah fito gashi kici." Ya fa蓷a yana bu蓷e ledar kifin tare da bu蓷e langar garin kwakin shi ya 蓷akko 茩atuwar jela ya jefa a ciki. Somaci yai ita kuma ta fito tana bin bango kamar wata marar gaskiya. Yadda taga Ya Ammani yana ha蓷awa ne ya bata sha'awa, tai saurin komawa cikin 蓷akin ta 蓷akko nata garin kwakin ta fito. Kasonta ya 蓷ora mata a cikin garin nata taja kwanonta, ya zatayi? Dole taci karta zo tayi biyu babu tunda gashi ku蓷i dai sun 茩are sauran ka蓷an. Suna ci Ya Ammani yake tambayarta wai me tayi aka bata har dubu goma? Tace,
"Kawai dan ya tsaida ni shine ya bani yace na 蓳ata min lokaci da ya yi ne."
"Kutimelesiii...! Lallai Guy 蓷in nan 蓷an wahala ne, amma dai mai ku蓷i ne ko Ameerah?" Ya tambaya yana juyawa ya kamfato ruwa a kofi kasancewar randar ruwan tana kusa dashi ya kafa kai yana sha.
"Ni ya za'ai na nasa Yaya?"
"Kuma fa haka ne tunda yau kika fara ganinsa ko? Ahhh lallai Ameerah da alama kinyi mugun kamu. Nifa tun ranar laraba da naje wajan budurwata tace wai na bata ku蓷in shampoo, kin ganni nan? Yasin har yanzu ban koma wajan ta ba. Toh ina na gansu nima bare nayi kyauta dasu. Gaskiya da alama kuma 茩ila sonki yake ko?."
"Tab蓷ijam so kuma Yaya?" Ameerah ta fa蓷a tana ha蓷e rai dan ita harga Allah tun farkon ganinta da guy 蓷in bai wani kwanta mata a rai ba. Hasali ma ba irin samarin nan bane da zata iya tsayawa da su ba da sunan soyayya.
"Kardai ki jawa kanki asara garin iyayi, naji kina wani maimaita so kuma? Jifa a lokaci guda kalar abincin mu ya canza. Kinsan Allah...." Bai 茩arasa ba Mama ta dakatar dashi ta hanyar cewa.
"Karka zuga min yarinya, kayi mata addu'a kawai Allah ya bata miji na gari." Ameerah tana zaro 茩ayar kifi tasa a baki tana fa蓷in.
"Ni karatu ma zanyi fa."
"Toh kaji ma." Cewar Mama cike da san gwale Ya Ammanin.
"Ai shikenan sai ki zauna ai wahala ce bata isheki ba." Ya Ammani ya fa蓷a yana tashi tsaye sai sakin gyatsa yake yi kamar wani wanda ya gama cin naman 蓷awisu. Ficewa yai Ameerah ta bishi da kallo, cikin ranta tana cewa.
"茦ato dashi bai san ya nemo ya kawo ba. Yanzu da ya bar min ku蓷ina har kayan kwalliya naso siya." Daga haka itama ta tashi ta nufi sashin Inno dan idan ta zauna a sashin Mama tana tuna hanata fita 蓷in nan sai taji zuciyarta na mata zafi.
Bayan wata 蓷aya
Gabaki 蓷aya ji da ganinta ne suka goshe na 蓷an 茩aramin lokaci, abinda taji ne yasa ta kasa gazgatawa hakan yasa ta shiga wani irin mugun shock. Kallanta kawai zaka yi ka gano zallar tsagwaran tashin hankalin da ta ke ciki, dan kuwa kirjinta bugawa kawai yake yi har ana iya hango yadda hijab 蓷in jikinta ke motsawa. Ga kuma wani uban gumi da ya gama ji茩a mata duka fuskarta kai kace ruwa ne ta zuba. Meenal da Husnah ne suke ta 茩o茩arin kamota amma ta茩i yadda kowa ya ta蓳a ta, jira kawai ta ke taji ance ta tashi daga wannan nannauyan baccin ace mata mafarki ne ba wai gaske ba. Yaseer ganin sai fama ake yi ta tashi amma taki, yasa shi yiwa Meenal inkiya da kansa alamar tazo suyi abinda ya dace. Yana zuwa suka ri茩o ta da karfi suka baro wajan da suka dubo result 蓷in jarabawar nan da suka yi. Dukkan su sun haye banda Ameerah, ganin bata samu ba yasa suma duk basa farin ciki.
"Meye na kukan nan ne Meerah? Haba wannan jarabawar fa ba ta lahira ba ce bare ki ce karahenki ne yazo. Please dan Allah ki bar kukan nan haka karki janyowa kanki wani ciwon." Ameerah ta 蓷ago rinannun idanunta da suka gama yin jawur ta kalli Meenal, ji ta ke kamar ta sha茩eta. A fusace kamar ita ce tayi mata laifin ta ke cewa.
"Sai yanzu nasan bakya kaunata Amina Uthman Kabo, ke ma茩iya ta ce da ban sani ba sai yanzu da Allah ya tona miki asiri. Da yake ke kin samu shine ni zaki ce min ba jarabawar lahira ba ce ba? Dama na ta蓳a ce miki jarabawar lahira na rubuta? Wannan munafunci ne, wato kin samu uban kowa ma ya rasa ko Meenal? Toh gashi na rasa 蓷in kin samu sai ki zuba ruwa kisha a 茩asa kinji?" Tana kaiwa nan ta mi茩e zata bar wajan Yaseer ya yi saurin tare ta yana langa蓳e kai. Kwata-kwata baya san fa蓷a bare kuma rigima shi yasa yake iya zama da kowa lafiya.
"Ya isa haka Meerah zauna muyi magana." Ya fa蓷a cikin sanyin murya. Ameerah da yake a wuya ta ke, kawai tsaki taja tabar musu wajan kamar wacce aka yiwa gorin tafiya. Meenal kuwa kasa motsawa tayi saboda mamakin irin maganganun da aminiyarta ta a yanzu ta gama gaggasa mata irin haka a gaban mutane. Yaseer ya rasa wajan wa zai tsaya, Ameerah zai bi wacce basu san ina ta nufa ba ko kuwa Meenal zai tsaya ya lallasa? Kanshi ya kulle. Da sauri ya isa wajan Meenal yana bata ha茩uri tare da nuna mata cewa Ameerah tana cikin fushi ne.
"Ba komai Yaseer nima ji nake dama banci jarabawar ba. Ameerah tasa rai sosai akan cin jarabawar nan, kullum cewa ta ke zata bar 茩asar nan zata zama abar kwatance. Ni da kai ne bamu damu da irin burin ta ba. Yaseer idan ana canzawa a sake a saka sunanta na bar mata wallahi." Wasu dake gefe ne suka daki cinya suna cewa.
"Lallai ma ke Amina Kabo, ta gama ci miki mutunci sai kace wata uwarki kice wai zaki bar mata damarki da kika samu? Allah ne ma ya gwadata ta hanyar hanata cin jarabawar nan, yarinyar nan sai shegiyar karya taji da talaucin da ta ke ciki amma tana kai kanta inda bai dace da ita ba." Kansu Yaseer yai a fusace, da sauri wasu suka ri茩e shi, jijiyoyin kansa duk sun mi茩e saboda masifar da take cinsa yace.
"Sannunku 拼a拼an masu ku蓷in duniya, wannan izgilanci kuke yiwa ubangiji tunda shine ya yi ta a talaucin. Ku kuma 拼a拼an waye munafukai kawai."
"Mu tafi Yaseer dan Allah ka dena kulasu." Meenal ta fa蓷a tana nuna masa hanya da nufin su tafi. Yaseer na huci ya fice.
Ameerah kuwa tana fitowa kuka ne ya sake kwace mata, ko gabanta bata iya gani tafiya kawai ta ke yi saboda tashin hankali. Mubasshir na yin parking ya dinga hango ta, tun yana hasashe itace ko ba ita bace, har zuciyarsa ta gama tabbatar masa da ita 蓷in ce. Yadda ya ganta ya 蓷aga masa hankali dan kuwa ya gane bata cikin nutsuwa. Da sauri yabi bayanta yana kwala mata 茩ira amma inaaaa, hakan yasa shi ha蓷awa da 蓷an gudu-gudu. Ji kawai tayi an ri茩o hijab 蓷inta, ta juyo a fuska ce duk a zaton ta su Meenal ne kawai taga Mubasshir saurayin nan da ya ta蓳a gwangwaje ta da dubunnai har guda goma. Maimakon taji da蓷in ganin shi, sai taji kamar ta kai masa duka amma ba dama tunda ko babu komai shi 蓷in ba sa'anta ba ne ba.
"Irin wannan yanayin bai dace dake ba, girmanki yafi 茩arfin ki dinga bari zuciyarki tana shiga wani yanayi ba farin ciki ba. Anyway, ki taimaka ki zo muje na tayaki karewa mutuncinki mutuncin da ya fi dacewa dake. Komai yake cikin zuciyarki kiyi addu'a Allah yana tare da ke. Ina fatan gimbiyar gida zataje ta bani dama na 茩arasar da ita cikin girmamawa?" Duk da zuciyar Ameerah ba ta gama amincewa da mutumin ba, dan gabaki 蓷aya ma ta manta dashi. Haka ta amincewa zuciyarta akan binsa, da har zata musa masa, sai kuma taga tana da bu茩atar a taimaka mata wajan kaita gidan.
Kai tsaya motar sa suka nufa, da kanshi ya bu蓷e mata ta shiga duk da har lokacin ba wai ta dena kukan bane ba. Daidai lokacin da su Yaseer suka hango ta shige motar, suka kalli juna shida Meenal hankalinsu a tashe. Kafin suyi wani yunkuri, tuni mai motar nan yaja sunbar wajan wanda sun gane shi shine wanda ya bata ku蓷i kwanakin baya..........