Free chapter · Read without an account

Barrister Hibba

by Nusaiba Ibrahim Rimi · Barrister Hibba

đź’Ą BARRISTER HIBBA đź’Ą

✍️Nusy bee

Page 7

ALI MUHAMMAD KABO AREA, RAILWAY ESTATE, KANO STATE, NIGERIA

Gobe ne za'a saurari ƙarar da Rahama jaafar shuwaki ta shigar kan matar mahaifin ta Hajiya Fatima Yusuf Dala,da take zargin da sa hannun ta a kisan mahaifin nata Alhaji Ja'afar shuwaki,tare da taimakawar ƙanin ta Suraj Yusuf Dala,shekaru biyu kenan ana zaman Court ɗin, watanni bakwai baya akayi zama na ƙarshe kafin yau,sai gobe da ake fatan ƙarƙare shari'ar da Hibba ke jagorantar ta,tare da marawar wasu ƙwararrun lauyoyin nan, abin tashin hankalin tun bayan zaman kotu na huɗu aka nemi Rahama aka rasa,kuma babu wata hujja ko ɗaya da tayi nuni da inda take,tabbas a lokacin Barrister Hibba ta shiga tashin hankalin da bazai misaltu ba,amma daga baya sai ta dake ta cigaba da jan ragamar kotun,to tun a zaman ƙarshe Hibba bata ƙara cikakken sati ɗaya a Nigeria ba ta cale ƙasar Germany bayan ta gama dukkan shirin ta akan ƙannen ta,da ta tabbatar shari'ar zata iya shafar su basu ji ba basu gani ba

Yanzu Ć™arfe goma da mintuna ashirin,tana zaune a harabar gidan Ć™arĆ™ashin wata thatch  rumfa, laptop ce a hannun ta,ma'aikatan gidan sai leĆ™en ta sukeyi suna magana Ć™asa-Ć™asa,don babu wanda yake da ikon magana da Ć™arfi indai tana wajen, musamman ma da idan tayi irin haka to aiki ya chaja mata kai kenan,idan da hali ko Ć™arar iska kar taji. Yau ma kamar kullum track suit ne a jikin ta,sai dai yau wandon ne kawai blue black da rigar Jersey na PSG,ta É—ora Jersey veil baĆ™i,idanun ta sanye da medicated glasses da take sakawa yawancin lokuta

Daidai nan akayi knocking ƙaramin gate, mas'udu ya buɗe ya leƙa,wani giant guy ya gani, kyakkyawa ne wankan tarwaɗa,sanye da ƙananan kaya designer,hatta da takalmin ƙafar shi mai tsananin tsada ne, idanun shi saye da baƙin glasses

Ganin irin kallon da mai gadin yake masa yasa ya É—aure fuska yace"malam uwar É—akin naku na nan?"

"Eh....eh tana nan,sannu yallaɓai"sai zare idanu yakeyi

Bai saurare shi ba ya kewaye shi ya shige gidan,yana tunanin ta inda zai ganta sai ya hango ta can nesa a zaune hankalin ta na kan computer ɗin gaban ta,da sassarfa ya ƙarasa, ma'aikatan sai kallon shi sukeyi saboda sun san Hibba bata taɓa kawo maza,infact,indai ba sabgar aiki ba babu abinda yake haɗa ta da maza

Da zuwan shi ya nuna ta da yatsa yana faɗin"You stupid!you wicked!!abinda kika ga dama kike yi ba abinda ya dace ba,kinayiwa waɗanda kika raina abinda kike so,to ni baki isa ba,last time kin ci min mutunci in front of people kinyi disgracing ɗina,ba ƙyale ki nayi ba,yanzu ma kin sake shiga gona ta,to a wanna karon zan ɗauki tsatstsauran mataki akanki,don ke ɗin ba komai bace,ba kowan kowa bace face shashasha,sakarai kuma kidahuma

Na baki nan da six hours ki tabbatar Zahraddeen ya koma gida, otherwise kuma zaki gane ke ƙaramar ƴar iska ce"tuni masu aikin gidan sun taru a gigice suna ƙoƙarin janye Hammad,wasu suna zagin shi wasu suna roƙar shi,amma abin mamaki ko ɗago kai ta kalle shi batayi ba,ko nuna alamar tasan akwai mutum a wajen batayi ba,ta cigaba da aikin ta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali batare da ko ɓurɓushin damuwa a fuskar ta ba

Muyassar ne ya ratso cikin ma'aikatan, yayiwa Hammad sallama tare da miƙa masa hannu, Hammad ya kalle shi,sai kuma yayi masa kwarjini,ya amsa masa sallama sannan ya miƙa masa hannu sukayi musabaha,a nutse Muyassar ya kalli sauran masu aikin yace "don girman Allah kowa ya koma bakin aikin shi,ba wani big deal bane,kawai rashin fahimta ne"ganin ko ɗagowa Hibba batayi ba yasa masu aikin suka wuce suna hararar Muyassar da suke masa kallon mai neman suna

Muyassar ya kalli Hammad cikin tausasawa yace "ayi haƙuri yallaɓai,idan rai ya ɓaci hankali kada ya gushe,Madam ɗin mu tayi maka ba daidai ba,kamata yayi ka zauna da ita kaji uzurin ta,maybe tana da hujjar yin hakan, maybe akwai abinda baka sani ba shiyasa"Hammad ya katse shi yana nuna Hibba da yatsa yace" baka san wannan matar bane,shaiɗaniya ce, azzaluma ce,amfani take da dukiyar ta tana taka duk wanda taga dama,yanzu abu ya biyo ta kan aboki na, gobe bansan ta kan wa zata bi ba"ɗan murmushi Muyassar yayi yace"ina mai baka haƙuri,indai abokin ka bashi da laipi in Sha Allahu zai koma gida a yau ɗin nan,kayi haƙuri, Please sir"da haka Muyassar ya lallaɓa Hammad ya raka shi har bakin motar shi

Dawowa yayi, daidai lokacin da twins suka fito a guje suna kuka cikin tashin hankali,sai yanzu labari ya same su wai wani yazo yana yunƙurin dukan yayar su,sai yanzu ta ɗago ta watsa musu mugun kallo,sai a lokacin suka tuna shigar da ke jikin su,ƴar top ce da wando three quarter,babu ɗan kwali akan su,da gudu suka juya suka nufi cikin gidan, musamman da suka ga yayar su cikin kwanciyar hankali,aikin ta ma takeyi

Muyassar yayi sallama,bai damu da yadda ta cigaba da aikin ta ba,ko nuna ta san da tsiron shi a wajen batayi ba,kamar dai yadda tayi wa Hammad,ya fara magana cikin kwantar da murya

"Ma'am I'm sorry for what I will say now,duk da kasancewar ki wata wadda Allah ya bawa muƙami da dukiya,ba chance bane na samun damar wulaƙanta ɗan adam,ya kamata ki gyara mu'amalar ki da mutane saboda watarana su zasu kai ki ga kabarin ki,wanda babu bambanci tsakanin waɗanda suka fi ki da waɗanda kika fi,har ma da ke kanki,wannan ɗabia ta janyo miki kyara da tsana tsakanin mutane,wannan abin duniyar da kike dashi ne ya sanya bakya gani, I'm sorry if I hurt you in any way"

Bisa ga tsananin mamaki sai gani yayi ta saki murmushi sosai har  dimples É—in ta suka bayyana,Ć™amewa yayi cike da mamaki yana kallon ta, still murmushin fuskar ta bai É“ace ba ta É—ago tana zare glasses É—in idanun ta,ta dube shi tace

"A tsawon shekaru kusan ashirin wannan shine karo na farko da wani ya ga nayi abu da yake gani ba daidai ba ya tunkare ni yayi min gyara batare da shakka ko tsoro ba, Weldone!

Amma ina so ka san wani abu,su mutane da kake ganin su idan ka nemi taimakon su a lokacin da baka dashi sai su hantare ka su ji haushin ka,idan ka ɗauka su tozarta ka, ka tuna yarinyar jiya?idan kuma ka zama wani abu sai su zage ka su munana maka zato,wannan shine karatun da nayi na mutane,karatu mai wuyar mantawa"ta runtse idanu tana girgiza kai, sannan ta buɗe,ta kalle shi ta cigaba da magana cikin jin raɗaɗi"a rayuwar da muke ciki, mutane masu son kai sunfi yawa, azzalumai, waɗanda ko yaya abu ya saɓa da ra'ayin su sai su ɗaga murya,bazan iya dakatar dasu ba,amma zan yaƙe su iyakar iyawa ta, beside,na gode da shawara,amma bazan saki Zahraddeen ba,in Sha Allah sai doka tayi aiki a kanshi"tana kaiwa nan ta mayar da kanta ta cigaba da abinda takeyi

Muyassar yayi shiru yana kallon ta maganganun ta na yi masa yawo akai,still ya shinshino wani abu da take ɓoyewa,batare da yace uffan ba ya miƙe cikin sanyin jiki ya bar wajen ya koma ɗan nesa da ita kaɗan ya zauna yana kallon yadda hawaye suke taruwa a idanun ta tana mayar dasu

LEKKI PHASE 1, LAGOS STATE, NIGERIA

Cikin sauri take shiryawa,don Flight ɗin su ƙarfe takwas na dare ne,gashi yanzu bakwai tana daf da yi, mijin ta abdulraheem chukuma ya ɗauki tilon ɗan su Mukhlis sukayo wajen parking lot,shi ya ja motar suka nufi Murtala Muhammad airport

Shi ya kai su airport,sai da ya tabbatar sun tashi sannan ya dawo gida

Bayan ta sauka ta samu taxi wadda zata kai ta Ali Muhammad kabo area, don tana buƙatar ganawa ta musamman da Hibba saboda zaman kotu na gobe

Tana shiga wayar ta tayi ƙara,ta ɗaga tana faɗin"an gaida Cobra!dodon azzalumai!"

"Khadijah kina ina ne?"

"I'm on my way,our plane just landed,Amma sai na fara Branching gidan ki kafin na wuce gida, saboda kin san komai"

"Alright I'm waiting my inyamura"Hibba ta ƙarasa tana ƴar dariya, Khadijat tayi tsaki ta kashe wayar don bata ƙaunar sunan

Wayar ta ta É—an cigaba da dannawa,amma me?

Daga ita har Mukhlis ɓingirewa sukayi da bacci,sai farkawa tayi ta ganta a cikin wani ɗaki mai tsananin duhu,cike da tashin hankali ta mike zaune tana zazzare idanu,sai kuma ta tuna da Mukhlis,cikin sauri ta fara laluben shi, zuciyar ta cike da tashin hankali,sai dai babu Mukhlis babu alamun shi

LAMIĆŠO CRESCENT,NASSARAWA GRA,KANO STATE

Zuru yayi yana kallon Nihla da Mifra da suke ta wasannin su sai labari na shirme suke bashi,zuwa can Mifra ta ɗaure fuska tace"Daddy you are not responding"firgigit yayi yana gyara zama,da murmushin yaƙe akan fuskar shi yace"ku bari na dawo, uncle Khaleed yace akwai patients da yawa,kuyi musu addu'a Allah ya basu lafiya"ya miƙe yana faɗin"idan Ummi ta dawo kuce mata naje asibitin"

Kusan tare suka haÉ—a baki suna faÉ—in"dady Allah ya kiyaye"ya amsa musu cikin kulawa sannan ya fice

A hanya yana driving yana tunani,shi fa gaba ɗaya ya rasa me yake damun shi,tunda ya tashi shi dai yasan ƙalau yake,amma yanzu yana jin wani iri,sai yanzu ya fara tunanin wataƙila abinda yayiwa Hibba ne,duk wanda ya sanshi ya san rashin mutunci ba ɗabiar shi bace,da alamu abinda yayiwa Hibba ke damunshi, fuskantar haka ya sa ya ja tsaki ya yakice komai a zuciyar shi ya mayar da hankali ga tuƙin shi

Kai tsaye asibitin su Khaleed ya nufa,a office ɗin shi ya same shi yana riƙe da wani result yana jinjinawa,ga wayar shi a ɗaya hannun,da alamu waya ya gama yi

Hammad ya samu waje ya zauna yana kallon shi,cikin sanyin murya Khaleed yace"man ka ƙaraso ne?"

"Me ya haÉ—a Zahraddeen da waccan Ć´ar iskar yarinyar har ta saka akayi arresting É—in shi?"

"I don't know Hammad,Amma na sani Hibba bazatayi haka ba sai da ƙaton dalili,amma tace very soon zaa shiga Court,ita kuma yanzu haka ma nasan tana hanyar zuwa nan"

Tsaki Hammad yayi yace "to idan tazo uban me zata yi? wallahi Ni mai iya lakaÉ—a mata duka a cikin asibitin nan ne"

Murmushin babu shiri Khaleed yayi yace"don Allah ka yayyafawa zuciyar ka ruwan sanyi,duk wannan ba mafita bace,mu bi komai a sannu"Hammad bai sake magana ba ya karɓi medical report ɗin hannun Khaleed yana dubawa,da wata iriyar gigita ya kalle shi yana faɗin"who is this Khaleed?"

AIYO MANSION,ALI MUHAMMAD KABO AREA, RAILWAY ESTATE, KANO STATE, NIGERIA

Da bala'in sassarfa Hibba ta fito daga cikin main building ɗin su sanye da track suit farare na PSG,a lokacin take ƙoƙarin gyara baby hijab ɗin da ta saka,ƙafar ta sanye da farin canvas, Maryam ta biyo ta tana shagwaɓa zata bi ta,da ta buga mata wata tsawa sai da ta ƙame sannan ta juya ta koma gidan a guje, Hibba ta ƙarasa da sauri tana cillawa Muyassar key,da sauri Muyassar ya fito da motar,babu ɓata lokaci ta faɗa,ya ja motar suka nufi asibitin su Khaleed

Har cikin harabar asibitin ta saka Muyassar ya shiga da motar,a kusan guje ta fito,cike da mamaki yake bin ta har office É—in Dr Khaleed,tana shiga a firgice ta dubi Khaleed tana faÉ—in"Dr what's the problem?"ko lura da Hammad da ke zaune batayi ba

Ɗaukar takardar yayi ya miƙa mata, Hammad da farko ɗauke kanshi yayi, amma da yaga ta karɓi takardar gwajin da shima ya firgita sai ya zuba mata idanu yaga m e zatayi,tana gama dubawa ta fara tafiya kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki,idanun ta tuni suka fara zubar da hawaye

Mamakin Muyassar ya ƙaru lokacin da yaga fitowar ta,waje ta samu akan kujera ta zauna,shi dai Muyassar mamakin abinda ya gani yakeyi,to ko wani ciwon ta kamu dashi haka?

"Dama tayi haka ne don ta É“ata ni a idanun duniya,wannan yarinyar ta cuce ni, Allah ya gani na bata tarbiyya,amma da yake tsinanniyar yarinya ce........"marin da ta É—auke mutumin mai kimanin shekaru hamsin zuwa da biyar ne ya dakatar dashi daga surutan da yakeyi,ya dafe kumatu yana zazzare idanu 

Hawaye yana zarya a idanun ta,cikin Muryar kuka tace"kayi asara,kaji kunya,ka cuci kanka da kanka,don dai wallahi baka cuci A'isha ba, wallahi da zuwan ka a matsayin uba gwara ace ba'a san uban ba, menene ribar ka don ka lalata rayuwar ƴar ka don ka samu abin duniya?to ka ƙirga kwanakin taɓewar ka daga yau,muddin ina numfashi sai kaji dama baka zo duniya ba,nayi maka alƙawarin sai ka gwammaci mutuwa da rayuwa,ba dai taƙamar ka ƴar ka bace?"

Da sauri yace"Hajiya ya kamata kiyi min adalci,ba wai duk abinda yarinya ta faÉ—a kawai ki hau kai ki zauna ba,tunda mahaifiyar ta ta  bar gida na take Ć™ulla mata kaidi iri iri tayi min,kawai don babu yadda zanyi daita ne"

Murmushin takaici tayi tace "really?to saurari wannan"ta goge hawayen fuskar  ta,wayar ta ta ciro ta kunna voice recording na muryar wani bawan Allah,ai kuwa ya fara fitowa tar

"Baby girl zo nan,gaya min,yaya sunan ki?"

"Suna na ruƙayya"

"To yanzu zan tambaye ki, idan kika amsa min dai-dai zan baki wannan alawar,kin yarda?"

"Eh na yarda"

"Yayyen ki nawa?"

"Biyu ne,yaya Amina da yaya A'ishah"

"A É—akin wa kike kwana a cikin su?"

"A É—akin yaya Amina"

"Meyasa bakya kwana da yaya A'ishah?"

"Ita ai ba'a gidanmu take kwana ba,baban mu ne yake kai ta unguwa da daddare,sai washegari kuma ta dawo"

"Sun taɓa zuwa unguwar da ke?"

"A'a,na taɓa cewa zan bi su umman mu tace ba wajen zuwa na bane"daga nan Hibba ta kashe record ɗin ta ƙara kunna wani,still Wanda yayi hira da ruƙayya ne

"Yaya sunan ki?"

Cikin kuka ta fara bayani"sunana A'isha Murtala"

"Shekarar ki nawa?"

"Sha huÉ—u"

"A'isha ga ki a asibiti,me ya same ki?"

Cikin kuka mai tsanani tace"baba na ne ya cuce ni, shine yake kaini wajen wani ɗan siyasa,a yadda naji yayi wa matar shi bayani batare da sun san naji su ba,wai bokan shi ne yace idan yana so ya samu kujerar shi sai ya tara da yarinya ƴar ƙasa da shekaru sha biyar, yanzu gashi ina da ciki,kuma ance inada wasu cututtukan"ta sake fashewa da kuka

Voice É—in yana kaiwa nan Hibba ta kashe tana goge hawayen fuskar ta,ta kalli Mutanen da suka tsaya suna saurara,ciki har da Muyassar da su Dr Hammad da Dr Khaleed,sai sallallami suke yi da tsananin mamaki,shi kuwa uban yarinyar duk ya firgice a tsorace,yana tunanin matakin da wannan masifaffiyar yarinyar zata É—auka akanshi,ta sake mayar da idanun ta kanshi tana kallon shi cikin tsananin tsana

"Kai kam bani da magana da kai,wasu mutanen idan suka aikata irin wannan ɓarnar ana ankarar dasu ne idan akayi musu batun ya zasuji idan akayi wa nasu,amma kai da kanka ka kai taka"ta kalli matar shi da ke gefe tana faɗin"ke kuma saboda A'isha ba ƴar ki bace shiyasa kika zuba idanu mahaifin ta ya lalata ta ko?"karaf matar tace"to Ni me ya shafe ni?ba ƴar shi bace?naga tare na gansu, shi bai san darajar ta ba sai ni?"

Wata dariya Hibba tayi tace"ke a tunanin ki zai lalata tashi da kanshi saboda kuɗi ke Kuma taki ta zama safe?ya ciyar da ita yayi mata gata sannan kuma ya zuba mata idanu?to ki binciki ƴar ki da uban riƙon ta"Amina wadda ta kai shekaru goma sha bakwai da ke laɓe bayan uwar ta ta fito tayi karaf cikin rashin kunya take faɗin"wallahi ƙarya ake min,ni....."

"Ke dalla yi min shiru,ko sai na kunna naki voice É—in ne da na saka akayi miki na bayanan maganin zubar da ciki da kike siya?"a firgice maman ta ta kalle ta, yarinyar ma tayi wani irin shock, Hibba bata sake kallon su ba ta tafa hannayen ta,Ć´an sandan farin kaya suka bayyana,ta nuna mahaifin A'isha tace"arrest him!"tana gama faÉ—in hakan ta wuce zuwa female ward

A can ta samu A'isha sai kuka takeyi,tausayin yarinyar ya kama ta,anyi mata raping a silar mahaifin ta,ga ciki ga ciwon sanyi ga kuma HIV/AIDS, ƙarasawa kusa da ita tayi ta rungume ta tana faɗin"is okay dear,take heart,komai zai wuce in Sha Allah,just move on,kiyi haƙuri kowa da ƙaddarar da Allah ya jarabce shi daita"ta zauna a gefen ta ta kwantar da murya tace

"Bari na baki labarin wata da irin ƙaddarar ki ta faɗa mata,bata da kowa,ba iyaye babu dangi,amma da ta cigaba da rayuwar ta yanzu haka ta zama abin burgewa,kema ina so ki zama kamar ita,idan Kuma kika karaya kinga mun faɗi mahaifin ki yayi nasara"

Hawaye ta share tace"to ta yaya Aunty?mutuwa zanyi fa?ance ina da ciwon AIDS"murmushi Hibba ta ƙara yi tace"kowa kika ga ya mutu lokacin shine yayi EESHA!akwai ciwukan da suka fi AIDS matsala amma idan aka kiyaye dokokin su ana rayuwa ƙalau,kema a haka zaki rayu,ki zama abar alfahari watarana,kiyi Aure ki haifi ƴaƴan ki masu albarka,kuma kyawawa kamar maman su"ta ƙarasa tana murmushi da jan kumatun ta

Haka tayi ta yi mata hira har kaso mai yawa na damuwar ta ya tafi

#Nusy_bee

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol