Free chapter · Read without an account

2

by Khadeejarth Sabi'u Yahyah · SO DAN RAYUWA!


*❉্᭄͜͡𝘚O 𝘿𝔸𝑵☆  R̲A̳Yᑌᗯᗩ ♥️*
         ☆♥︎L⋆o⋆v⋆e⋆ ᖴOᖇ 𐐛օv𝖊♥︎☆

𝗕Ⲩ 𝔸mmⅈ𝖊ყ ℓαуℓєян & ɴᴀɪɴᴀʀ kd♡

Page 2

OMER POV.

Karkaɗa ƙafa yake sannu a hankali yayin da idanunsa ke kafe bisa screen na wayar hannunsa, zuwa wannan lokacin da ya yi ma ta kira kashi-kashi yafi ashirin, amma ko ɗaya bata ɗa ga ba duk da wayar tana ringing shi ne abin da ya yafi ɓata masa rai musamman da ya tuna lokacin da yaji dirirar motar Fawaz da kuma sanda ya leƙa yaga ya daɗe da shiga Apartment ɗin, shi ya sa a Haukace ya fara lalubar lambar ESHERH  tare da danna kira wai dan ma kar Fawaz ɗin ya riga shi jin daddaɗar kuma sassanyar muryarta a wannan safiyar sai dai duk a banza domin bata ɗa ga ba, da ya gaji da kiran nata ne ya kira Maah ɗin ta sai dai ita bugu ɗaya ta ɗauka bayan sun gaisa take tabbatar masa da ESHERH na nan Qlau bayan ya tambaya har ma take ƙara wa da faɗin. “Ai Fawaz yana wurinta magani yake bata.”
A lokacin da ta faɗa hakan da ƙyar ya iya yi ma ta sallama, tsabar kishin da ya cika masa zuciya da jin wai Fawaz yana can wajen ESHERH. ‘To ko uban me yake yi?.’ wannan tambaya da mai bashi amsarta ita yake ta maimaita wa kansa yana jan tsuka lokaci-lokaci sannan bai haƙura da kiran layin ESHERH  ba amma ba amsa.
“Omer! Omer!! Wai lafiyarka kuwa tun ɗazu sai faman sakin tsaki kake kai ɗaya kana kuma danna waya?”
Matarsa dake lura da duk takunsa ta faɗa tana yi masa wani irin rikitaccen duba duk da tana ƙoƙarin danne baƙin kishin dake taso ma ta dan tasan a kan abu ɗaya yake wannan abu, da kai tsaye zata kira da hauka wato a kan wannan dai figaggiyar yarinya mai shegen kyau ESHERH  Allah ya gani ta tsana Yarinyar irin sosai ɗin nan.
A maimakon Omer ya bata amsa sai ma tsaki da ya kuma ja tare da tashi tsaye daga kujerar Dining ɗin da yake a Haukace ya miƙe hakan ya sa kujerar ta yi baya ta faɗa ƙasan ɗan tudun benen Dining ɗin. Basma da ta bi kujerar da kallo sannan cikin ɓacin rai ta sake ɗa gowa tana duban Omer da tamkar bai ga abin da ya yi ba ta buɗe baki tana shirin ta yi magana sai dai kafin ta kai ga furta komai sai gani ta yi a fusace ya juya fuuu ya yi hanyar ƙofa tare da ficewa daga Palon a hanzarce gaba ɗaya su biyun wato ita da ɗiyarsu mai kimanin shekaru huɗu a Duniya suka bi shi da kallo zuciyarta tana ƙara ƙuna da zarar ta tuna duk a kan wata mace daban yake wannan haukar sai dai kafin ta kai ga tunanin komai taji tashin Motarsa ya fice daga apartment ɗin.

Da dayake Estate ɗin da suke Rayuwa gaba ɗaya Ahalin JEDDY's ɗin a ciki wani irin hamshaƙi kuma ƙerarren Estate ne iya ganinka da a ka zubar da maƙudan kuɗaɗe wurin samar da shi Apartment ne iri-iri kamar a ƙasar turai ko wanne da nasa tsarin ginin da yanayin sa mai burgewa domin haɗaɗɗun villa ne ta ko'ina iya ganinka.

Bai gama daidaita parking motar Ba ya fito a hanzarce da kuma sassarfa ya shige ciki domin yadda zuciyarsa ta azalzalesa ya sa baya shakkar komai zai faru indai a kan ESHERH  ne yaji ya gani kuma zai ga uban abin da wancan Fawaz ɗin yake yi tun ɗazu a wurinta.

“ESHERH!”

Ya faɗa a fusace kuma kamar da ɗan tsawa lokacin da ya sama nasarar haurawa Ɗakin ta da yake ƙofar a buɗe yake shi ya sa ya shiga cikin sauƙi ba tare da ya ɓata lokacin kwankwasawa ba.

Daga ESHERH  da ta kawar da kai gefe daga ƙoƙarin miƙa ma ta magani da Fawaz ke yi har shi kansa Fawaz ɗin da ya ɗan duƙa domin bata maganin sai suka juya da sauri jin wannan uban kira da a ka kwala ma ta duk da sun san Mutum ɗaya ne zai iya hakan Wato Omer ille kuwa da shi suka yi arba yana tsaye sai wani sakin huci yake kamar wani gumurzun zaki.

“What the fuck! Are you out of your stupid mind da zaka shigowa mutane haka ɓakatatan babu checking excuses ko sallama da shirmenka na banza kana nema ka tsorata ƴar mutane?!”

Wannan kalaman da Fawaz ya jefe sa dasu su ne suka ƙara hura wutar tafarfasar da zuciyarsa ke yi amma da yake ba ta shi yake ba kuma badan shi ya zo ba shi ya sa yake ganin tsayawa bawa Fawaz ɗin amsa ma tamkar ɓata lokaci ne hakan ya sa shi kauda dubansa a kan Fawaz dake yi masa wani fusatacen duba sai dai a nutse ba'a harzuƙe kamar yadda shi yake ba, mayar da duban nasa ya sake kan ESHERH da har lokacin take lafe a kan Sofa ta ƙanƙame ko nace ta yi ma tattausan cushion runguma na musamman tamkar bata san abin da yake faruwa ba, tun kallo guda da ta yi ma Omer sannan ta watsar sai ma janyo wayarta da ta yi ta shiga what'ssapp da yake mafiya yawan lokuta da wifi da ya kasance kusan kowa na Estate ɗin yake amfani da shi ita ma haka ne, shi ya sa yanzu ma da shi ta yi amfani sannan ta fara duba saƙonni domin Akwai wanda take muradun gani sai ta watsar da lamarin Omer tamkar bata san da wanzuwarsa a wurin ba.

“ESHERH what on the earth are doing da tun ɗazu nake faman kiranki ashe ma kina gani amma baki ɗauka ba?”
Ya faɗa lokacin da ya yi daidai da ƙari sawarsa wurin da take zaune sannan ya sa hannu ya wafce wayar dake hannunta tare da shiga contacts ya nuna ma ta uban kira na babu adadi da ya dinga buga ma ta.

Kallon screen ɗin wayar ta yi sannan ta dubeshi ba tare da ta furta komai ba ta sake mayar da dubanta kan Fawaz da zuwa lokacin Allah ne kawai ya tsare bai kaima Omer kyakkyawan naushin da zai saka ganinsa da jin sa na ɗan lokaci suka bar gangar jikinsa ba domin da alama allurar tasa ta Soja ta motsa lura da hakan da Esherh ta yi ne ya sa cikin taushin murya da kwantar da hankali ta furta.

“Uncle Fawaz nasan kana da abubuwa masu yi muhimmanci da zaka gabatar a daidai wannan lokacin ba? To Please ka tafi dan banason wannan shirmen ya sa ka rasa kyakkyawar lokacinka a kan abin da bashi da amfani.”

Duk da kasancewar da biyu ta yi maganar na farko dai domin ƙuntatawa Omer kuma taga alama ya shaƙa na biyu kuma tana gudun kar Fawaz ɗin ya kasa riƙe fushinsa yaje ya illa ta Omer ɗin a Ɗakinta lamari ya kwaɓe shi ya sa ta furta wannan tausasan kalamai da hope ɗin Fawaz ɗin ya tafi dan shi Omer bata ɗauke shi a matsayin wani ajawali babba ba dan tasan ta yadda zata tafiyar da shi cikin ruwan sanyi.

“Taya kike tunanin zan iya tafiya na barki tare da wannan psycho ɗin da bai san inda keyi masa ciwo ba.”

“Fuck! Fuck! Ni kake kira da Psycho saboda ka mugun duban yanayina? Lallai ma Fawaz kake ko wa na rantse da Allah ka dena ganin kai ɗin Soja ne domin duk Ranar da ka sake kirana da Psycho to fa abin ba zai tafi mana daidai ba domin zan nuna maka cewar ni ɗin cikakken mahaukacin ne na gasken gaske ma!”

Fawaz zai sake magana amma Esherh ta yi masa alama da ido a kan ya yi haƙuri, kwafa ya ɗan ja sannan ya ciro wayarsa da ta fara ruri ganin MOO-tee (Mom shi ne Mutti in German ke nan) ke kiransa.

“Ohya zo kisha maganin kafin na wuce.”

Ba musu Esherh ta ƙari sa ta karɓa maganin duk da ba son sha take ba amma haka ta sha. Sannan Fawaz ya fita ba tare da ya sake duban inda Omer yake ba.

Ita kam Esherh komawa ta yi ta zauna ba tare da ta ce masa komai ba.

“Me kike nufi dani ne Esherh?”

Tajiyo muryarsa yana faɗin hakan sai dai wannan karon ba cikin tsawa ba.

“Kin san fa ina son ki me ya sa kike son azabtar da zuciyata ne haka ta hanyar kula mutanen da basu dace ba?”

Ya ƙara faɗa.

Wannan karon dubansa ta yi Allah ya gani magana ma batason yi a wannan taƙin dan ya gama ɓata ma ta rai dama ta tashi sai a hankali ya zo da shirmensa da yake kira so ya daɗa jagula ma ta rai.

“Yah Omer please ka tafi zamuyi maganar zuwa wani lokacin!”

Ta faɗa bayan ta miƙe tare da ƙari sawa wurinsa ta karɓa wayarta da ya riƙe.

“amma...!”

“Please ka tafi kawai.”

Ta katse shi daga ƙoƙarin sake magana da yake niyya. Sannan ta koma ta zauna tare da lumshe ido hakan ya sa Omer fita dole badan yaso ba.

Ajiyar zuciya ta sauke sai da ta ƙara aƙalla mintuna goma a haka sannan ta miƙe fitowa ta yi daga Ɗakin kai tsaye ta wuce na Maah ɗin ta, da sallama ta shiga Maah da fitowarta daga Bathroom ke nan tana zaune gaban mirror ta amsa ma ta sallamar tana juyowa murmushi mai kyau suka sakarwa juna sannan Esherh ta ƙari sa tana faɗin.

“Ai nayi tunanin ma tuni kin shirya ko dai kin fasa tafiya zuwa Lagos ɗin ne?”

Esherh ta ƙare maganar lokacin da ta ƙari sa sannan ta ɗauki Dryer ta fara drying hair na Maah ɗin cikin kwarewa.

“Zuwa sha biyu ne tafiyar yanzu kuma goma da wani abu ne shi ya sa na tsaya na shirya da wuri.”

Maah ta bata amsa cikin kulawa.

“Na kuwa ji daɗin hakan domin koba komai nayi fira da Maah ɗina.”

Murmushi kawai Maah ta yi jin abin da Esherh ɗin ta ce.

“Hmm wato Maah ashe ma kina jina da su Yah Omer shi ne ko kizo ki kwaceni ko?”

Esherh ta faɗa tana ɗan kwaɓe fuska.

“Ai bari nayi ki dinga solving matsalarki sa kanki.”

Maah ta bata amsa.

“Hmm wallahi Yah Omer mugun ciwon kai ne gaba ɗaya na rasa gane kanshi!”

Esherh ta faɗa tana ɗan dafe kai.

“Ki nutsu dai kiyima kanki zaɓen da ya dace domin ba zan hanaki kula su ba duka ƴan uwanki ne amma ki nutsu ki kuma san abin da ya dace ke ba Yarinya bace Esherh shekarunki ashirin da biyu baki da buƙatar sai na shiga miki komai a rayuwa domin kin kai Matakin da zaki ji da komai naki!”

Maah ta faɗa cikin siga ta bada shawara, domin Allah ya gani ba wani son Omer da ɗiyar nata take ba kwara ma Fawaz bashi da wata matsala sai dai Mahafiyarsa wato MOO-tee ita ce matsalar domin sam basa ga maciji da Maah kuma ba komai ne sila ba sai baƙin ciki da hassada da take yi ma Maah ɗin sai dai sam bata kulata kuma bata ɗauki tsana kamar yadda ita MOO-tee ɗin ta ɗauka ta ɗaura ma Esherh, ita Maah bata ɗaura a kan ƴaƴan ita MOO-tee ɗin ba kuma sosai suke shiri da Fawaz domin ko kaɗan bai ɗauko halin mahaifiyar nasa ba.

Shiru Esherh ta yi dan ta rasa ma mai zata ce Allah ya gani kaf cikinsu ba wanda zata ce tanayi ma wata aba wai SO abin da ta sani shi ne tana girmama su Matsayinsu na ƴan uwanta especially ma Fawaz sosai take bashi girma.

Kawar da zancen ta yi da faɗin.

“Ba ma wannan ba kin san fa yau ni da kaina zan rakaki har airport.”

“Da gaske?”

“Sosai ma kuwa Maah Tah!”

Esherh ta faɗa tana dariya cike da nishaɗi domin Maah ita ce Mutum na farko da Esherh take zagewa suyi fira da nishaɗi sosai daga ita kuma sai mutane biyun nan da suka biyo baya wato Kakanta Sai kuma babbar ƙawarta Eman da a halin yanzu bata ƙasar.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol