Free chapter · Read without an account

11&12

by Aisha Abbakar · SAHAAR

SAHAAR

ADABI WRITER'S ASSOCIATION.

BY

MOM MUHSEEN

🅿️....11&12

Oga Fauzan yace ma Yallab'ai, "Daddy Ina gani kawae ayi nasu Uhaimid d'in har yanzu ban samu wadda hankalina ya natsu da ita ba,a kara mun lokaci"

"Har yaushe za'a aita kara ma lokaci Fauzan? baka ganin shekarun ka kullum karuwa suke,karfa ka tun zura mahaifiyarka ta maka auren had'i"

Duk aka sanya dariya lokacin Ina wajen nazo yima Yallabai sannu da zuwa yaje asibiti Egypt, had'a ido mukai da Oga Fauzan ya mun wani kallo sai na sunkuyar da kaina,bai ta b'a mun wannan kallon ba sai naji duk na tsargu, Ammi tace "Kuma Yallab'ai kamar kasan ankusa zuwa lokacin inhar bayyi da gaske ba,abokan sa fa yanzu wani haihuwa ma ta biyu za'ai masa,"

"Ammi kiyi hkr komi fa lokaci garesa, Hamma shima badan son ranshi ba ko?"

Cewar Jidda tana duban shi da son kareshi, d'aga mata kai yayi yana cigaba da satar kallon Sahaar,ganin duk ta takure tun sadda ya mata kallon nan, Tashi nai ina masu saida safe na fice daga falon, Ina saukowa muka had'u da uwargida falon k'asa, muguwar fad'uwar gaba ta saman bakina na rawa na gaidata........"Rik'e gaisuwarki hamshak'iya mandiya,isassa watau kin samu waje kin mik'e k'afa ko?"

Kaina sadda bance uffan ba,haushi yasa ta fizgoni tana kama kunnena ta murd'a da karfi, "Shegiya mayya,wlh dana son samun waje kika zo gidan nan kozan mutu ba za'a ansheki ba,saidai uwar rikon taki ta idasa kasheki acan kauyen naku.........Mommy!"

Uhaimid ya kirata da d'an karfi kad'an, ta sakarmun kunen wani rad'ad'in azaba yana ratsani, hawaye suka wanke fuskata jikina yana rawa sosai tace "Wuce kitchen ki had'o mun coffee shegiya,kuma har abadan sunan yar aiki kike agidan nan wallahi"

Jikina yana rawa na wuce kitchen din da sauri,kuka na fashe dashi na d'ora kaina bisa island din ina abuna, jin kamar za'a shigo yasa nai saurin goge fuskata na dora mata coffee,shashsheka kurin nake inajin wani nauyi a kirjina,nasan har abadan Uwargida ba zata kaunace mu ba nida Anna,wata irin tsana take mana marar tushe..........koban waiwaiya ba nasan shine a bakin kofar kitchen d'in,saurin share fuskar nayi ban waiwaya ba na cigaba da tsayuwata a gaban gas,har ya tafasa na dauko cup na juye bayan na tace shi,sbd ita sai tace na dafawa takeso ba hadadde daga inji ba.

Saida nazo k'ofar na tsaya ban iya dago kaina ba,inata jan hanci sbd har sannan kirjina zafi yake inajin takaici da bakin cikin abunda ta mun, jinai yasa yatsarsa ya d'ago hab'ata idonsa cikin nawa, yana kallona sosai fuskar sa da sassauci ba kamar kwana biyun nan ba, "Kuka kikai har haka?"

Na kauda fuskar gefe bance komi ba,sai wasu hawayen dake sake silalowa, "Ohhh sheet!"

Ansar cup d'in yai daga hannuna ya aje bisa cabinet din kitchen din, yasa hannu aljihunsa ya ciro hanky, dago fuskar ya sakeyi muka had'a ido dashi, sai kawae ya shiga goge mun kwallar masifaffen kamshinsa yana bugar mun hanci,lumshe idona nai naji zuciyata ta ansa sosai na d'an ja baya muryata ba kuzari sosai, "zanje na kai mata"

"Kije ki kwanta kina da exam early morning,zan tai mata dashi"

Jinjina masa kai nayi zan wuce, ya sake cewa muryarsa cool sosai, "Karki sake kuka kinji"

Kasa hana kaina kallon shi nayi, sai ya lumshe idanunsa kurin, uffan bance ba na fice zuwa dakinmu.

*******

Washe gari aka tsayar da ranar auren Oga Uhaimid da Anti Jamila,gidan cike da yan uwa da abokan arxiki anata hidima,Anna dasu Humaira basa zaune shiyasa dana dawo exam na shige na kwanta nayi ta baccin gajiya,ban tashi ba sai karfe biyar nai wanka nayi salla na dibi abinci na d'anci kad'an, a lokacin ne naga kiran Jidda.

"Kina ina wai?"

Na sauke ajiyar zuciya nace, "Ina dakinmu,wani abunne?"

"No,daman Hamma Fauzan ke neman ki,ki samai waje can wajen Sahabi mai shago"

Sauke wayar nai inata kallon ta, kamar ita zata ban ansar tambayar dake raina, "kiran me yake mun?"

Duk da ba yau ya fara kirana ba,amma kawae naji anya da dalili, jiki a mace na tashi na wanke bakina na dauki madaidaiciyar hijab d'ina na saka,na fito da wayar ga hannuna har na fito get ban hadu da wanda na sani ba, can gaban wani shago dake unguwar na hangi motarshi, na karasa har inda take na tsaya dai-dai window d'in driver,sai driver ya bude yana kallona yace "ki zagayo oga na ciki"

Kamar ince wani abu amma banda wannan damar,sai na zagaya bayan na bud'e na shiga, "Ya salam"

Abunda na ambata kenan cikin zuciyata,wani sanyi mai gauraye da kamshin turarensa dana motar ya daki hancina,dole na na lumshe ido saboda sanyin dadinsa, yana cikin kujera ya rufe idanunsa ga computer bud'e bisa cinyarsa,kamar yana bacci yai relaxing cikin kujerar kamar wanda yasha uban aiki ya gaji, muryata har wata rawa-rawa take nace da sanyi, "Ina...Ina wuni Oga Fauzan"

Bud'e idanunsa yai ya saukesu akaina,gabana ya fad'i haka nan saboda yadda naga idanun sun d'an sauya,kamar bacci ke cinsa ko kuma yasha wasu abubuwan, "Ya exam d'in"

Kaina kasa Ina wasa da hannuna nace "Alhamdulillah"

"Yaushe kika dawo?"

"Karfe biyu da rabi na dawo,"

Yai shiru na wani lokaci,kafin yace "zaki mun rakiya ne yanzu,zaki bini?"

Sosai zuciyana ke bugawa,inda zan iya hud'e bakina tabbas zance masa yayi hkr bazan iya ba, amma bakina yai nauyi sosai kaina k'asa ina juya abunda zan fad'a, daker cikin in ina nace, "Uhmm daman.......Anna.....Anna bata san zan fita ba"

"Ai batasan kin dawo ba,ko ta sani?"

Ya katseni da fad'in hakan yana tsareni da kallo sosai, girgiza kaina nayi sannan yace "har munje mu dawo ba zamu jima ba ai"

Inaji Ina gani mukabar unguwar,HanKalina baya kwance inata kallon hanya dai,na ma kasa juyawa in dube shi,amma sai nakejin kamar shidin kallona yake,kuma irin kallon da Oga Uhaimid ke yawan mun har inji jikina yana rawa, wani katafaren gidan cin abinci ne muka iso,tunda nake ma ban tab'a zuwa gidan cin abinci ba sai yau,wurin iyakar had'uwa ya had'u har na so na rikice ma,amma na dake ina biye dashi har mazaunin daka tana da don bak'i.

Oder ya bayar yana kallona sosai "miza'a kawo miki"

Saurin kallon sa nayi da wararrun idanuna, "Ni kuma?"

Murmushi yai sosai yace, "to da waye nake tare Sahaara?"

Na sadda kaina ina jan yatsuna, nace "Oga Fauzan naci abinci gida ai"

"No, dole ki fadi wani abu fa"

Na shiga ukuna,taya zanci abinci cikin jama'a haka?kuma gabanshi inajin nauyinsa sosai, "lemu ya isa"

Girgiza kai kurin yai ya sallami mutumin, bada jimawa ba aka kawo masa lafiyayyen abinci irin na yan gayu kamarsa, da drinks masu dad'in gaske ga lafiyayyar kaza tasha gashi sai azabar kamshi take, zazzare kasusuwan yai tas ya dauki wani plate ya zuba mun naman, ya kuma daukar cup ya zuba mun drink, ya aje gabana yana kallona.

"Oya chup"

Kamar zan kuka nace "Allah Oga Fauzan........shiiiiiiit,bana son musu ko gardama kawae kici"

Hadiyar abu nai Ina satar kallon shi yadda yake cin abincin cikin natsuwa calmly kamar ba kowa wajen, "kibar satar kallona malama"

Na sunkuyar da kaina Ina murmushi, "ki gama ci ki gaya mun waye kike wa dariya jiya ana mun mgnr aure"

Na zazzaro ido waje Ina rufe bakina, "wallahi.......sai kin gama tukun nakeson jin ta bakin ki"

Na maida bakina na rufe na soma jujjuya fork din hannuna, don dole na soma ci a hankali wani kafirin dadi yana kaimun har kwalwata,sbd laushin naman ga dad'i amma ban zak'e ba naci kadan nasha lemun, nace "Don Allah karka ce in kara"

Dariya ma maganarta bashi ya murmusa yana kallona, "ba zance ba ai kinci kin biyani thank you"

Muka gama aka kwashe kayan har na mik'e na dauka tafia zamuyi yace na zauna, na zauna Ina ta alwallar k'uda, "Sahaar"

Mamaki ya cikani na dago ina kallon sa jin yau dai ya fad'i ainahin yadda sunan yake, "Na fad'a daidai ko?"

Ban san sadda murmushi ya kwace mun ba, na sunkuyar da kaina na kasa daina murmushin na d'aga kaina kurin, "ko dai zainab zance?"

Girgiza masa kai nayi nace "Aa Oga Fauzan Sahaar d"in dai"

"Miyasa bakiso ace zainab"

Ina juya dan siririn dan hannuna nace, "bana son sunan ne,"

Da mamaki yace "miyasa bakya son sunan ki?"

Na b'ata raina Ina yin shiru, kallonta yake sosai da alamun inta samu waje shagwab zata zuba abunta, yace "Pls ki gaya mun mana"

Kamar zan kuka nace "Sunan matar Baffa na ne,bana sonta kwata-kwata"

"Subhanallahi,miye ta miki da zafi haka?"

Kwalla suka ciko idona duk yadda naso boyesu kasawa nai, na dora kaina bisa table din Ina hawaye, hankalinsa ya tashi ya d'an matso da kujerar sa sosai yana mun magana da taushin murya,irin yadda ban tab'ajin yayi mgn dashi ba, "Please mana kibar kukan,I'm sorry na tada miki bad memories d'inki,bazan kuma miki mgn akan matar Baffanki ba"

Na dago fuskata tayi jaa ga hawaye, ya ban hanky dinsa Ina goge fuskar na dauki ruwa na wanke ta, sannan yace da sanyin rai "Sorry kinji"

Jinjina masa kaina nayi Ina cewa, "Ya wuce,kawae dai ta cutar dani ta cutar da Anna bazan iya yafe mata ba"

Har cikin zuciyarsa yaji tausayinta ainun,saboda shidai bazai iya cewa ga sadda aka kawota gidan ba,yadai dawo daga america ya iske the youngest girl tana aiki,bata wuce 12 years ba alokacin shi kuma ya gamo degree d'insa lokacin,tun lokacin Allah ya zuba masa tausayinta da burin inganta rayuwarta.

"Dare yayi inaso muje gida kar Anna tayi mun fad'a"

Jinjina kanshi yai yana cewa, "fatan watarana zaki ban labarin matar Baffanki?"

Jinjina masa kaina nayi kawae, haka muka baro wajen muka nufo gida,a motar ma ba mai mgn saidai kallona da yake lokaci lokaci,ana sallar magariba muka iso gida, Ina bude kofar na fito idona cikin na Oga Uhaimid,wani kallo daya mun sai naji kamar na b'ace saboda muninsa, jiki a mace na wuce bangarenmu ban tsaya ma yima Oga fauzan sallama ba.

********

Mun gama exam da lafia mukai hutun 2weeks muka koma second semester,wadda muka shigeta da zafi-zafi na kara zaburewa duk Oga Uhaimid ya rame mun karatu,ko zuwa nai baifi muyi na minty talatin ba yace ya gaji,kwata kwata ban ganin walwala tattare dashi tun ina ganin abun kamar na lokacine har ya fara wuce kima,nidai banda Right din tambayarsa miye yake damunsa ban isa ba,shiyasa na tsaya iya matsayina ban wuce gona da iri ba.

Wasu lokutan kuma mu yini da Jidda nan dakin Humaira muna karatun tare, na rage shiga cikin gida saboda uzzirawar Uwargida Hafsa,inhar taga Yallab'ai baya nan banda sak'at sai nayi dagaske ma inje makaranta,don ma Oga Fauzan inhar yana gida to sai yaga tafia ta sannan yake fita shima.

Wata kulawa ta musamman yake bani kamar dai uwa daya uba d'aya muke dashi,ko yana gidan ina gidan zai kirani a waya kawae yaita jana da fira,in kuma free yake yace inzo yaga hand out dina harma ya kara mun wani karatun,lokacin biki ya fara tahowa ni kuma karatu yana kara zafi don wata uku dama aka sanya daidai lokacin kammala aji d'ayan mu, sai naga dandanan shekarar ta kare.

Yallab'ai Attahir da Uwargida Hafsa da Ammi sai Anti Jamila,sai Jidda suka shirya tafia London siyayyar kayan daki da sauran su,zasu tsaya suyi ummara sannan su dawo,gidan ya rage mu kad'ai yan aiki don Oga Fauzan yanzu sai cikin dare yake dawowa daga company sa da aka bude kwana nan.

ban san miyasa Oga Uhaimid k'in zuwa ba a ranar dai na gama had'owa uwargida jarababben coffee ta naji tana ta lallaminsa, "Bafa za'a dauki dogon lokaci ba Uhai,dududu 3 weeks ne zuwa four mun dawo,kuma kana da damar yin tafiar nan baka da matsala da asibiti tunda Dr Farhan yana nan"

Idonsa rufe yana kwance cikin kujera three seater yace "Mommy please tunda dai nace bazan je ba pls ki kyaleni, tunda Baby ta shafa mun lfy kema don Allah ku kyaleni da mgnr tafiar nan bazan je ba"

"To kar kaje d'in,idan na dauko maka duk abunda naga dama karka sake kace bai ba,tunda kayan da zaka saka haddasu za'a siyo acan inason na sauya maka kaff kayanka kayi angonci dasu,sannan lefen ma duk acan za'a had'o hajia Kilishi a dubai zamu hadu mu wuce"

Uffan bai tanka ba nidai na gama gyara mata akaifar bayan na kawo coffee ta sallaman cikin izgilanci.

Ina ta assignment d'ina da wayata Anna nata jan carbi ta gama sallar isha'i, sai aka kira wayata ina dubawa naga ansa Kawuna, na kalli Anna Ina cewa "Kawu ne Anna,Allah yasa lafia saboda nidai na canfa kiranshi duk sadda zai kira to ba alkairi bane"

Ansar wayar tayi tana cewa, "bakin ki ya saba fad'in alkairi banda canfi"

Sallamar farko data mashi ban tunanin ya kai ga ansawa naji ta zabga uban salati tana k'arawa, sai kuma naga ta aje wayar ta fashe da kuka, hankalina yai tashin doron zabo na isa gareta ina dagota sosai, "Anna miye?wani abunne ya faru acan gida?don Allah kice wani abu?"

Cikin kukan tace "Baba malami ne Allah ya masa cikawa,shikenan na zama marainiyar karfi da yaji daman shine nake kallo matsayin uwata kuma ubana,zainab ya tafi shikenan kuma ke daya gareni yanzu"

Jikina yai sanyi saboda nasan cewae Anna na son Baba malami,shine ya rik'eta har ya aurar da ita ga Baffa na,ta rasa iyayenta tun tana budurwa aka barta hannun kishiyar uwa,bata rik'eta da kirki ba sai azaba kala da kala,kwatsam Baba malami yazo rugar tasu mafarin ya dauketa yatai da ita cikin iyalinsa har ya aurar da ita,shi matsayin abokin wasa yake da mamanta.

Sauran dangi kuma ba mai son Anna don Allah sai don abun hannunta,kasancewar tana aiki birni kuma tana samun abun hannunta shikenan suka maidata saniyar tatsa,wani lokacin ma nice ke murje idona ince wlh ba abunda xata basu muma ai ba koshi mukai ba.

Har shadayan dare munyi jugum jugum,Anna ta kasa tashi daga inda take damuwa sosai ta bayyana a fuskarta, hakuri naita bata Ina cewa Allah baya barin wani don Wani yaji dad'i,kuma mutuwar tana kan kowa muma zaman jiranta muke,kuma yadda Baba malami ya tsufa ga ciwo da sauransu ko tafia baya iyawa anata fama dashi aganina mutuwar itace tafi masa sauk'i,muna fatan ace can tafi masa nan.

Da wannan na shawo kanta ta d'an sake tana fara had'a kayanta don tace da asuba zata tafi,don ta isa da wuri tace mun "zamanki ke daya nan hankalina bazai kwanta ba,kodai mutafi tare zainab"

"Zan so inbiki Anna,amma kingani sauran yan kwana ki mu fara jarabawa Ina bukatar karatu sosai"

Tai shiru na wani lokaci tace "kwanaki ba qawarki tace daman ki dawo hostel ba?mizai hana kije ku zauna kafin in dawo hankalina zaifi kwanciya zainab"

Na sauke ajiyar zuciya nace "inhakan zai kwantar miki da hankali Anna zan koma,gobe idan zan tafi lectures sai in hada kayana in tafi dasu"

Asuba nayi ta shiga ta sanar da uwargida wadda suma d'in yau zasu wuce, Sai gata ta dawo da kud'i da yawa Ammi ta bata da Yallab'ai tayi kud'in mota.

Kirkin su yawa ne dashi bamuda abun saka masu dashi face addua.

Za'a zuba love fa mutanena ku kara gyara zama😉🫣😄

Mom muhseen

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.