Free chapter · Read without an account
Page 08
ƊAYAN BIYU
©️MEENAT A 'YANDOMA
Wattpad: Meenat_A_Yandoma
ArewaBooks: Meenatyandoma
MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION
MASU BUKATAR A TALLATA MASU HAJARSU SU YI MIN MAGANA A WANNAN NUMBER ***
Page 08
... A rikice Hajiya ke tambayarsa lafiya. Sai dai tsabar azabar da ya ke ji ce ta saka ya kasa yi mata magana sai faman ihu ya ke tsalawa.
Iya kuwa tuni jikinta ya hau rawar mazari domin jikinta ya bata hannun Adam ya karshe. Kuma abin da ta kula da shi da hannun da ya dauko Bintu ne ya karshe.
Alhaji ne ya katse muta tunani ta hanyar daukar Adam suka nufi asibiti. Tunda Iya ta baro gidan bata san inda kafarta ke sauka ba, zuciyarta cunkushe da tunane-tunane.
"To yanzu idan Adam ya mutu wace makoma gareta? Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!" Ta ci gaba da nanatawa.
Shawara ta yanke ta wuce gidan Babbar aminiyarta Yafundo.
Tunda ta shiga gidan ya fundo ta amshi Bintu Iya ta yi shuru tare da buga Uban tagumi. Da dai Yafundo ta ga tagumin ba mai karewa bane kafadar Iya ta dafa.
Da sauri ta zabura tare da kallonta.
"Ko baki fada ba da ganinki nasan kina cikin matsananciyar damuwa. Na san Shuhuda ita ce ta rage miki mai tausayinki tare da jin kanki a wannan duniyar. Amma ki saka a ranki, Ubangijin da ya amsheta ya fili bukatarta don haka ki cire duk wata damuwa a ranki"
Doguwar ajiyar zuciya Iya ta sauke tare da kallon yafundo.
"Maganar Shuhuda tuni Allah ya bani karfin zuciyar da na danga. Ya Fundo ina cikin gagarumar matsalar da ba za ki gane abin da nake nufi ba. "
Nan fa ta shiga zayyana mata abin da ya faru daga farko har karshe
Shuru ta yi domin ita dai a rayuwarta bata taba jin labarin abin da ya faru irin wannan ba.
"Iya akwai damuwa. Domin tun lokacin rasuwar Shuhuda na lura da jinjirar da da duk wani abu da take yi. Zamanta a wurinki ba zai dauki dogon lokaci ba, duk da ce War tun farko ma bai kamata su baki ita ba. Ke yanzu karfin ki ya kare baki iya rikon jika kuma jinjiri ina za ki da shi. Ke ma baki fi a ce kin koma gidan 'ya'yanki a na kula da ke ba. Komawar Bintu a gaban mahaifanta dole ce ko dan su tashi su hau nemar mata magani."
Jin abin da ta fada ya saka jikin Iya yin sanyi. "Ta saukarwa Shuhuda alkawarin kula da Bintu, sai dai ga shi tun kafin tafiya ta yi nisa magana na neman cenzawa"
"Duk da haka dole ki mayar da ita. Domin mayar da ita shi ne abin da za kiyi mata ki nuna mata gata. Zamanta a wajenki ba hanya mai bullewa ba ce"
Babu yadda Iya ta iya, dole ta yi na'am da abin da ta fada mata. Abincin da ta zo da shi ta dauko suka ci bayan sun gama ta nufi gida.
Tunda ta fara tafiyar Bintu ke mutsurniya ta na shakuwar ppta ki zama a bayan dole ta sauke ta.
Kasancewar sai ta bi ta wurin rafi ya saka Iya lullubeta da zanin goyon ta na tunanin ko kishin ruwa ta ke ji.
Da sallamarta ta matsa kusa da masu dibar ruwan ta bukaci su taimaka mata zata ba jinjira ruwa.
Kallonta suka yi tare da kallon Bintu da ke faman shan hannu.
"Mu ba ki ruwa da kika ce? To baiwar Allah ba haka muka fito yi ba, ke yanzu da tsufanki amma baki daina haihuwa ba. Ku fa dubi diyar kamar aljana tsabar kyau, gaskiya ba za mu ba ki ruwan nan ba ƙara gaba domin ke da ita duk ba mu yarda da ku ba"
Ta karasa maganar tare da tuntsurewa da dariya ita da aboyarta.
"Bayin Allah ruwa fa ne zaku taimakamin da shi. Yarinya sai shakuwa ta ke yi "
Iya ta karasa maganar cikin sigar tausayi.
Ɗayar budurwar ce ta hayayyakuwa Iya tamkar zata kai mata duka.
"Ke ba za mu bayar ba. In ke mayya ce sai dai ki fara cinye abin da ke hannunki"
Babu yadda iya ta Iya dole ta juya zata bar wurin sai dai abin da ya faru a gidan aikota ne ya sake faruwa. Bintu ta tura yatsan dama da haggu a cikin baki. Gaban Iya bai ƙarasa faduwa ba sai da ta jiyo kururuwa a bayanta.
"Jama'a ku taimaka mana, fadi ta fada rafi"
Ita ce maganar da ta daki dodon kunnen Iya.
Kafin ka ce me wuri ya cika jama'a an rasa wa zai shiga ya fito da ita, gata dai suna gani sai ta yi sama ta na daga hannu alamar a taimaketa sai kuma ruwan ya kara dannata can ƙasa.
Kyarma hannuwan Iya suka fara ta ma rasa me ke mata dadi. "Kenan da Bintu ta saka yatsunta na hannuwa biyu a cikin wani mugun abu ne zai faru. Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!"
Ita ce kalmar da ta shiga nanatawa.
Ganin an fito da ita babu rai ya saka Iya barin wurin cikin hanzari, gudun abin da zai je ya dawo.
Tafiya ta ke amma ba ta san in da kafarta ke sauka ba sunan Allah kawai ta ke nanawata.
Isarta kofar gidan ta ci karo da an fiddo Nuzula ba ta san wanda ke a kan ta ba, an saka a mota sun nufi asibiti.
Da mamaki take kallon lamarin to me ya faru bayan tafiyarta.
Wani yaro ta ke tambaya abin da ya faru. Nan ya sanar mata tun bayan tafiyarta take sheka amai da zawo ba ƙaƙƙautawa.
"Allah ya bada lafiya "ita ce kalmar da ta fada ta shige gida.
Da kudin da mijin Hajiya ya bata ta aika wani yaro ya siyo mata icce mai dan yawa wanda zai isheta ta rika yiwa Bintu wanka.
Ko da ta gama wankan yau ma bata yarda aka cireta daga cikin ruwan ba sai da ta kusa kwashe awa guda cur!
Wannan lamari shi ke kara tsorata Iya. Motsin da ta ji ne alamun an shigo ya sakata juyowa.
"Hussaina"
Iya ta furta cike da mamakin ganinta.
Bayan sun gaisa Bintu ta ɗora Mata saman cinya cike da murna ta fiddo madara ta mika ma Iya.
Murmushi iya ta yi
"Wa ya ba ki wannan madarar"
"Ni na dauko cikin wadda Baba ya kawo ma mama, tunda bai kawo ma Bintu ba ita ma rabonta ce na kawo mata"
"Ki daina dauko abu In ba a baki ba kinji, ba kyau. Gida an san nan kika taho?"
"Aa Iya. Aikena Inna ta yi shi ne na guda nan sai na ga kanwata. Iya don Allah ki maidota gudanmu, kema sai ki dawo nan da zama"
Dariya Iya ta yi.
"Kada ki da mu da ta yi arba'in zan dawo muku da ita gidanku"
Murna ta hau yi jin za a dawo masu da ƙanwarsu.
Ganin duhun maraice zai fara Iya ta saka Hussaina ta fi kada a yi mata fada.
Bayan Iya ta yi sallar magriba ta ji motsin a gidan Inna. Zata saka hijabi ta zagaya ta ji ya jikin Nuzula, sai ganin Inna ta yi ta fado ko sallama babu.
"To munafukai wanda makwaftaka da su ma bala'i ce. Ashe kinsan madarar da ki ka bani lalatacciya ce shi ya saka ba ki hana in dauka na kin san muguntar da kika shirya da ma?"
Da mamaki iya ke kallonta jin irin maganganun da ta ke furta wa.
"Lalatacciya kuma?"
"Eh mana dole ki hau borin kunya, tsaya ki ji na rantse miki da a ce wani abu ya samu ɗiyata da sai an maimaita abin da ya faru da Tala da kuma Shuhuda."
Da sauri Iya ta kalli Inna.
Wurgo Mata sauran madara daya da ta rage tayi
“Ga tsinyatakunki nan"
Ta karasa maganar tare da ficewa.
"To in ta lalace me ya sa in na ba Bintu ko amai ba tayi ba bare zawo. Anya kuwa gaskiya ne abin da Inna ke fada to me ya saka da Nuzula tasha ta bata mata ciki."
"Saboda ba don ita aka kawo ba"
Wata siririyar murya ta fada.
Waige-waige ta hau yi sai dai wayam bata ga kowa ba. Hannu bibbiyu ta saka tare da rafka tagumi.
"Ko ya jikin Adam, wadda ta fada ruwa da gasken mutuwa ta yi?"
Ta jefawa kanta tambayoyin ba tare da samun amsarsu ba.
Tashi ta yi ta yi sallar isha'i, bayan ta gama ta kwantar da Bintu bisa tabarmai ta shiga domin kakkabe masu ida zata zasu kwanta.
Sai dai bayan ta fita ba a inda ta ajiye Bintu ta same ta ba.
An canza mata wuri. Man fa Iya ta kara rikicewa ta ma rasa me ke mata dadi.
"Ko dai idanunta ne ke mata gizo"
Da wannan sabon tashin hankali ta dauke ta suka shiga dakin ta kwantar da ita duk da ta san ba bacci zata yi ba.
A subahin fari bayan ta ɗora ruwan wanka sallah ta tayar, ta na ganawa ta hau neman magungunan da Idi wanzam ya bata. Sai dai sama ko kasa bata gansu ba, abu kamar wasa magunguna sun bace sama ko ƙasa.
Da dai ta lura da gaske sun bace cike da damuwar wannan al'amari ta yi ma Bintu wanka ita ma ta shirya suka nufi gidan aiki.
Sai dai tun daga bakin kofar gidan gabanta ya fara faduwa, kamar karta shiga sai kuma wata zuciyar ta ce ta shiga.
Zaune ya ke saman kujera da hannunsa saƙale a wuya.
Bayan sun gaisa take jajanta ma Hajiyar nan take sanar da ita faduwar da ya yi karaya ce. Asibitin cikin gari aka daurasa.
Shi dai Adam tun bayan shigowarsu ya sha jinin jikinsa, domin shi kadai ya san me ya gani jiya a mafarki. Ita kanta Iya mamaki yadda Adam ya yi ladabi take yi ko ido baya yarda su hada.
Yau dai har ta yi aiki ta gama bata samu matsala da kowa ba, tunda jiyan ma Adam ne ya so kawo mata matsala.
Bintu ta goya tare da ɗaukar abincinta ta nufi gida.
Tunda ta biyo hanyar gida take jin gabanta ya tsananta faduwa. Daga nesa ta hangota tsaye a kofar gidanta.
Gabanta ta ji ya yanke ya fadi domin kuwa ita ce, to me ya kawo ta "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun"
Ta shiga maimaita wa ta de da jin kafarta ta kasa ci gama da tafiya tamkar an daddaureta...
SAURA PAGES BIYU FREE PAGE YA KARE. SAKAMAKON KORAFE KORAFEN DA NA SAMI MUTANE BA KUDI. ZAKU SAKA 300 A MAIMAKON 500 IDAN KWANA BIYU SUKA KARE YA DAWO AINAHIN KUDINSA WATO 500. ZA KU KUDINKU TA NAN
2294023532 UBA BANK
AMINA ABUBAKAR
Meenat A 'Yandoma
***