Free chapter · Read without an account

22

by Aisha Abbakar · SAHAAR

*_SAHAAR_*

ADABI WRITER'S ASSOCIATION.

BY

MOM MUHSEEN

🅿️.....22

Tafiya muke iska na kad'awa kamar hadari zai taso saboda har sanyi sanyin ruwan zakaji cikin iskan, sbd windows din motar a bud'e suke,tunda muka taho nake share hawaye na da suka kasa tsayawa, zuciyata a kakkarye take kullum maganganun Uwargida akanmu ba masu dad'i bane,ita bata dauki d'an adam baki komi ba inhar baka fito daga gidan masu hali ba,bata daraja dan adam wanda akace wannan talakane kuma karkashinta yake,zata iya tozartashi iyakar tozarci taci masa fuska iya son ranta batajin hakan komi a ranta, yanzu duk cikin masu aikin gidan da sukai yawa ta rasa wanda zata ce yaje caan gidan ya cigaba da aiki saini,sbd tunda aka fara maganar karatuna daman neman hanyar gintse manshi take,gashi na cinye shekara guda cikin nasara kwatsam tana son goge min komi,kodayaushe barazanar ta itace zata koreka, to zanso ta koremiun ai bakin da Allah ya tsaga bazai hana shi abinci ba,kuma duk ruwa da iska indai Allah yasa zamu rayu ba wanda ya isa ya gintse mana rayuwarmu,wadannan abubuwan ne suka sanya hawayena kasa tsayuwa,a raunane nakeji zuciyata ta cunkushe min sosai,baice mun uffan ba har sadda muka iso cikin tangamemen get d'in gidan, mamakin daya kamani gidan iri d'aya ne sak da gidan Hamma F wanda ya tab'a kaini,saboda nasan dai bazai yuwu ace gidanshi ya ansa zai zauna ba,nafi tunanin Yallabai Attahir ne ya gina masu shi kyauta iri daya.

Kama hannun k'ofar nayi in bud'e amma najita agintse,sai na daina wahalar da kaina wajen jan abun in fita, sbd nasan shine ya rufeta kuma yana da dalilinsa,shiru ne ya ratsa nida shi ba wanda yace komi tsawon wasu mintoci, kafun ya jiyo sosai yana fuskantata,kaina sadde k'asa Ina wasa da cover wayata har sannan kwalla ce ke d'iga bisa hannuna.

"Zainab"

Wani abune bak'o ya mun sallama sakamakon kiran sunana zahiri da yai,saboda ban tab'a ba ko Sahaar d'inma ba kira yake ba balle, "ki ansa mun"

Hannu nasa na share fuskata, na amsa cikin raunin murya cike da sanyi, "Na'am"

"Ki Jiyo muyi mgn pls"

Yana mun mgnr ne cikin wani irin kwantar da murya da sanyayata,hakan bai tab'a faruwa ba shiyasa abun yazo mun wani kala, jiyowar nayi ina fuskantar shi amma na gaza dago kaina in kalleshi.

"Kallan ni"

Girgiza kaina nayi ina jan hanci hawayena sun gaza tsayawa, sai ya mik'o mun hanky d'insa, "Zai taimaka miki"

Ansa nayi ina goge hawayen nawa, Ina sauke ajiyar zuciya akai akai, "Kiyi hkr da abunda ya faru kinji"

Wani irin Tsammmmm naji gaba d'aya tsikar jikina tayi,har bansan na d'ago idona ina kallonsa sosai ba, kallon ido cikin ido mukai ma juna yayin da hakan ya kara rikitar da kwakwalwata, da sauri na sauke idona bazan iya jure kallon kwayar idanunsa ba,wani yana yine da bazan iya bayyana shi ba a cikin idanunsa da fuskar sa, har nake tambayar kaina "Anya Oga Uhaimid ne? Hkr fa yake bani abunda bai tab'a faruwa ba tsawon lokaci,miye ya canza shi lokaci guda haka?" Banda wannan ansar na sake jinsa yace,

"Kiyi hakuri a madadin Mommy"

Girgiza kaina nayi muryata tana yar rawa nace "ka daina bani hkr Oga Uhaimid mun cancanci hakan ne........No,baku cancanta ba bakuba ma har sauran masu aikin basu cancanci wannan cin fuskar ba,wannan wani haline da d'abi'a nata wanda mu kanmu baya mana dad'i, kiyi hkr kinji"

Har yanzu a rud'e nake idan yana bani hkrn har cikin kasusuwana nakejin kalmar da soft voice d'insa wadda ban tab'a sanin yana da wanan muryan ba.

"Kar kiga laifina na tilasta miki kizo gidana kiyi mana aiki,banzo da wannan niyyar ba abunda nazo dashi shine cikin dattawan masu aikin abani guda saboda ta kama ma Jamila hidima gida bata da lafia,tunanina bai bani zatace ke ba da kwata kwata bazan zo da mgnr ba,"

Girgiza kaina nayi nace, "Karka damu kanka Oga Uhaimid indai aikine zanyi muku har iya inda karfina zai k'are,kar ka damu da sai kayi mun bayani.........inaso nai miki bayani Zainab"

"Innalillahi wa inna ilahir raju'un, Anya yasan ya nakeji idan yana kiran sunana haka?idan yana mun mgn da wannan yana yin nashi,zuciyata a rud'e take na k'osa matuk'a inbar cikin motar" duk cikin raina nake wannan mgnr.

"Game da karatunki insha Allahu zamanki gidana bazai dakatar miki da mkrnta ba,na miki wannan alkawarin,alfarma d'aya kawae nake nema gareki"

Na d'ago idanuna ina kallonsa ya lumshe idonsa tare da sauke numfashi a hankali, yace "Karki takura kanki,karki k'i sakewa a cikin gidan nan"

Jinjina masa kaina nayi kawae bansan miye zance d'in ba, "yaushe kuke koma wa mkrnta?"

"Nan da kwana biyar"

"Allah ya kaimu saiki zama cikin shiri insha Allah zaki koma sch"

Ya bud'e lock d'in motar na kama na bud'e, sai na jiyo Ina ce masa "Nagode"

D'an guntun smile ya saki baice komi ba ya fito shima daga motar, na zagaya in bude in fiddo jikkata na iske har ya fiddo mun, na mik'a hannu zan ansa ya girgiza Kanshi.

"Ta miki nauyi,muje kawae"

Mamakin sa kasheni yake har ma nakan rasa miye zance, binsa nayi har cikin gidan wlh komi yaji ko ina ka kalla gwanin kyau da sha'awa, TV ce kawae keta surutu babban falon na zauna cikin daya da cikin kujerun wurin,naga yai hanyar wata corridor da jikkar tawa,binsa da kallo nayi har yana yin tafiyarsa ba kuzari cikinta, "miye yake damun Oga Uhaimid,ya sauya ba karamar sauya wa ba kamar ba wanda yai aure sati biyu baya ba"

Ni kad'ai nake mgnr cikin zuciyata, Ina ta zaune a wajen naji alamun fitowar su shida ita, "Oyoyo ga Sahaar,da dai nace fushi nake dake ba ruwana dake sbd baki tab'a zuwa gidan nan ba,sai gashi naci sa'a Allah ya jeho munke"

Murmushi nayi Ina dan saukowa zan gaisheta, "Kin san banson wannan durkushin koma ki zauna"

Na koma na zauna Ina gaisheta, "Anti kiyi hkr wlh ayyuka nasu bari infito duk da muna hutu"

"Na yafe miki ai,tunda yanzu gani gaki gida guda Allah yasa dai zaki zauna damu"

Kaina k'asa ina murmushi nace "Mizai hana Anti,ai nama zauna na gama ya karfin jikin"

"Alhamdulillah Sahaar"

"Allah yasa kaffara ne,yanzu mi zan miki kafun ki kwanta"

Duk yana zaune cikin one seater yana danna wayarsa kamar baya wajen, ta kalle shi tana anshe wayar "mi zakaci yanzu?"

Yana gyara kwanciyar sa ya mik'e kafafunsa cikin kujerar yana cewa, "Only Coffee"

Ta b'ata fuska sosai "Ni gaskiya bana son wannan coffee,shi kad'ai bazai mgnin yunwa ba Baby"

Lumshe idonsa yai yace "To waye yace miki inajin yunwa,naci abinci gida ai"

Ta kalleni tace "Wai haka Sahaar,nasan bakimun karya"

"Watau saini zan miki karyar kenan?"

Ya fad'a yana harararta,yar dariya tayi tace "No baby,nasan halinka dai baka son abinci"

"To ai saita gaya miki inta sani ko"

Nace "Anti tunda yace yaci kila yaci d'in,bazan iya sani ba gaskiya"

Ta rausayar da kanta tace "Shikenan,had'o masa coffee ni kuma ki dafa mun Noodles irin wadda kike dafa mun d'in nan mai dad'i"

Nai murmushi na mik'e Ina cewa, "angama Anti yanzu zan kawo miki,ina ne kitchen din"

Ta juya tana kallon shi tana narke masa fuska, "Baby pls ka rakata kitchen kaji"

Yatsina fuska yai yana turo bakinsa saurin kauda kaina nayi daga kallon shi, "Kin cika sa aiki fa"

"Ai yanzu na samu Sahaar zan watsar dakai"

"Zaki sani nidai kike gaya ma hakan ko"

Dariya tayi tace "Sorry baby"

Tashi nai na bisa yana ce Mata, "Sorry for ur self"

Saida mika shiga wata kwana sannan muka sauka daga steps zai kai shidda,sannan muka iso ya nuna mun store sannan ya bud'e kitchen d'in, kamar ma ba'a tab'a yin komi cikinsa ba, kallon kitchen din nake sosai an narka dukiya iya dukiya ciki,amma ban tunanin ana amfani dashi,sai wasu tarkacen take away dake cikin shara.

"Yau za'a fara aiki cikin sa"

Na kallesa da mamaki,kafada ya d'aga yana shiga ciki sosai "Bata iya girki ba,and ko kunna gas banjin ta iya, kuma saiga rashin lfy that's why"

Nunnunu na mun komi yai a natse gas din nasu ma irin na turawa saida ya koya mun yadda zan anfani dashi,da stove da microwave duk kayan wuta saida ya nuna mun,to daman wasu ai can gidan duk muna anfani dasu,ma ajiyar kayan coffee d'in ya nuna mun da masarrafar shi sannan yace.

"Zan iya tafia?"

Na daga masa kai kurin,sannan ya fice daga kitchen din,sauke numfashi nayi Ina jin na samu natsuwa tunda ya shigo na kagara ya fita.

Cikin minty ashirin da biyar na kammala komi,k'amshi ya cika gidan kamar wasu kayan gaban na dafa, na dora komi cikin k'ayataccen tire na rufe indomin da plate na dora spoon sama,na daukar mata ruwa da lemun da takesha a gida na dora,na taho na kawo mata suna tsakiyar falon xaune k'asan carpet ta dora kanta jikin shoulder nashi, ina shigo ta tashi tana cewa "Sahaar tunda najiyo kamshi na k'osa inci,amma maida lemun bana shan lemu yanzu"

Nace "To Anti"

Na aje kasa sannan na koma na maida lemun na dauko masa coffee, dai-dai yana bata a baki na shigo,yana bata ta ansa ya aje spoon din yana ansar cup d'in coffee har hannuwan mu suna had'uwa, kad'an yasa ban saki cup din ya zube masa a jiki ba.

Nace "zanje in kwanta Anti naga shabiyu tayi"

"Ina zaki?zauna muci tare bazan iya cinye wa ba"

"Anti anciyo abinci........harara ta wurgo mun tace "Oya sit malama"

Zaman nayi kusada ita na sanya hannu na fara ci,gaba d'aya nayi mugun takura gabansu sai fira take masa yana d'an bata ansa sama-sama, wani lokacim ta sanyo ni cikin mgnr, Anti Jamila bata da matsala a rayuwa,Ina matukar sonta har raina saidai K'ADDARA TA GIFTA MANA NIDA ITA.

sai daya na iso dakina kamar yar wata hamshakin mai kud'i ga Ac ga lafiyayyen gado yasha katifar alfarma mai taushi kamar auduga ce zalla ciki,ga bedsheets shima. labulaye manya tagogin biyu manya masu azabar kyau windows d'in kanta in ana ruwa bazan iyajin karar shi ba,ga sofa ga wadrope da mirrow ga kuma toilet irin na masu kud'in gaske.

Canza kaya nayi zuwa na barci na haye gadon bayan na lalubi yadda zan rage Ac d'in,don sola ce gidan ba nepa ba don inza'a shekara ba nepa suba zasu tab'a ganewa ba.

********

Cikin kwanakin da suka biyo baya zan iya cewa na samu yanci a gidan oga uhaimid fiye da tunani,Anti jamila dai ga dukkan alamu cikine da ita kuma yana bata whl gaskiya,amma duk da haka bai hana tana zama dani muna fira ba,har takance mun ayyukana sunyi yawa zata sanya a karo wanda zai tayani, nace mata ni ai nan banga wani bakon abu wajena ba,inayin aikin dayafi wannan ta kuma sani daker na hanata cewa akaro d'in,don idan uwargida taji cewa zatai nice na gaza ko kuma nace a karo d'in.

Tsakanina dashi Oga Uhaimid ba tsanani ba tsanantawa,kamar yadda bai cika matsa mun da mgn ba,muna iya wuni ma daga gaisuwa shikenan,inya fita aiki kuma sai dare zai dawo duk abunda nasan zanyi kafun ya dawo zanyi musu na aje akan dining,har coffee d'insa jarabbabe saina had'a in saka a mug inda bazai huce ba,saboda Ina shiga wani yana yi idan ina cikinsu ba ruwansu soyayyarsu suke sha hankali kwance gabana, shiyasa ban cika zama zan tafi daki In bitar karatuna ko inyi research.

Hamma f fushi yai dani jin cewar wai ina gidan Oga Uhaimid,shiyasa ko a waya ya daina kirana amma zai mun text duk safiya da dare idan nazo bacci, kalamansa masu sanyi da sanyaya zuciya duk da yana Fushi amma kalamansa cike suke da nuna kulawa da kauna, har nakanji kewarsa a raina amma saboda har yanzu ban bashi tabbacin na ansheshi ko ban ansheshi ba shiyasa ban iya maida masa ansar sakonsa,saidai naji har raina ina bashi matsayi mai girma inajinsa sosai tamkar dai Anna ce ta haifesa.

Ranar ana gobe zan koma sch na gama duk abunda zanyi, kafun ya dawo nace mata bari naje na kwanta tunda goma tayi, tace "Watau indai Baby zai dawo baki tab'a zama muyi fira mu duka ko"

Ina murmushi nace "Haba Anti sai kawae inyita zama cikin ku,ai kunason space,kuma ni firar taku ce tayi tsayi har dayan dare baku kwanta ba,shiyasa kawae nake tafiya idona ni baya iya jurewa"

"Ai shikenan Sahaar saida safe to"

Na dawo na shiga wanka ina fitowa naji tsayuwar motar shi cikin compound, na tsaya jikin window d'in dakina ina dage labulen ina hangen shi,yana yinsa ya nuna agajiye yake sosai,iska ake ko ince hadarine ya taso ma don ga d'an yaf yaf nan ina hangowa, d'agowar da zanyi kawae idonsa cikin nawa,cikin wani irin sauri na sauke labulen zuciyata na bugawa sosai,tsoro ya kamani karya tuhumeni leken miye na ke masa,banda wannan ansar saboda nidai kawae na samu kaina da lek'awar.

Shiryawa nai cikin doguwar rigata iya guiwa na saka hularta na haye gadon na kwanta, har lokacin zuciyata bugawa take na dafe kirjina Ina rufe idona.

"Allah ka yayemun wannan bugun zuciyar, duk sadda zan ganshi,duk sadda zanji muryarsa ko turarensa ko wani alamarsa a waje zuciyata tana shiga rud'u sosai,tsoro ne ko fargaba ban sani ba nasan dai Ina tsananin tsoron had'a hanya dashi"

Ina kwancen nai shiru Ina ta sauraren bugun zuciyata naji alamun saukar ruwan sama,k'ara lafewa nayi ina jin sanyin yana d'an karuwa duk da cikin duvet nake,karshe dole na sauko don in kashe Ac d'in............kamar daga sama naji kawae an turo k'ofar dakin, mutuwar tsaye nayi Ina rik'e da remote din Ac har saida ya fad'i saboda razanar da nai,daman kuma bana kashe glubs din dakin saboda tsoro nakeji kwana cikin duhu, tsaye yake cikin suit d'insa daya dawo dasu amma babu ta saman yar cikin ce da wandonsa,yai crossing legs d'insa yana kallona da shanyayun idanunsa, a rikice nake sosai muryata na rawa na mance ma ya nake tsaye gabanshi, "Sa....san...sannu da dawowa Oga"

Bai ansa ba sai kawar naga ya fara takowa zuwa cikin d'akin, idanuna duka a warwaje ina magana cikin in Ina, Ina ja baya zuwa jikin madubi "Me....me..me kake buk'ata,na aje ma komi a dining har....har coffee ma yana a mug na aje...........na dangane da madubi ina jan numfashi da sauri da sauri inajin kamar zuciyata zata faso kirjina ta fito,tun daga fuskarta yake kallonta zuwa kirjinta dake d'agawa sosai saboda numfashin da takeja,zai iya ganin yadda bugun zuciyarta take halbawa sosai, cikin tsakiyar idanuna yake kallo yayin da ya fahimci wasu abubuwa, kusa yai sosai dani ya tsaya yana rungume hannunsa a kirji.

"Miyasa kike tsorona har haka?"

Girgiza kaina nake kawae kamar kadangaruwa, nama rasa abun cewa makoshina ya bushe kirjina bugawa yake,hankalina tashi yake idan yana kusanto kanshi dani.

"Dake nake fa"

Ya fada softly idanunsa suna lumshewa suna bud'ewa akaina, bakina na rawa sosai nace "Don.....Don Allah,kayakuri"

"Inyi hkr kuma?mi kika mun?ko don na kamaki kina lek'ena"

Girgiza kaina nayi,sai kawae naji hawaye sun kwace mun na sadda kaina k'asa,jikina rawa yake so nake ya kauce daga gabana kar jinina yahau.

"Ya salam"

Ya furta a hankali sai yace, "Kukan kuma na miye?"

Kaina dai na girgiza Ina yar shashsheka ina goge fuskata, "Don Allah ka.....ka....katafi"

Murmushi ya d'anyi yace "Dole ai,amma sai kin gaya mun kukan miye kike?na miki wani abunne,ko dan na kamaki kina lekena ta taga"

K'in dago kaina nayi na girgiza kaina, nace "Tsotsayi ne,nazo gyara labulen ne sai na ganka shin......shine kika tsaya kina karemun kallo ko?"

"Aa wlh ba haka bane"

"Hmm,karfe takwas ki shirya na ajeki mkrnta"

"To,nagode"

Daga haka ya fice daga dakin,silalewa k'asa nayi sai na kama kukan rashin sanin abunyi, na ringa tambayar kaina "Why?why?miyasa haka ke faruwa?ya zanyi to ya zanyi!!" Na fada da d'an karfi ina kukan,na dad'e a wajen kafun na tashi na kwanta dan danan bacci ya dauke ni."

"Baby rayuwar Sahaar tausayi take bani sosai,kasan Anna ta tab'a Ammi labarin rayuwarsu har dalilin zuwan Sahaar gida,taga rayuwa yarinyar sosai shiyasa nake tausaya mata inajinta kamar yar uwata,"

Shirin bacci yakeyi yana jinta, kamar baxai mgn ba saida ya gama yace "kowa da kalar jarabawar sa a rayuwa,hakan kuma baya nufin Allah baya sonka ne idan kayi hkr sai kaga ya kaika wani mataki na rayuwa"

"Haka ne sosai ma,shiyasa nake Mata wani fata da adduar yuwuwar wani abu,amma sai da yardarka"

Kallonta yake sosai yace "mikenan?"

"Aa da sauran lokaci idan lokacin yayi zan sanar dakai"

"Kin cika shirme da shiririta"

Ya hau gadon ya kwanta yana jawota jikinsa,zuciyarsa bugawa take tun d'azun baya son ma tana masa mgnr ta, duk wasu plan d'insa rushewa suke,duk wata dauriyar sa warwarewa take kwata kwata ba haka ya tsara ba, ya riga ya barwa Fauzan amma kusancinsu na yanzu yana rikitar masa da kwalwarsa yana sashi ya rikice,kwanciyar ta jikinsa yasa masa yar natsuwa da adduar Allah yasa bacci ya sace shi,abunda idanunsa suka gano masa dakinta dayaje neman haukata shi yake.

Bai samu bacci basai uku saura saida ya samu relief sannan baccin wuya ya dauke shi.

*******

Bamu fita gidan ba sai karfe tara da rabi saboda har na kammala ayyukana da breakfast Anti Jamila tace bai tashi ba, tace mun "karfe nawa kuke tashi?"

"Wlh ban sani ba Anti,amma Ina tunanin zamu iya kai yamma,shiyasa zan dawo da rana na miki girki saina koma........Aa haba dai Baby zai aiko mun da take away,kinsan abinci ma ai ba sosai nake ci ba"

Muna mgnr ne masifaffen kamshin sa ya baibaye wajen,duk freshener dana saka da turaren wuta sunyi gefe sai kamshinsa kawae, k'in yadda in had'a ido dashi nayi na dai gaidashi na tashi xan bar wajen, "Zoki wuce mu tafi mun makara office zan samu abunda naci"

Mukai mata sallama ta rakomu har bakin ,ta bud'e masa ya shiga ta risino tana manna masa kiss, "Love u baby"

Hada ido mukai dashi nai saurin kauda kaina kamar ban gansu ba, "Yace love u too bye"

Maigadi ya bud'e mana mota muka fice daga gidan, Ina gaba yana aikin sarrafa sikiyarin motar, "karfe hudu kuke tashi xan sanya driver ya kawoki office sai mu dawo tare"

Abunda ya fad'a kenan ba tare daya kalleni ba, cikin d'ari d'ari nace "Aa Oga Uhaimid ai zan iya koma wa gidan da kai.........wani kallo ya jefan dashi dole na kame bakina na maida mgnr a cikina, har bakin theater d'inmu yakaini, na fito Ina ce masa "Allah ya tsare nagode"

Har baisan ya lumshe idonsa ba,har cikin ranshi yaji dad'in adduar "Amin ayi karatu sosai"

Sai nayi d'an gutun murmushi "Insha Allah"

Saida yaga shigewa ta sannan ya iya barin mkrntar,zuciyarsa tana wani irin bugawa shin wai ya zayyi ne?Anya zai iya?miyasa zuciyarsa muguwa ce ne?kullum yana addua yana iya bakin kokarinsa na gujewa yana yin da yake gudun amma duk a banza, daga ranar da ta dawo gidansa kullum baccinsa ragagge ne,duk kokarinsa kar Jamila ta fahimce sa amma abun na neman gagararsa, haka yazo ya iske ayyuka sosai na jiransa bai samu sawaba ba sai sha d'aya ya karya sannan,ya kira driver can gida a waya bada jimawa ba yazo,sakon abincin Jamila ya bashi sannan yace ya tsaya restaurant ya siya ma Sahaar lunch itama,amma ya fara kaiwa Jamila sannan ya kaima Sahaar ya koma karfe hud'u ya daukota.

Muna tare da feedo sakon ya iskoni,na kalleta ta kalleni tace "Irin wannan kulawa haka Sahaar,Oga Uhaimid ya sauya"

Shiru nai ina kallon abincin ga lemu da ruwa da naman kaza daban, "Feedo kaina cunkushewa yake akan lamarin su,Hamma F kullum text d'insa na son sanin matsayinsa ne,shi kuma wancen banma San ina ya dosa ba,Ina zan sanya raina"

Ta dafa kafad'ata cikin son kwantar mun da hankali, "su dukan kowa yana sonki,amma ki tsaya ki natsu ki fahimci Ina zuciyarki tafi karkata,........bazan ma iya tsayawa sanin wannan ba,Anna ba zata barni na auri ko guda cikin su ba,Feedo batama kaina lokaci kawae xanyi karshe in shiga cikin whl,shiyasa kawai nake kauce masu amma......amma......"

Sai na sadda kaina idona yai rau rau kamar zan kuka, "Kin cika saurin kuka miye to"

"Oga Uhaimid.....ban.....banson yadda yake shige mun,duk da ya sauya sosai amma indai zamu had'u ko yazo waje jinake kamar in b'ace sbd yadda zuciyata takeyin kamar zata faso kirjina Feedo"

Feedo ta dauko abincin tana ta murmushi bata daice mata komi ba, "muci mu koma lectures"

Har muka koma class banjina daidai kaina ma nakejin yana ciwo,bama fahimta nayi sosai ba darasin,har aka tashi Feedo tace inzo muje Hostel nace "Bari kawae najira anan zai aiko a d'aukeni ne"

"Ki kwantar da hankali karki dora damuwa kizo ki kasa karatu,kije ki saurari zuciyarki ki gane ina tasa gaba,don yana yinki ne ya nuna mun kina son wani daga cikinsu"

Gabana yai muguwar fad'uwa, nace "Wlh ni bana jin son kowa Feedo,amma bazan iya cewa ga dalilin da yasa nakejin wani iri ba,Ga Hamma F yana fushi dani na kuma kasa kiranshi kar yaga cewar na ansa mashi tayinsa ne,sannan inajin tashin hankali in Anna tasan mike faruwa"

"Ki dage da addua da neman zab'in ubangiji"

Haka muka rabu na zauna bar driver yazo ya daukan muka wuce can asibitin,kamar ince masa don Allah ka kaini gida kawae amma ban da wannan karfin zuciyar.

Last free page

300 naira only

*** opay Aisha Abubakar

Saika turo shaida biyanka ta nan ***

Banda kati pls

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol