Free chapter · Read without an account
Page 10
ƊAYAN BIYU
©️MEENAT A 'YANDOMA
Wattpad: Meenat_A_Yandoma
ArewaBooks: Meenatyandoma
MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION
MASU BUKATAR A TALLATA MASU HAJARSU SU YI MIN MAGANA A WANNAN NUMBER ***
LAST FREE PAGE✅
Page 10
...Hannu ba tare da gangar jiki ba ne ya shake Murja da ta Jima da bata jikinta da fitsari tsabar tsoro.
Hajijiya ya rika yi da ita tamkar kana juya waina a tanda. Ga ihu ta na so ta yi ba hali yi. Kanta ne ya juye ta koma ganin komai bibbiyu, daga nan bata kara sanin me ke faruwa ba sai Inna ta ji ta na mata sannu.
Idanunta ta sauke a kan Hussaina da ke rike da Bintu. Zabura ta yi ta mike ta na kokarin kamo Hussainar, abin da aka mata dazu ne ya dawo mata sabo fill! Ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin in da aka gano su.
"Ai Murja kin auna arziki. Da muka gano yaran nan ba shakka da ke za a fita nemansu domin duk ke ce kika haddasa batansu. Shi ne kafin mu dawo za ki wani suma a cikin gida."
Murja kuwa sam bata bi ta kan Inna ba domin a yanzu ba abin da take da bukata kamar ta samu damar fita zuwa wurin Bokanya.
Da dai Inna ta ga Murja ta ki kulata shareta ta yi tare da tunanin irin kwanan da za su yi da yarinyar can.
"Ya kika iya? Dole kiyi hakuri da ita, domin dai ta riga da ta zame miki karfen kafa."
Kamar Bintu ta ji abin da Inna ta fada dariya ta ga ta na mata mai ban tsoro. Da sauri ta kauda kanta jikina kyarma.
Har dare ya yi Bintu na hannun Hussaina, sai da Hussainar ta yi bacci sannan Inna ta maidata dakinta ta na rarraba ido.
Shuru Inna ta yi ta rasa me ke mata dadi. Ita dai har ga Allah ba ta so a ka bata rikon wannan yarinyar ba, abin da ta kula da shi har yanzu ba ta yi bacci ba ga shi ita dai so ta ke ta yi bacci.
Shigowar Ɗan Inna ce ta saka ta jin hankalinta ya ɗan kwanta.
"Ɗan Inna hankalina ya kasa kwanciya, anya kuwa za mu iya rike yarinyar nan. Ni dai na kasa yadda ce wa mutum ce"
Shuru ya yi domin in da sabo ta saba da jin wadan nan maganganun, shi ma bai wani damu ba domin In ya ce ya na son Bintu ko ya da mu da ita tabbas ya yi karya.
"Hakuri za mu yi mu riketa. Domin In muka ce za mu mayarwa Iya da ita, to fa duniya ce zata zagemu ba shakka."
Jin abin da ya fada kuma sai ta gane haka ne don yanzu ma ta san suna shan zagi na ba Iya Bintu da suka yi a baya.
"Amma sai na ke ga inta girma ko dan ta bar gabanmu mu huta me zai hana mu kaita makarantar kwana?"
Shuru Inna ta yi jin abin da Ɗan Inna ya fada.
"Makarantar kwana fa ka ce, ko da ya ke ba kanmu farau ba. Yaran mai gari su biyu yanzu haka ya kasu, sai kuma yaran wurin Huwaila ita ma ance suna gama firamare can aka kai su."
Da haka suka rabe da shi akan wannan shawarar.
Bayan fitarsa Iya ta duba sama ko kasa bata ga Bintu ba.
Da saurinta ta fito don a tunaninta ko sun koma can wurin bishiyar kuka in da suka nemo su dazu.
Sai dai ta na aka kafarta bakin kofa abu ta hango ya na yawo cikin katuwar robar da ta cika da ruwa a kofar dakinta.
Da farko gabanta ne ta ji ya fadi.
"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Wa ya saka ki cikin robar ruwan nan? Yau ni Binta na shiga uku"
Ta karasa maganar tana kokarin fito da Bintu daga cikin robar ruwan.
Motsin Hassan da ta ji ya fito zai yi fitsari ne ta saka ta kwala mai kira. Da farko ya ji ya yi kamar bai san tana yi ba.
Sanin hali ya sakata luka mai zagi. A fusace ya zo tare da yi mata tsaye kerere. Domin bacci ne a idonsa sosai.
"Fiddo min yarinyar nan daga cikin ruwan nan"
Jin abin da Inna ta fada ya saka shi bude idanu
"Ban gane ba Inna. Ni na sakata? Ni fa bani son abin ka alakanta ni da wannan aljanar. "
Ya karasa maganar tare da yin gaba ya bar ta sake da baki.
Bintu kuwa wasanta take yi cikin ruwan tamkar ba dare ba. Da dai Inna ta ga ba sarki sai Allah hannu ta saka da zummar fiddo da Bintu.
Ihu ta saka ta na kokarin kwace hannunta da Bintu ta cije tare da datse bakinta. Duk ihun da iya ta kurma babu wanda ya jita duk da kasancewar dare ne.
An dauki dakiku kafin ta sakar mata shi.
Inna ta ke baje a kasa ta na mayar da numfashi daya bayan daya, hannunta ta duba sai ga sawun haƙora sun fito, baro baro.
Wasu yawun wahala ta hadiye. Tare da kallon Bintu da ke faman wasa cikin ruwan tamkar ba ita ta aikata ba.
Wannan shi ne farawa da iyawa.
"Na sha cizo kina jinjira, yanzu ma ki kara kafa min haƙora. Ya Allah wannan wace irin mayya ce ka hadani da ita. Allah in laifi na yi na tuba, wannan diya ta fi karfina."
Ta karasa maganar tana kokarin ta shi ta nufi daki.
sai dai kafarta ce ta rike gam! Ta kasa kwakkwaran motsi ko nan da can ne.
A haka ta na ji ta na gani suka kwana cikin sanyi Bintu a cikin ruwa ta na wasa. Ita kuma a yashe cikin ƙasa ga sanyi kasa ga na iska.
Baccin wahala ne ya kwashi Inna ba ita ta farka ba sai da garin Allah ya waye. Murja ta fito dumama tuwo.
Da mamaki take kallon Inna da ke kwance a kofar dakinta cikin kasa ta saka ƙatuwar robar ruwanta a gaba.
Ta yar da ita ta fara. Firgigit! Ta bude ido tana neman zabgawa da gudu.
"Inna lafiya, tsakar gida kika kwana? Kin ga yadda fuskarki ya kumbura kuwa?"
Ka sa magana Inna ta yi sai ma mikewa ta yi ta shige daki.
Mutuwar tsaye ta yi ganin Bintu kwance a saman gadon sanye da riga da wando jajayen an shirya ta tsaf! Ta na sharar bacci ga yatsa da ta tura cikin baki abinta .
Kara tsorata ta yi da lamari ta.
Yarinyar da suka kwana ita a cikin ruwa Inna kuma yashe a ƙasa. To wa ya shiryata haka, kenan bata bacci da dare sai gari ya waye.
"Tabbar ina cikin gagarumar masifa rayuwa da aljana"
Ta karasa maganar tare da fashewa da kuka wiwi tamkar karamar yarinya.
A rikice Ɗan Inna ke tambayarta lafiya.
Kaf abinda ya faru ta kwashe ta sanar da shi. Sai dai samun kansa ya yi da kin yarda da abin da ta fada masa. Shi dai ko a tatsuniya bai taba jin irin haka ba.
Lallaba Inna ya yi ganin hatta dumamen tuwo ta kasa ci. Da kyar ya samu ta ci ce War zai kai Bintu wurin mai magani ki dare ya yi. Da wannan dabara ya samu Inna ta saki jikinta.
Murja kuwa shiryawa ta yi a kan ce War zata je unguwa. Ba musu ya bata dama don haka da wuri ta ɗora musu abincin rana ta gama.
Bintu ce ta rarrafo ta fito daga dakin Inna.
Da sauri ta nufi Wurin Hassan da Hussaina ta na dariya.
Cikin rashin sa'a ta kama kafar Hassan, kafin ta yi aune kafa ya saka ya shureta ta fadi can gefe kanta ya hadu da kasa har goshinta ya dan gurje.
"Mayya mai suffar Aljanu, bani kaunarki uwata ma haka. Wannan munafukar za ki riƙa likema wa"
Ya karasa maganar a fusace. Saboda tun tashin sa ya tsani duk wani Abu da ke da alaka da Shuhuda sakamakon huɗubar uwa da ya dauka.
Da sauri Hussaina ta tayar da ita tana goge mata jiki. Mamaki Murja ta yi ganin irin buguwar da Bintu ta yi amma ko gezau sai ma yatsun dama da hagu data watsa cikin baki duka biyun tana tsotsa tare da Kurawa Hassan ido.
Inna da ke a gefe ta na kallon kaf abin da ya faru, mikewa ta yi tsam ta nufi daki a cewar ta ba zata tsaya in aljanu sun fara hukunci a raba da ita ba.
Murja kuwa mayafi ta yaga ta fice mashin ta hau suka dauki hanya. Sai da suka je karshen gari. Sannan suka sake yanke hanya suka dauki hanyar jeji, tafiya mai nisa ce ta isa da su a gefen wata korama gefenta kuma dutse ne.
Haka Murja ta haye wannan dutse tana rarraba ido.
Faduwa ta yi ta kwashi gaisuwa a wurin tsohuwar da kallo daya za ka yi mata ka gane babu digon imani a tattare da ita.
Dariyar data haddasama dutsen girgiza ta kwashe da ita.
"Tauraruwa mai wutsiya, ganinki ba alheri ba. Wannan fadan da kike son janyo mana ya fi karfina amma dai ba za a rasa yadda za ayi ba. Maganar sake mallake Inna da ɗan Inna abu ne mai sauki domin wannan mun saba. Sai dai ki sani jinjirar nan ba zata mutu yanzu ba abu daya ne za mu bata da farko zata haukace ta na rashin lafiya bayan kwanaki zata ce ga garinku nan. Amma ki sani maganin da zan ba ki ba ya da makari, sannan ki kiyayi wannan jinjira domin akwai wani boyayyan lamari da ke bibiyarta in ki Ka yi wasa za ki taro faɗan da ko ni ba zan iya tare miki shi ba"
"Na yarda na amince. A kan ganin bayan Shuhuda da abin da ta bari raina ne kadai ba zan iya bayarwa ba"
Tuntsurewa da dariya Bokanya ta sake yi.
"In dan wannan ne kin samu amma ina sake jaddada miki, maganin nan ba shi da makari mutuwa ce bayan wani lokaci kin amince"
"Na amince ya shugaba"
Kwarya cike da ruwa ta tsumbula hannunta sai ga shi ta fito da daurin magani. Na farko hayakin da zata yi ma Inna da Ɗan Inna ne. Sai na biyun na Bintu.
Tunda ta baro wurin Bokanya gabanta ke faduwa ta rasa dalili.
Dakewa ta yi tare da karfafa zuciyarta a kan zata iya ita da ta yi abin da ya wuce haka bare kuma wannan.
Ba ita ta dawo gidan ba sai bayan la'asar sai dai abin da ke bata mamaki har yanzu dama da hagu hannuwan Bintu na cikin baki ta na tsotsa.
Cikin dabara ta dauko maganin tare da zubama Bintu cikin madarar da Inna ta haɗa ta ajiye a gefe tare da shigewa daki.
Cikin rashin sa a Hassan da ya gamo wasansa shigowar gidansa kenan ya kyalla ido ya ga madarar Bintu.
"Munafuka duk da rarrafe take amma a bata abinci a bata madara. Yau sai dai ki sha uwarki, amma ba dai madarar nan ba"
Ya karasa maganar tare da cire kan fidar ya kafata a baki. Sai da ya shanyeta tas kafin ya mayar da fida inda ya dauke ta.
Murja da ta ji motsin mutum lekowa ta yi, ganin Hassan tsaye ya na lasar baki ya saka gabanta yanke wa ya fadi.
"Lafiya kuwa, me ka ci kake lasar ba ki haka?"
"Madarar Bintu ce na shanye"
Tamkar rugugin aradu haka ta ji saukar maganar Hassan
Riko shi da zata yi ji ta yi ya kwala ihu tare da dafe cikinsa.
Kukan da ta fara ta na kururuwar kiran Inna a tare suka fito daga dakin ita da Hussaina da ke rike da Bintu.
Lokacin da ta karaso Hassan ya baje a kasa ya na shure-shure ga wani irin farin kumfa mai kauri ya na fita a bakinsa.
Murja da ke faman kurma ihu ta na kiran sunansa sai gani suka yi ta sulale kasa babu alamun numfashi a tare da ita...
MASU BUKATAR CI GABA SU TURO DA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER
2294023532 UBA BANK
AMINA ABUBAKAR
Meenat A 'Yandoma
***