Free chapter · Read without an account
Page 26
*KARAGAR MULKI*
STORY & WRITTEN BY
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
JADEEDAH
And now...*KARAGAR MULKI*
*YOTA*
BOOK 1
PAGE 26
Bayan fitar Yarima Ishmal, tagumi Gimbiya Junainah ta yi da hannu bibiyu, ta na mai lulawa duniyar tunani,ba tare da tamasan tak`amaimai wanne irin tunani ta ke ba,saukar sanyin tafin hannu a saman fuskarta ya sa tai firgigit ta dawo cikin hayyacinta tamkar wacce ta farka daga barci"Jikata lafiya ki ke kuwa,na zo nan tun d`azu sai faman magana na ke amma ko kad`an ba ki ji ni ba,kin tafi duniyar tunanin?","Lafiyata k`lau `yar tsohuwa,yau d`in ce na ji ni duk a takure","Ayyah Allah ya sa dai ba jikin ba ne ba ?","A'a jiki Alhmdllh kawai dai ina d`an jin rashin k`arfin jiki ne shima kuma har da kewar Kawuna Ishmal "," Kewa kuma Kawun na ki da ki ke kwana ki na tashi a tare da shi shine ki ke zancen kewarsa ?","Ya shirya zai yi tafiya ne","Tafiya kuma zuwa ina ba tare da ya sanar da ni ba kuma ?", "Zuwa wata Masarauta kuma shima tafiyar riskarsa tai ba tare da ya shirya ma ta ba"," To ko kina da masaniyar dàlilin yin tafiyar ta sa ne ?",hakanan Gimbiya Junainah ta samu kan ta da son k`in gaya ma ta gaskiya sai cewa tai,"A'a ba na da masaniyar kamar yanda ki ka samu labarin haka ni ma na samai,sannan ki dakatar da wad`annan tarin tambayoyin na ki domin ni ba na cikin yanayin baki amsar su",sai da Malikat Juwairiyya ta sa ki d`an murmushi ka na ta ce,"Ko ba ki ce in dakata ba ni ma anan zan dakata kuma ina son in shaida ma ki na zo ma ki da labari mai dad`i sa`banin wanda ki ka tarbe ni da shi","Hmmmmm labari mai dad`i to ina sauraren ki Allah ya sa ba zolaya ta ki ke ba kamar yanda ki ka saba in kin gannin a cikin wani hali ki bi duk hanyar da za ki sa ni farinciki ko da ba gaskiya ba ce","Wannan karan abun ba haka ya ke ba na zo mi ki da busharar samun lafiya daga sanmu da akai mi ki ",ya mutsa fuska Gimbiya Junainah ta yi alamun zancen bai zo ma ta yanda ta ke so ko tai zato da tsammani ba," Kamar ya ni ban ga ne me ki ke nufi ba Kai tsaye ",sai da Malikat Juwairiyya ta zauna ku sa da Gimbiya Junainah sannan ta ba ta amsa da cewa,"Ina Bokanya Azizah da na ke ba ki labarin ta har na ke ce mi ki na aika da ta zo domin ta cire mi ki Aljanu gami da karya sanmun da a kai mi ki to ita ce ta zo yanzu ha ka ta na masauki mai kyau na sa an aje ta zuwa anjima in ta huta za to ta ganki daganan sai ta yi mi ki girka kamar yanda ta ce da ni"......"`Dan dakata wai ki na so ne ki ce min ni za ai ma girkar Aljanu, a d`aure ni sannan ta rik`a kiran sunayen Aljanu a saman kaina kuma ta na buguna ?", sai da Malikat Juwairiyya tai sasarai ta na kallonta baki a bud`e,sana ta ce " Me ki ke son ki ce da ni,Na rok`eki kar ki yi yunk`urin kunya ta ni a idon wannan Bokanyar ita d`in rik`ak`k`iya kuma sanannar mai cire Aljanu da karya duk wani mugun sihiri ce","Idan har rashin amincewa ta shi ke nufin kuyata ki to kishirya kwasarta,domin ba zan ta`ba yarda ko amincewa da hakan ba ni ba mushirika ka ba ce don haka ba yanda za ai in yarda a yi shirka a saman kaina,ke kan ki bai kamata ki zo min da irin wannan zancen ba,ita waccan asararriya dama can ta ta gama zama marar imani kar ki yarda ta rinjaye ko ki biye ma ta har ta kai ga samamaki wurin zama a cikin wuta","Hmmmmm da alama kin yi ma Bokanya Azizah muguwar fahimta ne, ita ai muslma ce ta na sallah ta na azumi duk kuma abinda ki ka ga ta na aikatawa ta na yi ne domin taimakon jama'a ne ma su lalurorin rayuwa,ba mushirika ba ce ba,mutuniyar kirki ce","Au a haka ki ka d`auke ta to ki je can ku k`arata ba ruwa na kuma in dai don ni ki ke k`ok`arin aikata wannan munmunan aiki to ba na so,kin ga ma tafiyata sai ki san yarda za ki yi da ita","A'a kar ki tafi Gimbiya..... Gimbiya..... Junainah ki dawo ",ha ka tai ta kiranta amma ko da wasa ba ta biyo ba balle ta sa ran zata dawo ba,kai tsaye Gimbiya Junainah sashen Kawunta Ishmal ta yi har ta na had`awa da gudu don son ta riske shi tun kafin ta tafi,don ta na da yak`inin shine kad`ai ya Isa ya hana ayi wannan shirkar a kan ta.
Sallamarsa kawai ta iske ya na k`ok`arin fitowa hannunsa d`auke da faranti wanda ya ke cike da kayan lambu,ko ta kan gaisuwa da ya ke ma ta ba tai ba ta ce da shi," Ina Kawuna Ishmal ya ke kar ka kuskura ka ce da ni ya tafi,ba zan iya jura ko d`aukar wannan kalmar ba,"Ki gafarce ni ya ke wannan Gimbiya amma tu ni Shugaba ya dad`e da tafiya don da ya shigo `yan kayan da zai buk`ata na yau da kullum kawai ya d`auka ya tafi",zaune ta kai a tantagaryar k`asa bakin ta d`auke da sallallami fuskarta na nanu halin alhinin da ta ke a ciki.
Sai da ta kwashe wani tsawon lokaci a gurin fuskarta sai kwaranyar hawaye ta ke,Kuyanga Jazila kam ta yi iya yinta akan da su tashi ko da daga bakin k`ofar d`akin Kawunta Ishmal ne amma ta k`i,"Ran ki shi dad`e ki rufa ma na asiri,ki tashi mu bar wurinnan ko turakarki ne mu tafi in ya so in mu ka je can sai mu zauna mu tattauna yanda za mu `bullo ma wannan lamarin ki fa kalli yanda bayi maza da mata ke kallonmu wasu sai su d`auka ko wani munmunan abun ne ya sa me mu ai","Kuyanga Jazila me ki ke son ki ce da ni,ko dai so ki ke ki ce min wannan lamarin bai kai mak`ura girma da tashin hankali ba ?,a gare ni kam kaf duniya ta ba ni da wani tashin hankali da musiba da na ke gudun su tunkari rayuwata kamar shi ba,Anya kuwa kin san Shirka da kuma bala'in da ke tattare da ita kuwa?,ke bari in tak`aice mi ki duk mai yinta ba shi ba shiga cikin Aljanna a wuta zai dauwama muddin bai bari ba har ya mutu bai tuba ba","Wace ni ni d`in banza in ce haka ai ko gegetonin haka ma ba zan fara ba,ni dai rok`on da na ke ma ki ki tashi mu shiga daga ciki ko me kenan ma tattauna gami da samo mafita",ba wai don Gimbiya Junainah ta so ba haka ta tashi su ka nufi sashenta.
Tunda su ka shiga Sashen su ba ta sa ke fitowa ba duk yanda Malikat Juwairiyya ta so su gana k`i tai har garin Allah ya waye,shima ta sa kai,su kai ta nemanta su ka rasa sai can hantsi ya d`aga Kuyanga Jazila ta risketa a lambun Masarautar fuskarta wasai ba alamun damuwa ko `bacin rai,sosai Kuyanga Jazila ta ke mamakin ta har ta kasa iya rik`e kanta ta tambayata da cewa,"Uwargijiyata kin jefa ni cikin wani rud`ad`d`an yanayi a jiya da daddare kin shiga cikin mak`urar tashin hankali amma kuma ga shi yanzu na gan ki ranki fes tamkar ba ki tare da wata matsala shin wani abun ya faru ne ko-ko an janye maganar girka ne ko kuma an samu mafita ne akan lamarin ?","Hmmmm ko d`aya ba a janye ta ba kuma ba a samu mafita ba,in ma sun samu to ni ban sa ni ba","To me ya faru da har yai sauri gami da yin nasarar sauya ki cikin k`ank`anin lokaci haka ?","Na yi fira ne da abokina ko ince da ke inuwar masoyina da na dad`e ban ganshi ba ko inji shi ",waige-waige Kuyanga Jazila ta fara da niya ko san ganin in da akwai wani a kusa da ita,amma ko motsin mutum ba ta ji,Kai in ka d`auke kukan tsintsaye da ke shawagi ba abinda ke a wurin,sai da ta had`eye wani abu da ya tsaya ma ta a mak`okwaronnta ta ce" Fira kuma da aboki Namiji kuma,to a taya haka ta kasance,ni dai a iya sa ni na ba wani d`a Namiji da ya ke da zarrar da zai iya shigowa nan inda ki ke,kuma a iya sa ni na da ke ban ta`ba ganin ki da wani a matsayin aboki ba",sai da Gimbiya Junainah ta sa ki murmushi sannan ta ce da ita, "Ai ba lalle ne ki san shi ba,domin ni kaina na dad`e ban ganshi ba,rabo na da shi tun kafin wad`annan matsalolin su zo su cunkushe rayuwata, duk da dama ba ganinsa na ke ba,sai dai inji muryarsa ko inga inuwarsa wani lokacin ma sai dai ya zo min a suffar filfilo ko in ce Malam bud`a mana littafi", ta k`are zancen na ta na mai fad`ad`a fara'ar fuskar ta," Anya ki na lafiya Uwargijiyata, shin kin san me ma ki ke fad`a kuwa duk kin hargitsa min tunanina,ina jin tamkar ki na son ki haukata ni ne,Kai tsaye zance da ke ni ban gane komi da ki ke fad`a ba, a duk cikin zancen da ki ke, in ba juya min tunani sama zuwa k`asa da ki kai ba","kin ga duk ki manta da wannan zancen me ye ke tafe da ke, domin duk yanda zan yi mi ki bayani ba za ki gane ba","Ki yi hak`uri ya shugabata amma ba zan iya samun natsuwar ruhi da na gangar jiki na ba ma damar ba ki yi min bayani dallah-dallah yanda zan gane ba"," To mi ki ke so ki sa ni ,bayan na riga da na fad`a mi ki iya abinda ya kamata ki sa ni,tun kuruciyata mu ke tare da Kazim ke in tak`aice mi ki har wasan k`asa munyi da shi a baya,ko a wancan lokacin da na ke zaune a ke`bantaccen Gidan lambu can ya kan yawan fad`o min a rai har in rik`a tunanin ga shi a tare da ni mu na zaune mu na hira,ke wani lokacin ma har ga ni na ke kamar ga shi munyi Aure ni da shi muna rayuwa cikin farinciki da walwala ke in tak`aita mi ki har da `yan yaranmu a tare da mu",ta k'are zancen ta na mai rufe fuska da tafin hannunta alamun jin kunya.wata irin zabura Kuyanga Jazila ta yi tana mai fara ja da baya alamun ta fara tsorata da lamarin Gimbiya Junainah,daga k`arshema zurawa da gudu ta ta nufi Sashen Malikat Juwairiyya sai faman numfarfashi ta ke ta ce da ita,"M...mmm....alikat...Allah ya k`ara mi ki tsawon rai da akwai babbar matsala da ta ke gab da rusa duk wani tanadi da buri da ki ke da shi a kan Gimbiya Junainah "," Ban ga ne ba,me ki ke shirin fad`a min ,ina ita Gimbiyar ta ke kuma me ya sameta ?","Ta na lafiya amma ba lau ba ",Nan ta kwashe labarin duk abinda ya faru da kuma wanda ta ji", wata irin fad`uwa gaba ce ta riski Malikat Juwairiyya, har ba ta San San da ta mik`e tsaye ta nufi hanyar lambun Masarautar ba.
*KARAGAR MULKI*