Free chapter · Read without an account

36

by Saliha Ahmad Na'ibi · REINA

36......da farar asuba Kamal suka iso, Saudat dake zaune saman darduma tana zikirin safiya tayi saurin miƙewa a kiɗime ganin suna tafe har da goggo halime tabbas wani mummunan abu ne ya samu Yaseer.

A maimakon ta amsa sallamar su sai cewa tayi "Allah yasa ba mutuwa yayi ba" ƙoƙari take ta sanya ma kanta dangana koma menene ya faru ta ɗau na annabawa, duk da haka burin ta bai wuce su ce mata A'a abinda take tunani ba haka bane.

"Kinga kwantar da hankalin ki, yana raye kuma zai kasance cikin aminci da izinin Ubangiji, yanzu bari mu samu muyi sallah sai muje mu duba shi ko?!". Goggo ta faɗi yayin da take ƙarasowa ciki, sai gaban Saudat ya ƙara tsinkewa.

"Goggo hatsari yayi?" Daga jin muryar ta zaka san a shirye take ta fara kuka, tausayin ta ya hana goggo cewa komai.

Kamal ya umarci Suhail da ya kawo masa ruwan alwala sannan ya tsuguna ya fara duk suka bar ta tsaye da gudun zuciya, gashi Kamal yaƙi yarda ko haɗa ido suyi.

"Hatsari ne ko?" Ta sake tambaya da muryar da tafi na farko rauni.

"A'a ba hatsari yayi ba. Yana hannun folisawa aka ce amma komai lafiya, ki kwantar da hankalin ki" Kamal ya amsa ta.

Ta kwantar da hankalin ta? Tun da suka maimaita har sau biyu dole abinda zata gani ya ɗaga mata hankali.

Don haka a sukwane ta jira suka idar da Sallah lokacin gari ya fara haske. 
bata basu damar addu'a ba tace "toh bari na je na tsare mana napep"

"A'a Saudatu, yayi wuri da yawa ba za'a samu abin hawa yanzu ba, sannan Yaseer ɗin zai buƙaci abin karyawa, ki haɗa sai mu tafi masa da shi"

Ta amsa goggo da "toh" Cike da jin daɗin cewa zai iya cin abinci ta miƙe ta shiga kitchen. Akwai ajiyayyen tuwon da tayi niyyar ɗumama musu da safiyar amma sai ta kwaɓa mishi ɗanwake na musamman ganin tana da sauran flour.

Sai da ta gama ɗanwaken ta zuba a food flask ɗin shi kafin ta ɗaura musu ɗumamen tuwon.
haka dai kowa ya taɓa sama-sama, duk yanda yaran suka so bin su goggo ta hana don ko su basu san me zasu je su ji a kan dalilin rufe Yaseer ɗin ba.

Tun daren jiya Kamal ya tambayi masu gadin gidan station ɗin da aka rufe Yaseer, don haka kai tsaye can suka nufa ba tare da sun tuntuɓi Alhaji Tahir ɗin da ya saka aka rufe shi ba.

.....

Kaman jiya ne Alhaji Tahir ya ziyarci Alhaji Abdou a lokacin da ya rasa Malika, shima yau gashi ya ziyarce shi a dalili makamancin sa.

Ya ɗauka Alhaji Abdou ya kiɗime a lokacin da ya rasa uwar Aicha, amma shi kuka yake da hawayen shi a rashin majinginar zuciyar shi, ba ta Reina ko Maama yake ba.

Sosai ya bawa Alhaji Abdou tausayi, rashi har guda biyu a lokacin ɗaya ba wasa ba. 
Amma ana buƙatar yayi ma Fauziyya gata ya sallace ta ya kai ta makwancin ta.

"Da ace na samu damar tunkarar ta a kan abinda ya sami Hafsatu, da ba zan taɓa yafewa kai na ba" zaune yake a dandamalin ƙasa hannun shi riƙe da kai, yana ji kaman ya ajiye shi ya huta da tunanukan da ƙwaƙwalwar shi yake faman kawo mishi. 

Ya zalinci Fauziyya, ya ɓata mata, ya shiga hakkin ta, amma bai samu damar roƙonta ta yafe mishi ba, gashi ta tafi lokaci ɗaya babu notice. yana tsoron Allah ya ɗaga su a ranar alƙiyama tana ƙullace da shi.

"Allah ya gafarta mata, ya yafe mana baki ɗaya. Amma sai ka jure Tahir, na sani akwai zafi, akwai ciwo amma bata buƙatar komai a halin yanzu bayan ka sada ta da gidan ta na gaskiya sannan ka bita da addu'a"

"Fauziyya na yafe miki, Allah ya yafe miki, Allah ya haɗa fuskokin mu a gidan aljannah."

"Ameen, In sha Allah "

.....

Bayan dogon roƙo da suka yi, da bayanin da aka musu wanda ya ɗaure musu kai, da ƙyar suka samu aka basu daman ganin Yaseer. domin sai da suka ga alamun Saudat tana niman sume musu a wurin.

Da ƙyar yake iya takawa don ji yake yi kaman sunyi mishi targaɗe a ƙafa, yana tafe suna angiza ƙeyar shi har idanun shi da suka kumbure suka shiga na iyayen shi da kakar shi, kamannin fuskar shi ya sauya baki ɗaya.

Kukan da Saudat ta riƙo kayan ta tun daga gida sai yanzu ta samu damar sake shi ganin yanda ɗan nata ya dawo a wuni ɗaya kawai.

Shi kuwa Yaseer ganin hawaye a idanun mahaifiyar shi ya tsotse nashi baki ɗaya, babban baƙin cikin shi a duniya shine ya zamo silar kukan iyayen shi.

Kuka take yi tana sheshsheƙa har sai da numfashin ta ya fara sama-sama, dama Kamal a shirye yake ya shiga shaƙa mata inhaler daman ya san hakan zai faru.

Yaseer da tsayuwa ya gagare shi saboda tsananin yunwa ya tsuguna a gaban Saudat ya riƙo ƙafar ta, amma sai tayi saurin kwacewa tana maida numfashi.

"Ka ji tsoron Allah Yaseer, hukuncin duniya kenan ina ga wanda Ubangiji zai yi maka mai tabbatuwa a ranar da muma ta kanmu muke yi? Idan ka ƙaryata zan yarda da kai amma ka sani ka ci amana ta irin cin amanar da ba'a taɓa min irin shi ba, kuma ba zan taɓa yafe maka ba. ko da ban sani ba Allah ya sani Yaseer, ko dan ban gani ba Allah ya gani, ko da ban ji ba Allah ya ji, kuma bayi barin hakkin wani a kan wani komin kashin sa. Kayi ma kan ka gata ka faɗi gaskiya, mai ita bayi taɓa taɓewa, zata wahalar da kai amma na ƙanƙanin lokaci ne, sai dai idan ka zaɓi kayi ƙarya wahala ta har abada ya tabbata a kan ka." Kalaman ta ke harɗewa don haka ta tsaya ta ja dogon numfashi ta fesar da shi kafin ta ɗaura da.

"Ba don ni ba, sai don wanda ya isa da kai da zuciyar ka, mai hukunta wanda yayi zalunci kuma gatan wanda aka zalunta..... Yaseer ka taɓa musu ƴa? Kana da laifi a kan abinda ake zargin ka da shi??"

Baki ɗaya bakin sa a fashe yake, don haka zafin tauna laɓɓan shi da yayi ya ratsa har cikin ƙwaƙwalwar shi.

"Wallahi Umma, na rantse miki da sarkin da babu wani bayan shi, na rantse miki da wanda tsaron rai na da lafiya ta yake hannun shi, Wallahi Wallahi ban yi ma Hafsatu komai ba, ban taɓa yunƙurin ketare iyakokin da Ubangiji ya gindaya min a kan cikakkiyar mace ba ma balle yarinyar shekara tara Umma. Hafsatu ƙanwata ce, na ɗauke ta yanda na ɗauki su Sabir da Irfan, ƙoƙari na a kullum shine in kare su daga cutarwa, ta yaya za'ayi ni kuma da hannu na in cutar da su?"

Bata bari ya sauƙe numfashi ba tace "Na yarda da kai. Idan ka yi min ƙarya ka cuci kanka Yaseer."

Ɗagowa yayi ya kalle ta cikin ido, tabbas ya gani, yardar da tayi da shi ɗari bisa ɗari don haka ya dubi mahaifinsa shima hakan ne, haka ma kakar shi, don haka zuciyar shi yayi mishi sanyi.

"Umma" ya kira Saudat.

"Na'am Yaseer" tayi ƙoƙarin saka murmushi a kan fuskar ta duk da hawaye bai daina mata zuba ba.

"Umma yunwa nake ji, amma ba zan iya saka komai a ciki na kina min kuka ba. Ina tsoron azabar Allah Umma, soyayyar shi kawai nake so"

Sai ta murmusa tana share hawaye da ƙasar hijabin ta. "Allah ya so ka ɗana, Allah ya ƙaunace ka, Allah ya ji ƙan ka yayi maka rahama ba sai ka mutu ba"

Da ameen ya amsa sannan suka fito mishi da food flask ɗin da suka zo da shi. Nan ma sai da aka yi daru da police, Kamal ya ɗan miƙa musu wani abu kafin suka yarda suka bar shi ya fara cin abincin. Sun fi so su luguiguita shi ne sosai yanda idan Alhaji Tahir ya zo zai ji daɗi yayi musu alheri.

A baki Saudat take bawa Yaseer abinci yana karɓa da wani zaƙuwa kamar zai cire mata yatsu, ita tsoron fama masa ciwon bakin shi take ji.

Kamal ya bari har sai da ya tabbatar da ya fara dawowa cikin hayyacin shi kafin yayi masa tambayar ya labarta musu ainihin abinda ya faru, yanda aka yi aka haihu a ragaya.

"..... Allah da bakinta ta amsa min. Jamal ne, Yaron gidan da nake zuwa in yi mishi lesson, kuma a tambayi Aunty mahaifiyar ta, na fara mata zancen mahaifiyar Jamal ɗin ta fito ta katse mu, ko ita Hafsatun ma a tambaye ta"

Kamal ya numfasa "Shikkenan, ni bari na je gidan Alhaji Tahir ɗin goggo, in same shi ko ita Hajiyar ma idan bayi gida, idan abu ya gagara kuma sai ki zo amma bamu fatan hakan"

Babu daɗewa suka sake tasa ƙeyar Yaseer zuwa ciki, kamal ya bada kuɗin magani da kuma dressing ɗin ciwon Yaseer ya dinga haɗa su da Allah su taimaka, dukkan su ƴan uwa ne kuskuren fahimta aka samu sai dai zasu warware komai nan ba da jimawa ba.

Sun dai ji shi, amma suna tafiya suka raba kuɗin a tsakanin su. 

Kamal ya fara saka goggo da Saudat a napep su tafi gida kafin ya tsari mashin ya ɗauki hanyar gidan Alhaji Tahir, ya riski unguwar ma gabaki ɗaya bata shiguwa da abun hawa.


......

Da ƙyar Alhaji Abdou ya lallaɓa Alhaji Tahir ya ɗauro alwala ya fito, yana tafiya kaman zai kifa.

yana fitowa yawan mutanen da ya gani ya saka shi sake rushewa da kuka, Ciki da wajen gidan ya cika maƙil.
Dandazon mutanen da ya gani sun zo su sallace Fauziyya ya ƙara narkar da zuciya da ruhin shi, karkarwa yake yi a yayin da ake yin ƙabbara ma Ubangiji a Saboda wa'innan halittu guda biyu da ya busa musu rai a lokacin da yaso kuma ya ɗauki ɗayan ba tare da ya shaƙi iskar duniya ba ma.
 
A cikin ƙanƙanin lokaci har sun kasance kamar ba'a yi ba, sun dawo tarihin da idan Reina ko Maama suka shiga halin maraici za'a kalle su ace 'Allah Sarki, Allah ya jiƙar mahaifiyar ku da ta rasu yayin haihuwa'.

.....
Gidan Hajiya Hauwa Meesha taje duba Yaseer. 
Tun jiya take niman layin shi a kashe baki ɗaya ta gagara samun nutsuwa, gashi tana jin kunya da kuma tsoron zuwa gidan su, kada ya ƙara fushi da ita a kan wanda yake yi yanzu.

Tana da yaƙini koma tace tabbacin zai zo yiwa Jamal lesson yau kasancewar shi lahadi. Saidai da isar ta aka sanar da ita gaba ɗaya masu gidan basu nan sun tafi gidan ƙanin mai gidan anyi rasuwa.

Tunanin ko ta kira Hajiya Hauwa ta tambaye ta Yaseer ya faɗo mata, amma ta lura itama ba son tarayyar su take yi ba tunda gashi ta fara kai gulma wurin iyayen ta. 

Toh ko taje gidan rasuwar ne ta tambayi Jamal ɗalibin shi?.

"Umm mai gadi nace Yaseer fa? Ya zo yau ɗin?"

Mutane da son gurmi wanda ba shi aka tambaya ba ya riƙe baki, "wani Yaseer ɗin? Yaron da yake zuwa laluɓe ƴar masu gida? Ai tuni ƴan audu suka zo suka yi waje da shi" da safiyar yau ya ji raɗeraɗin abinda yake faruwa shine shima yake son ayi da shi.

Yatsina fuska Meesha tayi cikin rashin fahimta tace "I don't understand, come again "

Ɗayan na ɗan tattaɓa shi don ya iya bakin sa amma ya share yace.
"Hajjaju! shi dai Yaseer abokin ki da yake zuwa yi ma yara karatu..."

"Uhm hmm?"

"Toh ashe zagawa yake yi yana laluɓe Hafsatu Rayina ƴar gidan Alhaji Tahir. Shine dubun shi ya cika Allah ya kama shi uban ya kama shi da idon shi"

"Reina dai?!" Meesha ta maimaita da mamaki ganin to ko iskanci Yaseer yaso yi me zai yi da wata Reina jaririyar da ko ƙirgen dangi da sauran ta?.

Amma shi sai ya ɗauka sunan da bai faɗa daidai bane take gyara mishi.

Yace "Ita dai" kana ya ɗaura da "ai ina faɗa miki Hajjaju mutane kina ganin su nan maha'inta ne ƴan kutumar kaza. Ki ɗauko mutum a bushe ana bashi maiƙo har ya fara tada komaɗa yana tafiya da dogon wuya zoƙai-zoƙai kaman jalbe amma shine duk cikin yaran duniya ya rasa wa zai taɓa sai ƴar alhajin Alhazawa..."

Zai ci gaba da magana Meesha ta gwada shi da yatsa "in sha Allah duk ranar da na dawo cikin gidan nan ka bar aiki. Wani station aka kai shi?"

A tsorace ya durƙusa yana ɗaga mata hannu kaman mai bara "dan girman Allah hajjaju a yafe ni, Wallahi suɓul da baka ne, bakin ne ba'a farsa shi ba tun haihuwa"

Reverse tayi zata bar ƙofar gidan ɗaya mai gadin ya faɗa mata address ɗin wurin gudun kada idan tazo tattarawa shima ta saka a haɗa da shi.

.....

Meesha bata yi musu kama da wanda zasu hana ta ganin Yaseer ba duk da suna tsoron Alhaji Tahir kuwa. 

Yana fitowa yaga ita ce ya juya zai koma, bai san kuma wata jarabar zata ƙara mishi ba yanzu, ta bar shi ya ji da abu ɗaya.

Da gudu ta ƙarasa ta riƙo hannun shi amma saboda raunin shi ya saki ɗan ƙara sai a lokacin ta matsa baya ta ƙare masa kallo da kyau.

"Yanzu shi Alhaji Tahir ɗin ne yayi maka haka? Wallahi ko duk duniya zasu taru a kai na ba zan taɓa yarda da sharrin da suke son ƙulla maka ba, kai ba mutumin banza bane"

Wasa-wasa kukan da Meesha tayi sai da ya kusa zarce na mahaifiyar shi ma. Aka dawo shine mai rarrashi da bada baki su kuma suka fita siyo mata ruwan gora mai sanyi saboda sun ganta da mota, gashi kana kallon ta kaga rich kid.

Da ƙyar ta bar station ɗin zuwa tunkarar Hajiya Hauwa a gidan mutuwa. Ita ta ɗauke shi aiki don haka ita ya kamata ta tsaya mishi tun da su suke morar shi.

.....

Yau ne gobe ne kamal zai dawo shiru. Har rana ya fara sanyi yana zaune cikin ƴan karɓar gaisuwa. Da goggo taji shirun yayi yawa ta kira shi don jin ba'asi ya sanar da ita ai Hajiya Fauziyya ce ta rasu sai ta ƙarfafa masa guiwar ya jinkirta da maganar suma gasu a hanya, don bata jin zata taɓa mantawa da kirki da kuma halaccin Fauziyya ɗiyar albarka.



~~~~~~~~~~~~

Idan Allah ya bamu aron rai, littafi na biyu zai zo paid ne. 500 posting document kuma 1000, Zaku iya fara payment yanzu ko zuwa lokacin da muka kammala littafi na ɗaya.
8021689184 Saliha Ahmad Na'ibi opay 
Sai a turo shaidan biya ta wannan number ***.




*Seemahwrites ✨*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.