Free chapter · Read without an account

Page 8

by Sumayya Usman · JADEEDA

*JADEEDAH*

         (It's a story of two love birds who are so different from each other ) 
STORY & WRITTEN BY :
 (*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin 
        MENE NE ABIN YI ?
        KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*

***
***


BOOK 1 



PAGE 8 ❤🔥
       FREE PAGE

"To fa wai wake ta faman kiran wannan wayar ne haka ?,in ka kira d`aya biyu ba a d`aga ba sai ka hak`ura alamun mai wayar ba ya kusa ne ko kuma yana wani abun mai muhimmanci da ya hana shi d`aga kiran", Cewar Hibba wacce sallame Sallahr Isha'in take nan tun tana Sallah ake  faman kiran wayar Abubakar da ya barta a charge ya tafi masalaci domin gabatar da tashi Sallahr.
    Har ta mik`e za ta je taga waye yake ta faman kiran wayar,sai wayar ta katse,sai da Hibba ta ja tsaki kafin ta koma ta zauna.
    "Grandma ya k`i d`aga kiran ko dai yasan muna cikin Garinnan ne shiyasa ya k`i d`aga kiran wayar ? ".
    " In ko haka ne da Daniel ya bani kunya,da ya aikata abinda ban ta`ba expecting daga gare shi ba".
    "To yanzu ya zamu yi Grandma, ko dai komawa Gida zamu yi ?".
    " God for bid, Cecelia ba inda za ni har sai na sanya Daniel a cikin idanuna "....
    Cecelia ta katseta da cewa," Kenan haka Na nufin zamu kwana a saman Street ? "," No my dear ba zamu kwana a saman titi ba,dole wata dabarar zamu sake wata k`ila muyi nasarar samun sa".
    "To ko dai wata wayar zamu ara sai mu Kira shi da ita in anyi sa'a  ya d`aga shikenan","To shikenan Cecelia gwada mu gani",wara idanu Cecelia ta fara yi a cikin tashar da suke,can ta hango wani shop,ta kalli Grandma tace ko can zamu je ga wani shop can sai mu rok`e shi ya ara mana wayar ?"," To mu je mu gani ko zamu da ce".
     A tare suka isa cikin Shagon,bayan sun gaisa Cecelia tace da shi,"Please ka ara mana wayar ka,muna so zamu yi kira tamu wayar ta mutu ne saboda rashin charge, gashi munyi tafiya  mai nisa".
   Wani irin kallon mai Shagon ya bisu da shi alamun kamar bai yarda da su ba.
   "Haba  Yarona ka taimaka ka ara mana,ba cutar da kai zamu yi ba, idan baka taimake mu ba,ba mu san ina zamu kwana ba,gashi ba mu san kowa a cikin Garinnan ba,please ka tai maka mana".
Haka ba dan ya so ba ya basu aron wayar,Cecelia ta sa number,tana fara shiga ta mik`awa Grandma wayar.
   Sai da Hibba ta ja dogon tsaki kafin ta yunk`ura da k`yar  ta nufi inda wayar take,ganin bak`uwar number ne ya sa ta d`aga kiran tare da yin Sallamar tare da cewa,"  Mai wayar baya kusa a sake Kira zuwa anjima ".
    Cikin d`aga murya Grandma ta ce, "Who the hell are you, wace ce ke da har zaki d`aga min wayar Yaro ina Daniel d`in yake ?".
  Ba Hibba kad`ai ba hatta Unborn d`in da ke cikinta sai da ya motsa sakamakon tsawar da kuma murya Grandma da ta ji".
  " Na ce maki ina Daniel d`in ya tafi a cikin irin wannan daren,kuma ke kuma wace ce da har aka samu wayarsa a hannunki?".
   Diriricewa Hibba tai Zufa sai faman tsa-tsafo mata take,ta rasa me zata ce da ita,shigowar Abbakar ya d`an saisaita mata tunanin da hanzarinta ta nufi inda yake ta na mai mik`a mashi wayar amma ta kasa iya cewa da shi komi.
    "Lafiya me yake faruwa ya na ganki a cikin irin wannan yanayin, ko dai jikin ne har yanzu ?"......
    " Grandma ce akan line"...shine abinda ta iya cewa kawai
    "Grandma kuma ina fatan dai baki d`aga ba ko ?","Yanzu haka tana kan layi tana jinka", sosai tsoro da fargaba suka bayyana akan fuskar shi,jikin shi a matuk`ar sanyaye ya kai wayar a kunnensa shi tare da kiran sunanta yanda zai samu tabbacin ita d`ince.
    " Eh ni d`in ce dai wace kake gudu, kenan saboda mace ka ne aikata mana duk abinda ka ga dama"...muryar shi na rawa ya fara k`ok`arin dakatar da ita,hanashi cewa komi tai sai itace ta cigaba da cewa,"Ka bar komi kake ka zo nan Tasha muna jiranka".
    "Tasha kuma wacce irin Tasha,to wai ma wacce tashar ki ke nufi".ya faɗa a firgice
    " Tashar Ubanka na ke nufi,ina nan cikin Garin Kano ka zo ka d`auke mu ,kana da za`bi  ko dai ka zo ka d`auke mu ko kuma mu juya mu koma inda muka fito ko kuma mu kwana a Street ya rage ruwanka".
    "A'a Grandma ba ayi haka ba,ku jirani ganinan zuwa".

   Haka ya kashe wayar ya nufi inda ya ke aje keys d`in motarsa,rasa ma Ina ya aje su yai sai yai gaba sai kuma ya dawo yai baya,ya ma rasa ne ya kamata yai sai Hibba ce ta d`auko mashi key d`in ya fita,ko da ya fita yawo kawai ya kama yi akan titi,sai daga baya tunanin shi ya fara dawowa jikinsa,sannan ya fiddo wayarsa ya Kira layin da su ka kirashi da shi ya Kira shi ya gayama sa Tashar da suke ya nufi can d`in.
    "Kin ji tashin hankali Cecelia, wai mace kuma ce ta d`aga wayar Daniel da farko","Mace kuma to wace ce ita,wanne matsayin ne da ita har haka ?"," Ban sani ba,a iya sani na Mace ba ta cikin d`abi'u ko halayyar Daniel ".
" Ko dai yana tare da fiance d`in sa ne ?","To in haka ne mai zai sa tun farko ba zai sanar da ni ba,sai ya rik`a gudunmu",
    "Tom ,ni dai bana ce komi ba ,sai dai mu bari ya zo sai mu ji gaskiya daga bakin sa".haka dai suka cigaba da wannan zancen har zuwa sanda ya iso tashar.
   Ko da isar shi tashar da hayaniya Grandma ta taso mashi,cikin ladabi da biyayya ya duk`ar da kanshi ya na mai cewa da ita," Na rok`e ki da kiyi hak`uri ki dakatar da duk wani `bacin rai ko fushi da ki ke ji a kaina har sai mun Isa Gida ,in ba haka ba nan mutane zasu taru su san wannan irin hali muke a ciki".
     Da k`yar Grandma ta iya had`iye abinda take ji a cikin ranta har suka bar cikin Tashar, ita kuwa Cecelia sai faman kallon shi kawai take gani ta ke kamar ba Brox Daniel d`in ta da ta sani ba, kamala da natsuwa duk sun bayyana a tattare da shi.
Yanda Abbakar ya fita cikin tashin hankali da damuwa hakama Hibba take a cikin shi,komi na ta ya tsaya ta rasa wanne tunanin ko kuma wani abu da zata aikata ya kawo sauk`in wannan lamarin da ya tun karo su,amma ina kanta a cunkushe yake,tunanin ta ya cure guri guda,babban abinda yafi tsaya mata a rai da kuma sake tada mata hankali muryarta da Grandma ta ji,ya zasu k`arke shin zata kar`beta a matsayin in-law ko kuwa za tai rejecting d`inta.
    Sanda taji k`arar bud`e gate d`in Gidan da shigowar su sai da numfashinta yai yunk`urin dakatawa da k`yar ta samu ta janyo shi da k`arfinta.
    Sanda suka shigo cikin Parlourn ba k`aramin sake hargitsewa tai ba,sai ji tai inama da ta sani `boyewa tai bata zauna sun isketa a cikin Parlourn ba.
     Cecelia ce ta matsa kusa da ita,tana mai binta da kallo tun daga sama har k`asa kafin ta jeho mata da tambaya,"Ke ce ki ka Picking  Call ɗin d`azu da akayi ?",a tsorace ta d`aga mata kai alamun eh itace ta d`aga wayar.
  "Wace ce ke ko dai fiancee d`in sa ce ke ?".
 Ba tare da Hibba ta iya tsayawa ta tantance ma'anar tambayar da Cecelia ta yi mata ba ,ta sake amsa mata da Eh.
   Grandma ma ce ta maida kallonta kan Daniel tana mai cewa da shi," Yanzu Daniel for the God sake mene ne haka saboda ka na tare da Mace sai ka manta da mu,ka fidda mu daga cikin rayuwar ka,ka tada hankalin ka ka tada hankalin mu,me ya same ka da har ka aikata hakan?".
   Abbakar rasa me ce yai ganin yanda suka sauyawa lamarin ma'ana da kuma yanda suka d`auki ke shi da sauk`i,ganin ya kasa iya cewa komi yasa Grandma ta maida hankalin ta kan Hibba, ganin yanda take a firgice yasa ta kamo hannunta suka zauna akan two seater dake kusa da su,cikin kwantar da murya ta ce da ita,"Kin ga My dear ki kwantar da hankalin ki ba abinda za mu yi miki,Na ga duk kin tashi hankalin ki,ko ba ki san cewa ba a san Pregnancy Woman tana shiga cikin tashin hankalin ko damuwa ba,  cikin na ki watan shi nawa yanzu?".
     Cikin rarraba kalami ta bata amsa da,"watan shi bakwai","Oh sannu kin ji ina rok`on Yesu Almasihu da ya kare ki ya sa ki sauka lafiya ke da abinda ke cikin ki".
     Cecelia ce tamasa cikin murna tare da cewa,"Ina fatan in an tashi a haifi mace sai a sanya mata sunana kin ga ta My first Daughter kuma gata name sake d`ina".
    Sosai wad`annan maganganun ma su suka tada ma Hibba hankali ba ma ita kad`ai ba hatta da shi Abbakar d`in sai da k`irjin shi ya buga da ya ji abinda su ke cewa.
    "Ka bani mamaki Daniel,ban ga dalilin da zai sa don ka fara Dating ka k`aurace mana ba, meye nawa don kana tare da wacce ka ke so,iyakacin fa in samu ku albarka tare da fatan alkairi, ba zan hana ka kayi rayuwa da wacce ka ke so ba".
    Sake baki su duka biyun su kai sosai Abbakar ya Lula duniyar tunanin da San gani dalilin da yasa suke d`auki lamarin ta wannan fuskar, sai a lokacin ya kai dubanta shi kan kayan da ke jikin Hibba k`ananun kaya ne a jikin ta saboda cikin Na sanyata yawan jin zafi,wa da hakan yasa su ke ganin lamarin ta wannan fuskar,su duk a zato da tsanmanin su itama Hibba Crista ce.
    " Ka tashi hankalina Daniel akan lamarinnan bana samun isasshen barci Na takura ,Na Sanya Pastor yana yi maka addu'a ni duk a tunanin ko wani mugun abun ne ya same ke".
    Dakatawa tai tana  maaida kallonta kan Hibba ta ce da ita,"Kar ki damu da zaran kin haihu zamu had`a da bikin suna da kuma bikin ku musha shagali biyu a lokaci d`aya,fad`a min ya sunan ki".....
    "Grandma ba fa abinda ku ke tunanin ba ne ba, ni da ita munyi Aure mu d`in mata da Miji ne".
    Kamar wad`anda aka d`aukewa wuta haka Grandma da Cecelia suka tsaya cak komi nasu ya dakata na wucin gadi.
    Cecelia ce tai k`arfinta halin sake tambayar shi abinda kunnuwansu ya jiye masu," Da gaske kake Brox Daniel, wannan ɗin Matar ka ce,kayi  Aure,kuma ba tare da mun sani ba, me hakan ke nufi?".
    Wani yak`e Wanda yafi kuka ciwo Grandma ta saki gami da cewa,"Kinga Cecelia bi komi a hankali ya riga da yayi Auren fa,ba wai zai yi ba ne ba,abu guda da za ki tambaye shi,me muka aikata mashi wanne laifi ne mai girman gaske da mu kai ma shi har da muka can-canci ya fiddamu a cikin lamarin rayuwar sa?",Grandma ta kai k`arshe batun muryarta ta fara rawa alamun batun ya ta`ba mata Zuciyarta.
    "Ka kunyatar da ni,ako da yaushe in na zauna cikin friends d`ina bani da abun fad`a da ya wuce My son Daniel ya girma,in Aurensa ya zo zan yi kaza,zan sai kaza,zan sa kaza a jikina amma shine za ka yyudare ni ka je can kai Auren ka ba tare da na sani ba?".....
"Ki gafarce ni Grandma ba na aikata hakan don son nuna ba ki isa a cikin rayuwata ba ,ko don kunyatar ki ba, a'a na kasa samun natsuwa , Zuciyata na faɗa min ba lalle ku amshi abinda na zo maku da shi ba,kullum cikin fargaba da tashin hankali na ke"...
"A'a Daniel ƙarya ka ke dama can ka ayi biyar kunyata ni,Kai Ni ban ma yarda da abinda ka ke cewa ba".
    "Ki gafarce ni Grandma da gaske ne nayi Aure,sunanan ta ma Hibba kuma musulma ce,ni ma kuma na dad`e da musulumta".
    Wani irin tafiya taga-taga Grandma tayi zata fad`i k`asa inba dan yana kusa da ita yai saurin tare ta ba da Allah kad`ai yasan irin fad`uwar da za tai.
    " A'a Daniel na rok`e ka da ka k`aryata abinda kunnuwana suka jiye min ka ce ba gaskiya ba ne ba,mafarki na ke,mafarkin abinda ba zai ta`ba yiwuwa ba",Grandma ta fad`a hawaye Na rige-rigen sauka akan fuskarta
    Shima hawayen yake sakamakon ganin ta na hawayen da k`yar ya iya cewa da ita,"Da gaske ne Grandma na yi Aure,kuma sannan Na musulumta ni yanzu ba mabiyin addinin Crista ba ne,ni musulmine ,suna Na Abbakar ba Daniel ba".
    "A'a Brox Daniel kar kai haka ,kar ka ce ka bar addinin gaskiya, Addinin iyayen da kakannin ka,shin ina wata gaskiya ta ke a cikin Addinin da ba addinin Crista ba,ka tuba ka dawo ya zuwa addinin ka ka ji d`an'uwana Daniel"...
    Da hannu ya dakatar da ita," Kar ki sake kirana da wannan sunan suna Abbakar ba Daniel ba".
    "Oh Jesus ka kawo min d`aukin ka, sun asirce min d`a shikenan sun raba ni da shi,ka ga ka biyo ni mu je can Jos in had`a ka da Pastor Yohanna ya ba ka makarin asirin da su ka yi maka".
    Cecelia ce ta matsa kusa da Hibba idanuwanta na zubda hawaye ta ce da ita,"Me ki ka yi ma d`an'uwana da har ki ka rabashi da tunanin sa ki ka raba shi da addinin shi", ta kai zance ta na mai daka mata tsawa.
    " A'a wallahi ba abinda nayi masa,hasalima shi da kan shi yai sha'awar shiga muslunci ba tare da an tursasa shi ba ". Hibba ta bata amsa bakinta na rawa
    "K`aryar ki ke dole da akwai abinda ku ka aikata ma shi ,to ki sani ina mai rantse maki da Allah d`aya sai kin rabu da shi,sai kin bar cikin Gidannan domin nan ba gurin zaman ki ba ne ba"..... Cikin d`aga murya Abbakar ya daka ma Cecelia tsawa tare da fara yi mata warning," Ki shiga hankalin Cecelia Mata ta ce fa,ki fita a harkata domin babu ruwanta a cikin wannan Maganar,don rad`in kaina na ce ina son in musulumta haka kuma ina cikin hankalina na ganta Na ce ina sonta".
   "A'a Daniel kar ka ce haka,ka zo mu bar wannan Garin zaman ka a ciki ba alkairi ba ne ba,ka rabu da wannan Matar ba son gaskiya ta ke maka ba tunda har ta iya raba ka da Addinin ka,kar ka manta tun kana d`an k`arami ka na raine ka,Na baka kulawa da Soyayya,me ye zai sa yanzu da rana tsaka ka za`bi wata bare kuma ka fifita akaina,don haka ina mai umartaka da ka tashi a yanzu ba sai gobe ba mu bar wannan k`addararen Garin da banga amfanin zaman ka a cikin sa ba,ita kuma kai divorce d`inta ta tafi Gidan Ubanta".
     Wasu hawayen ne suka sake zubowa daga Idon shi kafin ya duƙar da kan shi ƙasa ya ce da ita "Ki gafarce ni Grandma, nasan kinyi matuk`ar k`ok`ari a wajen rsino da tarbiyar mu,a kan haka nake baki hak`uri domin ba zan iya yi maki biyayya a dai-dai wannan ga`bar ba,Addinin da nake a kai yanzu ya ce babu biyayy ga abokin halitta indai a wajen sa`bawa Ubangiji ne,kuma ni Maganar gaskiya ina son Mata ta da abinda ke cikinta,kuma ban shiga cikin Addinin muslunci don in barshi ba,kuma ina yi maku Addu'ar Allah ya sa ku gane gaskiya ku dawo cikin sa".....
    "Dakata min mara kuyar banza mara kuyar wofi, ai ashe bayan nasarar fidda ka daga cikin Addinin ka da su kai har rashin kunya su ka koya ma ka,to bari ka ji madamar ba ka sake ta ka zo mun bar wannan Garin a yanzu,ka bar masu Addinin su anan,tunda dama nan ka same shi,ita kuma ka sake ta da zaran ta haihu sai mu zo mu amshe abinda ta haifa shikenan, in kuma ba haka ba sai dai ka za`ba ko ni ko ita,domin ba zan iya cigabada da ganin ka tare da ita ba".
    Sai da Abbakar ya duk`ar da kanshi k`asa, hawayen saman fuskarsa na tsananta zuba kafin ya iya cire baki ya ce da ita," Grandma ki gafarce ni amma ba zan iya aikata da`ya daga cikin abubuwan da ki ka lissafo ba,ina son Addini na da kuma Mata ta,haka ke ma ba zan iya rayuwa babu ke ba"....
    "A'a Broth don't do that, wannan babban kuskure ne ta ya za ka yarda ka rabu da whole family d`in ka akan wata Mace ,Haba Broth think wisely mana,tabbas ka sa na ji Na tsananin wannan Matar har ma da abinda ke cikin ta ban san su ban ko San ganin su,By the grace of God d`an cikin ma ba zai rayu ba,ba za a haife shi da rai ba".....kafin ta rufe bakin ta ya sharara mata mari har biyu da iya kacin k`arfin shi,K`ara mai k`arfi ta saki gami da k`ank`ame Grandma ta na mai ambaton sunan Jesus.
    "Ba ka da hankali ne a gabana zaka sa hannu ka dake ta kuma akan mace ? "," Grandma ki Na jinta fa,kin ji mugun bakin da kuma aibatawar da ta ke yima iyali na fa".
    Duka Grandma ta fara kai mashi ta ko ina a jikin sa tana yi tana cewa ya cuce ta tunda har ya yarda ya bar Addinin Crista ya koma musulmine,sai da tai iya yinta ta sanan ta dakata dan kanta kafin ta dakata,"Ka sani daga yau bani ba ka,Na fita daga cikin duk wani sha'ani na ka ko na rayuwar ka,sannan kai ma ina son ka fiddamu a cikin taka rayuwar ba mu ba ka tunda Addini ya raba mu,a yau ba sai gobe ba zamu bar maka Gidan ka ka cigaba da rayuwa da wacce ka za`ba".
    Tana kaiwa nan ta sa`bi jakar da suka zo da ita gami da kama hannu Cecelia suka nufi hanyar barin Gidan kowa a cikin su fuskar jik`e take da hawaye.
    "Grandma bai kamata ku fita a cikin wannan daren ba,biside ma ai nan Gidan ku ne,ku yi hak`uri zuwa gobe komi zai dai-daita, please amma kar kuce za ku fita a cikin darennan,gano Jus daga Kano a irin wannan daren ai ba k`aramin abu ba ne ba".
    Cikin fushi Grandma ta ce da shi,"Ba zan zauna a cikin wannan useless d`in Gidannan ba ko da kuwa ina da tabbacin in Na fita zan gami da accident a saman hayata to na gwammaci in tafi,Na tsanai duk seconds ko minutes da na ke k`arawa a cikin sa kai na gwammaci in kwana saman Street da in kwana a Gidan ka".
    Sosai jikin Abbakar yai sanyi sakamakon jin abinda ya fito daga bakin Grandma, ita kuwa Cecelia tun d`azu ba abinda take sai kuka gaba ki d`aya ta fita a hayyacinta,sai a lokacin ta d`an d`ago daga jikin Grandma ta na  mai cewa da ita," Kin yi kuskure Babba a rayuwar ki ,tunda har ki yarda kuma ki ka amince ki rabani da yayana mutumin da ko tsawa bai ta`ba yi min ba amma yau ki ka sa ya dake ni,ki sani sai kin biya wannan bashin you will regret it ".ta na kaiwa nan a zancenta ta sake boyewa a jikin Grandma don kar ta sake shiga hannunsa.
    Duk yanda Abbakar ya so su Grandma su zauna a cikin Gidan ko kwana ne suyi kafin Safiya k`in yarda su kai ,haka su ka bar Gidan a lokacin goma da wani abu na dare,kai tsaye Tashar da suka sauka nan suka koma inda Allah ya taimaka su suna zuwa suka samu wata motar kaya anyi Lodi za a tafi suka shiga,dukkanin su ba su cikin natsuwa su,Cecelia kuwa har su ka tashi ba ta daina kuka ba,sai bayan motar tasu ta tashi sannan Abbakar ya koma Gida domin kasa barin su yayi yana biye da su a baya har suka tafi, ranshi a cunkushe ya juya nufi na shi Gidan.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol