Free chapter · Read without an account
25
by Rufaida Umar · ALWASHI
ALWASHI 25 LAST FREE PAGE Assalamu alaikum, domin samun damar cigaba da karanta littafin Alwashi 2 hankali kwance, ka tura ₦500 zuwa asusun dake ƙasa👇🏼 *** Opaybank Ibrahim Rufaida Umar *** Haka Nihla ta cinye hutunta ta tattara ta bar Katsina ba tare da ta samu yadda ta so ba domin ko kallo ba ta isar Areef balle kuma a kai ga wata doguwar magana ta haɗo su bayan amsa gaisuwarta da yake. Rashin ganin fuskar ne ya sa ta kama kanta na dole, sai dai hakan da ya yi mata bai sa ta ji ko ɗarr akan sa ba. Wannan son da kwadayin kasancewa tare da shi da take yi babu abin da ya ragu sai ma wani ƙarfin da ta ji ya ƙaru. A ɓangaren Areef kuwa, ya fara saduda ya bar wa Allah komai ya bar cigiyar Sameera don bai ga alamun nasara ba. A ransa fata yake ya kasance ta yi aure ma kada baƙin fentin da ya goga mata ya hana ta samun mijin aure. Wannan ne ke ƙara dagula masa lissafi idan ya tuno zai iya faruwa. Amma kuma ya tsarkake zuciyarsa ya sa a rai in sha Allahu hakan ma zai tabbata. Yau tun wuri ya tashi ya yi wanka sannan ya fice sashin Mami. Bayan sun gaisa ya dube ta a nutse lokacin da take ba Balaraba mai mata hidima umarnin haɗo masa kayan kari, fuskarta babu yabo ba fallasa, kauda kai ya yi jikinsa a sanyaye. Ya san ɓacin ran bai wuce na tafiyar da zai ƙara yi America a satin da suke ciki. Da ya lissafa sauran masa kwanaki uku a ƙasar kafin ya wuce. Ta zo masa da zancen aure ya ba ta haƙuri, ba domin ba shi da ra'ayin auren ba. Amma bai samu yarinyar da ta kwanta masa ba, ƙarshe yace mata ta nemo masa matar shi kuma zai yi biyayya, nan kuma ta ce bai isa ba, ta fi ƙaunar ya kawo mata don kansa. Rashin jin gamsasshen zance daga wurinsa ne ya sa Mamin ranta ya ɓaci. Koda Balaraba ta ajiye masa tire dauke da kayan shayi sai ko ɗan fulas mai ferfesun nama da dankali. Godiya kawai ya yi mata amma ya kwashi tsawon mintuna biyar bai taɓa ba, hakanan kansa na duƙe a ƙasa bai ɗago ba. Fushin Mami ba ya yi masa daɗi ko kadan. Ita kuwa Mamin kallonsa ta yi ta gefen idanunta, yadda ya sunkuyar da kai ta tabbata ba zai taɓa magana ba, kuma abincin da ba zai ci ba kenan. Duk surutunsa ma a baya yakan yi mata wannan miskilancin idan ya kula da cewar ya ɓata mata rai ballantana kuma yanzun da dalili. Sai ta kauda kai, to me za ta ce? Ita a duniya ba ta da burin da ya wuce na ganin ya yi aure, kuma auren ne ta kula ba shi da niyyar yi. Abu ne dai ya riga ya faru, ƙaddararsa ce. Idan har da shi yake fakewa to fa ba za ta fasa nuna masa fushinta ba. Tun jiyan dai ta riga da ta yanke hukuncin abin yi don haka ta dube shi. "Ka ci abincin sai mu yi magana." Da sauri ya ɗago ya dube ta, idanunsa sun kaɗa. Zurfin da ya yi a tunanin abin da ya shuɗe ne ya haifar da hakan. Maganar Mamin kuma sai ya ji ta tamkar daga sama, yanayinsa ya ɗan taɓa zuciyarta. Ta kauda kai. "Ina jiranka." Daga nan ta miƙe ta ɗauki wayarta ta nufi hanyar ɗaki, ajiyar zuciya ya sauke, bai iya ya ci wani abin kirki ba ya miƙe yana zuci-zucin me za ta ce da shi ya bi bayanta. Waya ya same ta tana amsawa, jin tana yarensu na fulatanci ya sa shi gane da can gida take waya, koda ya saurari kaɗan a zancen kuwa, ya gane da Dada mahaifiyarta take magana, zama kawai ya yi jin batun bai shafe shi ba. Koda suka kammala ta katse kiran, dubansa ta yi a nutse. "A jiya da ka damƙa min zaɓin samar maka matar aure, abin ya ɓatan rai saboda na ɗauki hakan matsayin rainin hankali Areef." Ya dube ta, ta gyaɗa kai. "Eh rainin hankali mana, ko kana so ka cemin kaf yara matan da suke sonka ba ni da labarinsu? Nan ƙawayen ƙannenka ga su nan, a baya wasu dalilin su ganka ne kawai yasa suke takowa gidan nan. Na maka wannan tunin ne saboda ka san cewa ba wai farin jinin ka rasa ba. To wace mace ma za ta ƙi ka Areef? Wata ma ko don arziƙin gidan ubanka ai za ta so ta aureka. Da na yi maka batun aure ba nufina ka yi gaggawa ba, ba kuma nufina ka ba ni zaɓi ba. Kai nake so ka nutsu ka bai wa Allah zaɓi kuma ka tsaida hankali ka bar share ƴan matan da suke nuna maka so, ka zaɓi ɗaya a cikinsu wacce ta kwanta maka, ka kuma yi na'am da tarbiyyar gidansu da ma nagartarta, toh irinta nake so. Yarinyar da abin duniya ba su ne a gabanta ba a dalilin nata iyayen su ma da ƙarfinsu. Ka fahimci hausata?" Kallon Mamin kawai yake, itama ba ta nemi ya ce ɗin ba ta faɗaɗa bayaninta, "Ma'ana ƴar gidan masu kuɗi. Na fi son ƙwarya ta bi ƙwarya, kar ka nemo aure a gidan da suke ƙasa da namu, fannin arziƙi, nasaba da komai ma. Hakan ne kaɗai zai sa ku yi daidai da tsarin juna. Areef wallahi aurenka na daga cikin burikana a duniyarnan, da ace Aishar Fareed tana da ƙanwa na rantse maka da Allah can zan tura ka ka ɗauko min ita saboda ka ga dai ba ni ce mahaifiyar Fareed ba, amma Aisha tana matuƙar nuna kulawarta gareni da ma ƙoƙarin zumunci da ni. Yadda take haka nake son kai ma taka matar ta kasance. Ina maka addu'a koyaushe. Na sani Nihla tana sonka, na kula da duk wasu take-takenta, sai dai salon rayuwarta ba ta burgeni ba, ba na son ka auri wacce ba ka isa ka hukunta ba, wacce iyayenta za su dinga kutse a lamarin aurenku. Rashin ingancin tarbiyyarta ne ya sa ta yi failing a wurina." Mami ta numfasa kaɗan, shi dai Areef ya maida kansa ƙasa kawai yana sauraronta. Ta ɗora da faɗin, "Ba zan hanaka tafiyarka ba, sai dai ban amince ka je ka ƙara zaman da ka yi irin wannan ba, na fi ƙaunar dawowarka a kusa. Idan ka tashi dawo min, ka zo min da zance mai daɗi Areef. Allah ya shige maka gaba, ya tsare ka dukkan sharri. Ya yi maka zaɓin abokiyar zama ta arziƙi." A hankali ya amsa da amin. Ya ƙara kallon Mamin karo na barkatai "I hope kin yafe min yanzu Mamina?" Ta yi masa murmushin da ya fito tun daga zuciyarta. "Ta ya zan yi fushi mai tsawo da kai? Kar ka damu komai ya wuce. Kawai dai kar na ji labarin da ba zai min daɗi ba idan ka dawo." Ya yi murmushin shi ma gami da faɗin, "In sha Allah." Sun ɗan taɓa hira kafin ya miƙe, "Mami bari na je mu yi sallama da Inna daga nan na shiga wajen su Adda Maryama." Ta gyaɗa kai. "Aikuwa akwai saƙon dambun naman da na yi mata sai ka wuce da shi. Muje." Ya bi bayan Mamin sadda ta yi gaba zuwa falon, ba zai iya tuna adadin kyautatawar da Mami ke yi wa Inna ba, kusan idan yace kullum bai yi ƙarya ba. Tun bai yi wayo ba take aiken su Maryama ko Mardiyya gidan Innar. Akan idanunsa ya sha ganin yadda Inna ke kushe kyautukan a baya, daga bisani kuma sai ya ga an samu sauyi ba kaɗan ba, ta sakarwa Maminsa fuska. Tana kuma matuƙar nuna musu ƙauna, koda dai su dama bai taɓa ganin ta nuna musu wata ƙiyayyar ba daidai da sakan. Haka Mamin ta ba shi ƙatuwar leda kakkaura wacce a ciki roba ce doguwa cike taf da dambun naman sa. Yana tuƙin a nutse amma rabin hankalinsa na ga tunanin zantukan da suka yi da Mahaifiyarsa, gaskiya ta faɗa, ya dace ya yi aure. Amma kuma abu ɗaya ne, ba shi da wani ra'ayi na cewa lallai sai ya auri ƴar masu kuɗi. Ya yarda so ba ya duba arziƙin mutum ko talaucinsa, kai shi so bai ma san asalin mutum da rashin asali ba, bai kuma san wani abu mai suna dace ba. Ya aminta so ba shi da yare na kansa. Koda ace bai taɓa tsintar zuciya da gangar jikinsa a cikin yanayin ba, ya san abu ne mai wuyar sha'ani da zai wahala a yi masa iyakar inda kaɗai ake son ya afku. Har ya ƙarasa gidan Inna bai bar saƙe-saƙen zuci ba. Ita ɗin ma jin zai koma Amurka ta hau bambamin faɗa. "Na gaji da ganinka kana yawo a sama kamar wani tsuntsu kai ɗaya Balarabe, daga wancan ƙasar sai wannan garin, su iyayen naka sun zuba idanu sun bar ka da ra'ayin kanka. To zan samu shi Sada ɗin don ya saka a binciki lafiyarka, amma ace mutumin da ya haura talatin har yanzu ko zancen aure ba ya yi kuma an ƙyale shi. Koda dai ga Babanka Dakta can ma, ko shi sai ya duba min lafiyarka kafin kuma na san matakin ɗauka, don na rantse auren dole zan maka, a kanka za'a fara a dangi." Idan da abin da Areef ya jima bai yi shi, to fa dariya ne. Maganar Inna ta ba shi dariya sosai da har sai da ya dara ɗin, ta yi galala tana dubansa. "Ja'iri, dariya ma na baka kenan? To madallah. Ko haka kaɗai ya nuna min lafiyarka sumul kawai boko ka aura. Ai shikenan tunda ka fi ƙaunar ƙasa ta rufe min idanu ban ga ƴaƴanka ba." Areef dai hularsa ya cire yana shafar kwantaccen sumar gashinsa wanda ya ƙara ciccikowa sosai har ya ɗan yi tudu. Yana murmushi yake duban Inna kafin ya ce. "Ba za ki mutu ba ki gan su ba Inna. Ku taya ni addu'a, bana son na yi gaggawar da zai zame mana dana sani gaba ɗaya don Allah. Ki taushi zuciyarki, ki kara tausar ta iyayena, in sha Allahu zan kawo muku wacce zan aura nan kusa. Aure da mutuwa duka lokaci gare su, ina roƙon Allah ya ba ki tsawon ran da za ki ga auren Balaraben nan naki har ma ki ɗauko bebinsa." Ta yi dariya, "To ai shikenan, kai dai ka iya siye mutum da baki. Allah ya zaɓa maka abokiyar zama ta gari. Na so ace ko wurin Gwaggonka Falmata ka duba cikin ƙannenka ai, to yaran yanzu ne ba a musu dole." "Ke dai ki cigaba da roƙa min zaɓin Allah kawai. Aure zan yi shi in sha Allah." "Allahu ya sa." "Amin." Ya amsa da murmushi. A gidan Inna ya ci abincin rana ya yi sallah sannan ya wuce gidan Adda Diyya wacce ta fi kusa da Inna kafin ya je ga Maryama. Dukkansu dai zancen ɗaya ne, ya kuma kula babu wacce ta mishi batun Sameera. Ba kuma wai don ba su san abin da ya farun ba ne, sai dai kawai ya lura Mami ta hana kowa tada zancen ne. Idan akwai wasu abokan shawarar Mamin, to ya biyo bayan su biyun idan ka ɗauke Dada. Ranar da zai bar ƙasar, ya shiga da safe yi wa matan Abba sallama. Hajja ta kasa ɓoye baƙin cikinta a fili ta dube shi ta ce. "To, ya dai kamata ka bar zama cikin jajayen fata babu aure. Rayuwar nan ba zai yiwu baligin namiji ya dinga zama babu aure ba musamman ma kai ɗin nan wanda an san komai da ya faru ya janyo silar ɓacewarka daga ƙasar nan. Koda dai Salma da Abban naka sun rufe batun, amma hakan ba zai sa mai hali ya fasa ba. Auren dai shi ne cikar kamala ba laluben na banza ba." Maganganun sun dake shi ainun, ya yi wa Hajja farin sani na irin ƙiyayyar da take mishi, ya kuma fahimci tana iyakar ƙoƙarin ganin ta danne amma hakan ya faskara. Waɗannan zantukan nata sun mishi ciwo ainun don haka ya ɗago kai yana mata wani kallo mai kaifi da tarin ma'anoni, hakan ya sa Hajja kauda nata kan gami da miƙewa tsaye. "Allah ya kiyaye hanya, bari na ƙarasa ciki aiki nake." Ba ta jira cewar Areef din ba ta fice a falon zuwa uwar ɗaka tana doka murmushi, ko babu komai ai ta rage wani zafin da ya tsaya a maƙoshinta. Ya miƙe ya fice daga falon zuciyarsa na tafarfasa, gaba ɗaya ya juye daga Areef ɗinsa wanda Mami da Abba suka samu ya fara sassautowa zuwa ainahin wanda yake kallon kansa a mai laifi tsawon watannin baya. Mami da Fareed dama su Benazir da suke tsaye a farfajiyar gidan tana jira ya fito su ƙara sallama. Ta hango shi ɗin, cikin shigarsa ta yadinsa dark blue, duk da irin haskaka shi da kayan suka yi amma fuskar Areef gaba ɗaya babu ɗigon annuri. Ta yi mishi ƙuri da idanu har ya ƙaraso bayan ya rufe idanunsa da baƙin gilashi. A hankali ta riƙe hannunsa ta yi amfani da ɗayan ta cire gilashin da ya rufe kwayoyin idanun, yadda suka kaɗa ne ya tabbatar mata ya shaƙi marar daɗi a wurin Hajja. Murmushin ƙarfin hali ta masa kafin ta ce, "Annabinmu Muhammadu s.a.w, shi ya fi kowane bawa daraja da matsayi a wurin Allah, ya fi mu ɗaukaka, nasaba da ma ƙarfin kusanci a wurin Allah. Ya fi kowa haƙuri, gaskiya, riƙon amana da son a zauna lafiya. Hakan bai saka maƙiyansa sun so shi sun ƙauna ce shi, cikin maƙiyan nan har da na jikinsa, yan uwansa. Da lamarin ya tsananta sai da ya yi hijira zuwa Madina ya bar mahaifarsa da yake so wato Makkah. Idan har Annabi mai daraja zai fuskanci jarrabawa har haka, mu su waye Areef? Ka yi haƙuri, ko me ka ji ko ka gani, ka ɗauki hakan matsayin dama can Allah ya ƙaddara sai an furta maka ɗin. Maza yi min murmushin nan naka." Tun ma kafin ta kai aya ya murmusa ɗin, Maminsa kenan. Idan ta yi wani abin sai ta sosa ransa, idan kuwa aka juya ta wani fannin, sai ya ga kamar ba Maminsa da a wasu lokutan take da son kanta da ma zuciyarta ba. Dama an ce duk wani ɗan adam tara yake bai cika goma ba. Ya kama hannunta ya sumbata. "Sanya albarkarki da na Abba kaɗai sun ishe ni a rayuwata Mamina." Ita ma murmushin ta yi gami da dafa kansa tana mai shi mishi albarka da kuma nema masa tsari daga shaiɗan da danginsa. Daga haka suka yi sallama ya shiga motar zuciyarsa a wanke fes kamar ba shi ba. Nan suka kama hanya zuwa garin Kano, direban Fareed ke jan su, inda a can ne zasu hau jirgin da zai tsaya a Dubai kafin su ƙarasa Amurka. *** BAYAN WATANNI BIYU... Ta tashi da jin wani irin kuzarin jiki da ma zuciya, ranta fari ƙal yake a yau. Ta kammala shirinta tsaf cikin doguwar rigar abayarta kalar sea green da aka yi wa zanen ja da baƙin fulawoyi. Ba ta yi kwalliya ba ko kaɗan amma kuma fuskarta ta yi kyau ainun. Fatarta ta yi wani irin murjewa, ta ɗan ƙara ƙiba kaɗan wanda bai sa ta muni ba, hakan ma sai ya ƙara sanya duk wasu halittunta fitowa suka kuma zama masu fisgar samari gareta. Dalili kenan da ba ta cika fita daga gidan ba. A gaggauce ta yi rolling mayafin abayarta ta ɗauki jakarta baƙa ta dan rike a hannunta tare da wani tafkeken gilashinta baƙi wuluk. Takalminta mai tudu ta zura sannan ta ƙara feshe jikinta da turarukanta masu sanyin ƙamshi. "Laila kina ina ne? Kada fa rana ta yi maki." Muryar Momi Fannah ta ji daga falonsu, da sauri ta ɗauki babbar wayarta da ma ƙarama mai torchlight dake saman gado ta fito. "Momi na kammala." Momi Fannah ta dube ta, "Kuma kin yi kyau abinki kuwa, kada fa a je wani malamin naku na firamare ko sakandire ya ƙyasa." "Kai Momina." Ta yi furucin cike da shagwaɓa, suka yi dariya lokaci guda. "Nima wasa nake, Laila sai ɗan mai faɗa a ji ko mai faɗa a ji din in sha Allahu." "Uhum." Shi ne furucin da Lailar ta yi kawai tana wani ɗan murmushi. Nan suka fito, falon Alh Mu'az suka ƙarasa ta yi mishi sallama, ya ɗauki kuɗi ya ba ta wai koda za ta nemi wani abin a hanya. Ta karɓa ba don ba ta da shi ba ta yi godiya. Daga haka ta fito ta shiga wurin Gwaggo Samha, nan ma fatan alkhairi ta bi ta da shi da ƙara jaddada mata yin addu'ar matafiya. Ta amsa da toh. Tana fitowa ta iske direbansu Malam Nasir yana jiranta a farfajiyar gidan. Bayan sun gaisa ta shige bayan motar ya ja suka fice a gidan, sai garin katsina! *** KATSINA "Welcome to Katsina." Wannan marhaban da ta gani a farkon shigarsu garin sai da ta ji ƙirjinta ya harba, ta daure ta lumshe idanu tana ambaton sunayen Allah, abubuwan da koyaushe ke binne a cikin ranta suna dawo mata daki-daki. A karshe ta numfasa ta shiga yi wa Mlm Nasir kwatancen inda suka nufa. Ba ta ko yi gigin kallon hanyar tsohuwar unguwarsu ba balle ta ji kwaɗayin shigarta. Kai tsaye makarantar da ta yi firamare da sakandire ta shiga wanda duk a haɗe suke sai dai kowanne da ɓangarensa. Ta ci sa'ar samun nasarar abin da ya kai ta, tun ƙarfe goma na safe suka isa, amma cikin ikon Allah wuraren ƙarfe ɗaya ta kammala. A nan cikin makarantar ta samu wuri ta yi salla, Mlm Nasir shi ma ya tafi sauke nasa faralin. Sai da ta jira ya je ya ci abinci da kuɗin da ta ba sa, ita kuwa ta nemi ƙasan wata bishiya ta zauna tana kallon yaran da ke fitowa an tashe su. Hasko kanta da yar uwarta Sameera ta yi a hanyarsu ta komawa gida, irin yadda take jan tsokana ta bar Sameera da cin duka ya dawo mata, irin yadda take kama duk waɗanda suka doki Sameera ta bi su da yakushi da cizo duk suka dawo kwanyarta tamkar yanzun ne abin ke faruwa. Ta dubi ƙasan bishiyar mangwaron da take zaune, hawayenta suka cicciko, sun sha zama a nan ita da Sameera, su siyo awara su ci abin su, ko fara, ko kuma wainar fulawa da su rake. Yau ga ta nan ta zo karɓar musu satifiket na makaranta don har na Sameera ta karɓa, amma babu Sameera a raye. Shikenan rayuwar ta ƙare, Sameera ta zama tarihi. Ta share hawayenta jin da ta yi ana hon. Duba ta kai ga wajen, Mlm Nasir ne ya dawo don haka ta miƙe jiki a saluɓe ta kakkaɓe rigarta hannunta riƙe da katon envelope na takardun da aka ba ta sai ko jakarta ta buɗe gidan baya ta shiga. Har sun fita daga makarantar ta ji tana son shiga unguwar Barhim, koda sau ɗaya ne, tana son ta yi tozali da gidan da ta ci alwashi a kan Maigidan da ma matarsa. "Mlm Nasir idan ba damuwa za ka kai ni wata unguwa ne, akwai wacce nake son mu gaisa." "Ah ba damuwa Laila, ai an ma yi sauri. In sha Allahu ba zamu yi tafiyar dare ba." Ta yi godiya, nan ta shiga yi masa kwatancen unguwar, koda suka shiga ta dinga bin gidajen layin da ta riƙe cewa tabbas nan Sameera ta taɓa yi musu kwatancen tana zuwa kitso har ma ta yi mata caa a lokacin ta nuna ita ba ta son ji, tabbas ta gane layin don haka ana zuwa ta dakatar da Mlm Nasir. "Ɗan faka a nan, bari na shiga na fito yanzu." "To mu ƙarasa ciki mana ko?" Ya faɗi yana dubanta, har za ta amsa da to sai kuma dai ta girgiza kai. "No, ba jimawa zan ba. Ina zuwa." Ba ta jira amsarsa ba ta dauki jakarta bayan ta rufe idanunta da gilas ta buɗe motar ta fita. A hankali take takawa tana shiga layin har ta ƙarasa daidai ƙaton ginin gidan wanda daga shi babu wata hanya, kuma layin ba ya ɓulla, ko ba ta tambayi kowa ba ma, ga shi nan a rubuce an rubuta Alh Sada's Residence a jikin wani ɗan allo da aka yi wa adon baƙi da ruwan zinare. Ba ta ƙarasa ba sai ta yi tsaye cak tana kallon ƙaton ƙyauren gidan da tunano abubuwa da dama da suka shuɗe a rayuwarsu amma ba a cikin ƙwaƙwalensu ba. Ya sanyo hancin motarsa cikin unguwar tasu, ransa gaba ɗaya a jagule yake sakamakon matarsa Hadeeya da ya koma ya iske ta yi kaɗawarta yawon ba ta gida, ya kira a waya sun zagi juna iya zagi kafin a fusace ya taho wurin Hajja don samun abinda zai sa a cikinsa. Kamar an ce ta kalli gefensa, daidai sadda ta sa hannu ta cire gilashin idanunta. Suka yi ido huɗu da shi. Zakari ji ya yi sitiyarin na neman ƙwacewa daga hannunsa, ita kuwa ɗaure fuska ta yi ba ta ji ko ɗarr ba don ba ta ma san waye ba, ta san dai gidan ya nufa tunda babu hanya. Kawai sai ta juya ta soma takawa za ta bar wurin. Cike da zafin nama ya tsayar da motar a gefe ya kashe ya fito da sauri har yana tuntuɓe, Laila ba ta yi aune ba ya sha gabanta. Ta tsaya cak tana kallonsa da rinannun idanunta da suka ƙara ƙanƙancewa. Kallon da ya ƙara tunasar da shi tabbas ita ce. "Sameera! Dama kina garin nan?!" Ta ƙara dubansa a nutse, ya san Sameera har haka da bai kasa mance fuskarta ba? Bai ga wani abu da ya sa ta sauya ba? Ta tuna Sameera mai faran faran da son mutane, amma ta sani ba ta da sakin jiki da maza. To ko ɗan gidan ne? Amma kuma haka a hargitse? Ta tambayi kanta, sai kuma kawai ta gifta shi za ta wuce ya yi saurin ƙara magana. "Sameera kar ki tafi ki bani dama mu yi magana, na san wanda ya yi raping ɗinki a gidanmu." Wannan ya tsayar da Laila cak! Ƙirjinta ya shiga bugu da sauri-sauri. Ta juyo lokaci guda tana dubansa, wannan karon har wasu ƙwalla ta ji sun cicciko mata. Shi kuwa Zaks da ke ƙaremata kallo ganin yadda ta ƙara cika fiye da baya, ga wani kyau da ta yi. Sai a ransa ya shiga tunanin ƙila ƙofar karuwanci Areef ya buɗewa Sameera da ya kwanta da ita. "Ta ya aka yi ka sani?" Tambayar da Laila ta jefa masa kenan. Ya shafi sumarsa yana duban hanya, "Na san komai, babu abin da ban sani ba akan abin da ya faru da ke na rashin adalci da zalunci. Idan har kin shirya ni ma na shirya taimakonki ta kowace hanya matuƙar za ki kwatarwa kanki haƙƙi. Yanzu muna hanya, da za ki yarda mu je mu nemi wani wurin mu yi maga..." "Ka na tunanin zan ƙara yarda da wani mahaluƙi dake cikin gidan Alh Sada? Never." Ya yi murmushi. "Ki yarda da ni Sameera, ina maki rantsuwa da Allah zan taimaka maki, ni da mahaifiyata mun jima muna nemanki domin mu taya ki kwatar haƙƙinki. Ki bani dama Sameera." Ba ta ƙara uffan ba bayan tsakin da ta ja tana mai jin kamar ta kifa masa mari domin ita ta fi ƙarfin waninsu ya yaudare ta. Ta cigaba da tafiya don akwai ƴar tazara da inda ta saka Mlm Nasir ya yi fakin kaɗan. Shi kuwa juyawa ya yi a gaggauce ya buɗe motarsa jiki na rawa don baya so ta kufce masa a wannan karon, dama ce suka samu shi da Hajjansa. Kai tsaye takarda ya laluba ya yaga ya fiddo biro a aljihun gaban rigarsa ya rubuta duk lambobin wayarsa guda biyu. Da sauri ya rufe motar ya mara mata baya, lokacin har ta fice daga layin. Ya dinga bin ta har ta kai motar da ta kawo ta bata saurare shi ba. Kawai tana shiga za ta rufe ya riƙe murfin wanda hakan ya sa Mlm Nasir faɗin. "Malam lafiya?" Zakari ya dan kalle shi sannan ya maida duba ga Sameera bayan ya ƙara tabbatar da zargin wani mai danshin ta samu har da yake ba da mota ta yi yawonta a ciki. Dole Sameera ta yi wuyar gani ashe. Ita kuwa Laila kallonsa ta yi ranta a tsananin ɓace, kafin ta yi magana ya ajiye mata takardar saman jakarta dake kan cinyarta. "If you are set on getting your revenge take my number call me anytime I’ll be ready. The name is Zakari Sada Bakori." ( Idan kin shirya daukar fansa, ga lambata nan. Duk sadda kika kira a shirye nake na taimaka maki Sameera. Sunana Zakari Sada Bakori) Daga haka ya rufe murfin motar ya na ɗan ɗagawa Malam Nasir hannu. "A yi haƙuri Baba." Daga haka Laila ta ba Malam Nasir umarnin su tafi. Shi kuwa Zakari ya bi lambar motar da idanu, ƴar dariya ya yi a fili ya ce, "Ah ka ga manya, ashe Kano ta koma da zama? Nice one Sameera." Daga haka ya yi gaba yana jin zuciyarsa a wanke fes, ya sani yau babban albishir zai je ma Hajja da shi. *** Ranar gaba ɗaya Laila kasa baccin kirki ta yi, ta zurfafa cikin tunani. Wannan fa dama ce ta zo mata a sauƙaƙe, sai dai kuma tunaninta dole Zakari yana da tasa manufar. Tunani barkatai ta dinga yi a wannan daren, har a ƙarshe ta yi wani ƙuduri a ranta. Washegari bayan ta tashi da safe, ta jawo wayarta da jakarta, takardar da Zakari ya rubuta mata lambobinsa ta fiddo. Ɗaya a ciki ta ɗauka ta rubuta masa gajeran saƙo ta tura. Daga haka ta koma bacci bayan ta saka wayarta a silent domin bacci ne fal a idonta. *** A can kuwa Zakari yana tashi ya dauki wayarsa jin shigowar saƙo, wannan ne saƙo sama da ashirin daga jiya zuwa yau da ya duba amma sai zuciyarsa ta karye saboda ba daga wacce yake zato ba ne. Sai dai me, wannan karon abin da ke ƙunshe cikin ƙaramin text din ya kusan gigita shi saboda murna. "I’ve made my decision Zakari. It’s time. Give me the plan." (Na shirya ƙwatarwa kaina haƙƙi. Ina sauraron shirinka) Wannan ne kaɗai abin da ta rubuta a saƙon. Bai yi wata wata ba ya kira Hajja a waya. Tana ɗauka ya yi wata dariya, ita ma sai ta taya shi kafin ta ce. "An dace kenan?" Yana dariyar ya amsa "Yes Hajja, mun dace." Suka ƙara darawa. "Sai ka zo mu san shirin da zamu yi kafin mu yi joining hands da ita. Yanzu aka fara wasan. Madallah da Sameera." Daga haka suka katse wayar ransu fari ƙal. ƘARSHEN FREE PAGES KENAN NA ALWASHI. *** TO FA! Shin me Hajja da Zakari ke ƙullawa? Ga dai Laila za ta haɗa kai da su, ya ya kuke ganin wasan zai kasance? Ta ya ya za su ɓullowa Areef? Ya kuke hango haɗuwar Areef da Laila? Laila ga dukkan alamu ta zo musu matsayin Sameera, kuna ganin haƙanta zai cimma ruwa? Haidar fa? A gefe ga Alh Affan wanda ya ci alwashin kashe Kubra mahaifiyar Laila? Ina mahaifin Laila da Sameera ya shige? Duk ku biyo ni a Alwashi 2 don jin yadda za ta kasance. Da Naira ₦500 kacal dinku za ku shiga group dina na Telegram a ƙarƙare wasan tare da ku. Soyayya, tausayi, nadama, da ma baƙin ciki iri iri, babu wanda ba za ku tsinta a tafiyar Alwashi part 2 ba. Kuna iya payment ta wannan asusun: *** Opaybank. Ibrahim Rufaida Umar Ku ƙara 0 a farkon lambar ku turo receipt. Taku har kullum; RUFAIDA UMAR