Free chapter · Read without an account

5&6

by Aisha Abbakar · SAHAAR

SAHAAR

ADABI WRITER'S ASSOCIATION.

BY

MOM MUHSEEN

🅿️5&6

TWO WEEKS LATER

Dukkan ayyukan da suka rataya wuyana ina bakin kokarina wajen ganin nayisu yadda ya dace,amma ban yarda in shiga dakin U'HAIMID ba muddin yana nan,zanyita jan lokaci dakin Anti jamila muna fira da ita har sadda zanji fitar shi,sannan in sauri na shiga na gyara gashi mugun makyuyaci komi a warwatse sai na dauke,amma kuma baida k'azantar toilet dakin ne dai kayansa ko ina yaga dama yake xubarwa,a haka muka cike sati biyu ko hanya bata had'ani dashi,cikin hakan ne su Yallab'ai suka sauka daga Australia shida Ammi da Fauzan,wani sanyin dad'i ya dirar mun saboda kowa dake cikin gidan nan in har Ammi da Yallabai basa nan babu mai sakewa,sanan za'aci a koshi ka kuma fita yadda kake so,saboda duk taurin kan UWARGIDA HAFSA tana tsananin Shakkar Yallab'ai,shiyasa take tsahir tawa in ya dawo.

Dawowar tasu ta haifar mun da walwala sosai saboda zanje islamiyya kuma zanyi aikina ba tare da hantara ko kyara ba, Ammi itace mata ta biyu ga Yallabai Attahir muktar,saidai yarsu d'aya mace daga ita basu kara haihuwa ba,tana Germany tana karatun ta acan wannan year take dawowa ta kammala,yarinya mai d'a'a da sanin darajar mutane ga fara'a da son mutane da girmama manya,Fauzan kuma agola ne yayan Jidda ne sosai akalla ya bata shekara goma haka,dukkan dawainiyar Fauzan Yallab'ai shine yake dauka tun zuwanshi har kawo yanxu,Ya d'an girmi U'haimid kadan duk da bazan iya cewa ga shekarun ba,amma daga yadda yake da natsuwa da kamala ga sanin darajar mutane,zaka gane cewar akwai yar tazarar shekaru tsakanin su.

Anti Jamila d'iyar qanwar UWARGIDA hafsa ce ta daukota tun tana qarama kafun ya haihu,saboda itama ta jima bata haihu ba sai akan U'HAIMID shiyasa ta sangartashi sosai don ma YALLABAI tsayayye ne da banajin U'haimid zai samu tarbiya ko ya take.

Babban attajirine mai kud'i,sai kuma yazo ya auri Ammi Gimbiya Waseela,yar sarkin abuja ce tayi auren farko mijin ya rasu yabarta da Fauzan,sun gaji dukiya sosai da sosai data auri Yallabai Attahir ta mallaka masa ita ya cigaba da juya mata kafun sadda Fauzan zai taso ya anshi ragamar komi.

Shiyasa duk iya she UWARGIDA tana sassautawa idan Ammi na nan da Yallab'ai,saboda karya take ta nuna isarta akan abunda suka zartar,salaf take komawa indai suna nan,to kasuwancin su ne ke yawan sanya su tafiye tafiye,ita kuma Uwargida Hafsa aikin gwammanti take karkarshin NNPC.

yau muke aikin dare nida Anna,to tayi bakuwa sai tabarni Ina idasawa ina ta aikin cikin natsuwa kamshin girkin duk ya cika gidan, don daman girki uku ake a dinner in lunch ne kuma ana yin har biyar munfi shan wuya idan ma Yallab'ai da Ammi suna nan wurin girki,saboda suna cin abubuwa kusan iri d'aya ita kuma Uwargida Hafsa bata cin kalar nasu sai tace ayi mata nata ita da U'haimid daban,Anti Jamila bata da matsala ko kadan komi akai ci take haka Oga Fauzan.

Hankalina ya tafi ga Haddar da zan bada gobe asabar tahfiz da safe ban ida haddacewa ba, naji sallamarsa da muryar nan mai cike da natsuwa,na juya Ina ansawa "Barka da yamma Oga Fauzan"

Frig ya bud'e yana dauko bottle water yana cewa, "Bani cup"

Na aje abunda nake na d'auko masa ya ansa tare da fad'an, "thank you"

Na koma na cigaba da aikina hankali kwance, koba komi yana yinsu ma da Wancen dan iskan ba d'aya ba, har na kammala had'a Fruit salad yana jingine da cabinet din kitchen din yana surban ruwan tare da danna wayayyar wayarsa, na saka fruit salad din frig kenan naji yace dani, "Sahaara"

D'an murmushi nai nace "Oga Fauzan Sahaar yake sunan"

Gajeran murmushi yai shima yana d'agowa daga waya yana kallona, "Sahaara nafi iyawa ni kuma,ko ba zaki ansa yadda na iyan ba"

"Aa Oga fauzan ban isa ba ai"

Ya jinjina kai yana yin shiru,sai na cigaba da abubuwan dake gabana,na duba naman da nake gasawa oven na kara abunda zan kara na rufe.

"Wai ke yaushe zaki cigaba da karatu ne?"

Na waigo ina kallon shi kamar yadda yake kallona, "Eh dake nake"

Na sadda kaina Ina wasa da hannuna,kafun ince komi ya rigani "Bakya sha'awar karatu?"

Ban san ansar dazan bashi ba,sai na zab'i da inyi shiru kawae, aje cup din yai bayan shanye karamar roba ta ruwa yana cewa, "kiyi magana da Anna idan ta yadda zan dauki nauyin makarantarki"

Daga haka bai jira ansar dazan bashi ba ya fice, na fesar da huci ina tunanin yadda zan tunkari Anna da maganar wata makaranta,shekara uku kenan dana k'are secondary sakamakon kuma ba wani kyau yayi ba,ba zance ina da kokari ba gaskiya ba kuma zan kira kaina dak'ik'iya ba,hasali ma karatun bai wani dameni ba saboda nasan nid'in ba yar kowa bace,iyakar ma gaba da primary din da nai zan iya cewa alhamdulilla ya isheni,amma bazan watsa masa k'asa a ido ba idan Anna ta barni zan jaraba muga inda Allah zai kainin.

K'amshin turaren nashi mai karfi ya ratsa mun hanci har kaina, shi indai zai abu saiya wuce na kima duk inda yake to kamshin sa shine abu na farko dazai fara sallama,kafin takunsa ya iskoka sannan sallama bata damai ba kamar ba d'an musulmi ba,amma ban sani ba ko nice bai yi ma sallamar oho!

Nidai KO waigowa banyi ba balle ince nasan dashi,na soma tattare kayan abinci ina zuba su a warmers, ya gaji da tsayuwar kawae ya finciko ni da zafi har marfin kula yana fad'uwa, "Ke ni sa'an ki ne ba zaki iya gaishe ni ba?"

Na dago fararen lulu eyes dina na zuba masa,fuskata a tamke duk da gabana yana fad'uwa rashin kunyar da nake kokarin yi masa amma idan ban masa haka ba bazai fita sabgata ba.

"Malam kayi hkr ka sake min hannu don Allah,ka fadi abunda zan baka aiki nake"

Waro idonsa yai yana kallona da mamaki, "idan na k'i sakin hannun sai miye zai faru"

Na kaudar da kaina gefe ina tausar zuciyata, "ka fita harkata don Allah Oga Uhaimid,Uwargida ta shata mun layi dakai miyasa kakeson jawo mun wulakanci da tozarci,mina tare maka ne wai?"

Dage girarsa yai yana min wani makirin kallo fuskar sa murtike sosai, "Idan kika ce zaki fara min rashin kunya to wallahi duk gidan nan ba wanda ya isa ya ceceki daga uk'uba ta"

Ya tillar hannun nawa da zafi, "warning na farko kuma na karshe dazan miki shine kar na sake ganinki da wancen koda na second d'aya ne kunyi magana hope kina fahimta"

Kallon shi nake da mamaki sosai a fuskata, har ya fice daga kitchen d'in,sai na rasa ma abunda zanyi na jima tsaye kafun na iya fara zuwa jera kayan a dining.

*******

Tilawar nake tayi ta qur'ani amma hankalina yana rabuwa kashe-kashi,har dai Anna dake bisa sallaya tana jan cazbaha ta kallan, "Mike damunki ne?"

Rufe Qur'anin nayi nai shiru na wani lokaci kafun ta sake cewa, "Dake nake magana zainabu"

"Anna wata magana ce Oga Fauzan........kinga,kinga Zainab ki fita idanuna"

"Anna ki bari kiji abunda zance mana,kibar saurin yanke min hukunci"

Ta sauke numfashi tana cewa da sanyin rai, "Ina jiye miki tsoron abubuwa da dama ne zainabu,bana sonki da shige ma mutanan gidan nan duk da nasan cewar Fauzan da U'haimid akwai banbaci sosai"

Jingina bayana nayi da bango nace "Anna wallahi inajin na fiki taka tsantsan dasu,duk abunda zai jawo min wulakanci Ina kokarin guje masa,Ina kitchen ya shigo yai mun mgnr"

"Miya ce miki?"

Saida nayi jimm kafun na kalleta naga ni take ta kallo, na sadda kaina ina jan yatsuna kafun nace "Cewa yai na miki mgn zai dauki nauyi karatuna na gaba da secondary inkin amunce"

Tsareni tayi da idanu na sadda kaina ban sake magana ba,kamar ba za tace komi ba har na mik'e zan wuce cikin uwar d'aka tace mun" dawo nan Zainabu"

Na dawo na durk'usa gabanta, "Wane irin karatu ne zaki yanzu?na dauka a yanzu aure ne kawae kike jira,shekarunki nata karuwa mi zaki da karatu?"

"Anna bani na masa magana ba fa,wlh ina kitchen ya sameni da maganar kuma cewa yai idan kin amunce,ni banda wani zab'i sai abunda kika ce Anna"

Ta jinjina kanta kafun tace "jeki zanyi tunani"

Daga haka ban kuma tada mata maganar ba itama kuma bata sake min mgnr ba,shima bamu hadu ba balle ya tuna ya ji ta bakina.

********

Jidda ce zata dawo Ammi ta sayani gyaran dakin ta dake jikin na Anti Jamila,na gama aikin na wuce dakin Anti Jamilar tana shirin zata fita wurin bautar kasar da takeyi, "Sahaar yanzu kin gujeni ko,sai in wuni ban ganki ba dakin gama aiki shikenan"

Nai murmushi nace "ba haka bane Anti,ayyuakan sun k'aru tun dawowar su Ammi"

"Amma ai da kina zuwa mun fira da daddare,yanzu kuma kin daina kodai Anna ta hanaki?"

Girgiza kaina nayi da sauri nace, "Laa ba ruwan Anna wani lokacin Hadda nake tsayawa inyi shiyasa wlh"

Fira mukai tayi da ita har ta gama shirin ta nima na gama aikin,na fito don zuwa gyara d'akin Oga U'haimid, tare muka nufi dakin da ita tasha kayanta na bautar k'asa sunyi mata kyau sosai, Anti Jamila ba dai kyau ba komin ta mai tsari da burgewa,bata da rawar kai ko alama saidai Soyayyar U'haimid tana sanya ta yin wasu abubuwan da basu dace ba,KO bata fad'a ba in suna tare zaka iya cewa lallai wannan tana son sosai.

Ina daga bakin k'ofa ban kai ga shiga ba ita ta fara gaba, naji tana masa magana sannan kamshin sabulun wankan shi ya iskeni,alamun bai jima da fitowa wanka ba, sai na juya don in dawo inya fita saboda yana barin dakin bud'e saboda aikina.

Ina saukowa k'asan na hangi Ammi a kitchen,cikin sauri na k'ara ina gaisheta "Ammi ai da kin kirani mi za'ai miki?"

Tana murmushinta kamar koyaushe tace "Yau aikin lada zanyi,Yallab'ai zan dafa ma maganin sanyi ya tashi da mura sosai muryar sa ta dishe"

Cikin nuna alhini nace "Ayya,Allah ya bashi lafia yasa kaffara ne dame zan kama miki"

Tana kunna gas da kanta tace "Wannan zaki daka mun a turmin karfe"

Ta mik'o min wasu magunguna na soma gyarawa ina sawa a turmin, nace mata "Da za'a samu kajiji da tafarnuwa da citta kad'an suma suna maganin irin wannan mura Ammi"

Tace "Allah ya miki albarka,anjima zan hadaki da driver kuje kasuwa a samo da d'an dama a aje saboda yana yawan mura"

Muna ta firar cikin natsuwa kamar dai ba yar aiki take kallona ba,tana min firar Jidda cewar gobe zata dawo da kuma abubuwan da zan siyo mata kafun ta dawo d'in.

Saida muka gama sannan muka fito dai-dai Sadda Anti Jamila Oga U'haimid da Oga Fauzan duk suka fito zasu fita, gaishe gaishe suka tsaya yi,nima na gaida sun Oga Fauzan yace dani "Sahaara"

Na dawo Ina d'an risinawa, "ya maganar mune?"

Na sadda kaina bance komi ba,Ammi tace "wace mgn kenan"

Yace "Tsakanin mu ne fa Ammi kiyi tafiyarki"

Tace "To na tafin Fauzan"

Anti Jamila tai dariya tana cewa, mun wuce Ammi tai musu a dawo lafia,shi kam kamar baya wajen yana duk'e yana d'aura igiyar combos d'insa.

"Ki tabbatar idan na dawo anjima kina da ansar da zaki bani"

Daga ya wuce ban Iya cewa komi ba, nayi ma Anti Jamila a dawo lafia na koma sama don na masa gyaran dakin.

*******

Yinin ranar da tunanin abunda zance ma Oga Fauzan nayi sa,da naji karar mota gabana fad'uwa yake ban San miyasa nakejin ba dad'i ba,saboda kamar yayi min wani gagarumin alkairi ne nake niyyar tunkud'eshi,banso na matsa ma Anna akan mgnr tunda nima ba wani ra'ayi nake ba,amma ba dad'i nace masa bazan yi ba Ko kuma Anna ta hana,har naje islamiyya karfe shabiyu na samu Humaira suke aikin rana, nace mata "Inkin kammala inaso muyi magana don Allah"

Tace toshikenan zata sameni daki,nace"aa zan jiraki dakinki nidai"

Haka muka rabu na wuce ga Anna tunda sai dare zamu shiga kitchen mu kuma.

Sai wajen karfe uku Humaira ta shigo dakin nata, Ina ta duba wani littafi novel da take karantawa, "Na rasa miye kikeji cikin karanta labaran karya"

Dariya tayi tana zama "ba zaki gane ba kinji,yanzu miye damuwar?"

Na gyara kwanciyata nake gaya mata yadda mukai da Oga Fauzan kwanaki,da yadda mukai da Anna da maganar da ya min d'azun, tayi d'an jimmm kafin tace dani "Maganar gaskiya idan kika ce Anna ta hana ko kuma kika ce baki ra'ayi kamar kin maida hannun kyauta baya ne,amma ni a tawa shawarar idan ya nemi yaji ta bakin ki kice masa yai magana da Anna,duk abunda tace dashi zakiyi anfani kar ki fara nuna masa cewar kinyi mata maganar"

"Tabbas wannan shawarar tayi,nagoda sosai"

Mun jima muna fira sosai Humaira kusan tsarar juna muke amma zata ban KO shekara biyu haka,ita yar kano ce qanwar mamanta ta kawota aikatau,daga sadda ta kawota bata sake bibiyarta ba haka muketa rayuwar mu.

Da yake Ammi tana da hadimanta da tazo dasu gidan,shiyasa bamu zuwa mata aiki ko shara da goge goge,duk akwai masu yi mata sai tayi ra'ayin samu aiki take samu,ga kyauta kamar me da take mana.

Uwargida Hafsa kau marowaciya ce ta bugawa a jarida,abinci ma bata iya bari suci su k'oshi indai Yallab'ai baya gari,tsurar albashin su kawae take iya basu,amma Ammi duk shekara ta raba masu turame hadda leshi da kudin d'inki,Oga Fauzan ya rarraba mana kudi shi kuma,Yallab'ai ma kudi yake bamu amma Uwargida ko tsinke.

Har nayi shirin bacci Aka aiko kirana Inji Oga Fauzan, "Kiran me yake miki?"

"Anna ban sani ba nima"

Na bata ansa ina zira hijab bisa kayan jikina na bacci dana sauya, "kar kije ki dad'e"

Kamar zan kuka nace "Anna kodai in fasa zuwa?sai sharudda kike samun"

"Ke yarinya ce har yanzu,nidai nace karki dad'e"

Tara ma tayi lokacin duk yawancin yan aikin duk sun kwanta ma,falon kasan ba kowa sai na wuce part din Ammi don acan zan same shi a nashi part d'in.

Mom muhsen✍🏻

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol