Free chapter · Read without an account

Chapter 21

by Rufaida Umar · ALWASHI

ALWASHI

21

©Rufaida Umar

"You didn't greet your brother." (Ba ki gaida Yayan naki ba)

Nihla ta ji maganar mahaifin nata tamkar daga can wata duniya ta daban sakamakon shagaltuwar da ta yi wurin kallon Areef, shi ɗin ma sai a lokacin ya kai nasa idanun kanta, ji ta yi gaba ɗaya tsikar jikinta ta tashi tsabar ɗaukar hankalinta da kallon ya yi. Shi kuwa kauda kai ya yi, kafin ta kai ga yunƙurin gaida shi Hajja ta yi sallama ta shigo. Ita ma wuri ta nema gefen mijin nasu ta zauna. Fuska a sake suka gaisa da Daddy Affan da Momi Inayah. Nihla wannan karon don kanta ta gaida Hajja Zayha, ita ma ta amsa kamar ta hadiye ta don yarinyar ta burge ta kwarai saboda ko daga yanayin shigarta ma ka san a waye take ga uwa uba irin dukiyar da mahaifinta ke da ita.

Nan dai aka shiga hirarraki kafin su miƙe sakamakon kiraye kirayen sallah da aka soma yi. Areef da su Najeeb da Khalid gaba ɗaya suka jera da iyayen nasu maza aka fita don gabatar da sallar Azahar, Hajja Zayha kuwa ta ja Momi Inayah da Nihla sashenta don su yi tasu sallar. Mami kuwa a nan ɓangaren Abban ta yi nata sallar kasancewar girkinta ne. Tana zaune a falon Abba na biyu Afrah ta shigo, bayan ta shafa addu'a ta dube ta.

"Sun dawo daga masallacin ne?"

"A'a ba su ƙaraso ba."

"Lafiya ke kuma kike ta wani turɓune fuska?" Ta yi tambayar tana duban ɗiyarta.

"Waccan Nihla din ce ta ban haushi, wai Mami ba ki ga yadda gaba ɗaya ta ƙurawa Yaya Areef idanu ba?"

Ɗan murmushi Mami ta yi, ashe ba ita kaɗai ta ankara ba, abin kuma bai mata daɗi ba tabbas don ita kam ta tsani mace marar kamun kai. Ga shi tarbiyyar yarinyar ma bai wani yi mata na a zo a gani ba, fatanta Allah yasa kar wata maganar ta ɓullo don ba ta jin za ta lamunta. Ta dai yi mamakin hangen nesa irin na yarinyar.

"To ke mene naki da kallon da ta ke mishi? Ai ba mayya ba ce ballantana ki ce cinye shi za ta yi ko?"

Afrah dai ta ƙara turo bakinta, hakan ya ƙara fiddo da tsantsar kamannin da ta yi da yayan nata don ko su Mardiyya da Maryam ba sa kama da shi, su din sun fi kwaso kamannin mahaifinsu ne. Ita da Areef din kuwa Mami suka fi ɗebowa har da farin fatar. 

Kafin ta lalubo amsar ba Mami na abin da take tsoron faruwarsa sai suka ji tashin muryoyin Abba da Daddy Affan din a falon Abban. Mami ta miƙe tana faɗin,

"Mu je kafin ya fara kira."

Afrah ta mike ta yi gaba, Mami ta mara mata baya bayan ta gyara zaman rufin mayafin abayar dake jikinta.

Kai tsaye wurin cin abinci suka nufa baki ɗaya. Nan Mami da su Afrah suka shiga zubawa a farantai. Daddy Affan da iyalansa suka zaɓi abin da suke buƙata, Areef dai rabin hankalinsa na ga kiran da ya ke amsawa yana magana cikin turancinsa mai daɗi. Zakari wanda bai jima da shigowa gidan ba sai da ya ji kamar ya kama wuyansa ya shaƙe, yana ji shi ya fi dacewa a matsayin Areef din, shi ya fi kyautuwa ace shi ne tsaye kan dukiyar uban nasu amma damar ta kufce masa a kan idanunsa. Hajja ita kanta haka ta ji wayar Areef din kamar zagi yake ɗura mata, babu kamar da ya miƙe bayan ya nemi excuse ya koma cikin falon ya zauna ya cigaba da amsa wayar, ta ji Abba na mitar don me ba zai bari sai an kammala ba ya amsa wayar, Daddy Affan ko yana dariya yana amsawa Abban da cewa wai kusan halinsu guda da Areef din, maida hankali da ba neman kuɗi muhimmanci.

A gefen Nihla kuwa, ji ta yi kamar ta yi tsuntsuwa ta bi bayansa, ta kada haƙura cikin narkar da murya ta dubi Daddy Affan ta ce,

"Amma Daddy ba ka da gaskiya a nan, Abba fa ya fi ka gaskiya, ya dace Bro Areef ya ci abinci tukunna, lafiyarsa a saman komai take."

Mami ta ji abin banbarakwai da har ta ɗan ɗago kai ta dubi Nihla wacce ko a jikinta, Afrah kuwa da Benazir kallon juna suka yi su ma abin ya zo musu a hagunce balle kuma sauran yaran gidan da ba su saba ji ana ƙaryata babba ba. Ga mamakinsu kuwa Daddy Affan dariya ya yi har da ɗan buga kafadar Nihla din wacce ke gefensa, shi ma Abban taya shi ya yi.

"Yauwa ɗiyata, ai ka ji zance." Faɗin Abba. Kafin ma wani ya tanka ta ja kujerarta baya ta miƙe.

"Let me go and bring him back."

Tana maganar ne ya yin da take takawa, Zakari ya bi manyan mazaunanta da idanu yana haɗiyar yawu. Wani irin mugun sha'awarta ke taso masa tun da ya yi tozali da ita, ga leshinta kalar green da fari da ke jikinta ya zauna ɗabas, ɗinkin kuwa ya fallasa saman ƙirjinta wanda ko chantily din da ta yafa lemon green bai rufe komai ba. Ya kauda kai ransa na ƙuna ganin wai ta tafi kiran Areef ta dawo tebur din. Haɗa idanu ya yi da Hajja, ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba wurin aikamasa da saƙon harara. Maganar Anti Amarya ce ta sa duk aka maida hankali gareta.

"Ga dukkan alamu dai ɗanmu ya farauto zuciyar Nihla. To ko ƴar gida za'a yi ne?"

Duk suka kalle ta, Mami ji ta yi ƙirjinta ya ba da wani irin dam! Eh ta na son Areef ya yi aure, amma ba irin wannan yarinyar ba da idanunta suke a buɗe tarwai. Afrah ko salati ta shiga maimaitawa a zuciyarta don abin da take gudu ne ta ga kamar yana shirin afkuwa. Daddy Affan da Momi Inayah kuwa sun fi kowa jin daɗin wannan batu na Anti Amarya, Abba ma murmushi kawai ya yi da bai kai zuci ba. Shi fa a duniya yana son ƴaƴansa, ba ya son tashin hankulansu ba domin haka ba ai da tuni ya zartar da hukuncin auren don ko babu komai zai fi kaunar Areef din ya samu yarinyar da ta fito a gida irin na Alh Affan din, gidan da suke yan boko kuma ga arziƙi kamar me. To yaushe ma aka samu ya dawo gidan ballantana a maida gaba ya koma baya.

"Ai kuwa Hajjaju kin yi gaskiya, da hakan zai tabbata kuwa da na fi kowa farin ciki saboda ƙaunar da nake yiwa Alh Sada zan so na haɗa zuri'a da shi."

Maganar Daddy Affan ya sa Abba kallonsa, sai ya biye masa da dariya kawai ya ɗora da faɗin.

"Ni kaina zan so hakan, amma yaran yanzu ne ba a yi musu dole."

Shi ma ya yi saurin ɗaga hannu kaɗan,

"No no no, dama babu tilastawa. Ra'ayinsu ne, idan har kansu ya haɗu shikenan. Nasan kai ma za ka so haka."

Har wata ajiyar zuciya Abba ya saki don ko ba komai da ace alfarmar kai tsaye Alh Affan din ya roƙa bai san me zai ce masa ba.

"Tabbas zan so ace su fahimci junan nasu saboda ganin auren Areef na ɗaya daga cikin burikana a yanzu. Allah ya tabbatar mana da alheri."

Aka amsa amin ban da Hajja da Zakari waɗanda abin sam bai musu ba. Mami ma dannewa kawai ta yi.

A ɓangaren Areef da ke falo zaune kuwa, bai ankara ba sai ganin Nihla ta yi ta nemi saman teburin dake tsakar falon ta zauna suna fuskantar juna har gwuiwarsu na haɗuwa. Ya ɗago idanunsa ya watsa a kanta, yanayin ta ji shi irin na ɗazu, ita ta kasa ma tantance wane irin so take ji a kan gayen. Ya kauda ƙafarsa daga kusa da ita a daidai sadda yake sallama da Steven ya miƙe ba tare da ya ce mata komai ba ita ma ta yi saurin miƙewa ta ɗan riƙo gefen rigarsa, dole ya dakata ya juyo ya ƙara kallonta, wannan karon fuskarsa sai ka rantse bai taɓa koda murmushi ba a duniya. Nan da nan ta ɗan sha jinin jikinta ta narkar da fuska sa'ilin da ta sakarmasa riga ta ce,

"Hey Bro, kawai na ga bamu gaisa ba ne tun ɗazun. Kuma na ga ka taho making call alhalin an haɗu gaba ɗaya za'a ci lunch and you left the gathering sai na ji wani iri."

Kalmar ƙarshe da ta furta na wai ta ji wani iri ya sa shi ƙara kallonta karo na uku, murmushi ta sakar masa. Shi kuma kawai ya juya ya yi gaba ta mara mishi baya tana ƙarewa takunsa kallo. Ta kula kamar ba shi da hayaniya, ba mai son magana ba ne. Sai ta ga ya fita daban da irin samarin da suka saba bibiyarta suna mata nacin son su yi soyayya da ita alhalin ita mafi yawansu ma ta ɗauke su kawai abokan shan mint don ita a soyayya irin nata, wasu hugs and kisses ba ta ɗauke su a bakin komai ba. Kalar wayewar rashin tarbiyya da ta girma a cikinsa kenan.

Sai dab da la'asar suka yi musu sallama zasu wuce masauki ban da Nihla wacce ta dage ita kawai a bar ta za ta kwana a nan idan ya so goben idan sun shigo sai su wuce tunda da safe zasu bi jirgi su koma Abuja. Hakan ya yi wa Abba dadi, koda suka fito rakiyar su gaban mota ya dubi Daddy Affan ya ce,

"Ba za ka shiga Kano ba ka duba jikin Injiniya?" (Injiniya Kamal na ɗaya daga cikin abokin kasuwancinsu dake zaune a Kano da iyalinsa)

Daddy Affan ya ɗan yi jim kafin ya yi wani ɗan murmushi,

"Next time zan samu na je, kasan na faɗamaka nan zuwa jibi zan koma London."

"Oh, hakane." Abba ya amsa.

Shi kuwa Daddy Affan koda suka yi sallama direban Abban ya ja motar zai kai su Hotel mafi tsada a garin Katsina saboda duk iya nacin Abban, Daddy Affan ya nuna ba zai kwana a gidan ba.

Ya kwantar da kansa jikin kujera ya rufe idanu, ji yake yi koda zai shiga Kano da saura lokaci, ba yanzu ba. Sai ya kai ga ganewa idanunsa kabarin Kubra. Idan kuma ba kabarinta ba, to fa sai ya gan ta sun yi ido huɗu ta yadda zai murɗe wuyanta da hannunsa. A lokacin ne kaɗai zai san babu wani abu da zai gigita rayuwarsa a garin Kano, koda dai ko yau idan ya so zai iya shiga garin ya fita ba tare da kowa ya ankara ba, amma garin ne ma ba ya burge shi. Ko ba komai yakan tuna masa da asalinsa na shege.

"Akwai sauran rina a kaba."

"Me kenan?"

Sai da ya tsinci muryar Momi Inayah a gefensa ne sannan ya fahimci cewa a fili ya yi furucin. Riƙo hannunta ya yi yana murmushi kaɗan.

"Ba komai. Suna da kirki ko?"

Ta maida mishi martanin murmushin.

"Yes, irin sosai ɗin nan ma. But what is bothering me bai wuce yadda na ga kamar wannan Areef din bai wani damu da Nihla ba. Ka na ganin zai so ta?"

Ya yi dariya.

"Our daughter is beautiful just like you, ki saka a ranki with time za su fahimci juna. Ba ki ganin mu bar ta a nan idan tana so har mu dawo daga London?"

Momi Inayah ta yi shiru, ba ta taɓa yin nesa da ɗiyarta ba, ji ta yi yanzun ma kamar ba za ta iya ba. Babu batun wai makaranta tunda Nihla na jiran admission dinta ya fito ne a jami'ar Oxford wanda zai fito a watan farko na sabuwar shekarar bature da bai fi sati biyu a shige shi ba (January).

"Na tabbatar za ta samu kulawa daga Alh Sada da ahalinsa tamkar tana gabanmu, amma fa sai idan ita din tana ra'ayi. Idan ba ta so ba zan tursasa ta ba."

Daddy Affan ya ƙara faɗi. Ajiyar zuciya Momi Inayah ta sauke gami da jinina mishi kai alamar gamsuwa da hakan. Wato ra'ayin Nihla.

***

"No Abba, i prefer to sleep on Mami's side." (A'a Abba, na fi son kwana a bangaren Mami)

Shi ne amsar da Nihla ta ba Abba a sadda ya ce ta bi Hajja ɓangarenta, ita kuwa Nihla tunda ta ji cewa ai Mami ita ce mahaifiyar Areef din ta ji nan duniya ta fi so ta kwana a can, wataƙila za ta yi arba da sanyin idanunta. Mami kuwa yaƙe kawai ta yi don ba ta so hakan ba, Hajja ma yaƙen ta yi gami da cewa.

"Ai duk ɗaya ne ɗiyata. Afrah ku tafi da ita wajen naku ta kwana can."

Haka Afrah ta ja ta suka wuce, su kuwa kowa ya koma bangarensa. Areef dama tun tafiyar su Daddy Affan din ya shige na sa ɓangaren cike da takaicin yadda zuwansu ya dakatar masa ayyuka. Ya ji fitar ma a yau din ya fita ransa.

***

Nihla kuwa sake jikinta ta yi sosai a ɗakin su Afrah, ita da Benazir kawai suke hira tana ba ta labarin makarantar sakandire da ta yi a can London da kuma yanzun da take shirin shiga jami'ar dake can. Mami ta shigo ta tabbatar babu abin da Afrah ta rasa kafin ta koma nata ɗakin.

Nihla koda ta gaji ta dubi Benazir ta ce

"Brother dinku ba ya shigowa nan ne? Ko fita ya yi?"

Sai a lokacib Afrah ta dube ta da murmushin da ya fi kama da na yaƙe da takaicinta ta ce.

"Yana da ayyukan da yake gudanarwa, ba lallai ma ya ƙara shigowa nan ba sai da safe."

Nihla ta gyaɗa kai gami da furucin ok a sanyaye. Benazir ta ɗan harari Afrah a fakaice ganin dagaske dai take nuna ƙin jinin yarinyar.

Haka kuwa dai har aka cinye sauran lokutan ranar ba ta ga ƙeyarsa ba. Ta dai karɓi lambarsa wurin Benazir har wacce yake amfani da ita a London.

Washegari da safe kuwa wuraren takwas na safe ta kasa ko shirin tafiyarsu duk da Mami ta shigo ta sanar da ita isowar Daddy da Mominta, ita fa dagaske take jin Areef din, gani take idan ta taka ta bar Katsina kamar ta bar shi ne gaba ɗaya. Iyakar tunanin da ta yi ta fahimci to tana gaban idanunsa ma bai ishe ta kallo ba, ta ya ya zai so ta idan ta sa ƙafa ta bar ƙasar ma duka? Haka ta miƙe ba don ta so ba ta yi wanka ta jawo akwatin kayanta da su Momi Inayah suka taho mata da shi a safiyar yau ta shiga shiri, wata doguwar rigar atamfa wanda shi ma duk ya kama mata jiki, ko ɗankwali ba ta ɗora ba haka ta yi amfani da ɗan mayafinta chantily ta rufa a kan nata. Ita a dole ma ta ke sanya manyan kayan saboda Daddy Affan ya ce mata wai inda zasu zo din an fi ganin darajar mutum idan ya saka kayan gargajiya. Sai lokacin ta tuna ashe fa su Benazir sun tashe ta yin sallah ta ƙi tashi, ta dubi agogon wayarta sannan ta ja guntun tsaki, a fili ta ce,

"Time ya wuce ai, zan haɗa da na gobe kawai."

Daga haka ta zura takalminta ta fito falon Mami din.

Benazir na ganinta ta suka sakarwa junansu murmushi.

"Kin fito?" Nihla ta gyaɗa kai.

"Muje toh, suna jiranki ku yi breakfast."

Daga nan suka ɗunguma zuwa ɓangaren Abba. Wannan karon Anti Amarya ce ta shirya karin kumallon don ita ta karɓi girki.

"Morning Abba, Daddy, Momi, Mami and the rest, hope kun tashi lafiya?"

Wannan shi ne gaisuwar da Nihla ta yi musu, Abba ya amsa mata haka su Mami da ke daurewa kawai tunda ko babu komai ai an kusa a rabu, ba yadda kuma za ka yi da abin da ba tarbiyyarka ba.

"Baby ya dai? You look unhappy."

Tambayar Daddy Affan ga ɗiyarsa babu ko kunyar idanun mutanen gidan ya ba da mamaki, shi kuwa Abba bai nuna mamakinsa ba tunda yakan yi wa Daddy Affan uzurin kasancewar Nihla din ƴa guda ɗaya tilo a wurinsa. Ta turɓune fuska domin sam ba ta ji dadin rashin ganin Areef din ba a tebur.

"No, kawai ba na son tafiyar ne. Ina son su."

Murmushi Abba ya yi jin furucinta har da dan sauke ajiyar zuciya.

"To ko mu bar ki zuwa lokacin da admission dinki zai fito?"

Aikuwa jin batun Daddyn nata sai ta yi dariya tana jijjiga kai kamar kadangaruwa.

"Yes yes Daddy, zan so haka."

"Innalillahi.." Fadin Afrah ƙasa kasa, Benazir dake gefenta ta ɗan taka kafarta kaɗan alamun ta yi shiru.

Abba kuwa shima ya ji dadin abin da tace, Momi Inayah ba ta so hakan ba amma kuma dole za ta bi tunda farin cikin diyarta kenan.

Haka kuwa aka yi, Daddy Affan da Momi Inayah suka wuce suka bar Nihla a gidan. Hajja ta so ace wajenta ta sauka ko don ta zuge ta akan Areef din, sam ba ta so yadda yarinyar ta kafe akan sai ɓangaren Mami ba. Tun lokacin ta ji ta tsane ta ma. Tana kuma fatan ma kar auren ya ƙullu don ta fi ƙaunar yarinyar da za ta iya juyawa a gidan Areef din.

***

MAIDUGURI...

Women Of Words Writers

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol