Free chapter · Read without an account

CHAPTER TWO

by Rahinat Hussein (R.Hussain) · TAEESH

__Karɓi wannan ma wanke shi, bari na kewaya sai in tafi" cike da biyayya Umma ta karɓi ɗayan allon ta jingine ta ciki gaba da wanke wanda yake hannunta, sai da ta gama wankewa ta ɗaure cikin leda sannan ta fito, barorin da aka bata guda biyu ta gani tsaye bakin zaure, "Allah ya taimaki Uwar Babbar giwa Fulani Ƙarama na miƙo gaisuwa" murmushi Umma ta yi tana faɗin" ta tashi cikin ƙoshin lafiya" Sa'adatu wacce take dattijuwa ta ce" da ikon Allah, tana cikin ƙoshin lafiya" Umma ta ce"alhamdulillah nagode za ku iya tafiya" take suka juya don komawa inda suke da zama a cikin gidan.

San Dawaki ne ya fito cikin shigarsa ta Bayin sarki, sanye yake da babbar riga mai launin shuɗi da kore ya kima rawaninsa " Ni zan tafi Fada" Umma ta ce" to Allah ya tsare a dawo lafiya" ya ce"amin" ya fita . Gaisuwa ake ta aika masa ko ta ina, ya sami ƙarin girmamawa ne dalilin auren ɗiyarsa da Sarki yake yi, duk da Malam Rabi'u ba kowa ba ne face Sarkin Dawakai, ya gaji wannan sarauta ne tun kaka da Kakanni, su suke kula da dawakan da ke cikin gidan Sarki, ko haniniya doki ya yi ya san ma'anarta, inma lafiya inma akasin haka.

Cikin gidan Sarki Suhaid ya nufa, " Allah ya taimaki San dawaki Fulani ƙarama na son ganinka" cike da ƙaunar Rahama ya ce" to,to ba laifi mu je" take suka koma bayansa tamkar wani Sarki suna yi masa kirari na Sarauntarsa "lafiya San dawaki je ka lafiya Uban ƙaramar giwa, Allah ne ya baku ba mutum ba, kowa ya ja da ikon Allah ya taɓe" har suka isa ɓangaren Rahama ana yi masa kirari.

Tunda ta ji shigowar Baiwarta Batula ta tashi daga kishingidan da ta yi, "Allah ya taimake ki, Uban Mai martaba ya iso cikin amince" tashi ta yi tsaye cike da son ganin Babanta ta ce" ya shigo mana, ban hana ku wannan al'adar akan Mahaifina ba, wai dole ne yin ison nan ne iyee!" cike da nuna ɓacin rai ta yi maganar " Allah ya huci zuciyar Uwar Yarima mai zuwa" ta juya da hanzari.

Shi kaɗai ya shigo yana sallama, da sauri Rahama ta tare shi tana amsawa, sannu da zuwa Baba" zama ya yi a kan kujera yana mai fara'a ganinta cikin ƙoshin lafiya. A ƙasa ta duƙa tana gaishe shi, ya amsa yana faɗin" tashi ki zauna Rahama" ƙara sun kuyar da kai ƙasa ta yi tana faɗin" nan ma ya isa Baba" rubutun ya ɗauko cikin aljihu yace "ga shi ki sha ki shafe jikin ki, Allah ya raba lafiya" ta karɓa cike da kunya tana faɗin" nagode Allah ya ƙara girma, ya Ummana" ya ce"ta na lafiya ta na gaishe ki, a ci gaba da haƙuri kinji zaman aure ibada ne".

"Lafiya ɗan turon giwa gaba salamun baya salamun, ɗawisu sarkin ado,sarki jikan sarki, uban sarki kakan sarki da ikon Allah, taka lafiya namijin duniya" ƙamshin da ta jiyo ya isa sanar da ita wanda ke nufo sashin nata, Baba ya miƙe domin girmamawa ga Sarki Suhaid, parlor'n ya shigo tare da rakiyar dogarai, hannu ya ɗaga alamar su dakata daga nan, cike da bin Umarni suka rufe ƙofar su ka tsaya anan bakin ƙofa daga waje tamkar an dasa su.

"Ranka ya daɗe Allah ya taimaki mai Martaba" Cewar Malam Rabi'u ya durƙushe gaba ɗayansa domin kai gaisuwa ga sarki, hannunsa a dunƙule yana kai jinjina.

Sarki Suhaid ya amsa cikin sassanyar murna irin ta sarakai " an gaishe da Malam kai ne tafe" Baba ya ce" eh Allah ya ƙara maka lafiya, na zo ne kawo mata rubutu, Allah ya sauke ta lafiya" Sarki Suhaid ya ce" an gaishe da San dawaki muna godiya" Baba ya tashi yana gyara babbar riga duk ya rikice saboda kwarjinin Sarkin Suhaid, ya na faɗin" na barku lafiya" ya fita da hanzari, ganin yanda mahaifinta yake yi yasa taji babu daɗi, duk ya ruɗe akan ganin mijin nata, "barka da isowa ranka ya daɗe" cewar Fulani Rahama, cike da ƙasaita ya zauna ya na kallonta ganin babu walwala a fuskarta yasa yasan akwai abinda ke damunta, ya ce" ya jikin?" ta ce" da sauƙi" murmushi ya yi yana faɗin" fushi ake yi na sa Baba ya fita ko?" ƙasa ta yi da kanta tana murza zoben zinaren da ke hannunta, ya ce" tuba nake Mai babban ɗaki nima fa zuwa na yi duba nawa ƙwan, sai kuma aga laifi na uhum" murmushi ta yi tana rufe fuskarta, murmushi ya yi yana ƙara jin sonta na huda duk wata magudanar jini na jikinsa, ɗabi'arta ta kunya na ƙara mata ƙima a idonsa, sannan ya ce" doctor ya ce babu wata matsala kuma za ki iya haihuwa a nan ƙasar kuma nima naga alamun hakan, ko akwai abinda kike ji?" take ta girgiza kai ya ce" zo nan na duba da kaina" sanin bazai taɓa fita ba sai ya shafa cikin da ke jikinta, yasa ba musu ta nufe shi.A jikinsa ya zaunar da ita ya na ɗaga doguwar rigar da ke jikinta,daga ita sai pant, bin santala-santalar cinyoyinta ya yi da kallo, sannan ya yi kissing cikin yana shafawa daɗi yake ji, shima zai sami magaji.Kusan minti talatin ya yi sannan ya gyara shirinsa ya na faɗin"ki kula min da kanki" ta nufi ƙofa knocking door ta yi, take Fadawa suka buɗe, Sarki ya fita suka ci gaba da kirari, Ruƙayya da Batula suka shigo suna faɗin " ranki ya daɗe akwai abinda kike buƙata?" kai ta girgiza sannan ta ce" Batula zo ki matsa min ƙafata ciwo take" da sauri ta zauna ta na faɗin" sannu uwar ɗakina" Ruƙayya ta ce"ko a kira likita ranki ya daɗe" a'a ta faɗa tana faɗin " ba ni apple ɗin nan" Ruƙayya ta ɗauko mata basket ɗin ta ajiye a gabanta ta na miƙa mata ɗaya.

Batula da Ruƙayya su ne amintattun bayinta, ko da abu aka kawo wanda ba su aminta da shi ba, sai sun ɗanɗana kafin su kai gareta domin ransu fansa ne ga uwargijiyan su.

A Ɓangaren matan sarki kuwa an turawa Dr.Salim naira million talatin, sosai Dr.Salim ya ɗauki alwashin ganin bayan cikin Fulani Rahama, alkhairi yake samu ta kowanne ɓangare akan cikin nan, Sarki da dukkan masoyansa ma ba a barsu a baya ba, Dr.Salim ya tara abubuwa da dama.

Kwance yake yana lissafa sauran kwanakin E.D.D ɗin Fulani Rahama, "doctor what's happen to you?"Cewar matarsa Zainab, ta na murza idanunta gami da kunna lamp, 03:14am na dare, Dr Salim ya ce" nothing nima yanzun na farka ne" Zainab tace"a'a akwai abinda kake ɓoye min duk wani motsinka ina sane da shi, kusan wata biyu kenan kana cikin damuwa, but you don't tell me, pls doctor tell me what's wrong with you?" Cikin fusata ya hau faɗin" nace miki nothing a'a ko ke uwata ce da za ki saka ni a ga a da tambaya, I'm not a small boy, I'm educated person, I used to my sense to solve anything, don't hurt me pls barrister" ya shige toilet zama ya yi ya na dafe kansa domin neman mafita.

Zainab ta zuba tagumi tana bin ƙofar toilet ɗin da ido, ganin ya banko ƙofar yasa ta taɓe baki gami da kashe gasken ta juyawa ta koma baccinta.

Tunda watan haihuwar Fulani ya shiga maimartaba Sarki Suhaid yake ta sadaka da kyauta ko da yaushe cikin farinciki da walwala yake.

Tara matansa ya yi a turakarsa su huɗu Fulani ta Gabas, Fulani Amina,Fulani Zaitun da Fulani Rahama, kowacce sai yatsina da shan ƙamshi take ana ta aikawa Fulani Rahama harara, tunda ta sa kanta ƙasa bata ɗago ba, bare tasan suna yi, cikin tsare gida Sarki Suhaid ya fara magana cike da hikima ya ce" ina fatan kowacce tana sane da abinda yake shirin faruwa na farinciki a wannan masarauta tamu, ƴar'uwarku Rahama ta shiga watan haihuwarta" a tare faɗuwar gaba ta ziyarce su, yayin da tashin hankalinsu ya fito fili.

"Uhum kai ma sha Allahu ashe abun ya zo,in ji mai tsoron wanka, to Allah ya raba lafiya" cewar Fulani Zaitun tana yaƙe, Fulani ta gabas ta saita nutsuwarta ta ce" Allah ya raba lafiya, oh ranar nasan tambura za su ta tashi magajin sarki ya zo duniya" tsabar murmushin da mai martaba yake har sai da haƙoransa suka bayyana. Yana faɗin " in sha Allahu, to shine nake nemawa ƙanwar taku alfarma?" Fulani Amina ta ce" ranka ya daɗe faɗi ko mene ne anyi angama, ai yanzu ba mu da wani buri da ya wuce ganin magaji ko magajiya sun zo lafiya ko ba haka ba Fulani" ta faɗa tana kallon matan sarki, taɓe baki ta Gabas ta yi tana ɗauke kai.

Sarki Suhaid yace" ina son zan kasance da ita har lokacin da zata haihu domin hankalina ba zai kwanta ba ko dawa na haɗata" Fulani Zaitun da ke da tsananin kishi ta ce" ranka ya daɗe kana nufin gaba ɗaya kwanakin namu zamu tarkata mu bar mata kenan?" Mai martaba ya ce" a'a Zaitun ba haka nake nufi ba, idan kika duba da zarar ta sauka lafiya ba ita a raba kwana sai bayan ta yi arba'in, to mene ne don kin kun ara mata kwanaki kaɗan?" uhum " Allah ya sauketa lafiya, hakan ma ya yi Allah ya ƙara maka lafiya, ai kamar yau ne" cewar ta gabas tana yiwa Fulani Zaitun inkiya da ido, Rahama da zaman ya isheta ta gyara zama gami da yatsina fuska, saboda mararta data karta, cike da kulawa sarki Suhaid ya ce"sannu" ta ce" da abari Mahaifiyata sai ta zo ta zauna da ni ba sai an ba ni kwanan su ba Allah ya taimake ka" Sarki Suhaid ya ce" abinda na ce to dole haka za a yi" Fulani Amina ta ce" haka yake Allah ya huci zuciyar Sarki mun amince gaba ɗaya burin mu dai ta haihun lafiya" Fulani Zaitun ta hau kumbure-kumbure saboda bata iya ɓoye kishin da take yi da Rahama.

"Na gama magana" cewar Sarki, "Allah ya baka nasara, mun amince zamu iya shiga ciki?" ya ce" eh" a tare suka miƙe suna aikawa da Rahama kallon banza, wacce tashin ma sai da kyar take yinsa.

Sai sannu yake mata cike da tausayi, ta ce" na barka lafiya" ta fita, part ɗin Fulani ta Gabas suka nufa duk kansu barori na take musu baya, ta nufi nata sashin da kuyangunta Batula da Ruƙayya.

BAYAN SATI ƊAYA

Tun safe take jin ciwo sama-sama, Umma da ke tare da ita, tana kallon yanda take ta faman hura hanci ta juya can ta koma can, ganin Rahama bata da niyyar sanar da ita, yasa ta kira Batula domin aikata fada.

Jakadiya Tabawa ce ta shigo da sallama, ta na faɗin "sannu uwarɗakin mu" da sauri Umma ta ce" yauwa Baba Tabawa don Allah a sanarwa da mai martaba Rahama na kan gwiwa" Jakadiya ta hau faɗin" la'ila masalli ilah banga ta zama ba, yanzu kuwa" ta fita da gudu-gudu ta nufi fada, ba tare da wani iso ba, ta zube gaban Mai martaba " Allah ya baka nasara Fulani na kan gwiwa magaji na hanya" fadawa suka hau faɗin" angaishe ki Jakadiya" Sarki Suhaid ya dake yana faɗin " a fito da mota yanzu a tafi asibiti Allah ya raba lafiya" amin sarki mai adalci.

Nan da nan aka kaiwa su Fulani rahoto, hankalinsu a tashe suka hau kiran Dr.Salim, doctor da yake ta jiran wannan rana ya sanar da su, babu abinda zai gagara, zai kira su da zarar komai ya kammala.

KMC hospital akai da Fulani cikin sauri, aka karɓeta a VIP labour room aka yi da ita, Dr.Salim ya taho yana sanya hand gloves, fuskarsa sanye da facemask, ya nufi ɗakin. Umma da Jakadiya da Hajiya Binta(matar Ciroma Ubaid ƙani ga Sarki Suhaid) sun yi shiru a parlour'n da yake tamkar reception a vip ɗin.

Malam ya shigo da sauri hannunsa ɗauke da rubutun naƙuda ya na faɗin " Ramlatu ta sauka ne?" kai dallah Malam rufa mana baki" ka wani tawo fuɗur-fuɗur wai kai nan mai ƴa mtswww" cewar Hajiya Binta wacce take cike da baƙincikin Sarki Suhaid zai sami magaji, bayan bata da burin da ya wuce a ce mijinta Ciroma Ubaid ne zai gaji Sarautar bayan shi kuma ɗaya daga cikin ƴaƴanta Abdallah ko Abubakar wani ya zama sarki bayan ba mahaifinsu, sai gashi Sarki Suhaid zai sami magaji.

Jikin Baba ne yayi sanyi, hakama Umma suka koma gefe su na ta addu'a a ransu Allah ya sauki ɗiyar tasu lafiya.........

***

Zinariya ce✍🏻

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol