Free chapter · Read without an account

Chapter one

by Rahinat Hussein (R.Hussain) · TAEESH

___Cincirindon mutane ne cike a wani waje ana ta jimami da al'ajabi, in banda salati da hailala babu abinda ke tashi a wajen.

Innalillahi'wa'inna'ilaihirrajiun! yanzu ɗan mutum aka zo aka yasar anan wajen" wata tsohuwa ta faɗa tana tafa hannuwa gami da kama haɓa. Da sauri Malam Bala ya ɗauki jaririn da aka naɗe cikin zani, yana ta canyara kuka, cikin galabaita.

"Mace ce" cewar Malam Bala, gaba ɗaya manyan gurin suka ƙara ruɗewa, kasancewar safiya ce sosai gari bai gama haske ba, Inna da buhunta na shimfiɗar sallah da ke hannunta ya faɗi tace" Malam Bala ka tabbata mutum ce?" Malam Ashir ya ce" gashi kuwa kina gani Inna" take ta hau tsinuwa da la'antar wanda ya yarda jaririya a mararrarbar hanya cikin ciyayi, abin ka ga ƙaramin gari take maganar ta baza ko ina, guri ya kuma cika da mutane yara da manya.

Ya kamata mu kaita gun Maigari, mutane sai faɗin kawota nan Allah sarki baiwar Allah suke, Inna ce ta karɓeta tana kuma kunsheta cikin zanin, shiru jaririya ta yi, tana sanya yatsa a baki ta na tsotsa idanunta a rufe.

"Tubarakallah ma sha Allahu kyakkyawa da ita" yara aka kora mata suka koma gida.Su Inna suka nufi fadar Maigari.

Kafin su Malam Bala su ƙarasa labari ya iske Maigari Mallam Manu, hankalinsa a tashe ya ke kallon jaririyar yana faɗin" yaushe aka ganta?" Malam Bala ya ce" Allah ya baka lafiya, mun fito daga masallacin da muke sallah ni da malam Lawan, da yake kusan ko yaushe a ciki muke taƙarar karatu, sai muka ji kuka kamar na jariri da fari ma mun aza ko mace ce da goyo, muka duba ba mu ga kowa ba, Malam Lawan ne ya jiyo ta inda kukan yake fita, muna dubawa mu ka ga jaririya a ka ajiye acikin ciyayi tsabar rashin imani".

Innalillahi wa'inna'ilaihirrajiun a wannan garin nawa na Ɗankada aka samu wannan abun?" cewar Maigari. Cikin girmamawa Malam Lawan ya ce" ranka ya daɗe ina so a bani jaririyar nan na riƙe" sai Malam Audi ma ya ce" ni ma zan riƙeta a bani ita" sai Inna ta ce" a'a ni zan ɗauketa ranka ya daɗe".

Wani mutum ne ya ƙaraso tumbar ta Maigari da sauri, yana saɓe da fatanya da alama gona zai tafi, ya faɗi a gaban Maigari yana gaisuwa, Malam Ali kenan, tsawon shekara ashirin da aure bai taɓa haihuwa ba, ya ce" ranka ya daɗe ina neman arziki don Allah a ba ni abin da aka ce an tsinta zan riƙe, a duba wannan alfarman a yi min Allah ya baka nasara" tamkar ruwa ya cinye jama'ar da ke wajen, shiru aka yi kowa yana sauraren hukuncin da maigari zai yanke.

Malam Ali ya shiga share hawaye yana fatan a bashi wannan jaririya shima ya riƙe a matsayin ƴarsa. Maigari ya yi gyaran murya ya na faɗin "Liman ka ji abinda ke faruwa ya za a yi?" Liman ya gyara zama ya ce" Allah ya gafarta ai masalaha za a yi a junansu su sasanta, sai a bawa wanda Allah ya ciyar" Inna ta ce" ranka ya daɗe kar a ce na yi azarɓaɓi to me zai hana a bawa Ali tunda shi Allah bai kawo rabo ba" Liman ya jinjina kai, don gamsuwa da bayanin Inna, hakama Maigari.

Take kuwa koya ya amince da hakan, Malam Bala ya ce" gaskiya ne Inna" ba tare da ja-in-ja ba, kuwa Maigari ya ce" mun amince za mu baka amanar wannan baiwar Allah Malam Ali" take Malam Ali ya hau murna yana faɗin"alhamdulillah nagode nagode Allah ya taimake ka" take Inna ta miƙa masa jaririya,hannunsa na kakkarwa ya karɓi jaririya yana jin duk wata damuwarsa ta yaye, kallon yarinyar ya yi take ya ji wani sanyi na ratsa zuciyarsa.

Malam Garba ya ciro kuɗi har naira dubu ɗaya ya ce"ga wannan a siya mata riga" take aka hau yi masa alkhairi, mai ɗari mai goma, Malam Ali yana hawaye yana godiya, tunda yake bai taɓa jin farinciki irin na wannan ranar ba.

Maigari ya ce zai yo aike gida anjima, Malam Ali ya nufi gida da jaririya a hannu.

Ai matarsa na gyara garken awakai ta ji sallamar Malam,"assalamu alaikum,Ai,Ai kina ina?" fuskarsa cike da annuri, amsawa ta yi tana fitowa daga rumfar, turus ta yi ganinsa da jariri a hannu. "albishirinki" kasa amsawa ta yi, tana kallon hannunsa, dariya ya yi yana kama hannunta ya zaunar a kan tabarmar da ke yashe a tsakar gidan ya ce" Allah ya amsa roƙonmu ya bamu ɗiya ta inda ba mu taɓa zata ba" Ai ta ce" bangane ba" nan ya labarta mata komai, sai ta fashe da kukan murna tana karɓar ƴar wacce ta fara motsi don yunwa take ji.

"Allah mun gode maka, kai ke bawa wanda ka so, kuma ka hana wanda ka so, Allah mun roƙa baka bamu ba, ka bawa wasu bayin naka, sun yi butulci sun jefar, Allah mun gode maka, oh nima zan zama uwa" sai ta sa dariya, cike da tausayin kansu ya ce"kin ma zama, yanzu me zamu fara bata tasha" Ai ta ce" ai malam banga ta zama ba, zuwa zan yi wajen Tasalla ta ba ni magani in samu ruwan nono sai in shayar da ita" ya ce" shikenan ma maza tashi ki je kafin ta tashi" nan da nan ta shirya ta tafi.

Tasallah da tasan komai ta ce ai bata taɓa haihuwa ba, bazata shayar ba, sai dai a dinga bata dafaffiyar madarar shanu, jiki a sanyaye Ai ta dawo, Malam Ali ma bai ji daɗin hakan ba, dole ya nufi cikin rugar Baffa ya samo madara ya dawo, mata sukai ta zuwa ana ganin jaririya.Wasu dan ganin ƙwaƙwaf da gulma suke zuwa.

Bayan kwana bakwai Malam Ali ya siyo biscuits da dabino ya kai masallacin Maigari don a raɗawa ƴarsa suna, Maigari ya bashi zaɓin sunan da yake so a sanyawa jaririya, babu musu ya ce a sa mata Faɗimatu,take aka shelanta sunan, Malam Ali sai ƙwallah, huɗuba ya yi mata da Faɗimatu TAEESH(mai rayuwa cikin albarkar Ubangiji).

Daga gidan Maigari aka aiko da ƙaton rago aka yanka, Ai ta yi kwalliya tare da jaririyarta akai suna mai ƙayatarwa.

Ana fatan Allah ya raya TAEESH.

MASARAUTAR HAUREN GIWA

Tsawon kwanaki bakwai bata san wanda ke kanta ba, hankalin Mai martaba Sarki SUHAID a tashe yake, ganin Fulani Rahama a kwance cikin Comer babu abinda ke motsi a jikinta daga haihuwa gashi anyi nasarar ciro abinda aka haifa amma babu rai, cikin da ya kwallafawa rai yake sa ran ganin gudan jininsa ashe ba mai rayuwa ba ne.

Fulani ta Gabas wacce take uwargidan mai martaba Sarki SUHAID ce zaune a palour ta kishingiɗa da tum-tum irin na gidan sarakai tana shan inibi, sai murmushi take yi, zuciyarta fes sai yanzu hankalinta ya kwanta ganin burinta ya cika na salwantar da cikin Rahama wacce take mata ta huɗu cikin matan Sarki Suhaid.

Tsahon shekaru goma sha biyar da hawan Sarki SUHAID kujerar Mulki, tun bayan mutuwar mahaifinsu Sarki Abdallah, SUHAID shine babban ɗa a gidan, hakan yasa ya gaji Sarautar garin Hauren Giwa Sarki Suhaid ba shi da burin da ya ke so, irin ganin ya haifi magaji, ko da daga ƙwarƙwara ne amma shiru.

Katsam ya ga Rahama ƴar gidan Sarkin Dawakai ya ji yanaso, abin ya zama abin kaico da Allah wadai a masarautar Hauren Giwa, Fulanin ta Gabas, Fulanin Amina, Fulani Zaitun duk ƴaƴan sarakai ne, da ƙarfin mulki ya auri Fulani Rahama, wacce ta zama tamkar Mujiya a gidan don baƙin jini, duk kishin da suke a junansu bai musu ciwo ba kamar yanda ƴar talakansu ta shigo cikinsu.

Rahama mace ce mara son hayaniya kuma ita ce ƙarama a cikin matan mai martaba, shekarunta sha tara a duniya, bayinta da barorinta ma abin ƙyama ne a wajen barorin su Fulani, kyara tsangwama babu wanda ba a yi wa Fulani Rahama.

Wata shida da aurota Allah ya bata rabo, Murna wajen Sarki SUHAID ba a magana, ya dinga kyauta yana raba kujerar Hajji domin a je ayi masa addu'ar Allah ya bara Rahama da cikinta lafiya.

Hankalinsu Fulanin Gabas ya yi mummunan tashi jin wannan labari, take suka shiga bin bokaye da malaman tsibbo domin a zubar da cikin Rahama, haka sukaita kashe dukiya amma babu abinda ya samu wannnan ciki sai ma lafiya da Rahama take ƙara samu.

Sarki kuwa ya tare a wajenta ko da ba kwananta ba ne, haka zai baro turakarsa ya zo dubata komai dare, sai ya yi zuwa uku, huɗu cikin dare don duba halin da take ciki, abin nan na matuƙar ɓata wa matan sarki rai.

Dr.Salim shine amintaccen likitan Sarki SUHAID shi ke kula da Fulani Rahama.

Ranar wata Litinin da safe ya zo duba Fulani Rahama, saƙo ya iske shi, Fulanin Gabas na neman sa, sai da ya gama yiwa Rahama awo gami da bata shawarwari don kula da lafiyarta, a lokacin cikin yana wata bakwai.

Tare suke su uku, kowacce cikin shiga ta alfarma a sashin Fulanin gabas, gabansu cike yake da fruits da gasasshen naman ɗawisu sai tacacciyar zuma a killace, babu motsin komai cikin palour sai sautin AC kuyangu na ta kai kawo a bakin ƙofar, Dr.Salim ya nemi iso, take akai masa, cike da girmamawa ya yi gaisuwa, "zauna sosai mana Doctor" cewar Amina, ɗurƙushewa ya yi a kan carpet yana mai nutsuwa.

"Dr.Salim wana irin ci gaba ake samu game da Rahama da abinda ke cikinta?" cike da jindaɗi ya ce"ai ranku ya daɗe suna cikin ƙoshin lafiya in sha Allahu zuwa wani ɗan lokaci zata sauka lafiy......Kaiii dallah dakata abinda aka tambaye ka daban abinda kake faɗa daban mtsww!" Cewar Ta Gabas,take Dr.Salim ya nutsu yana faɗin "a yi min gafara ranki ya daɗe tuba nake" Fulani Zaitun ta ce" yi masa a hankali mana ranki ya daɗe ta Gabas, doctor ba so muke ta haihu ba, ya za a yi a zubar da cikin da ke jikinta, don wallahi tunda bamu haihu ba babu wacce ta isa ta haihu a gidan nan" ta ƙarasa maganan cikin tsananin kishi" ka faɗi ko nawa kake so a biya ka daga million ɗaya zuwa million hamsin?" ce war Fulani Amina.

Take gumi ya shiga tsattsafo wa Dr.Salim ga ƙoshi ga kwanan yunwa, bakinsa na rawa ya ce" ranku ya daɗe cikin ya yi girman da idan aka ce za a zubar za a iya rasa rayuwarta" to sai me don wannan ƴar takalawan ta mutu sai me?" cewar ta Gabas, Fulani Amina ta ce" ba damuwar mu ba ce da ta mutu ko ta rayu mu dai burinmu shine kar ta haifi wannan cikin da ke jikinta" Dr.Salim ya ce" angama Allah ya ƙara muku lafiya, zan yi duk yanda zan yi don ganin bata haifi cikin da rai ba, amma yanzu ko yaya aka samu matsala mai martaba ba zai bari ba, don yanzu ma ba a ƙasar nan yake so ta haihu ba" juyawa suka yi a tare suna kallon juna, cikin haɗin baki suka ce" to sai a ina?" Dr.Salim ya ce" A Saudiya sai dai Doctor Maheer ɗin baya nan, dalili kenan da ya sa ma ba su tafi yanzu ba, ana sauraren dawowar sa, don ya ce nan da wata biyu zai dawo" kafin wata biyun muke so aikin da muka baka ya kammala" cewar Fulani Zaitun, murmushi ya yi ya ce" a yanzu zan mayarda watannin cikin baya, kafin lokacin an gama komai"

"Good idea hakan ya yi" Cewar Fulani ta Gabas" Zaka iya tafiya, akwai saƙo Hadiza zata baka" Dr.Salim ya yi godiya ya tashi ya tafi.

Tunda Dr.Salim ya koma gida yake sintiri romon kuɗaɗen da aka ambata masa ya kasa barin brain ɗinsa, take ya ji karsashi na cika burin su Fulani ko don ya tsira da mutuncinsa da kuma millions of Naira.

Bayan Sati Uku da faruwar wannan al'amari.

Fulani Rahama da Sarki Suhaid ne zaune suna magana game da tafiyarta Saudiya, "ranka ya daɗe da son samu na ne, a barni na haihu a nan da Saudiya da nan ɗin duk ɗaya ne, fata dai kawai Allah ya sauke ni lafiya" Sarki Suhaid ya yi murmushi yana faɗin" ba tun yanzu na fahimci ba kyason tafiyar nan ba, hakama ƴan uwanki na dai gane kowa so yake a ce shi ya fara ganin abinda za a haifo ko" sun kuyar da kai ƙasa ta yi tana murmushi, ya ɗora da faɗin" okay tunda haka kuke so shikenan, Allah ya raba lafiya" a zuci ta amsa da amin.

SAN DAWAKI FAV

Zaune yake yana rubutu a allo, Inna Laure ta shigo" assalamu alaikum, sannu Malam" waalekissalam yauwa Lamratu, ɗauki allon nan ki wanke shi, don ina zuwa fada zan sa akai mata" Ramlat(Laure) tace" to Malam ni tunda watan nan ya tsaya nake cikin fargaba akan cikin yarinyar nan wallahi, ji nake kamar mutuw.....Cikin hanzari Malam ya ce" a'uzubillahi haba Lamratu wana irin tunani ne wannan ke fa Uwa ce, ke da za ki tsananta addu'ar Allah ya raba su lafiya Mai martaba ya samu magaji ita Kuma Uwata ta samu lafiya amma kike wannan mummunan furuci"

"Allah ya sauketa lafiya, a yi hakuri" ta ɗaukin allon ta hau wankewa, amma zuciyarta na ta tsinkewa...........

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol