Free chapter · Read without an account

SEVENTEEN

by Rahinat Hussein (R.Hussain) · TAEESH

Ganin yadda suke kewayeta yasa tasan akwai shirin da suka zo da shi, cike da jarumta ta ce "Da me kuka zo?" Fulani Amina wacce ita ce ta biyu ta ce "Tagabas kin ci amana, tabbas kin nuna mana ba a aminta da kishiya duk daɗin zaman da ake da ita" Tagabas ta sa dariya tana faɗin "hahh hahh lallai Amina sai yanzu kika sani ai da ku da Rahama duk sunanku kishiyoyi don haka iya ruwa fidda kai, kowa ya iya allonsa ya wanke" Fulani Zaitun ta ce "Haka kika ce ko, to shikenan mu zuba mu gani" Fulani Amina ta ce "Hum ɗan adam butulu mun haɗa kai don ganin bayan Rahama ashe aiki muke yi miki" Tagabas ta ce "Duk yadda kuka ɗauka to hakane, ni bazan tsaya kishi da ku ba saboda da ni da ku ɗin duk jirgi ɗaya ya ɗebo mu babu mai haihuwa cikin ku ba da ku zan yi yaƙi ba da waccen yarinyar zan yi, don ku a nan kuke" ta nuna tafin hannunta.

"Don haka ku bar min ɗaki" Fulani Zaitun ta ce "Ba faɗa ne ya kawo mu gurinki ba, mun zo ne kawai mu muna miki duk abin da kike muna sane da ke, amma tunda kin ce haka shikenan yadda kike ƴar sarki haka muma ƴaƴan sarakai ne, yadda kike taƙama mijinki Suhaid Abdallah ibn Zayyad mijinki ne, haka muma mijin mu ne babu abin da zaki nuna mana, mu zuba mu da ke yanzu aka fara wasan. Ya fice a fusace, Fulani Amina ta ja tsaki ita ma ta bar ɗakin, "mtsww!!! Har abada babu haɗin kai da kishiyoyi" ta gyara zama tana ɗaukan ruwan da ke gefenta ta sha.

Barorinta ne suka dawo domin kulawa da ita, ganin yadda ranta yake a ɓace yasa suka hau yi mana kirari da koɗata gami da ban haƙuri cikin hikima.

Tun daga lokacin haɗin kan matan sarki ya tarwatse kowacce ita kaɗai take tuggunta.

Ɓangaren gidan Ciroma Ubaid kuwa, hankalin kowa a tashe yake, har ranar da za a tafi da Ciroma Ubaid Singapore.

Tafiyar da ta haɗa da Abubakar da Suhaid (Ameer) sai Sadiya matarsa ta uku, Hajiya Binta ta yi baƙinciki jin ba da ita za a yi wannan tafiyar ba, sarki Suhaid ya riga da ya ce jininta ya hau ba za a ta iya kula da shi ba.

Dole ta haƙura, kiran Abubakar ta yi, ta na faɗin ya kula da mahaifinsa kuma ya sa ido sosai akan Hajiya Sadiya, duk da Abubakar yaro ne amma yasan mahaifiyarsa da tsananin kishi, dole ya amsa mata duk da kawai kallon su yake a zancen shirme, yasan yadda suke zaune tun da suka taso a tare yagansu don yawancin su sa'anni ne, ana goyon wannna sai a haifi wannan a haka duk aka haife su.

Ciroma Ubaid ne jingine da gadonsa a kmc hospital familynsa duk sun zagaye shi, cikinsa kamar ana hura masa wuta. Hannusa na dama dafe da cikin ya fara magana a hankali "Mai martaba ya sanar da ni abin da ke damuna, sanin kanku ne babu abin da ke damuna sai halin da ɗan uwana yake ciki na rashin magaji, duk da ni ban yadda da abin da doctors suka faɗa ba, nasan wannan ciwon jarabawa ne, mai martabar ya sanar da ni yau zamu tafi asibitin TanTock Seng dake Singapore, ya sanarwa da Dr.Ryan Xavier, don haka Ina baku amanar kanku da ƴaƴana da mutuncin masarautarmu, don Allah ku kula da komai, idan Allah ya nufa zan dawo to idan kuma ba zan dawo a raye ba, ina neman yafiyarku, ni na yafe muku" dukkan su kuka suke yi, suna faɗin "don Allah Abba ka daina faɗar wannan maganar in sha Allah zaka samu lafiya" Hajiya Nafisa kuwa kasa tsayuwa ta yi, ɗurƙusawa kawai ta yi tana ta kuka, hakama yaransa mata. Addu'ar samun lafiya kawai suke yi masa.

Dr. Salim ne ya shigo tare da wasu nurses maza su biyu Mubarak da Ahmad, ya ce "Allah ya baku nasara an shirya Ambulance idan kun gama shiryawa za'a tafi" Ciroma Ubaid da yake ji tamkar numfashinsa zai ɗauke ya ɗaga kai kawai.

Komai nasa an gama shiryawa.

Tun da ya dawo daga sallar asuba, ya zauna ya zabga tagumi. Kallonsa kawai take cike da tausayi, a hankali ta ƙarasa kusa da shi, dafa kafaɗarsa ta yi, ɗagowa ya yi, ya zuba mata rinannun idanusa da suka sauya kala daga fari zuwa jajaye, sun kumbura saboda rashin bacci, cikin nutsuwa fulani Rahama ta fara magana "Ranka ya daɗe, cuta ba mutuwa ba ce, tun jiya ina lura da kai ko bacci baka samu ka yi ba, Ciroma babu abin da yake buƙata a yanzu face addu'armu, don Allah ka dinga sassautawa kanka wannan damuwar" sumbatar hannun nata ya yi, yana mai karashi kan kuncinsa janyo da ita jikinsa ya yi ya rungume cikin chest ɗinsa, ya haɗe hannuwansa a bayanta, so yake ya ji zuciyarsa ta yi sanyi, ajiyar zuciya kawai yake yana sauke numfashi mai ɗumi. After few minutes ya sassauta riƙon da ya yi mata, kallon juna suke tamkar su cinye kansu, murmushi ta sakar masa, hakan yasa Sarki Suhaid murmusawa, kallon clock ta yi, ta miƙe da sauri ta ce "Ranka ya daɗe mu je ka yi wanka kar ka makara" riƙe hannunta ya yi gam, yana faɗin " Ya Azizatee ba ni da kuzarin wanka ko na shiga bansan yadda zan yi ba" ɗago shi ta yi suka nufi toilet ɗin tare, haɗa ruwan ta yi da sprays masu daɗin ƙamshi, shigar da shi bathtub ɗin ta yi, ta wanke shi, kallonta kawai yake sonta na ƙara huda zuciyarsa.

Duk ta jiƙe bata damu da hakan ba, sai da ta gama yi masa, sannan ta shiga yi wa kanta, ƙarɓa ya yi don taimaka mata, duk da ta hanashi sai da ya tayata, towel babba ta ɗauko a drawer da ke manne a toilet ɗin, ta ɗauta, sannan ta ɗaura masa, da kanta ta yi masa brush, ɗayan towel ɗin na hannunta suka fito, kan mirror ta hau, sannan ta yafa shi akansa ta shiga tsane masa kansa da gemunsa, ita ta shirya shi, rawanin ne bata iya naɗawa ba, shima ɗana masa ake yi.Hijab kawai ta zura.

Zuma ta ɗauko ta shiga bashi a baki tana faɗin "Nasan da wahala ka tsaya shan wani abu da safen nan, amma zuma abinci ce kuma magani ce" spoon ɗin ne ya ɗan zame ya ɓata masa baki, harshenta tasa don lashewa, tamkar mai jira tana kai bakinta ya yi saurin cafkar nata harshen ya shiga tsotsa, cikin hikima ta zame nata, tana nuna masa lokaci.

Da sauri ya tashi yana faɗin " Mu je banason shida ta yi ina nan banje wajen Ubaid ba, duk da na baro shi jiya jikin da sauƙi" babban palour'nsa ta buɗe suka fito tare, masu yi masa naɗi da basa nisa, Jakadiya ta yi wa iso, suka shiga russunawa suka yi sukai gaisuwa, sannan Fulani Rahama ta yi umarni da a ɗauki rawanin a ɗana masa.

Shigar fari da green ya yi, ba ƙaramin kyau yayi ba, ga wani ƙyalli da fuskarsa take.

Matansa ne suka shigo kowacce cikin shiga ta alfarma, Fulani Rahama ta nufi nata ɓangaren ta shirya bayan ta gama ganin shigar da kowaccensu ta yi, irin shigar mai martaba ta yi, shadda green tasa, sai Alkyabba fara mai adon green a jikinta sai golden shoe da palse golden, yari da sarƙa na gold tasanya ƙirar Dubai, bata fi minti goma ba ta dawo.

Kuyangunta na ƙara gyara mata zaman kayan a jikinta, Fulani Zaitun ta kalli shigarta brown and milk ne a jikinta, fulani Amina kuwa shigar blue black ta yi, Tagabas kuwa shigar ash zallah ta yi.

Mai martaba ne ya yi umarni da a tashi a tafi, iya gaba suna bayansa.

Fulani Tagabas da fulani Amina daga dama, fulani Zaitun da fulani Rahama daga hago, sai bayi a baya. Wata rantsattsiyar mota aka buɗe musu suka hau, mai martaba ne a tsakiya sai Fulani Rahama a gefen damansa, hagu kuma fulani Tagabas ce, Zaitun da Amina suna daga kusa da su.

Motoci biyu ne suka rufa musu baya, har kmc hospital.

Zuwan mai martaba da iyalansa yasa kowa ya saurara da kukan da suke yi, gaba ɗaya ahali ɗaya ne a ɗakin, Ciroma Ubaid ya yi murmushin ƙarfin hali ga sarki Ubaid, kusa da shi ya nufa, yana kama hannunsa ya ce "Ya jikin naka" a hankali ya ce "Alhamdulillah" su Fulani ne suka ƙaraso suna duba shi, sosai ya ji daɗin ganinsu gaba ɗaya, har sai da hakan ya bayyana akan fuskarsa.

Mai martaba ni zan tafi, bansani ba ko zan dawo ko bazan dawo ba, naso naga jininka a doron ƙasa, kuma ban fitar da rai da hakan ba, amma ina jin ciwon nan kamar bazan kai ba....Hannu Sarki Ubaid yasa a bakin Ciroma yana faɗin "Banason irin wannan maganganun Ubaid ina fatan Allah ya baka lafiya, ka gaji sarautar Hauren Giwa, ba ni da burin da ya fi wannan a rayuwata" riƙe hannun juna suka yi jam, Ciroma ya jujjuya kai yana faɗin "Fatana Allah ya dauwar da sarautar Hauren Giwa daga tsatsunka Yaya ba ni da wata damuwa da ta wuce in ga jininka a rayuwata, da wani na iya sauyawa bawa ƙaddara da na sauya taka ɗan uwana" gaba ɗaya ɗakin kukan tausayinsu suke yi, Rahama kuwa mutuwar jaririyarta ce ta dawo mata sabuwa, hakan yasa ta tsananta da kukanta.

Babu mai rarrashin su daga yara har manyan, sai da mai martaba ya yi magana sannan suka sarara, ɗaukar Ciroma aka yi a gadon marasa lafiya aka tafi da shi, aka sa shi a ambulance.

Sarki da tawagarsa suka rakasu har airport, sai da suka ga tafiyarsu sannan suka dawo.

Hajiya Binta kuwa tunda Ciroma yake bayani ya mugun ƙona mata rai, ya bata haushi sosai.

In banda mita babu abin da take a zuciyarta, suna komawa gida, ta sa anemo mata Jazuli.

Ƙarfe goma na safe ya dira a gabanta.

Tana huci tana cika tana batsewa ta ce " Ya batun damon fatan an samu?" a hankali jiki na rawa ya ce "Allah ya baki nasara tunda naga mai girma Ciroman Hauren Giwa babu lafiya hankali a tashe ban koma garin b.....Tas!!! Ta ɗauke shi da mari. "Kai dabba ne ko kuwa ubanka ne Ciroman da zaka yi min wasa da aiki, kasan halin da nake ciki a gidan nan kuwa, maza-maza ka je ka tabbata ba za ka dawo min haka ba, sai da kyakkyawan labari"

"Allah ya huci zuciyar ki, tuba nake ranki ya daɗe" ya faɗa jiki na rawa.

"Ɓace min da gani, sha-sha-sha mara amfani" da sauri ya fito bai tsaya ko ina ba sai cikin mota, driving ya shiga yi ya nufi ƙauyen Bojo, addu'a kawai yake Allah yasa an samu damon, don yasan ko karen hauka ne ya cije shi bai isa ya koma babu labarin samun makahon Damo ba.

A Ɓangaren sarkin farauta kuwa ganin har dare babu labarin Adamu babu na Jazuli, haka ya kwanta yana fatan Allah yasa lafiya, suna cikin bacci da misalin ƙarfe biyu na dare, sarkin Farauta ya ji ana buga ƙofar gida, da hanzari ya ɗauki kwari sa baka, ya haɗa sannan ya ce "Wane ne?" "Ni ne Baba, Adamu ne" washe baki ya yi cikin fara'a ya buɗe ƙofar yana faɗin "Dare kuke yi haka Adamu, ya haɗa hannuwansa biyu suka yi crossing ya ce "Sa'a dai, sa'a dai Baba" malam Ibrahim ya ce "ina saƙon da na ce ka zo da shi?" wani ɗan ƙaramin abu mai kama da keji ya nuna masa" Damo ne a takure a ciki" malam Ibrahim ya hau dariya, sannan ya mayar da ƙofar ya rufe, suka shiga ciki. Matarsa Huwaila da ke tsaye ita ma ta hau murna ganin ɗanta ya dawo lafiya.

Damon ya ciro daga keji, ya haska shi sosai da fitila, ba shi da idanu, sarkin farauta ya ce "Ma sha Allah na ji daɗin farauta ka ta yau, zubo masa sauran abinci ya ci" Adamu wanda yake ƙaura, jiki duk guraye da layu, ya sa wata doguwar hula akansa.

Buhun da yake ɗauke da shi ya ajiye yana faɗin "Ku koma ku kwanta, kwana na uku ban runtsa ba" yana faɗa yana ɗurawa makahon Damo ruwa a bakinsa.

Malam Ibrahim ya ce "Ai ni na gama bacci tashi ka je ka ci abinci sai ka kwanta, ba ni nan na bashi ruwan da kaina" karɓa ya yi, Adamu ya ɗauki tuwon accar da miyar kuɓewa ya nufi ɗakinsa...

.Zinariya ce✍🏻

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol