Free chapter · Read without an account

13

by Rufaida Umar · ALWASHI

ALWASHI

13

***

***

***

***

Muku-mukun sanyin da aka tashi da shi a ranar har ya fi wanda aka ɗan busa a kwanakin da suka wuce, wataran akan yi rana, wani bin kuwa sanyi da iska su yi ta kaɗawa. A lokacin Sameera da Laila koyaushe suna gida sana'arsu ta kitso da ƙunshi kuwa sai gaba yake yi. Laila a sannan ta mallaki wayar kanta itama sai dai ba ta taɓa kokarin gwada bibiyar shawarar da jama'a ke ba ta ba akan ɗaukar hotunan lallenta tana ɗorawa a shafukan sada zumunta ba wanda ko ɗaya a ciki ba ta buɗe ba don a cewarta ba ta ga da wa za ta tsaya sada zumuntar ba bayan mahaifiyarta da yar uwarta da koyaushe suke a tare.

  Sameera itama kofofin alheri ta ko'ina sun budemata sanadin kitso, Maman Zakiyya kwana biyu itama dayake ta je Umrah daga nan za ta tsaya a Dubai yin siyayyar kayayyakin kasuwancinta sai ya kasance su Zakiyya har gidan suke zuwa idan suna buƙatar kitso. Koda wasa Sameera ba ta taɓa nunawa a gidansu wai ta taɓa samun matsala a gidan Mamin Barhim ba, (sunan da take kiran Haj Salma ta Unguwar Barhim da shi kenan) hakan yasa hankalin Laila ya kwanta kaɗan amma da irin yadda take ji Sameera na yabawa yan gidan amma ta rasa meyasa a ƙasan rai take jin da ace gaba ɗaya Sameera za ta haƙura da zuwa gidajen mutane kitse musu kai da hakan ya fi mata dadi.

To shiyasa kwanakin nan suke jituwa sosai da Laila ganin har an ci kusan wata ɗaya babu inda Sameera ke fita koyaushe tana gida sai dai a zo.

Kwatsam kuma sai ga shi a wannan ranar ta Talata suna zaune Sameera na gyaran alayyahu, Laila na gefe tana hutawa bayan kammala yiwa mutum biyu da suka zo lalle, sai Mama da ke zaune gefe ana hira dukkansu cikin shigar sanyi, wayar Sameera ta ɗauki ƙara. Ta kai hannu saman taga ta ɗauka bayan ta ɗan goge hannun a zaninta. Ganin sunan Afrah ɗaya daga cikin yaran gidan Mamin Barhim ya sa ta ɗagawa. Bayan gaisuwar kwana biyu ne ta ce mata tana so ta shigo gobe idan da dama zata yi mata kitso tare da Maminsu. Sameera ta amsa da toh. Daga bisani suka yi sallama, idanunta ya sauka a kan Laila da ta zubamata na mujiya, kauda kai ta yi tana cigaba da aikinta lokaci guda take sanar da Mama. Itama Mama cewa ta yi Allah ya kaimu. Laila dai uffan ba ta ce ba wannan karon don ta fara jin gajiyawa ma da ɓata yawun bakinta wurin bayyana ƙiyayyarta da zuwa gidajen mutanen da Sameerar ke yi.

Washegari da misalin ƙarfe ɗaya da mintuna na rana wanda yanayi na sanyi da hazo zai sa ka yi zaton har an yi sallar la'asar ma, Sameera ta shirya tsaf ta sanya rigar sanyinta a ƙasan dogon hijabin dake jikinta,  har da safa sai ko facemask da ta rufe hanci da bakinta. Ta fito ta nufi titi ta samu abin hawa bayan Mama ta jaddada mata kar ta jima da zarar ta kammala kamar koyaushe ta taho, na biyu kuma ta bar wayarta a kusa saboda ba ta son ta kira ta ji ba a ɗauka ba. Sameera murmushi ta yi a sannan, ta san Mama kusan ta fi Laila damuwa a kan fitarta don ita da zarar ta ga an ja lokaci mai tsawo ba ta dawo ba ko ba ta ɗaga waya ba to fa yanzun hankalinta zia tashi ba ta kuma samun nutsuwa har sai ka biyo kiranta koda flashing ne ko kuma ta ga ka shigo gidan lafiya sai ta sauke ajiyar zuciya ta samun nutsuwa.

   Dab da cikar ƙarfe biyu ta ƙarasa daidai bakin katon ƙyauren gidan Alh Sada, bayan ta sallami ɗan acaɓan da ya sauke ta ne ta shiga ƙyauren suka gaisa da Maigadin wanda shima ɗan leƙowa ya yi daga ƙofar ɗakinsa saboda sanyi ya hana shi zama a waje.

Haka ta niƙi tafiya tana kula da yanayin shiru na harabar gidan kamar ba mutane, cikin kalle-kallenta ne ta hango Zaks dake tsaye jikin window yana kallonta ta sama, kauda kai ta yi tana jan guntun tsaki lokaci guda kuma tana neman tsari daga sharrinsa.

Madadin sanyin da ta ji a waje, a falon Mamin wani irin ɗumi ne mai daɗi ga kuma ƙamshin turaren wuta wanda ɗan jimawar da ta yi a zaune sai da ta kai ta cire safar ƙafarta da ma hijab saboda zufa da ta fara. Ashe wai heater ce da su mai ɗumama ɗaki a lokacin sanyi. Afrah din ta soma yi wa kitson, dayake ba wasu ƙananu suka yi, ibira ne nan da nan aka kammala. Mami ce dai aka yi mata ƙananun don ba ta fiye yin wani manyan kitso ba, tana yi kuma tana tashi amsa waya hakan ya janyo ba su kammala ba sai wuraren biyar na yammaci don sadda lokacin sallah ya yi sai da suka gabatar kuma aka zubawa Sameera abinci. Su a lokacin ne ma suke cin na rana, karinsu kuwa wuraren sha biyu suke yi matukar dai ba taron jama'a ne a gidan ba. Kaɗan ta tsakura ma don ita gaba ɗaya hankalinta ta ji ya yi gida, wani irin bugu take ji ƙirjinta na yi, ta kuma kira Mama da wayon tambayar ko wata da suka yi maganar kitso ta zo, Mama tace aa. Jin muryar Mamar lafiya lau sai ma tuni da take mata akan ta hanzarta tahowa da zarar sun kammala yasa ta samun nutsuwa. Da ace Laila ce ba lafiya ko ita Maman to a wayar da ta yi za ta fahimci wani abu, amma kuma babu ɗaya, sia ta shiga fargabar dalilin bugun da ƙirjinta ke yi har haka.

A daddafe tana kammalawa Mami ta karɓi haƙƙinta tare da yi musu sallama ta fito.

  Kamar ɗazun, yanzu ma ba ta haɗu da kowa ba sai wani irin shiru da gidan ya ɗauka sai ko kukan tsuntsaye, iska duk ya dame ta, ta tuno ta bar facemask dinta a gidan, kamar ta koma kawai ta fasa musamman da ta auna tazarar dake tsakanin inda take da kuma inda za ta koma ɗin, tafiya ce miƙaƙƙa, tana tafe har ta ƙaraso daidai garden ɗinnan, ba ta kai ga giftawa ba kawai ta ji an riƙo ta ta baya za ta yi ihu ta ji an yi saurin toshe bakin da hancin nata da wani hankicif, ba ta san me ta shaƙa ba amma kuma gaba ɗaya ta nemi kanta ta rasa jikinta ya saki ta yi luf jikin mai shi a sume.

  ***

  Mama da Laila suka zuba idanu suna kallon ƙofa a kai-a kai, burinsu su ga shigowar Sameera. Kowannensu abin na cinsa amma ba su yi wa juna maganar ba sai ja da hirar ƙarfin hali. Can ganin har an idar da sallar Magriba gari ya ɗauki shiru ana jira a yi isha'i a shige gida sakamakon sanyi ya sa Mama ƙara danna kiran wayar Sameera karo na ba adadi. Amma abu ɗaya ne, har ya kammala ƙara ba'a ɗaga ba.

"Mama kodai mu bi sahunta ne? Shirun na fa ya tsorata ni. Nan ma irin namu unguwannin ya muka ƙare ballantana kuma irin nasu na manya a lokacin nan da abin hawa ma ba lallai mutum ya samu kai tsaye ba? Ni dai jikina yana ba ni Sameera na cikin matsal..."

"Yi shiru kar ma ki ƙarasa Laila, ki yi tunanin alheri sai ya tabbata. Tashi ki saka hijabi muje gidan Haj Nabeela ko ɗan rakiya ne ta haɗa mu da shi muje mu dubo ta."

Faɗin hakan ya sanya suka miƙe a tare, Laila ta ɗauko hijabinta, Mama dama tana sanye da nata a saman darduma tun sallar Magrib. Sun fito Laila na ƙoƙarin ƙulle gidan ne wayar Mama ta yi ƙara, da gudu- gudu ta ciro ta ɗaga ganin sunan Sameera a kai.

"Sameera! Kina ina? Kin..."

"Barka da dare Hajiya, me wayar na tsince ta ne a yashe a gefen kwalta ba ta cikin hayyacinta. Da na bincika jakarta na ga wayar shi ne na kira lambarki don sunan ya nuna ke ce mahaifiyarta ko?"

Mama ta yi salati jiki na rawa ga Laila wacce ba ta ji me ake cewa ba amma kuma itama na ta hankalin ya yi mugun tashi tana jiran ta ji me ake cewa Mama, tuni hawaye sun wanke mata fuska, kirjinta sai lugude yake yi.

"Eh ni ce mahaifiyarta, ka taimake ni bawan Allah ka ban kwatance  wurin zan karaso yanzu."

"A'a Hajiya, bari dai na kawomaku ita zai fi. Ku yimin kwatancen inda kuke."

Mama dai hankalinta bai kwanta ba, ta so ya bar ta ta je amma kuma tunanin da ta yi na ba lallai ne samun abin hawa a kan lokaci ba ta amince musamman da ta ji yana ambaton a motarsa zasu taho yasa ta fahimci yana da abin hawa. Nan ta yi masa kwatance, amma fa koda ta kammala wayar tana hawaye ta sanar da Laila komai, ba su iya komawa cikin gidan ba, nan suka yi dakon jira gaba ɗaya suka wani jeme kamar waɗanda suka yi cutar kwanaki tsabar tashin hankali da masifar da suke jin kansu ciki.   Can kuwa sai ga wata mota ta faka a gabansu. Koda ta tsaya aka buɗe murfin motar ta gefensu, Sameera ce ta fito, kallo ɗaya suka yi mata ƙirjinsu ya buga da ƙarfi, tana tsaye ne amma kuma jiri ke neman kwasarta sai rangaji take yi, hijabinta suka kalla da yake a cukurkuɗe, da sauri Mama ta yi ƙarfin halin ƙarasawa gare ta ta riƙo.

"Sameera? Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Me ya sameki?"

Sameera da ke dafe da kanta cikin yanayin zubar hawaye ta riƙe hijabin Mama gam!

"Ma..ma."

Iya abin da ta iya cewa kenan, tabbas abubuwa da dama a yanayin nan suna kokarin dawowa kanta amma kuma tana jin ta sama-sama ne.

"Assalamu alaikum, barka da dare Hajiya."

Laila ta ƙarasa wurin mutumin ba tare da ko amsa sallamar ba kusan a haukace take magana.

"Me ya faru da yar uwata? A ina ka gan ta?!"

Mutumin dai kasa cewa komai ya yi don ta ƙi bari ya yi magana sai ruwan tambayoyin da take zubo masa. Mama wacce ta gama lura da abin da ya afku ga Sameera ta yi saurin dakawa Laila tsawa a kan ta buɗe gidan saboda ta kaɗu tana kuma jin tsoron hankulan mutane su yo kansu. Laila cikin hawaye da rawar jiki wanda yasa daƙyar ta buɗe gidan suka shiga don ta mance ma ba wani ƙullewa ta yi ba sai da aka ba ta umarnin buɗewar ne ta rufe duk a dalilin rashin nutsuwa da tashin hankali.  Iznin shigowa Mama ta yi wa mutumin, bayan sun shiga Sameera ta kwanta ta ƙudundune a jikin Mama, Mama ta dube ta hawaye mai ɗumi ya kwaranyo mata. Ta kuma nutsu ta maida duba ga mutumin tana jiran bayanin da zai fito daga bakinsa wanda shi dai tun ganin da ya yi wa Laila ya gane yan biyu ne sai ya ji sun ba shi tausayi a gefe kuma bai ji dadin tuhumar da Laila ke masa ba da irin kallon da take watsa masa kai kace ba abin arziƙi ya yi ba na taimakawa yar uwarta.

"Na fito daga ma'aikatarmu na yi hanyar da za ta kai ni gidana dake can bayan unguwar Barhim, na ga kamar mace a durƙushe a gefen titi, har na yi gaba kuma sai na kasa nutsuwa na dawo bakina ɗauke da sunayen Allah na dakata a gabanta na fito. Sallama na yi mata amma ba ta amsa ba sai kukan da take yi tana kiran don Allah a taimake ta a kai ta gidansu. Yanayin maganar nata ya fahimtar da ni ba a cikin hayyacinta take ba, to da farko raina ya ɓaci har zan bar ta a wurin saboda nayi tunanin ko irin matan da suka gagari iyayensu ne, kawai yawonta ta yi ta sha abinda ya fi ƙarfin kanta, sai dai kuma da na ga yadda take ta salati tana ambaton Allah tana kuma kiran an cuce ta yasa jikina ya yi sanyi, ta yi kwance a wurin na kuma kula ko mene ne ta sha bai gama sakinta ba, dole na ɗauki jakarta na laluba sai na ci sa'ar samun wayarta shi ne na kira. Farko na yi tunanin damƙa ta hannun hukuma amma kuma sai na yi nazarin kada hakan ya janyo ɓatancin suna ga iyayenta tun da ban san ko su waye ba, dalili kenan na zaɓi na kira ɗin na sadata da ahalinta da kaina. Wannan shi ne iyakacin abin da na sani Hajiya, amma yanzu ku bari ta farfaɗo ta dawo hayyacinta ta wartsake, in sha Allahu nasan ko mene ne za ta sanar da ku."

Mama da ke sharar hawaye ta dubi Sameera wacce bacci ya yi awon gaba da ita sosai, runtse idanu ta ɗan yi ƙirjinta na wani raɗaɗi da zafi, wannan wata sabuwar jarabawar ce kuma ta iso gare su? Laila itama kanta ta cusa a cinyoyinta tana kuka har da shessheƙa.

"Mun gode bawan Allah, Allah ya saka da alheri. Wallahi gidan kitso kawai ta je a can unguwar Barhim ɗin, to shi ne muka ji shiru  ya yi yawa hankulanmu suka tashi, har mun fita da niyyar zuwa dubiyar sai ga kiranka a wayarta. In sha Allahu ko mene ne zamu bincika mu ji. Allah ya saka maka da aljanna. Mun gode."

Mama ta yi furucin daƙyar da rawar baki, ya amsa shima cike da tsantsar tausayinsu, yasan babu ce kawai za ta saka budurwa kyakkyawa irinta yawon gidajen jama'a domin neman halak. Shi ma fatan alheri ya yi musu sannan ya kara ba su hakuri ya fice.

"Laila yau ga irin tsautsayin da kike gudu ya afku, kaicon wannan rana, inama ace tun farko na yi aiki da shawararki na yankewa Sameera fita. Da yau ban ga wannan ranar baƙin cikin da za'a wayi gari wai an ketawa Sameera haddi ba."

Kalaman Mama na ƙarshe ya sa Laila ta ɗago kanta a gigice yayinda ta fiddo idanunta waɗanda suka yi jajir tare da fuskarta baki ɗaya saboda kuka, tuni ma ta nemi kukan ta rasa. Ɗif wurin ya yi na wucin gadi, Laila sai dai ta kalli Maman ta kuma maida duba ga Sameera. Can ta samu ƙarfin halin yin magana,

"Mama me kike nufi da an ketawa Sameera haddi? Fyaɗe?"

Mama ta runtse idanu hawaye masu zafi suka ƙara zubo mata, zuwa lokacin ita kaɗai tasan me take ji a ƙirjinta don numfashinta kamar zai ɗauke take ji kawai ƙoƙari take wurin fisgo shi da ƙarfi. Shirun Mama ya ba Laila tabbacin  eh hakan ne. Da sauri ta kunna hasken wayarta ta ƙata duban Sameera dakyau, gaba ɗaya jini a bushe ya yi layi a jikin ƙafarta kamar wacce ta fara al'ada. Ba don bai fi kwanaki da kammala hailar Sameerar ba to za ta rantse shi ne ya zo mata a yanayin ruɗanin da take ciki. Ba ta san sadda ta saki wata ƙara ba ta yi baya ta kife a sume. Mama ta yi saurin cire Sameera dake jikinta ta ɗauko ruwa ta yayyafa ga Laila nan da nan ta farfaɗo amma kuma ta fashe da kuka mai tsanani, kira take inama mutuwa ta risƙe ta irin yanda ta risƙi mahaifinta kafin zuwan wannan rana, daƙyar Mama ta saka ta yin istigfari da kuma bin ta da nasiha. Nan suka daure suka miƙe don gabatar da sallar isha'i, Mama ta rufe musu gidan bayan ta yi addu'a, Sameera suka dawo suka ƙara zubawa idanu kawai jira suke yi ta farfaɗo don a cikinsu ma babu wanda ya bi ta kan abincin dare. Tausayi mai tsanani ne cike maƙil a zuciyoyinsu duk na Sameerar. Tana da kirki wanda wasu lokutan Laila kan ja tsaki tace kirkinta ya yi yawa ta rage, har Mama ta yi ta dariya ta ce ban da shirme irin na Laila ta yaya mutum zai rage bain alheri wanda ba wai yana yi ne don riya ba? Sameera me sanyi da hakuri, mai yawan fara'a da saurin sabo da mutane, mai kuma kamewa a inda ya dace, yau ita ce wannan mummunan ƙaddarar ta afkawa?

Misalin ƙarfe sha biyu saura na daren ne, Sameera ta farka tana mai ambaton La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin iyakar ƙarfinta sai dai gaba ɗaya muryar ta dusashe ba ta fita amma tabbas a kokarin ihu take yi. Mama da Laila suka zabura suka riƙe ta suna ambaton sunanta. Ganin Mama da Laila kawai sis Sameera ta damƙo hannun kowannensu tana ta kokarin magana amma wani danƙararren kuka da yake taso mata kuma murya a shaƙe ta kasa fitarwa ya hana su ji me ma take kokarin faɗi, kawai sai Mama ta rungumeta, duk dakiyarta kar ta rushe da kuka don kada ta karya zuƙatan yaran nata hakan bai yiwu ba sai da ta fashe da kuka mai ƙarfi da ya taso da na Sameerar, ya saka Laila itama ƙara nata kukan tana maimaita Innalillahi zuwa ƙarshensa a fili.

©Rufaida Umar

Women of Words Writers Ass.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol