Free chapter · Read without an account
Chapter 1: Page 1
*MENENE ABIN YI?*
By
Sumayya Usman
(*Cwt-sumiey* )
Repost
*****
*Page 1*
✍Yadda na fara littafin nan ina rokon Allah Subhanahu wata'ala da ya ba ni ikon kammala shi lafiya, alfarmar Annabi Muhammad(SAW). Allah Ya ba ni ikon faɗakarwa da kuma ilmantarwa harma da nishaɗantarwa, Ubangiji Allah ya kare ni daga rubutu abin da ba zai amfani al'ummar Annabi ba (*Ameenn*).✍️
Kamar koda yaushe zaune nake a gidana wanda nai mashi lak'abi da duniyata,na rabka uban tagumi hannu bibbiyu,wanda hakan ya k'ara taimaka min wajen lulawa dogon tunanin abun da ya shafi rayuwata,da kuma tarin k'alubalen dake cikinta ban san kowa ba even my self in ka tambaye ni zance ma ban san koni wace ce ba,wanda ya wuce sunana ba, gidan da nake zaune babban gida ne wanda ya amsa sunansa,ya kuma haɗa komi da komi na buk'atar rayuwa,wanda ko da a alk'arya aka gina sa,to ba makawa zai amsa sunansa gida mai kyau,sai dai wani abu da zai baku matuk'ar mamaki shine , wannan gidan ya kasance a cikin tsakiyar dokar daji ne ,ba gida gaba kuma ba gida baya,ban san komi game da rayuwata ba hatta parents d'ina ban san suba only one thing I know akwai mutum uku dana sani,kuma suke zuwa wuri na ,Uncle Y wanda sai bayan two to three weeks yake zuwa inda nake, sai kuma Nanny mace mai kirki ita ɗin a matsayin "yar aiki take gare ni amma ni na ɗauke ta a matsayin Aunty a wajena kasancewar yadda take tafiyar dani tamkar wacce muke uwa ɗaya, ko kadan bata bari na inyi kewar wani abu wanda na rasa sai ko in bama tare da ita, sai kuma mutum na k'arshem wanda ban san saba ban ta'ba gani ko da kwayar idansa ba ma bare in sa ran ganin fuskarsa,ya kan zo min cikin shiga mafi muni ko tsoratarwa,kuma ba tare da ya bar alamar da zan iya gane ko shi waye ba, yana zuwa inda nake a duk time ɗin da suke buk'atar in yi masu aiki,aikin da ni kaina ban san suwaye asalin waɗanda suke sakani yin saba ko suke cin gajiyar abun da nake aikatawa ba.
Ban ta'ba attending ɗin wata school ba a rayuwata in ba online ba, kusan komi na rayuwata da nakeyi nakoye shi ne through my phone and system,Prof Mathura itace macen da ta jajurce a b'angaren karatuna itama muna karatun ne ta hanyar distance learning, macece nai kaifin basira a ta 'bangaren sanin na'ura mai kwakwalwa a kimiyance, baya ga mutanen dana lissafo muku abaya ban ta'ba ɗora idanuna akan wata halitta ba,kar kuyi tunanin gidan da nake zagaye ya ke da bodyguard, security ko wata na'urar bindiddigi da ka iya hanani shiga da fita a cikin gidan,kawai an ɗan farar da zuciyata akan hakan ta hanyar tsoratarwa,cutarwa har ma da azabtarwa.
Duk wani abu na more rayuwa da jin daɗin ta Uncle Y ya tanadar man shi kama daga suturar da zan sa, abinci ko abun sha bai ta'ba bari na nemi wani abu na rasa a wajen saba.
Daka kalli fuskata a kallon farko zaka fahimci koni wacece don ko ɗaya ban iya 'boye wani abu da ya shafe ni koya danganci rayuwata ba.
Babban abunda nake so a rayuwata shine farin ciki sai dai me?, amman iyaka da duk wani abu ko hanyar da take sakani kasancewa a cikin farin cikin.
Ko a wanne yanayi nake walau na farin ciki ko a kasin haka to baka ta'ba raba fuskata da walwala da kuma farin ciki any time any how fuskata ɗauke take da murmushi.
Anan zaune da nake ba k'ananan laifuffuka nake aikatawa ba wanda da zakuji tabbas nasan ɗaya daga cikin ku ko mafiya rinjayen cikin ku zasu hukunta ni don a tunani na mafi saukin zuciya a cikin ku ne zai iya k'onani da raina ko ya binne ni da raina.
Naso ace Ina da family,friends ko relative's dazan iya d'ora kaina akan kafaɗar su inyi kuka ko na faɗa masu abunda yake damuna.
Haka zalika Ina da tarin tambayoyin danake son inyi masu akan karan kaina,Tambayar da a kullum nake yawan yima kaina kuma tafi tsayaman a rai .Tambayar kuwa itace. (*WACECE NI,MI NAKE AIKATAWA,MENENE DALILIN ZAMANA A KE'BANTACCEN GIDANNAN?*)
Har yau har gobe ban ta'ba manta ranar dana farasa k'afata na taka gidan nan ba sai dai menene yafaru wanda yazama dalili ko silar dayasa na shigo gidan da kuma menene yafara faruwa kafin in shigo gidan duk ban sani ba.
"Mahanoor, mahanoor,wai me yake faruwa da ke ne?".
Sautin kiran suna na ne yasa nai firgigit tare da dawowa cikin hayyacina.
"Me yake faruwa ne,tun ɗazu ina can ina nemanki,ashe kinanan a backyard zaune?".
"Eh...eh wlh Ina ɗan hutawa ne Nanny",na samu da k'yar na bata amsa domin kaucewa daga saitin fuskarta don gudun tambayoyin da zasu iya biyo baya.
"Ban saba ganin ki a cikin irin wannan yanayin ba Mahnoor, me yake faruwa,ko wani abun na damun ki ne?".
"A'a Nanny ba abun da yake damuna,kawai yau ɗin ne kamar an sa abun tariya an tariyo man dukkanin rayuwata da ta shuɗe da kuma wacce nake fuskanta a yanzu".
"In na fahimta kai tsaye kina so kice man har yanzu baki ɗauki shawarar da na baki ba ko?".
"Ba haka bane ,ke kan ki in ki ka dubeni duba na tsanaki ,zaki gane me na ke son faɗa maki, ko kin manta ne,da irin rayuwar da na ke kuma nake fuskanta?,ina cikin irin wannan rayuwar sannan a ce bazan shiga damuwa ko inyi dogon tunani ba,wai a haka Uncle Y yake tunanin duk wani jin daɗin da yake bani shi zai maye mani gurbin sauran abubuwan da na rasa?".
"Bana da amsar wannan tambayar taki".
Sai da ta turo bakinta gaba sannan tace," Ai dama nasan haka zaki ce ,dan kusan duk tambayoyin da zan maki ba kya bani amsa na rasa mene ne dalilin haka ?".
"Ba wani dalili ko ɗaya,don haka kar kibar maganar ta samu wurin zama a cikin zuciyar ki".
"Okay ba damuwa,kuma in Sha Allah zanyi k'ok'arin aikata hakan".
"Ni ko ke ba zamu ta'ba iya goge *ZANEN K'ADDARARMU* ba,kamar yanda *K'ADDARA* ta kawo ki gidannan haka nima itace ta kawo ni ,don haka ina mai faɗa maki addu'ah ce kawai zata iya tseratar da mu".
"Sai dai maganar gaskiya Ina tsoran kar ace rashin sanin *MENE NE ABIN YI ?* Ya zama kuskure mafi girman munin da zamu aikata a rayuwata".
"In sha ALLAHU hakan ma bazata ta'ba faruwa ba,kuma da sannu duk wani abu da yake 'boye a k'asa wata rana sai ya bayyana".
"Ameenn suma ameenn Nanny , Allah ya sa hakan ya faru nan kwana kusa".
"That my little sis , yanzu ta so muje cikin gida na haɗa maki wani abu mai daɗin gaske",da wannan ta rinjaye ta suka shige cikin suna masu fara'a da dariya.
<<<<<<<<<<<<<<<<<<<
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
A matuk'ar fusace da kuma hanzari ta ke driving ɗin motar kallo ɗaya zaka yi mata kagane cewa ranta a matuk'ar 'bace yake.
Gefenta sit ɗin mai zaman banza Barrister Junaid ne zaune cikin sanyi da tausasa lafazi ya ke cewa da ita,"Barr. shuraimah menene kike aikatawa haka ya kamata ki natsu kiyiwa justice Ali Rabe uzuri"..........na katse shi da sauri da cewa, "uzirin me zan yi mashi kai kanka kasan ya zuwa yanzu yakamata ace yakawo karshe wannan shari'ar amma kullum sai kara janta yake,kuma duk wani evidences da'aka buk'ata masu karfi babu abun da bamu gabatar da shi a gaban court ba to me yake jira dan ALLAH?".
"Ba wannan ne abun da zaki duba ba ,nagartar shi Justice Ali Rabe za ki duba kece fa da kan ki,ki ka shiga kika fita kuma kika tsaya tsayin daka har kika samu damar da zai gabatar da wannan shari'ar, saboda kin yarda dashi da adalcin shi ga kowa ".
"Eh duk nasan da wannan amma fa ka duba how long muke ta abu ɗaya har iyayen yarinyar nan sun fara ganin kamar baza ai masu adalci ba" .
"Har yau har gobe nasara tana 'bangarenmu kuma ki duba kiga yanda HUMAN RIGHT (hukumar kare hakin d'an Adam) tashiga zancennan ga "yan jarida da social media to ko iya haka ya isa yasa ki kwantar da hankalinki, wanda ina da tabbacin ko basu shiga cikin case ɗin nan ba ke karan kanki kad'ai zaki iya tsayawa a kan case ɗinnan kuma ki yi nasara don haka ki kwantar da hankalinki zamuyi nasara in sha ALLAH".
"OK zanyi k'ok'arin haka kaji Barr Junaid yauwa kaga ma na tuna Ina record tape ɗin da mukayi recording akan casa ɗin "yar gidan Mal.Musa mai gadi yake?".
"Ai nabaki shi tun ranar damuka dawo".
"Subahanallah aiko namanta Ina na ajeshi bari in duba cikin dashboard konan na saka shi".
Kasan cewar hankalinta ya koma wajen duba record tape ɗin yasa hannunta yafara rawa wajen driving ɗin,cikin sauri Barr Junaid yace mata, "kinga bari in duba maki ki mai da hankalinki akan driving kar kije ki watsar damu akan titi".
"A'a bari ma kamar gashi nan Ina jiyosa" tana kara tura hannunta cikin dashboard ɗin suna cikin wannan gardamar saijin wata k'ara mai k'arfi su kai alamar sun bige wani abun,tuni Barr shuraimah ta rikice Wanda hakan yasa motar kwacewa daga hannunta kaitsaye motar ta nufi wata bishiya dake gefan titi da k'yar Barr Junaid yai k'ok'arin tsaida motar kafin ta k'arasa wajen da bishiyar take.
Cikin matuk'ar sauri su duka biyun suks fito domin su k'arasa wajen wanda suka bige dake kwance a kan titi tamkar matacce......................✍✍✍✍✍✍
*Shin ya wannan rikicin yake ne? Kun hasko wani abu cikin labarin ko sai mun ƙara nutso a cikin tafiyar?*.