Free chapter · Read without an account
2
by Rufaida Umar · ALWASHI
ALWASHI
02
Sun samu kyakkyawan tarba daga shugabar gidan marayun wato Haj Rabi'atu Gwarzo. Bayan gama sauraron abin da ke tafe da su, ta yi musu jagora da kanta suka fara zagaye ɗakunan yaran. Tausayi da kaunar yaran suka mamaye zuciyar Khalisat, ji ta yi ita da ace ma tana da damar rayuwa cikinsu ta zamewa kowannen Uwa mai share kokensu, toh fa tabbas da ta yi hakan. Hankalinta ya kai kan wani yaro da bai wuce shekaru uku a duniya ba dake gefe yana ta kuka yayin da sauran yara ke faman wasanninsu. A hankali ta zare yatsunta daga na Hammad ta ƙarasa ga yaron, duk suka bi ta da kallo, baƙi ne wuluk, da ka gan shi ka ga bahaushe na usuli. Sai dai Allah ya ba shi manyan idanuwa masha Allah da kuma karan hanci sai bakin nan ɗan tsurut. Ta shafi kansa dake a cike da gashi tana murmushi. Tuni yaro ya bar kuka ya na kallonta, hannunsa ta riƙo cikin nata.
"Me aka yi maka kake kuka?"
Ya taɓe baki kamar mai shirin ƙara fashewa da kukan kuwa.
"Affan kenan, shi ai ba ya rabo da koke-koke tun ma bai kai girman haka ba. Ga shi nan dai kamar ba wayo."
Khalisat ta tsinci muryar Haj Rabi a gefenta, sai lokacin ta fahimci biyo bayanta suka yi, sauran yaran tuni sun ɗan yi shiru suna kallonsu ganin Mama da baƙin fuskar da ba su taɓa gani ba.
Ita kuwa Khalisat ji ta yi wani abu na tsarga mata a kan yaron nan, kamar yadda shi ma Hammad da ke kallon yaron ya ji ya shiga ransa ya kuma rasa dalili. Shi ma dan ranƙwafowa ya yi yana jawo yaron a jiki.
"Affan kenan, tun yana zanin goyo aka ajiye shi a ƙofar wannan gidan cikin kwali ko cibinsa ba a yanke ba. Ba mu san wanda ya kawo shi ba. Har yanzu iyakar bincikenmu mun kasa samun wani labari da zai haska mana waye shi. Yaron ya kasa sabo da sauran ma'aikatan gidan tun bayan da mai rainonsa Yahanasu ta rasu ake shan fama yau wata uku kenan."
Bayanin Haj Rabi kenan a kan Affan daidai sadda suke takawa za su koma ofishinta, har da Khalisat wacce ta ɗauki Affan a kafaɗarta tana kuma jin ƙaunar yaron da ma tausayinsa na ratsa ta. Koda suka ƙarasa, Haj Rabi a ofishin ta ɗan bar su domin su yi shawara. Hannunta Hammad ya riƙo, kafin ya kai ga cewa wani abu ta riga shi muryarta a karye.
"Ina son Affan."
Murmushi Hammad ya yi yana jinjina kai gami da kallon yaron da ya yi luf a jikinta yana wasa da awarwaron zinaren dake hannun.
"Shikenan."
Daidai lokacin Haj Rabi ta dawo, nan suka sanar da ita abin da suka yanke. Ta ji dadin hakan kwarai, aka yi cike-cike da saka hannu na duk abin da ya kama ta. Ta ba su takardar haihuwar Affan din ko don buƙatar karatu idan ya taso, sai da aka kammala dukkan wani abin da ya dace aka ba su kayan Affan, suka ƙi karɓa, Hammad ya ce a ba sa'anninsa dake gidan. Kudi masu kauri ya damƙawa Haj Rabi a yi wa yara siyayya. Ya kuma rabawa ma'aikatan gidan nasu.
Haka Khalisat suka kama hanya da Affan wanda shima koda wasa bai rabu da jikinta ba. Har tsokanarsa ma'aikatan gidan suka yi ta hanyar mika hannu kamar za su karɓe shi, sai ya tsala ihun kuka ya ruƙunƙume Khalisat. Aka dinga dariya har ita wacce ranar take jinsa tamkar an ba ta tikitin tafiya Makkah.
Khalisat da Hammad suka dawo gidansu cikin kauna da kulawa suka ci gaba da nunawa Affan ƙauna. Yaron ya yi matukar sabo da shaƙuwa da su. Ya kasance gaba daya Khalisat ba ta da wata damuwa a rayuwa domin har ranta take jin cewa shigowar Affan rayuwarta ya shafe mata komai na ƙunci da tunani. Koda ya isa shiga makaranta, suka sanya shi a makaranta mai kyau da tsada.
Mai rai ba ya cire rai da rahmar Allah, wannan haka yake, koda dai Khalisat ta bar damun kanta ta kuma yarda da ƙaddarar cewa ba ta da rabon ganin gudan jininta a doron ƙasa, wannan dalilin ne ya sa shigar ciki jikinta ya zo mata a bazata. Ta kasa yarda har sai da suka dangana da zuwa asibiti. Likitan ya basu tabbacin ta samu ciki har na watanni uki. Hawayen farin ciki ya shiga fita a saman fuskokin ma'auratan. Hammad a ranar haka ya dinga kyauta ga bayin Allah marasa ƙarfi. Kowa na gidan kuwa ya shaida irin farin cikin da yake ciki.
A lokacin da Khalisat ta haifi ɗiyarta mace wacce ta ci sunan Kakarta Hadiza suke ce mata Kubra, shekarun Affan goma sha uku a duniya yana sakandire. Haihuwar Kubra bai rage komai na kulawar da suke ba Affan ba, shi ma yaron duk sadda ya dawo daga makaranta to fa kusan shi ke rainon Kubra. Koda zai tafi karatu ƙasar waje bayan kammala Sakandire a lokacin Kubra na da shekaru huɗu a duniya amma kuka sosai ta sha don ta shaƙu da Affan. Daidai da Hammad, Khalisat sai da suka ji kamar a fasa tafiyar ya yi karatun a gabansu amma kuma duk don neman a rufuwar asirinsa ga tabon da suke gudun a fama masa a garin duk da cewa ya riga da yasan shi ba wai su suka haife shi ba, ya sa dole suka haƙura ya tafi jami'ar London domin karantar fannin kasuwanci.
Shekaru huɗu ya kammala ya dawo Nijeriya, sa'ilin Kubra na firamare. A lokacin Affan ya kamawa mahaifin nasa ayyukan kasuwa. Kusan komai shi ke tsaye a kai kuma da iyakar gaskiyarsa yake kula masa da dukiyoyi.
Har a wannan lokacin Alh Hammad ba su wani ɗinke da Alh Sabi'u sosai ba amma kuma sukan je wa juna jaje ko taya murna idan wani abun ya tasowa ɗayan.
A kwana a tashi, cikin hukuncin Allah aka wayi gari Kubra ta kammala sakandire. Zuwa lokacin kuma sosai Alh Hammad ke yi wa Affan nacin ya fiddo matar aure amma ya yi biris. A lokacin farin cikin Kubra biyu ya kasu, ga na murnar kammala sakandire a gefe kuma ga murnar mahaifin nasu zai cika alkawarin da ya dauka na kai ta Maiduguri wajen danginsa. Garin da koyaushe Affan ke yi mata ƙwalelan rashin ziyarta don shi ya je har sau biyu ma, tana kuka yana tsokanarta har sai Abban ya shiga tsakani tukunna.
Ana gobe zasu bar wuce Maiduguri kuma sai ta ji gaba daya jikinta ya yi mugun sanyi. Ta rasa dalilin yadda duk wani ɗokinta don a tafi ta neme shi ta rasa. Har iyayen sai da suka kula da hakan, Affan na zolayarta wai kodai a fasa amma ta yi biris da shi kawai. Haka ta yi lamo a jikin kafaɗar mahaifiyarta wacce tun soma tafiyarsu a saman titi take riƙe da littafin addu'o'i tana karantawa. Hammad ke tuƙin don bai bukaci tafiya da direbansa ba, sai Affan a gefensa wanda shima ya iya mota. Khalisat da Kubra suna zaune a baya.
Sun yi tafiya har sun wuce garin Yobe, daidai wani daji ba gida gaba babu a baya kawai ba zato Hammad ya taka ƙusa a titin. Nan da nan tayarsa ta gaba ta fashe cikin taimakon Allah ya dakata a gefen hanya. Kubra da ta ji kirjinta na bugu ta yi saurin fiddo idanunta masa kama da na Hammad din, kasancewar komai nata na Hammad ta ɗauko hatta da farin nasa wanda idan ka gani ka san Shuwa Arab ne na usuli. Gashinta kuwa ko kitso ba ta iya yi sai dai ta yi mata manyan kalba su yi kwance a gadon bayanta.
"Subhanallah, ai tayar nan ta.."
Hammad bai kai ga ƙarasa yi wa Affan da shima ya buɗe murfin motar ya fito bayani ba sakamakon ƙarar bindigar da suka ji, a razane dukansu suka juya suka kai duba ga ƙattan mazan da zasu kai su goma da suka keto ta dajin wadanda ba su ko ankara da zuwansu ba sai da suka cimmasu. Cikin Kubra dake cikin motar ya kaɗa, ta ruƙunƙume Khalisat wacce ke ta ambaton sunayen Allah a baka itama tana riƙe ɗiyarta gam!
"Ku durƙusa! Ku kwanta nace!" Babban nasu ya dakawa su Hammad tsawa, ba shiri duk suka zube a ƙasa. Hammad salati ya sanya. Bai yi aune ba ya ga an bude motar an hankaɗo Khalisat da Kubra waje su ma an sa su kwanciya rub da ciki a ƙasa.
"Don Allah don Annabi s.a.w ku yi mana rai, wallahi idan kuɗi kuke da buƙata ko nawa ne zaku samu." Abin da Hammad ya ce kenan cikin rawar murya.
Ya yi kokarin ɗagowa babu wani zance kawai suka harbe shi a ƙirji, ba sau daya ba kuma ba biyu ko uku ba, Affan ya fasa ƙara a gigice ya miƙe suka kawo masa harbi a ƙafa, ba don ya yi wani irin wuntsilawa ba da babu abin da zai hana harsashin samunsa.
"Affan kama 'yar uwarka ku gudu!" Khalisat ta furta cikin wani karaji da kuka.
Kubra da jikinta ya ɗauki rawa ga firgicin da ta shiga na harbin Mahaifinta da aka yi, ta kasa komai. Affan kuwa ya yi kukan kura ya yi kan mai rike da bindigar wanda tuni ya kai wa Khalisat harbi a gefen cikinta sau biyu, tuni jinin ya shiga malala ta daina motsi. Faɗi yake,
"Kubra tashi ki gudu! Ki tashi!"
Kamar wacce ya yiwa tuni kuwa, ta zabura ta mike sadda suka yi wa Afgan rubdugu ganin ya kai wa Boss dinsu naushi, ta juya ta koma hanyar da suka fito da gudunta kuma ba a hayyaci ba, gudun take yi ba tare da ta san ma inda take jefa ƙafafunta ba. Jin amon ƙarar Affan ya mamaye dajin ya sa ta tsayawa gami da juyowa a hanzarce, shikenan shi ma sun kashe shi! Hango wasu biyu da ta yi suna biye da ita a guje ya sa ta ƙara ƙaimi wajen gudunta. Ba ta yi aune ba da motar da ta taho sai kawai ji kake kuu an yi sama da ita an buga ta a kwalta. Nan da nan jini ya wanke fuskarta ta sume. Wannan ya yi sanadin juyawar waɗanda suka biyo ta don a yadda suka hangi motar ta yi sama da faɗi da ita, suna da tabbacin ita ma ta bar duniyar baki ɗaya.
***
Farkawa ta yi a hankali tana bin ɗakin da kallo, ta kasa tuno abin da ya faru. A hankali kuma ta ji komai yana dawo mata daki-daki a kwanyarta. Sadda aka harbi mahaifinta, da kuma salatin mahaifiyarta a sa'ilin da ranta ke kokarin ficewa sakamakon harbinta da aka yi. Ba ta kuma mance amon sautin muryar tilon ɗan uwan nata ba. Nan ita ma ta fasa ihu mai ƙarfi wanda ya ja hankalin wani matashin saurayi da dattijuwar dake gefe suna hirarsu, sam ba su kula da farkawarta ba sai a lokacin. Nan da nan suka yi kanta ganin tana kokarin fisge ruwan da ake ƙara mata, ga kuma kafafunta babu damar motsa su sakamakon ɗaurin da aka yi mata na karaya. Daidai nan Likita ta faɗo ɗakin don dama suna yin ward round ne. Aka sa matashin nan da dattijuwar fita. Suka ba ta dukkan kulawa, Likitar ta kuma gane ta dawo hayyacinta ne. Daƙyar komai ya lafa dai. Nan ta ce su yi kokarin ganin ta sanya abu a cikinta ko ya ya ne, kuma su lallaɓa ta da rarrashi.
Kubra dai har Likitan ta fice kuka kawai take yi musamman da ta ji wai tana cikin satinta na uku a kwance a gadon asibitin. Dattijuwar nan ta dinga yi mata nasiha bayan ta ji abin da ya sanya ta kuka da kuma nuna mata muhimmancin yarda da kaddara, shi kuwa Matashin nan kallonta kawai yake yi. Tun sadda ya kaɗe ta da mota, har zuwa ranar da suke ciki zuciyarsa ba ta samu nutsuwa da tunaninta ba. Bai ma taɓa jin abin da ya ji har ransa yana kauna a farar ɗaya ba sai Kubra. Yanzun da yake jin labarin maraicinta, sai ya ji tausayi da kaunar sun ninka na baya.
Ita ma Kubra a bakin Dattijuwar ta ji cewa ai matashin mai suna Adam Yaƙub Kibiya shi ne ya kaɗe ta kuma ya kawo ta asibitin. Tafiya ce zai yi zuwa Maiduguri halartar wani daurin aure na abokin aikinsa dan jarida, wannan tsautsayi ya dakatar da tafiyar.
Sai da ta ƙara sati biyu a asibitin kafin a sallame ta, zuwa lokacin wasu a cikin yan uwan Adam sun zo har asibitin sun duba ta. Ta kuma gane cewa dattijuwar nan 'yar uwa ce a wuri mahaifiyarsa, Gwaggo suke kiranta. Ba wai ita ce ta haife shi ba. Jikinta ya yi sanyi sadda ta ji wai Gwaggon ce za ta tafi da ita gidanta, farko tsoron da take da fargaba bai wuce na inda za ta dosa ba, wajen wanda za ta je da sunan dangi.
Haka rayuwar Kubra ya koma hannun Gwaggo wacce duka yaranta maza ne kuma sun yi aure. Zamansu gwanin burgewa, kullum kuwa Adam yana jelar zuwa gidan Gwaggo daga wajen aikinsa. A watarana ne ma a bakin Gwaggo take jin cewa Adam ɗan jarida ne sananne a garin nasu na Yobe, mutum ne jajirtacce marar tsoro. Haka yake fayyace sirrikan 'yan siyasa komai girmansa idan ya ji. Allah ne kawai ke tsare Adam Kibiya, a cewar Gwaggo, saboda an sha kawo masa hari Allah na tsallakar da shi daga tarkonsu. Mahaifiyarsa kuwa, wato ƙanwa ga Gwaggon, ƙaunar duniya ta ɗora a kansa ba kuma don shi kaɗai ne ɗa namiji ba, kuma ba don yana auta a mazan ba, sai dai kusan a yaranta shida ya fi kowa tausayi da kokarin kyautata mata. Kubra ta so ta tambayi meyasa ba ta taɓa ganinta a asibitin ba, amma kuma ta yi shiru don ba huruminta ba ne. Kuma ita din ba wai zuri'arsu take ba don haka ba ta da ta cewa.
Ita ma bayan ta samu nutsuwa sosai ne, a watarana da Adam ya zo ta fayyace musu komai dangane da tarihin rayuwarta. Adam ya yi mata tambayoyi a kan yan uwansu na Maiduguri, ko sunan unguwar ba ta sani ba. Ita kusan za a ce babu wanda ta sani cikinsu sai wasu yan uwan Hammad da ta taɓa gaisawa da su ta waya. Sunayensu kawai ta riƙe da kuma sunan mahaifin Hammad din wato Yusuf. Sosai suka tausaya mata.
Wasa-wasa, soyayya mai karfi ta ratsa tsakanin Adam da Kubra. Gwaggo duk iyakar ɓoyonsu sai da ta ɗago. Adam bai yi kasa a gwuiwa ba ya samu mahaifinsa da zancen, mutum mai son yaransa da duk abin da suke so musamman Hammad, sai ya ji ba zai iya hana shi ba tunda dai ya ji ya gani yana so. Kuma a cewar mahaifin ai ɗa na kowa ne. Mahaifiyar Adam, Ruƙayya da suke kira da Nene, ta rantse ta kuma akan cewa ba ta yarda ba. A ranar farko kuma da ta saka Kubra a idanunta don takanas ta tako har gidan Gwaggo ta ci mata mutunci ta kuma ce da Gwaggo idan har ta yarda ita ce 'yar uwarta ta jini ba Kubra ba, to ta saka Kubra ta bar gidanta. Gwaggo kuwa ranta ya ɓaci, ta rantse babu abin da zai sa Kubra barin gidanta sai ko idan mutuwa ɗayansu ya yi.
Sosai aka yi rikici kafin kuma da ƙarfin addu'ar masoyan da ma Mahaifin Adam wanda yake cikakken ɗan boko kuma jajirtacce a gidansa, shi ya tsaya tsayin daka aka yi auren.
Kubra ya tare a gidan Adam din wanda ke kallon gidan iyayensa da ya gina tun ma kafin ya hadu da Kubra, duk kuma saboda shi ma ba ya son yin nesa da iyayen nasa musamman ma saboda yanayin aikinsa da ba sa so ganin yadda ake masa bi ta da ƙulli da ma kokarin salwantar da rayuwarsa ga uwa uba harin da aka taɓa kawo masa na Acid, Allah ya taimaka bai zuba a fuskarsa ba sai aka same shi a kafaɗa kaɗan shi ma saboda yana kokarin kaucewa ne. Tabon yana nan babba a kafaɗarsa ta hagu.
Tsangwama da kyara, babu irin wanda Kubra ba ta gani a wurin Nene, zaune take da Adam tana rayuwa da shi don kawai suna son junansu ba don haka ba a yanayin takurar da Nene ke mata da tuni ta gudu ta bar garin ko duniyar ce ta shiga kawai a cewarta. Shekararsu daya da aure amma ko ɓatan wata ba ta taɓa yi ba, a lokacin kuma Allah ya yi wa mahaifin Adam rasuwa, nan ne ta cigaba da shan azabar Nene kala-kala. Don Nene ko abincinta ba ta bari Adam ya ci, ta kuma buga Allah ya isa duk radda ya kai abin da Kubra ta dafa bakinsa. Ta kuma rantse sai Adam ya ƙara aure ba zai cigaba da zama da shegiyar da ba a san asalinta ba.
Ire-iren wannan zagi da cin zarafi na Nene sukan damu Kubra a zuciya, abin ya kasance ba ma ita kadai ba, zuwa lokacin yan uwan Adam din ma sun fita harkarta. Gani ake yi ta mallake Adam din ta yadda ko maganar Nene ya daina ji, ya kuma daina yi musu hidima kamar a baya komai ya ƙare a wajenta. Takan yi kuka da roƙon Adam akan ya sauwaƙe mata kawai, shi kuwa sai dai ya ba ta haƙuri ya kuma yi mata rantsuwar babu abin da zai raba su, aurensu mutu-ka-rab a ne.
Cikin ikon Allah, aurensu na da shekara ɗaya da rabi ta samu ciki, murna a wajensu ba a magana. Ta fara laulayi mai zafi ga kuma tafiya da ta kama Adam, ya tattara ya maida ta wajen Gwaggo duk da itama a lokacin fama take da ciwon sugar duk ta bi ta rame sosai.
Wannan cikin ya tayarwa da Nene hankali, har gidan Gwaggo ta bi Kubra ta zage ta tas har da su Allah ya isa wai za ta kawomata jinin shegu zuri'a. Tsatson da har gobe ba a san asalinsa ba. Kubra ta yi kuka tamkar ranta zai fita, zuwa lokacin Gwaggo ya bar saka baki a zancenta ba don komai ba sai don goranta mata da Nenen ta yi wai ai mugunta ce ta saka Gwaggon bari Kubra ta auri ɗanta, idan dagaske kaunarta take meyasa ba ta aura wa ɗaya daga cikin yaranta ba. Kuma wai Gwaggon ta nunamata 'yan ubanci, ta nuna cewa ba daki ɗaya suka fito ba. Abin dai har ya so zama rigima tsakanin Nene da yaran Gwaggon maza waɗanda ke wurin ake cin mutuncin mahaifiyarsu. Gwaggo har hawaye ta zubar, lokacin ta yi wa kanta alƙawari ba za ta ƙara tankawa Nene ba, amma kuma duk sadda Adam yake da wata buƙatar ba zai hana ta yi masa ba a dalilin magiya da kuka da ban hakurin da ya zo yana mata kan abin da Nenen ta yi gare ta. Wannan ya kara assasa tsanar Kubra a wurin yan uwan Adam, a cewarsu ta raba zumunci ita da ba kowa ba a zuri'a.
Hatta da kawo Kubra da Adam ya yi, daƙyar Gwaggo ta karɓe ta gudun abin da zai je ya zo, amma kuma ba ta tsira ba sai da Nenen ta zo ta ƙara wata tijarar ta fice, ba ta ce mata komai ba. Hakuri kawai ta dinga ba Kubra. Abuja Adam ya ce musu zai je, bai kuma dawo ba sai da ya shafe sati biyu, aiki suka je yi na hira da wani shahararren ɗan siyasa dake neman takarar shugabancin ƙasa. Tambayoyi masu zafi Adam ya dinga yi masa yayyafinsu da kowa ya shaida har a fuskar dan siyasan ya shaƙa ainun.
Koyaushe Gwaggo takan ankarar da kubra ta dage da yi wa mijinta addu'a, aikinsa yana da hatsari ainun. Hakan kuwa aka yi, sam ba ta bacci da daddare sai ta yi nafila da addu'o'i ga mijin nata. Koda ya dawo ya dauke ta suka koma gida, wani lokacin za ta ga ya zuba mata idanu ya yi shiru kamar mai tunani, har sai ta tsargu ta tambaye shi ko yana son wani abu. Murmushi yakan yi kawai. Cikinta wata hudu amma girmansa sai ka zaci ya kai watanni bakwai haka. Adam yakan ce anya ba 'yan biyu za ta haifa ba duba da yanayin girman cikin. Ita kuwa takan ji dadin wannan hasashen ko babu komai za ta so ta tara zuri'a mai yawa a yadda take a yanzu ba ta da kowa.
Haka suka yi ta rainon cikin, wani lokacin kuma sai dai ta ga Adam ya na ta rubuce-rubuce ya kuma zama shiru-shiru. Wasu lokutan kuwa kallon nan da yake mata duk sai ta ji ba ta so, a gefe guda kuma takurar Nene, ga kuma aure da ta za ta yiwa Adam din wanda ba a son ransa ba sai kawai biyayyar iyaye. Kubra ba ta tashi hankalinta ba sai ma bashi baki da nasiha da ta dinga yi.
Wataranar juma'a tana zaune da tulelan cikinta da ya shiga wata na tara da kwanaki, Adam ya shigo fuskarsa ta yi jawur ga idanunsa sun kaɗa sosai. Tana ganinsa ta ji kirjinta na bugu da ƙarfi, ta kasa magana amma ta san wata matsalar ce. Bai ce mata komai ba ya dauki hijabinta ya miƙa mata. Kubra sai ta shiga hawaye, murya na rawa take kallonsa amma ta kasa cewa uffan. Ya rungume ta yana rarrashi, a nutse kuma bayan ya haɗa da nasiha yake sanar da ita rasuwar Gwaggo. Kuka mai karfi ta saki tana maimaita salatin da ta ji yana yi. Wai ciwo ne ya motsa mata cikin dare kafin a kai ga isa asibiti ta rasu.
Koda suka tafi gidan Gwaggo, Kubra tana yin ido hudu da gawarta ba ta san sadda naƙuda ya motsa mata ba. Nan matar babban ɗan Gwaggo da wata makwafciyar Gwaggon da suka saba da Kubra suka kwashe ta aka yi asibiti da ita. Adam shima ana kai Gwaggo makwancinta na gaskiya ya bi su zuwa asibitin. Kamar jira ake ya ƙarasa kuwa, Kubra ta haifo yaranta biyu mata cikin ƙoshin lafiya.
Rufaida Umar