Free chapter · Read without an account

Matar Khalees

by Nusaiba Ibrahim Rimi · Matar Khalees

*****MATAR KHALEES*****

✍️ Nusy bee

Page 11

Kafin Deeja ta kuma cewa wani abu ta zaro waya ta fara kiran Khalees,ganin kiran doctor su'ad ya Sanya shi azamar ɗaga kiran,yana ɗagawa tace"kazo ɗakin da aka kwantar da Madam ɗin ka"bata jira amsar shi ba  ta kashe kiran

Minti biyu tsakani sai gashi ya shigo cikin sauri,ganin ta a zaune yayi saurin nufar ta,amma ta dakatar dashi cikin ƙaraji

"Kar ka ƙaraso in da nake Khalees,kar ka soma, Wallahi na tsane ka macuci, mayaudari, azzalumi,wanda bei san darajar mace ba,wallahi abinda kukayi min sai Allah ya saka min,don bazan taɓa yafe muku ba, munafukai annamimai,kuma na gama auren ka,dole ka sake ni,maƙaryaci kawai"idanun ta sun kaɗa sunyi jawur,amma ko ɗigon hawaye babu,don dama can ita ba mai saurin kuka bace

Ba Khalees ba,itama Dr su'ad abin ya ɗaure mata kai,suka shiga bin ta da kallo, Dr su'ad ta matsa kusa da ita tana faɗin"haba malam!mijin ki ne fa,a ƙalla ya samu wannan alfarmar ko?"ita kanta Dr jikin ta rawa yakeyi, ballantana Khalees da ya shiga mummunan tashin hankali

Deeja ta ƙarasa zare hannun ta gami da faɗin"a da yake amsa sunan miji a waje na,amma a yanzu"ta girgiza kai gami da miƙewa tsaye

Duk yanda suka so Deeja ta saurare su hakan yaci tura,a ranar Khalees yaga ainihin kalar matar shi,dole suna ji suna gani ta fice daga asibitin

Bin ta sukayi da kallo,tana fita Khalees ya lallaɓa ya bi bayan ta,napep ta tsare,ta shiga, shima ya shiga motar shi ya bi su

Kai tsaye gidan Aunty Bintu ta nufa,mai adaidaita sahun yayi parking, wajen mai gadin ta ranci kuɗi ta sallami mai adaidaitan,sannan ta shiga cikin gidan

Khalees ne ya fito daga  motar shi ya baiwa mai gadin maƙudan kuɗaɗe,mai gadin ya fara godiya,yayi saurin dakatar dashi yace"kuɗin da Deeja ta karɓa a Wajen ka ne,ragowar kuma ka riƙe"yana gama faɗar hakan ya koma cikin motar shi ya tayar ya tafi 

Deeja kuwa a hargitse ta shiga cikin gidan,intisar tana zaune a falo tana buga game a wata Deeja ta shigo

Cikin tsoro da mamaki intisar ta tare ta tana faɗin"sannu da zuwa,lafiya Aunty Deeja?"don ta san Deeja da nutsuwa

Deeja ta kalle ta da rinannun idanun ta tace"ina Aunty Bintu?"

"Ta tafi dubiya,ɗan wata ƙawar ta aka kwantar a asibiti"

Deeja ta nemi waje ta zauna tana sauke ajiyar zuciya,ita dai intisar kallon ta kawai takeyi a ɗimauce,zuwa can Deeja ta kalli intisar tace

"Kina da ɗari biyar?"

"Eh,amma dubu ɗaya ce"

"Babu laifi,kai wa baba mai gadi ki ce ya ɗauki kuɗin shi"babu musu intisar ta miƙe ta nufi harabar gidan,jim kaɗan ta dawo ta shaidawa Deeja cewa baba mai gadi yace wani ya biya kuɗin

Sai da gaban Deeja ya faɗi,don bata raba ɗayan biyu Khalees ne, saboda tayi zargin ya biyo ta,amma sai bata nuna ba,sai ma kwanciya da tayi tana tunanin mafita

Intisar bata sakeyi mata Magana ba,ta koma kan computer ta cigaba da danne-dannen ta

A haka suka kasance har sanda aunty Bintu ta dawo,da sallama ta shigo falon

Dukan su suka amsa mata,tayi mamakin ganin Deeja,amma sai ta ɓoye,sukayi mata sannu da zuwa,ta amsa da sakin fuska,ta dubi Deeja da sigar tsokana tace

"A'a!mai jegon gobe,yau wacce rana mai girma Khalees ya bamu aron ki?"

Dukan su sukayi ƴar dariya, amma Aunty Bintu ta gane dariyar dole Deeja takeyi, saboda alamun damuwa sun bayyana akan fuskar ta

Amma a lokacin Aunty Bintu bata nuna mata komai ba,ko ba komai bai kamata ta sanya ta tona cikin ta a gaban intisar ba

Wajen ƙarfe tara na dare Aunty Bintu suna tare da Deeja a ɗakin Auntyn,in da suka bar intisar da salim da mei bi wa salim sumayya suna kallo a parlour,su Kuma suka zame suka nufi cikin ɗaki

Cikin kulawa Aunty Bintu ta kalli Deeja tace"Deeja,ko baki gaya min ba akwai alamun damuwa a tare da ke,damuwar da ce ta dawo ko wata sabuwa ce?"

Duk abinda ke faruwa zuciyar Deeja a dake take,sai yanzu ta fashe da kuka mei cin rai,sai da tayi mai isar ta,aunty Bintu batayi ƙoƙarin dakatar daita ba,ta kalli aunty Bintu tace

"Aunty Ina cikin wani hali,aunty ina cikin tsaka mai wuyar fita,Aunty Ni dai tawa ta ƙare,Aunty Ni kam......."

"Wait!wait!!yaya kikeyi min wasu zantuka kamar wata jahila?me kike nufi da hakan?ki fito kiyi min bayani  sai nafi fahimtar ki,ko sakin ki Khalees ɗin yayi?"

Cikin kuka tace"ƙanin saki yayi min aunty,Wai.....Wai kishiya zeiyi min"

Cikin takaici Aunty Bintu ta ja dogon tsaki tace "to sai me?kishiya kan ki aka fara?ko akan ki za'a ƙare?ko a kanki zata zauna?"duk da cewar maganar ta doki ran ta

"Aunty ƙawar matar Imran fa zai aura,,tace wai sai ta raba Ni dashi fa"

"Ƙawar matar Imran kamar yaya?"Aunty Bintu ta tambaya a ɗan firgice

"Wallahi ƙawar matar Imran zai aura,saura kwana uku ɗaurin auren"

Aunty Bintu ta danne damuwar tava matsayin ta na babba tace"to sai me?ya auro ko waye ma?me zai tsorata ki?ke fa jinin ISHAQ ce,kuma kin san mu Bama sanya da addini,don haka kar kiyi wasa da addu'a,idan da nufi akayi auren kina zaune gayyar zata watse,idan ba da nufi bane ma zaki gani,na sanki da dauriya,to ki ƙara daurewa,kiji ki nuna baki ji ba,ki gani ki kauda kai,kar ki kuskura ki nuna musu ɓacin ranki,don zasuyi miki dariya, Allah shine gatan mu baki ɗaya,duk abinda ya samu bawa dama can tun kafin halittar shi Allah ya ƙaddara haka,don haka ki maida dukkan lamuran ki ga Allah"

Kalaman Aunty Bintu sun sanyaya mata jiki,tayi shiru tana nazari, cikin kwantar da murya Aunty Bintu ta ƙara da cewa

"Ki daina saka damuwa irin wannan a ranki, tabbas nasan akwai ciwo amma idan baki ɗauke shi da zafi ba zai zo miki a sauƙaƙe,kinga dai baki da wadatacciyar lafiya,kuma bake kaɗai bace,idan kika yi ganganci da Rayuwar ki har kika mutu mu kikayiwa asara,mijin ki wata zai auro,burin kishiyar taki kenan,to ina ranar wannan abu?"

Likers sa commentors wannan naku ne👍👍👍🥰

#Nusy_bee

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.