Free chapter · Read without an account

Page 6

by Amina Abubakar Yandoma · DAYAN BIYU

ƊAYAN BIYU

©️MEENAT A 'YANDOMA

Wattpad: Meenat_A_Yandoma

ArewaBooks: Meenatyandoma

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

MASU BUKATAR A TALLATA MASU HAJARSU SU YI MIN MAGANA A WANNAN NUMBER ***

Page 06

...Salatin da ta yi shi ne ya tayar da sauran mutanen da ke a dakin.

"Lafiya Iya. me ya faru haka?"

"Ba lafiya Jaririya ta bace"

ta karasa maganar muryarta na kyarma.

"jaririyar kafafu gareta ko fiffike da za a naimeta a rasa. Mu dai kara bincika wa "

Daya daga cikin dangin Iya ta fada suna kara bincike dakin.

Wasa-wasa sai ga wankin hula na Naiman kai su dare.

Motsin da Iya ta ji daga karkashin gado ne ya sakata kunna fitilar wayar marigayiya ta haska.

Salati ta kuma yi cike da al'ajabin wannan lamari.

A kwance ta hango Bintu a karkashin gadon ta na ta wasa da kafafu. Fiddo ta yi kowa ya yi tsit! An rasa mai magana. "To ko dai kina bacci ta fado ta mulmula karkashin gadon duk ba ki sani ba"

Doguwar ajiyar zuciya Iya ta sauke tare da jin wani abu ya tokare mata zuciya.

"Tabbas akwai gagarumar matsala. Abin da ta ke tunani ya na naiman ya zama gaskiya, duk mai hankali in ya ga abubuwan da suke faru ya san jinjirar nan ba lafiya take ba"

Iya ta karasa maganar a cikin zuciyarta.

Daren ranar haka ta karasa shi ido biyu curr! Domin abin da ta lura ita ma jinjirar idonta biyu.

Bayan gari ya waye Inna da danginta gasarar da aka markado jiya suka dama koko da ita. Dan karamin bokiti suka zubawa Iya ita da ahalinta.

Duk da ɗaya daga cikin dangin Iya da ta so ta tayar da bore iya ce ta tausheta.

"Rayuwar duka nawa take, wadda ta haɗa kanta Ubangiji ya amsa abinsa. Kwana nawa ya rage muyi a gidan tafiya za mu yi kowa ya kara hakuri"

Ba don sun so ba haka suka amshi wannan koko da tsaf mutum biyu zai iya shanye sa.

Tunda garin Allah ya waye iya ke zuba ido ta ga ta inda Ɗan inna zai zo ya gaishesu, ko dan ya ga diyarsa amma shuru kake ji. A gaban idonta ta ga ya fito daga dakin Inna ya na dariya tamkar ba wanda aka yi wa mutu jiya jiyan nan ba.

Murja kuwa babu mutumci bare su saka ran samun gaisuwar arziki. Ita ma tare take da danginta suna ta hira da shewa tamkar ba gidan mutuwa ba.

Hawayen da bata san da zubowarsu ba ta share.

"Na yarda wanda aka yiwa mutuwa shi ta shafa. Shuhuda kin tafi kin barni tare da jinjira Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Allah ka na ji kuma kana gani. Kai ka san yadda zaka yi da mu."

Ta karasa maganar ta na tunanin inda za a samu ruwan zafin da za a wanke jinjirar ganin har rana ta fara, ga masu gaisuwa sun fara shigowa.

Da kanta ta nufi dakin Iya da ke cike da danginta.

Sallamar da ta tayi ma da kyar suka amsa ta.

"Dama ce wa na yi ruwan zafin da za a yima jinjirar wanka, na ga rana nata kara yi kada ta fara kuka"

"Ki duba tukunyar da na dama koko akwai sauran ruwan zafi a ciki"

"To Inna! Ko ke zan debomawa sai ki wanke takwararta ki?"

Jin abin da Iya ta fada a zaune take amma sai da ta mike tsaye.

"Ki turamin asiri, ki je can dai kiyi mata. Idanuwana yau bana gani sosai ki je dai kiyi mata"

Mamaki ne ya kama Iya ganin da gaske Inna gudun Bintu ta ke. Haka ta baro dakin jiki a sanyaye.

Da kanta ta kwaso ruwan zafin ta sheka bayan ya huce ta hau wanke Bintu.

Sai dai tun bayan fara wankan ta lura da abin da ya yi mummunan daga mata hankali. Da farko ta zata idanunta ne ke nuna mata ba daidai ba sai daga baya ta lura da gaske fa Dariya marar sauti Bintu ke yi.

Kuma ga dukkan alamu wasa take yi ita da wani a cikin ruwan. Ganin yadda take kallon gefe daya tare da tuntsurewa da dariya.

"Tabbas akwai abin da ke shirin faruwa ko kuma ya riga da ya ma faru. In ba haka ba ya za ai jinjira ta rika dariya, ko a tarihi ban taba ji ba"

Ta kasara magana a cikin zuciyarta.

Bata kara tabbatar da abin da take zargi ba sai da ta fito da Bintu daga cikin ruwan. Kuka ta fashe da shi, da sauri ta mayar da ita cikin dabara ta na yin tamkar ta na gargasata da ruwan.

A kalla ta dauki awa ɗaya a cikin ruwan har yan gaisuwa suka shisshigo. Ganin yadda ta jima a cikin ruwan ya saka Iya fito da ita

Sai dai a wannan lokacin shuru ta yi tana rarraba ido tare da karewa mutanen dakin kallon ta na tsotsar hannu.

Garwashi Iya ta saka aka debo mata. Sai dai abin da ta ke gani tamkar a mafarki, murza idaniyarta ta yi domin tabbatarwa shin gizo ne ko kuma gaske.

Gaske ne, ba Gizo bane an gasa cibiyar domin har duhu tayi alamun jiya ma an gasata.

"To waye ya gasa mata ita, bayan jiyan muna cikin tashin hankali"

Ta ma rasa wa zata fadawa wannan matsalar, shin mahaifinta da bai damu da ita ba ko kuma kakarta da a zahiri take gudunta. Ko jama'a da su ma suka fara tsoronta.

"Ke daya za ki fadawa kanki. Domin a halin da kike ciki ke ce mai bawa kanki shawara, muddun ki ka bari wani daga cikin wadanda kika lissafo ya ji wannan maganar. Ke da ita sai kun zama ababe tsana a cikin al'umma."

Wata zuciyar ta yi saurin gargadinta.

A daddafe suka karasa kwana bakwai.

A tsawon kwanan bakwai sam Ɗan Inna ya daina shiga ya ga lafiyar Bintu. A takaice ma ya ki yanka abin suna koda dan taure ne.

Ganin babu tsayayyar maganar da suka mata har maraice yayi ankara ta yi Dan inna ya fada dakin Inna ya sa ta ji karfin tunkararsu.

Da sallamarta a bakinta ta shiga dakin.

Sai dai yanayin amsawar da suka yi mata hakan ne ya kara tabbatar mata da bata samu tarbar kirki ba.

"Dama ce wa na yi tunda yau kwana bakwai da rasuwar Shuhuda. Ya kamata mu san abin yi game da abin da ta bari."

Gaban Inna ne ya yanke ragass! Ya fadi.

"Ni dai har ga Allah na so rike Bintu amma na duba na ga hakan ba zai yiwu ba. Ni kaina da kyar na ke ciyar da kaina bare kuma jigilar Jaririya ga kuma kullum karfina karewa ya ke yi. Shi ne na ce ko ke za a barma ita tunda kinga ga Murja ke ba aikin gida za ki yi ba kinfi samun damar kula da jinjirar, kama daga madara da duk wani abu na bukata ga Dan Inna nan zai siyo miki"

Ai bata bari Iya ta kai aya ba ta kwace zancen.

"In riƙe wa? In raini wa? To ni kaina abin da nake son fada miki In aka samu wanda zai raine Ni ba zan ki ba. Ni da lamuran duniya duk suka fara kwance mini ta ya za ki hadani da jinjira in kai ta ina?"

Baki sake cike da zallar mamaki Iya ke kallon Inna jin irin abin da ke fitowa daga bakinta.

"Kuma ma kingan ni nan? In dare ya yi ina da dundumi bana gani sosai ta ya zan iya rainon Bintu. Ke dai ki je da ita in ya so in ta yi Wayo sai ki kawota, Muja ta haɗa da tagwayenta maganar raino ki cireni a ciki. Ga ubanta nan duk in madararta ta kare zai kawo miki"

Iya kuwa samun kanta tayi da amsa musu.

"To babu damuwa Ubangiji ya ba Ni ikon kula da wannan marainiya"

Caraf Inna ta amshe da amin.

Wurin bankwana kuwa Hussaina hada kukanta zata bi Iya. Sai da Murja ta lulluka mata ashar kafin ta yi shuru.

Haka Iya ta baro gidan hawaye na fita a fuskarta ga goyon Bintu ga kullin da kayanta a ka.

Ta na cikin tafiya ta tuna ba a yi wa Bintu gyaran komai ba. Ganin ta na gaf da gidan Idi wanzam duk da duhun magriba da ya fara gidan ta shige.

Ta ko yi sa a ya na nan. Bayan sun gaisa ya amsa Bintu da ke faman tsotsar hannu.

Kare mata kallon yayi tare da duba ta tsaf.

"Iya ko dai rasuwar ce ta ƙara ruɗaki har haka. Wannan jinjirar ai an jima da yi mata gyara"

"An mata gyara da ka ce?"

"Kwarai kuwa"

Ya bata amsa

"Sake dai dubawa domin tunda mahaifiyarta ta rasu babu wanda ya bi ta kanta a kan ayi mata gyara kamar yadda al'ada ta tsara. To in an mata gyara ya a ka yi gashin kanta ga shi nan ba a aske ba?"

"To kamar dai yadda na fada miki da farko. Kin sani ko ba ki sani ba wannan jinjira dai an yi mata gyara. Gashin kanta kuma ko da wasa kada ki bari wani ya ce zai yi mata aski ku barta da kayanta. Domin wasu abubuwan ido ba zai iya hango su ba"

A rikice Iya ke kallonsu domin ita yanzu lamarin Bintu ya fara tsorata ta.

"Na rantse maka da Allah wanzam ba a yi mata gyara ba"

Ganin yadda ta ke maganar ya saka wanzam amincewa. To amma wa ya yi mata wadannan abubuwa.

"na Fahimci abin da ki ke fada. To abin da zan fada miki shi ne Ɗayan biyu, ko dai aljanu na shirin shiga a jikin jikarki ko kuma wani abu daban. Amma babu damuwa zan ba ki wasu magunguna ki riƙa yi mata amfani da su. Domin ni kaina na hango abubuwa da dama game da ita. Ki bi sannu da Jaririyar ki saka ido kuma ki kula"

Jikin iya kara yin sanyi yayi ganin irin magungunan da ya hado mata.

Lokacin da Iya ta baro gidan ana ta sallar isha'i gari ya yi duhu sosai sakamakon daharin da ya hadu.

Sauri ta kara yi gudun ka da ruwa ya tare ta a hanya ga kuma danyar jinjira. Kiciɓus ta yi da daya daga cikin matasan da ke a unguwar. Bayan sun gaisa ya mata gaisuwa ya ke. Sanar da ita wata mata ta kawo masarar jarirai mai uban yawa da sauran abubuwa, ta ce Kawar Shuhuda ce bata samu komawa can gidan kamar yadda ta fada musu ba.

"Ni ma da kika ganni tsaye a nan ta bani kudi ne a kan in tsare miki gidan har ki dawo, tunda kin dawo nima Bari in fice"

Ya yi gaba ba tare da jiran abin da zata fada ba.

Gaban Iya dakan uku-uku ya fara. Cikin hanzarinta ta shige gidan.

Yar fitilar wayar marigayiya ta haska. "Subhanallah"

Ita ce kalmar da Iya ta furta a lokacin da ta yi tozali da uwar madarar jariran da aka jera mata cikin daki. Gefe guda kuma kayan jarirai ne sabbi Dal! Kama daga overroll tsadaddu,famfas 'yan kanti abin mamaki yan kanti hada oversize wato waɗanda ko da ta girma zata saka ga kuma na yan shekara daga daya zuwa biyu. kai duk wani abu na bukatar jariri a aje mata.

Ta ma rasa shin wannan matar wace irin alaƙa ce a tsakaninsu da Shuhuda da za ta rika yi wa ɗiyarta hidima har haka. A ƙalla madarar da aka jingine mata zata kaita wata goma.

Iya ta gyara kafitar ta da ke baje a kasa ta share dakin tare da kwashe kayan jariran ta zuba a cikin sif dinta data gaji da wargajewa domin murfi daya gareta dayan ya fita.

Madarar ta dama ta ba Bintu, ta kwantar da ita ita ma ta kwanta.

Iskan da aka fara ne ya tabbatar mata da ruwa na iya sauka a ko wane lokaci. Kyauren dakinta ta samu ta rufe tare da danna akwatin karfenta a bakin kofar.

Ruwa aka kece da shi tamkar da bakin kwarya. Kara shigar da Bintu da ke ta faman tsotsar hannu ta yi a jikinta, a haka bacci ya yi awon gaba da ita.

Tafiyar da ta ji ana yi ce an nufo dakinta ta saka Iya bude ido a firgice. Ƙarar kwankwasa kofar da aka fara ce ta sakata mikewa zaune a gigice tare da rasa sauran nutsuwarta...

Meenat A 'Yandoma

***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol