Free chapter · Read without an account
CHAPTER TEN
____"What? It's can't be possible, it's not k.m.c (for sure), innalillahi wa'inna'ilaihirrajiun" rikicewa ya yi, wani zazzafan gumi na karyo masa, Brr. Zainab ce ta riƙe shi "relax, relax, comedown, ka yi addu'a doctor" fuzge jikinsa ya yi, ya nufi barin ɗakin, daga shi sai short niker, hijab ta zura da sauri,ta ɗauki jallabiya ta bi bayansa. Karɓar car's key ɗin ta yi, ta miƙa masa rigar ya karɓa ya zuba, sannan suka tafi.
Fire service ne ko ta ina cikin asibitin, an yi nasarar kashe wutar, ba ta ci sosai ba, block ɗaya ta kama, ba a yi asarar rayuka ba, sai dai asarar milliyoyin kuɗin, inginan da ake tests, da kuma computer ne suka ƙone, ya yin da matasa suke ta yin video da hotuna ana ta ɗorawa a kafafan yaɗa labarai( social media).
Dr. Umar ne ya nufi in da yake, kafaɗarsa ya dafa yana faɗin " sorry doctor sai haƙuri, but mun gode wa Allah da ba ta ci kowa ba, har aka yi nasarar kashe wutar" Dr. Salim ya ce" me ne ya yi causing fire ɗin, kuna ina har hakan ta faru?" Dr. Faisal ne ya amsa masa da faɗin " har yanzu ba a san abin da ya sa wutar tashi ba, amma suna kan yin buncike" Brr. Zainab ta ce" alhamdulillah tunda akan dukiya abun ya tsaya ai da sauƙi" asibitin duk ya rikice, wasu suna ta a ba su sallama, don sun tsorata sosai.
Ward - ward Barrister Zainab da sauran nurses ɗin suka dinga bi suna kwantar musu da hankali, abin ka da lauya, nan da nan suka gamsu da abin da ta faɗa.
Ƴan jarida ma sai tambayar Dr. Salim suke ta ya ya wannan abu ya faru, rasa abun da zai faɗa yake, sai su Dr. Faisal ke bayani.
Ranar ba ƙaramin tashin hankali Dr. Salim ya shiga, babu abun da ke ɗaga masa hankali irin ta ina zai sami kuɗin da zai ƙara shigo da wasu injinan ƙasar nan, ga shi ko shekara ba a yi da shigo da wasu ba ma.
Kiransa ake ta ko ina ana ta jajanta masa wannan lamari, amma bai ga kiran matan sarki ba, abun ya ba shi mamaki, sai kuma ya yi tunanin su ai manya ne.
Brr. Zainab ce ke ƙara kwantar masa da hankali, amma tamkar zautacce kullum sai ya yi zancen asarar da ya yi.
Daga ɓangare guda kuma, an matsantawa Brr. Zainab .A. Maitama da barazana akan case ɗin da take akan ɗan minister of finance da ya yi rapping, ƴar maƙotansu, yarinya ƴar shekara goma sha shida.
TRUST COURT
Cike kotun take da jama'a, kama daga masu hannu da shuni, har talakawa ko Ina ka duba a cike, sai lawyers and barristers, registrar's, da sauran ma'aikan cikin kotun.
Barrister Zainab .A. Maitama ce sanye cikin shigarsu ta lauya, sanye take da medical glass tana duba wasu papers da ke hannunta, agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunta ta duba, goma saura minti uku, an kusa a fara sauraren shari'ar su.
Alƙali Ɗahiru Haruna Ammani wanda ake wa laƙabi da (Damisa ƙi sabo) shi ne ya ke jagorantar shari'a a Kotun.
Rigistara ne ya miƙe ɗauke da takarda a hannunsa ya ce" a yau ɗaya ga watan yuni na shekara ta dubu biyu da ashirin da huɗu, za mu ci gaba da sauraren ƙarar da Alhaji Bashir ya shigar da Salim akan zargin fyaɗe da aka yi wa ƴar yayansa" ya miƙa takarda ga Alƙali, rubuce-rubuce Alƙali ya yi sannan ya ce" ko yaron da ake ƙara yana kotu?" Barrister Kamal ya ce" Yes my Lord" sannan Alƙali ya kuma ce wa" idan lauyoyin da suke ƙara suna kusa su gabatar da kansu?" nan ma Brr. Kamal ya tashi yana gyara rigarsa " ya ce" sunan Barista Kamal Shehu ni ne nake kare wanda ake zargi" ya zauna, Brr. Zainab ma ta tashi ta ce " suna na Zainab Aliyu Maitama ni ce lauyar masu ƙara" ta zauna.
Wani matashi na tsaye cikin teburin tuhuma, da gani babu tsoro ko nadama a tare da shi.
Brr. Kamal ya tashi ya na faɗin" ya mai shari'a ina so in gabatar da shaida ta gaba a gaban kotu" dama Alƙali ya ba shi, shigo da wata tsohuwa aka yi, ma'aikaciya ce a gidan minister, Brr. Kamal ya ce" Baba ko za ki faɗawa Kotu sunanki?" ta ce" suna na Jummai shekarata ashirin da biyar ina aiki a gidan Alhaji Yusuf. Ya ce" ko zaki iya faɗawa Kotu a ranar goma ga watan Mayu da misalin ƙarfe biyar na yamma Salim yana ina?" tsohuwa ta ce" a wannan rana Salim bai je ko ina ba, don ba ni mantawa har abokin shi, Saifullahi ya zo don su fita ya ce masa ba ya jin daɗi ba zai iya fita ba,to har dare suna tare" Brr.Kamal ya ce" to kuma aka ce ya aikata wa Ameera fyaɗe da misalin ƙarfe biyar na yammacin ranar" da sauri ta ce" a'a ba shi ba ne ba, kawai sharri aka yi masa, mutumin da bai ma fita daga gida ba wannan duk zance ne" Brr. Kamal ya ce" muna godiya da bamu shaida, za ki iya tafiya, mun gode" ya juya ga alƙali ya ce" ya mai girma mai shari'a da wannan hujja ta ƙarshe nake so a yi watsi da wannan ƙara, kuma a bi wa wanda ake zargi haƙƙinsa, kuma wannan Kotu mai adalci ta wanke shi daga wannan mummunan ƙazafi da aka yi masa" Brr. Zainab ta miƙe tsaye tana faɗin "objection my Lord bai kamata wanda yake kariya ga wanda ake zargi da ya dinga yanke hukunci akan wanda ake tuhuma da laifi ba, saboda har yanzu babu wata ƙwaƙƙwarar hujja da ta nuna ba shi ba ne ya aikata hakan, idan ba shi ba ne to waye?" Alƙali ya ce" Brr. Kamal a kiyaye" Kamal ya ce" na gode mai shari'a" ya koma ya zauna. Alƙali ya juya ga Brr. Zainab ya ce "Barrister ko kina da abin ce wa ga Jummai" Brr. Zainab ta miƙe ta tsaya a gaban Jummai mai aiki ta ce" Baba kin ce a lokacin da abun ya faru Salim yana gida babu inda yaje a wancen rana, hakane?" Tsohuwa ta ce" ƙwarai da gaske" murmushi Brr. Zainab ta yi ta ce" good to ya aka yi da farko ya ce ya ga Ameera tsaye da wani a bakin gate ɗin gidansu, kenan wannan ma ba gaskiya ba ne?" take tsohuwa ta fara rikicewa " a'a um, uɓ ni kam dai bansan da wannan ba, iya abin da nasani na faɗa" Brr. Zainab ta ce" okay muna godiya Baba za ki iya koma wa ki zauna" da sauri ta sauka daga wajen har tana tuntuɓe.
"Ya mai girma mai shari'a ina so zan gabatar da shaida ta gaba" Alƙali ya ce" an baki dama" ta ce" a shigo da Dr. Haisam" wani likita ne ya shigo, kowa ya juya yana kallonsa, don tun zaman farko aka kawo shi, ya bada shaida, sai gashi a karo na biyu na dawo.
Ta ce" Doctor ka gabatarwa da kotu kanka" ya ce" sunana doctor Haisam Hussein ni likitan mata ne na asibitin Federal Unity dake Hauren Giwa" ta Kuma ce wa" doctor ko kasan waccen yarinyar?" ta yi showing Ameera da ke zaune ta jingina jikinta a kafaɗar mamanta, ya ce" tabbas na santa, don a ranar da abin ya faru, ni ne a duty kuma ni na dubata" ko za ka faɗa mana me ya sameta?" ya ce" tabbas an yi rapping ɗinta, don ni ne na tabbatar da hakan, ga shaida ma ina tare da ita, ya ciro wani file daga cikin rigarsa ya miƙa, ta ce" mene wannan ɗin?" ya ce" report ɗin police ne da kuma duk wani abu da ya faru da Ameera a ranar har na asibiti da komai da aka yi na treatment da bills ɗinta" ta ce" amma doctor kasan da haka meyasa baka faɗa ba tun a zama na farko" ya ce" dalili shine..Ya ciro waya sai ga muryar Brr. Kamal da doctor ta bayyana inda ya je har asibitin ya yi masa tayin kuɗaɗe akan ya ɓata result ɗin ya kuma ƙaryata fyaɗen da aka ce anyi. Gumi kawai Brr. Kamal ya shiga yi, hakama Alhaji Yusuf Ayuba.
Take Kotu ta ruɗe da hayaniya ana Allah wadaran halin masu kuɗin garin nan, na ƙin bin gaskiya, Alƙali ya ce" Brr. Kamal ko kana da abin ce wa?" kai kawai ya girgiza yana faɗin " babu ya mai shari'a" aka ce "Brr. Zainab ko akwai wata shaidar ta ce " eh ya mai shari'a, ina son ganin Ameera anan" Ameera ta fito tafiya take tamkar mara lafiya ta tsaya, Brr. Zainab ta ce" kar ki ji tsoro a gaban kotu mai adalci kike" ko za ki ƙara nuna mana wanda yayi miki fyaɗe?" take ta kuma nuna Salim, hawaye na wanke mata fuska, sun kuyar da kai ya yi, nadama da danasani suka shige shi.
Brr. Zainab ta ce" za ki iya komawa" ta juya da gudu ta bar cikin kotun tana kuka mai tsuma zuciya.
Gaban Salim Brr. Zainab ta je ta tsaya ta ce"Salim ka ji abun da ake tuhumarka da shi, shin da gaske ne?" take ya ce" eh ni ne na aikata, amma ina roƙon kotu da a yi min sassauci, wallahi sharrin shaiɗan ne, da kuma irin shigar da ta ke yi ne yasa ni aikata haka" ya fashe da kuka, Hajiya Jidda ma sai kuka ganin ya amsa da kansa.
Brr. Zainab ta ce" ya mai girma mai shari'a da wannan nake fatan kotu za ta ƙwatarwa Ameera haƙƙinta na ɓata masa rayuwa da aka yi, na gode" ta koma ta zauna.
Alƙali ya yi rubuce-rubucensa sannan ya gyara zaman glass ɗinsa ya ce" bisa jin hujjoji da shaidun gani da ido, da kuma furucin da shi wanda ake zargi ya yi, kotu ta tabbatar da ce wa Salim Yusuf Ayuba shi ne ya aikata fyaɗe ga Ameera Ahmad Bashir, bisa ga wannan furuci, Kotu ta yanke wa Salim hukuncin zaman gidan yari na tsahon shekara goma ba tare da zaɓin tara ba, sannan za su bawa Ameera diyya ta naira million ɗaya domin rage mata raɗaɗin illar da aka yi mata" ya buga wani hammer da ke kusa da shi, bom-bom-bom "Kooootuuuuuu!!!!!" kowa ya miƙe Alƙali ya bi ƙofar da ya shigo ya koma.
Ƴan uwan Ameera suna ta murna, gami da binta harabar kotun suka rumgumeta suna murnar sun yi nasara, barristers suka shiga gaisawa da Brr. Zainab ana yi mata congratulations na nasarar da ta yi a wannan shari'ar.
Salim da ya zube yana kuka, yana ihu Mahaifinsa ne ya je da niyyar kama shi, ma'aitan prison suka yi gaba da shi, Mommy (Jiddah) ta na kuka ta bi bayansu tana faɗin " don Allah kar ku kai shi prison" riƙeta a ka yi ana bata baki.
Brr. Zainab ta fito tana ta farinciki, Dr. Salim ya jinjina mata, yana mai dunƙule hannu yana ɗaga babban yatsansa, " I'm proud of you my wife, Allah ya ƙara miki ƙwarin gwiwa" murmushi ta yi tana faɗin " amin ya Allah Mijina abin alfahari na, nasarata ai tana tare da goyon bayan da kake ba ni ne, kai da iyayena ne kuka nuna min hanya, don haka zan yi gaskiya, zan bi gaskiya zan tsayawa mai gaskiya, zan tsaya akan gaskiya, zan yi gaskiya ko da akam kaina ne, ko akan iyayena ne, kuma ko da akan mijina ne, na yi alƙawarin bayyanata a duk inda take" ya ce" ina alfahari da ke matata Allah ya baki nasara" minister Alhaji Yusuf ne ya fito da ahalinsa, tsayawa ya yi a gaban Brr. Zainab ya kafeta da ido, cikin tsananin baƙinciki da muguwar ƙiyayya, ya na nunata da ɗan yatsa ya ce" kin yi nasara akai mu, ina miki murna, amma ki sani bakin rijiya ba wajen wasan makaho ba ne" ya yi gaba.
Dr. Salim ya ce" ɗan wahala, ai gaskiya dai ɗaya take don haka babu abun da zai sami mata ta" ta ce" manta kawai Doctor, na gaji mu tafi kawai" rungumarta ta ji anyi ta baya,Ameera ce, tare ƴan uwanta suka zo. Godiya sukai ta yi wa Brr. Zainab, Ameera kuwa ta kasa magana sai kukan murna, haka dai suka rabo cikin farinciki. Dr. na ajiyeta a gida ya wuce kmc hospital.......
GARIN ƊAN KADA
"Wasila don Allah zan ɗan fita nan maƙota dubiya, ki kula da gidan" A'i ta faɗa tana sa hijab ɗinta, Wasila ta fito daga ɗakinta tana faɗin " to sai kin dawo" A'i ta ce "yauwa" ta fice.
Da sauri Wasila ta kandami ruwa ta shiga wanka, nan da nan ta fito ta shiga ɗaki, ta sake kwalliya jar hoda kamar ta yi magana a fuskata, ta ranbaɗa kwalli, ga mi da jambaki, ta ɗauko wata matacciyar t-shirt fara ce asalinta, amma ta koma milk-milk brown-brown ta sa, ta ɗaura zani brown da ɗankwalinta irin na daa, ta fito tamkar wata aljana, slipper ɗinta da ya siɗe tsabar tsufa har ya ɓule ta sa, ta zauna a ƙofar ɗaki, sanin yaya Ali ta kusa dawowa.
Bata fi mintina goma da zama ba, Ali ya yi sallama yana tura kekensa ciki, da sauri ta tashi tana ƙoƙarin karɓar masa keken ta jingine " hannu da zuwa yaya" ta faɗa tana kararraye-kararraye, yauwa sannu da gida, ina matar gidan ne?" ya faɗa yana dube-dube , ta ce" tab ai ta fita tun ɗazu wai dubiya za ta je nima sai jiranta nake, alkur'an tsoron gidanma nake ji, ina tunanin fita sai gaka ka dawo" ya ce" dubiyar ne bata je tun da safe ba sai yanzu da yamman nan sakaliya" ta ce" uhum bari in kai maka ruwan wanka, au ka higa ka zauna bari in fara baka ruwan hya(sha)" ya ce" to Wasila na gode Allah ya yi albarka" cikin jin daɗi ta nufi randa, tana juya mazauna tamkar an kifa kwarya, ya shige ɗakinsa.
Da sallama ta shiga ta ajiye masa ruwan, ya ɗauka ya sha, zama ta yi a gefensa tana faɗin" ka sha aiki yaya, ko in kawo maka abinci ka ci, ka fin ka yi wankan?" ya ce" a'a Wasila idan na tsaya cin abinci sai ki ga magriba ta yi ban yi wankan ba" hahhh au kuma fa hakane, bari in kai ruwan" ta faɗa tana tashi ta zuba ruwa ta kai banɗaki, har da ɗaukan kwandon wanka da zuba wani a buta duk ta kai masa.
"Na kai Yayana" ta faɗa tana ɗaga labulen ɗakin nasa, ya ce" to gani nan fitowa yanzu" ta ce" tom ka bani kayan na wanke" ya ce" a'a ki barshi idan ta dawo ta wanke" cikin shagwaɓa da kissa ta karya murya tana faɗin " haba yaya ni dai a'a na ƙi wayon, nima yau ni zan samu ladan" murmushi ya yi yana faɗin" to shikenan bari na fito miki da kayan" daɗi kamar ya kashe Wasila ganin ta samu abun da take so.
Wanka ya shiga, ita kuma ta duƙa tana wanke masa kayan da ya yi aikin gona da su, tana yi tana waƙarta ta soyayya "ci gabanka nake so baby na, ɗaga hannu hubbina, addu'a zan yi maka zaɓi na, komai nace fa kace amin.....Ta na ta yi abun ta, fitowa ya yi ya na faɗin sannu da ƙoƙari" hmmm murmushi ta yi tana faɗin " kai ne da sannu kai da kake ta wahala kullum, Allah dai ya yanke maka, ya baka magajin da zai hutar da kai" yana son wannan addu'ar ya ce "amin amin" sai kuma ta ce" uhm ba dan kar na yi laifi ba da nace wani abu, ya ce" mene ne faɗi mana" ta ce" da sai na ce kawai a yi ƴar gida, kasan Allah har yau ina sonka yaya Ali, ina ji a jikina ni zan haifa maka magaji" take ya haɗe rai yana faɗin " banason wannan shashancin naki, na zaci kin yi hankali ashe har yau da saura" tura baki gaba ta yi tana faɗi, "to wai kai yaya me ye ba ni da hi da baka so na, ta hau juyi a gabansa, gami da kwaɓe fuska tamkar za ta yi kuka. "Tsaki ya yi, ya ɗauki butar ya yi ƙofar gida, da kallo ta bi shi tana faɗin " ai alkur'an sai na kori matarka ka aure ni ahe" tana murguɗa baki, sannan ta ci gaba da wankinta.
" A'a Malam har ka dawo, sannu da zuwa" ce war A'i da ta dawo ganinsa yana alwala a ƙofar gida, ko amsawa bai yi ba ya shigo ciki, binsa ta yi sanin bayaso ya dawo bata gida, su Alawiyya ne suka tsareta da hira,
" don Allah ka yi haƙuri Malam wallahi ban fita da wuri ba ne, kasan TAEESH ce take ta kashin haƙori, to sai da naga ta ɗan samu sauƙi shine muka je a gurguje ma na je, ko zama ban yi ba" cikin fusata ya ce" tun yaushe kika tafi, ai kinsan lokacin da nake dawowa kin fi kowa sani" Wasila ta ce" kai matar Yaya aikuwa kin ɗan daɗe da fita kam gaskiya" masallaci ya tafi, A'i ta sauke TAEESH da ke hannuta ta ce" Wasila idan ina magana da mijina kar ki ƙara samin baki" Wasila ta ce "heheheh ma su miji manya, kinsan da ya kusa dawowa kika sa ƙafa kika fice, ba don Allah yasa ina nan ba waye zai masa hidima, ta tura ɗankwali goshi ta kama shanya kayan Ali, kishi ne ya kama Ai ta ce" waye ya baki damar yi masa wanki?" Wasila ta ce" a'a kar fa ki manta ɗan'uwa na ne, jini ɗaya ya fi ƙarfin wasa, ke mata ce a yau zai iya sauya ki, ni kuwa fa, har abada ni ɗin jininsa ce, bar ganin na zo gidanki kina wulaƙanta ni, jin motsin Ali yasa Wasila fashewa da kuka.
TAEESH na jin ihu, sai ita ta tsorata ta canyare da kuka.............
Zinariya ce✍🏻