Free chapter · Read without an account
BABI NA TAKWAS
by Fatima Eshak · SAFEENATU
*SAFEENATU*
NA
*UMM ASGHAR*
Arewa books @UmmAsghar
*BABI NA TAKWAS*
Shiryawa nayi cikin wani soft cotton material da aka yiwa ɗinkin skirt da riga. Sassauƙar kwalliya nayi a fuskata, siririyar sarƙa da stud earing na english gold na saka. Sai wasu siraran gold bangles guda shida dana saka a hannuna na dama, ɗaya hannun kuma na ɗaura agogo. Turarukana nabi jikina dasu, kada ku manta ni wajen son ƙamshi. Ban ɗaura ɗankwalin kayan ba sai ƙaramin veil daya shiga da kayan na rufa a kaina. Ban fita daga ɗakin ba sai da na karkaɗe gadon na gyara. A parlour na tarar dashi yayi wankan shima yayi shiri cikin ƙananan kaya wandon jeans kalar baƙi da cream polo shirt.
Yana ganina ya ware hannayen shi wai naje, noƙe kafaɗa nayi a kunyace ina dariya. Tasowa yayi yana cewa "baby ni ko? Mun ɓata."
Dariya nayi ganin yadda yayi da fuska kamar wani ƙaramin yaro. Wajen dining table muka nufa, food warmers ne a jere akai. Kujera ya janyo mini na zauna kafin shima ya zauna. Shi ya bubbuɗe warmers ɗin yana tambayata abinda zan ci. Akwai peppersoup na naman rago da sinasir, sai soyayyen dankali da egg sauce sai kuma flask ɗin kunun gyaɗa dana tea. Tea ɗin nace zan sha sai dankalin. A plate ɗaya ya zuba mana sai kuma ya haɗa mini tea, shi kunun gyaɗar ya ɗiba. A tare muka ci abincin kuma naci sosai ko don ina jin yunwa ne yasa na zage naci da yawa shine ban sani ba amma naci da yawa abinda ni kaina ya bani mamaki matuƙa.
Bayan mun gama na tashi zan tattare wurin ya hanani, shi ya miƙa kayan kitchen. Fitowa yayi yace na tashi mu shiga cikin gida mu gaishe da su Umma. Ɗakina na koma na yafa babban mayafi na fito. A jere muka fita muna cike da nishaɗi yana yi mini ƴar hira ina sauraren shi. Muna ta wuce ma'aikatan gidan suna miƙo mana gaisuwa haɗe da yi mana fatan alkhairi yana amsawa don ni dai kunya baza ta bari na amsa ba sai dai cikin zuciyata. Har muka ƙarasa part ɗin Umma. Akwai ragowar ƴan biki da basu gama tafiya ba. Anan parlour muka zauna, cike da girmamawa na russuna na gaishe su. Bayan mun gama gaisawa Albi ya tambayi inda Umma take.
"Tana ɗakinta bata daɗe da shiga ba." Inji wata mata.
Miƙewa yayi yace "tashi muje mu gaishe da Umma."
Yana gaba ina biye dashi a baya muka tafi ɗakin. Da sallama muka shiga sai dai muna shiga na tsaya daga bakin ƙofa ganin wani irin kallo data watsa mini.
"Shigo mana Feenah, ya zaki tsaya daga bakin ƙofa." yace. Jiki a sanyaye na ƙarasa ciki na zauna daga ƙasa cike da tsantsar ladabi nace
"Umma ina kwana, an tashi lafia?"
Yanayin yadda ta amsa mini ya sanyayar mini da jiki ƙwarai sai dai hakan bai sa na kawo wani abu a cikin raina ba. Daga gaisuwar nan wata magana bata ƙara haɗa mu ba, shiru ne ya ɗan biyo baya kafin kuma ta fara jan shi da hira yana amsa mata cike da kulawa. Na lura akwai soyayya da shaƙuwa sosai a tsakanin su, tun ba yau ba nasan bai haɗa al'amarin Umman shi da kowa ba shi yasa ban yi mamakin jin yadda suke hirar ba kamar irinnsun daɗe basu haɗu ba ɗinnan.
Mun ɗan jima a ɗakin suna ta hirarsu ni dai ina jin su, sai zuwa can yace
"Umma bari muje mu gaida Baba daga nan zamu wuce."
Kamar dai bata so yace zai tafi ba haka nan ta amsa mishi da "to."
"Feenah tashi mu tafi ko." Yace mini.
Ɗan russunawa nayi nace "Umma zamu tafi, a huta lafiya."
Yi tayi kamar bata ji maganata ba sai da yace "Umma Safeenah nayi miki sallama."
Da ƙyar ta buɗe baki tace "Ameen."
Daga ɗakin Umma part ɗin Baaba Musa muka je. Shi kam da fara'ar shi ya karɓe ni. Cike da girmamawa na durƙusa na gaishe shi.
"Tashi ki zauna sosai ƴa ta."
Ban iya komawa kan kujera na zauna ba kamar yadda ya umurceni sai gyara zamana da nayi akan carpet.
"To ya baƙunta?" Ya tambaye ni.
Cike da jin nauyi na amsa mishi da "Alhamdulillah."
"Masha Allah, Allah yayi muku albarka ya baku zaman lafiya. Sai ayi ta haƙuri kin ji, zaman aure gabaki ɗayan shi ɗan haƙuri ne, idan ɗaya ya hau sai ɗaya ya sauka sai kiga an zauna lafiya. Banda rashin kunya, kiyi mishi biyayya bakin gwargwado, kunga dai ku kuka haɗa kawunanku to kada ku bamu kunya kuyi ƙoƙari ku zauna lafiya, ayi ta haƙuri ana yiwa juna uzuri. Allah yayi muku albarka ya baku zuri'a ɗayyiba."
Hamza ne ya amsa "Ameen" ɗin. Mun ɗan jima a wurin shi yana yi mana nasiha kafin ya sallame mu muka koma part ɗin mu.
Muna shiga Albi ya rungumoni ta baya ya cusa fuskar shi a wuya na yace "gashi dai muna tare amma i miss being close to you. Yarinyar nan anya zaki bar ni na koma office ma kuwa?"
Kasa magana nayi saboda wani abu da nake ji yana yawo a jikina gashi kuma ya kasa tsayar da hannun shi wuri ɗaya. Hannayen shi ya cusa cikin rigata yana shafa fatar cikina, a hankali yayi sama da hannun zuwa ƙirjina. Wata irin shafa yake yiwa wurin da tasa na kusa rasa nutsuwata.
Yini muka yi a maƙale da juna muna zuba soyayya. Albi bai fita ba sai da yamma lokacin na fara yin baƙi. Su Zahra ne da Jeddah da wasu daga cikin cousins ɗin mu da basu tafi ba. Mun daɗe tare dasu muna hira, sune ma suka tayani shirya kayana a cikin wardrobe kafin suka yi mini sallama bayan magrib suka tafi. Ɗan zaman da nayi dasu sosai naji daɗin shi, wallahi sai naji kamar kada su tafi su bar ni, gashi Albi tunda ya fita bai dawo ba sai naji kewa duk ta isheni.
Wanka na tashi na shiga bayan na fito na shirya cikin fitted gown ta atampa. Sosai kayan suka zauna a jikina suka yi mini kyau, gani dama tubarakallah Masha Allah, Allah ya ƙawata mini halittar jikina. Ba yabon kai ba perfect figure eight ne dani shi yasa kowane irin kaya na saka yake yi mini kyau.
Daga parlour na jiyo ƙarar wayata inda na barta. Kafin na fito ta katse don haka na tsaya na ƙarasa shirina a tsanake. Sai da na gama na fita na ɗauki wayar sai naga ashe Khadija ce ta kirani. Bin bayan kiran nata nayi, tana ɗauka tace
"Hala angon na kusa ne Feenah shi yasa kika kasa ɗaukar waya."
Dariya nayi nace "ko kusa wallahi ina dai ɗaki wayar tana parlour kafin na fito kuma kiran ya katse."
"Ai na ɗauka yana kusa shi yasa kika kasa ɗaukar wayar."
"Baya nan ma tun zuwan su Jeddah ɗazu da yamma ya fita har yanzu bai shigo ba, yanzu nake tunanin na kira shi a waya."
Ajiyar zuciya ta sauke tace "ina ma nice na samu Honey ya fita ya bani wuri na ɗan sarara."
"A haba dai amaryar Mallam Sadiq tun daga yanzu, ko duk amarcin ne?"
Ƙwafa tayi tace "wane amarci kuwa banda wahalar dana karɓa a hannun Honey."
Cike da shakiyanci nace "ah haba dai na ɗauka kin shiryawa auren ai."
Tsaki tayi tace
"baza ki gane ba Feenah, wallahi Honey baya da tausayi, wai duk magiyata bawan Allahn nan ya kasa ɗaga mini ƙafa."
Dariya kawai nayi nace "don Allah kada ki bada mata mana, a yadda kika shiryawa auren nan ban tsammaci jin any complain daga gareki ba."
Kawai ji nayi an rungumoni ta baya an zare wayar daga kunnena, bakin shi ya kai saitin kunne na yace "a ƙyale duk wata hira haka nan, yanzu lokacina ne."
A kunyace na ɗago na kalleshi cike da shagwaɓa nace "kai Albi, yanzu kawai sai Khadija taji na kashe mata waya. To idan kuma Anty ce fa, da haka zaka bani kunya."
"Bare ma ba Anty bace tunda da bakin ki kika ce Khadija ce, ita kuwa babu ƴar kunya a tsakaninku. Besides ina ta baro mijinta a daidai wannan lokacin da zata tsare mini ke da hira."
"Ni dai ka bani kunya Allah Albi."
Kafaɗun shi ya ɗage irin i don't care ɗinnan. Hannuna ya kama zuwa wajen dining table ya zaunar dani kafin yace "ni yunwa nake ji don haka zo muci abinci daga nan sai na baki labari mai daɗi." Ya ƙarashe maganar haɗe da kanne mini ido ɗaya.
Kawar da kaina nayi ina murmushi. A same plate ya haɗa mana abincin don yace in dai yana gida to ba zamu raba kwano ba a tare zamu riƙa cin abimci.
Bai barni na riƙe spoon ba shi ya riƙa ciyar dani a baki, yana ci yana bani a haka har muka gama cin abincin.
Na tashi zan tattare wurin ya hanani ya tashi zai yi da kanshi sai dai ban zauna ba sai na tashi na tayashi muka kai kayan kitchen. Tare muka wanke kayan da muka ɓata muka gyara wurin kafin ya karkashe fitilu ya rufe ƙofofi muka tafi ɗaki don yace bacci zamu je muyi.
Yana riƙe da hannuna har bathroom inda ya haɗa ruwa a bathtub. Hannu yasa ya zuge zip ɗin rigata ta sauka ƙasa. Da sauri na riƙe hannun ina cewa "Albi me zaka yi?"
"Wanka zamu yi." Ya amsa mini cikin wata irin murya da daga ji kasan fitina cw tsantsa cikinta.
Murya na rawa nace "to ai ni nayi wanka ɗazun nan." Wane irin muyi wanka tare saboda Allah, yaushe aka yi daren da har garin zai waye.
Hannu yasa yana shafa wasu sassa na jikina abinda yasa jikina mutuwa.
"Sai ki sake wani wankan," kawai yace ya tsunduma ni a bathtub. Shi ya cire mini kayan jikina ina noƙewa ina komai amma sai da muka yi wankan nan, a inda muka ɓata lokaci mai yawa yana gwada mini kalolin wasannin shi masu tsayawa a zuciya da sanya nishaɗi.
Bayan mun fito ɗakin shi ya wuce yaje ya shirya, ni ɗin ma shirin nayi cikin kayan bacci cotton riga ce mai yankakken hannu data tsaya mini iya gwiwa kalarta purple. Sosai na wadata jikina da turaruka masu sanyin ƙamshi na haye gado na kwanta. Ban daɗe da kwanciya ba ya shigo ɗakin, sai da ya kashe fitila kafin ya isko ni akan gadon. Yana hawa ya janyoni jikin shi.
Luf nayi kwance akan ƙirjin shi don a kwana ɗayan nan har na fara sabawa da kasancewa a cikin jikin shi.
A yau ma dai Albi bai sarara mini ba har sai da ya samu nutsuwa kafin ya koma lallashina domin dai sosai nake yi mishi kuka saboda yadda na wahala, ni dai ban wani gane bambancin jiya daya kasance farko a gareni ba da kuma yau.....