Free chapter · Read without an account

Page 7

by Amina Abubakar Yandoma · DAYAN BIYU

ƊAYAN BIYU

©️MEENAT A 'YANDOMA

Wattpad: Meenat_A_Yandoma

ArewaBooks: Meenatyandoma

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

MASU BUKATAR A TALLATA MASU HAJARSU SU YI MIN MAGANA A WANNAN NUMBER ***

Page 07

...A ɗan rikice ta shafa gefen da Shatu ke kwance, sai dai wayam bata ji a lamun mutum ba. A rikice ta janyo fitilar da ta ke gefenta ta kunna.

Sake kallonta ta yi tare da murza idanunta ko abin da suka saba yi mata ne yanzu ma suke mata, wato gizo?

Jike jikin Bintu ya ke sharaf da ruwa. Ba wai jikin kayanta kadai ba har saman kanta ruwa ne tamkar an tsomata an fiddo.

Tsoron ƙara kama Iya ya yi sai dai ta lura motsin da ta ji yanzu an daina shuru har bugon kofar ya dakata.

Iya ta ma rasa ta ina zata fara

"Shin wa ya tsoma Bintu cikin ruwa? Ko dai fitsarin kwance ne ta yi?"

"Fitsari kuma shi ne har saman sumar kanta?"

Wata zuciyar ta yi saurin tunatar da ita.

Cikin hanzarin ta mike ta na cire mata kayan, sai dai abin da ya bata mamaki Babu alamun Bintu na jin sanyin da ke a jikin kayan.

Ta na gama saka mata kaya ta goya ta ba a jima ba a ka fara kiran asuba.

Har ta zo bude daki ta ji gabanta ya fadi da ta tuna abin da ya faru jiya.

Dakewa ta yi a bakin kofar ta kasa gaba bare baya.

Addu'a ta yi tare da yin imani da Allah ta bude kofar ta fito. Alwala ta yi bayan ta gama sallar nan bacci ya kwasheta har gari ya waye.

Hayaniyar Inna Zulai ita ta tayar da ita daga baccin da take yi.

"Ai dama na fada miki sai dai ayi gawa biyu. Kamar yadda ta kashemin Tala ita ma wannan duniyar ta fi karfinta. "

Duk da maganganun Zulai sun yi wa Iya zafi amma haka ta daure tare da yin yaƙe wanda ya fi kuka ciwo.

"A kullum kamar yadda nake fada miki kiji tsoron Allah, yau ma zan sake fada miki. Kiji tsoron Allah sannan duk nisan jifa kasa zai fado, Allah ne ya baki dama kiyi duk abin da za ki yi kafin ya miki kamun kazar kuku. Kin azabtar da ni tun da rayuwar mijinmu yanzu ma babu shi amma ba za ki barni in shaki iskan 'yanci na. Sannan maganar da ki ke yi ta tunda Tala ta mutu sai Shuhuda ta take mata baya, ki sani ke baki isa kiyi abinda Allah bai amince ba. Har cikin raina na yarda lokaci ta ne ya yi shi ya sa Allah ya amshi a barsa."

Tuntsurewa da dariya Zulai ta yi.

"Kin gama? Na ce kin gama ko da saura. To bude kunnuwanki da kyau ki saurareni, a tunaninki da mijin da muke aure ya rasu shi kenan mun rabu? Ai kuskure na farko da kika yi a rayuwarki shi ne auren mijina da kika yi. Ki sani har abada ba zai daina bibiyarki da sharri ba har sai ranar da kasa ta rufe miki ido ko kuma ni ta rufe nawa ido."

Shuru Iya ta yi domin da mutumcinta, yadda kowa na unguwar ke mutuntata ba zata bari a ji kansu da Zulai ba.

"Kamar madara na ke gani, waye ya kawo miki madara har haka? Ko da ya ke tunda kin dauka wannan aljanar diyar dole sai da madara. A ciki akwai hakkinmu, don haka bari ki gani dole in daukarwa Nuzula Tunda wa ma ya sani ko wani abokin mahaifinsu ne ya kawo ki kahandame tare da hana kowa"

Ta karasa maganar tare da ɗaukar madarar har gwangwani uku ta fice

Girgiza kai Iya ta yi cike da takaici.

"Komai ki ka yi don kanki Zulai."

Iya ta fada tare da dama madara ta ba Bintu.

Bacci ne ya kwasheta, kallonta Iya ke yi ganin yadda bata bacci da dare sai garin Allah ya waye.

Ruwan zafi ta ɗora da sauran itace da suka rage mata kafin Bintu ta gama bacci.

Tagumi ta tafka da duka hannuwanta biyun.

Ya rayuwarta zata kasance tare da Bintu? Ita kanta da kyar ta ke ciyar da kanta. Daren da Shuhuda zata rasu ta je gidan kansila neman aikatau wanda zata rike kanta ko abinci ta rika samu. Sun amsa mata ta zo washe gari sai ga wannan abu ya faru ta san da wahala in ba su samu sabuwar mai aiki ba.

Kamzon da ya rage mata ta dauko ta daka tare da jika shi, sai da ta tabbatar da ya jiku ta zuba gishiri ta ci. Sallamar da ta ji a na mata ce ta sakata juyawa da sauri.

Dattijuwa ce ba zata wuce sa'arta ba. Bayan sun gaisa take mata gaisuwa tare da shaida mata daga gidan kasilan kauyen ta ke. Sun aikota ne ta yi mata gaisuwa sannan ta shaida mata zata Iya cigaba da zuwa aiki daga yau. Ba karamin dadi Iya ta ji ba ko ba komai zata samu abin ci har ma da kudin da zata yi hidimar gabanta.

Bayan tafiyar dattijuwar ruwan wankan ta sirka sai dai har yanzu bacci ta ke. Sakata cikin ruwan da ta yi shi ya sakata bude dara-daran idanunta tare da sauke su a kan Iya.

Samun kanta ta yi da jin gabanta ya fadi sai dai bata wani damu ba domin In da sabo ta saba da jin gabanta na faduwa.

Babbar damuwarta kada su ce ba su son karamin yaro ita ko ina zata kai Bintu.

Ta dauki minti talatin ta na mata wanka data fito da ita sai ta fashe da kuka, dole ta maidata cikin ruwan. Awa gudu suka kwashe suna abu daya kafin ta fito da ita daga cikin ruwan.

Mayukan da ke cikin kayan da aka kawo mata ne duk da bata san a inda ake shafa wasu ba haka ta shafa mata wasu ta na rirrigata duk dan ta koma bacci amma ina idonta biyu tarr! Wasu hadaddun riga da wando ta fiddo daga cikin ledarsu ta saka mata tare da sa mata hula mai haɗe da safarta kala ɗaya.

Kwantar da ita ta yi a saman katifa da nufin ta je ta yo wanka sai su wuce wurin aiki.

Kasancewar jiya da dare an kwana a na ruwa ruwan sama ta sirka da sauran ruwan zafin da ya rage ta kai bayan gida.

Kamar wasa sawun kafar karamin yaro ta gani kwance kasar da ta jike ta tsakar gida. Sawaye sosai

"To amma wa ya ya shigo mata gida kenan? Ko da ya ke ta kwana biyu bata nan kuma gidan babu kyaure dole ko yara ne su shigo suna mata wasa."

Da wannan tunanin ta yi wanka ta shirya tare da goya Bintu ta nufi gidan aiki.

Mutsirniyar Bintu ta hauyi cikin hijabi, ba arziki ta dage hijabin sai ga shi ta nutsu. Mamaki ne ya kama Iya.

"Ko wata daya bata yi ba sati daya da 'yan kwanaki amma ita ce ke son a dage mata hijabi?" Da wannan tunanin ta karasa gidan kasilan.

Sunyi mamaki ganinta da Jaririya domin sun san tsohuwa. Bayanin da ta yi masu ce War jikata ce wadda mahaifiyarta ta rasu sai ba su da mu ba duk da dai Hajiyar bata son masu aiko na zo mata da yara haka ta hakura.

An fiddama Iya ayyukan da zata rika yi. Share gida da dakuna sai gyara madafar abinci. In ta gama ita ce zata dafa abincin rana, suna da wadda ke masu na dare kudin albashinta dubu goma duk wata. Sannan zata iya dibar abincin ta tafi da shi gida, amma fa safko zata rika yi.

Safko jinjirar da Hajiyar ta ga anyi sai da gabanta ya fadi. Ita dai a kaf rayuwarta ta jima kafin ta ga mai kyawun wannan yarinya. Aiko Iya zata yi aiki ne a yanzu kafin diyar nan ta zaka budurwa, domin wannan in na bari har ta zama budurwa a na zo min da ita gida tsaf zata aure maka miji. "To amma ina tsohuwar nan ta samu kaya masu tsada ta saka mata. A iya sani na wanda ke da kudin Siyan kayan nan ba zai zo ya na naiman aiki ba. Ko da ya ke ai tana da uba kila shi ya siya mata su"

Hajiya ta fada a cikin ranta. Shigowar Alhaji da kansa ya yi ma Iya gaisuwa tare da bata dubu uku a kan ta rika hawan mashin In Zata zo, tunda ba ita ɗaya ba ce hada jinjira.

Ba karamin dadi kudin nan suka yi mata ba, musamman da ta tuna da abubuwan da ta ke Naima kuma ga shi bata da kudi.

Dakin Hajiyar ta fara gyarawa sannan ta nufi dakin ɗan Hajiyar Adam Dan shekara goma sha biyar. Kallon banza ya watsama Iya tare da ficewa ya bar mata dakin.

Dakin ta gyara tsaf tare da kwantar da Bintu gefen gadon ta shiga kewayen da ke cikin dakin ta na wanke wa.

Shigowar da zai yi ya hango jaririya kwance a saman gadonsa. Ashar ya kunduma ya na kallon yarinyar da ke faman tsotsar hannu.

Kallonta yayi ya kara yi

"Kamar fa ba diyar mutane ba"

Ya fada a zuciyarsa. Duk da ya ga Jaririya ce amma haka ya ficikota daga saman gadon tare da kwalwa iya kira.

Gani irin daukar da ya yi mata hannunta zai iya karshewa shi ya firgita ta.

"Wa ya baki izinin doramin ita saman gado. Daga daukarki aiki za ki sakamin ita a inda nake kwana salon ta yi min fitsari."

"Don Allah kayi hakuri ka bani ita hannunta zai iya karyewa. Kuma wallahi a kwai famfas a jikinta shi ya sa ma na dorata"

Tamkar wasu kayan wanki haka ya watso mata ita Ubangiji ya rage mata wahala ta yi saurin rikota gabanta na tsananta faduwa.

Ko a jikinsa haka ya fice daga dakin. Kallonta Iya ta yi ganin duk matsar nan da ta sha bata yi kuka ba sai ma dayan hannunta data saka a baki ya kasance duka hannuwanta biyu kowane ta saka yatsa daya a cikin baki.

Sake da baki Iya ke kallon wannan ikon Allah. Ita dai tunda ta zo duniya ta sha ganin masu tsotsar yatsu biyu wasu har ma uku, amma yau gata ta samu mai saka duka hannuwanta biyu ko wanne ta saka yatsa daya.

Gudun kada wani ya gani saurin goyata tayi tare da fitowa ta nufi madafar abinci.

Inna Zulai kuwa bayan ta ba Nuzula madarar ta mata shan mugunta, hada kwabawa ta shafa a fuska domin ta ji ance 'yan burni kyawun da suke hada madara suke shafawa a fuska. Haka ta sameta ta yaba a fuska ta baje tsakar daki ta na kwasar bacci.

Tamkar wadda aka tsirama Allura ta fada kewaye da gudu. Ƙarar fitar zawon shi ya cika gidan dole Inna Zulai ta fito. A daddafe Nuzula ta fito daga bayan gidan tana sharce gumi.

"Hala wurin ciye ciyen tsiya kika kika ciyo abin da zai sakaki zawo"

"Ni inna ba abin da na ce abin da duk yau ban ma kai ga fita ba.."

Maganar ta ce ta makale sakamakon amai da ta shiga kwarayawa. Kafin ka ce me jikinta ya fara saki.

Ba tare data gama aman ba a guje ta fada bayi.

Tamkar an kunna famfo haka amai da zawo ke fita.

Ga wani irin uban ƙaiƙayi da fuskarta ke yi.

Da kyar ta fito tare da wanke fuskarta sai dai duk in da ta sosai wasu irin kuraje ne ke Kunno Kai.

Bajewa ta yi a tsakar gidan a galabaice, kafin ka ce kwabo zawo da amai sun kuma balle mata a inda take kwance ta kasa daga ko da ɗan yatsanta ne. Inna Zulai ce ta fito ta na salallami.

Iya kuwa tsaye take a cikin falon, bayan ta gama aikinta ta goya Bintu hannunta rike da kullin abincinta ta na jiran Hajiyar ta fito suyi bankwana.

"ƙyal-ƙyal-ƙyal"

Iya ta ji Bintu da ke bayanta ta kwashe da dariya. Firgita ta yi domin yau ne karo na farko a tsawon rayuwarta da ta ji jinjiri ya yi dariya.

Mamaki bai gama sakinta ba Adam ya sako ƙafarsa cikin falon ba tare da sallama ba. Cikin ikon Allah ƙafarsa ta goce, tamkar wanda aka dauka aka buga da kasa sai gani Iya ta yi ya na taga-taga zai fadi.

Can gefe aka watsar da shi. Ji kake hannunsa ya bada sauti ƙasss! Ihun da ya kwala shi ya saka Hajiyar da fitowarta kenan ita da Iya yin kan sa a gigice...

Meenat A 'Yandoma

***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol