Free chapter 路 Read without an account
26
馃敟ZINARE馃敟
SASAAL
Page 26
Har muka gama Exams ban daina tunanin tattaunawarmu na zuwa Babban Birnin Abyad ba. Amma na sawa raina amincewar Kaka shi ne nawa.
Da murna Kaka ta tarbeni bayan girki-girke ma su da蓷i da ta shiryamin. Bayan na huta na ci abinci, na so sakomata zancen zuwana Babban Birnin Abyad amma tsoron yadda zata fassara zancen ya sa na kasa.
鈽卙ar washe gari na kasa yi mata zancen tafiyar, Sai ita da kanta ta kalleni cikin dariyar da ya ha蓷e da mamaki tana cewa;
"Me kikeson fa蓷a kika kasa Naila? Tun jiya ina ankare da ke, karki ji nauyi ki fa蓷amin zan fahimceki kinji"
Murmushi na yi ina murza goshina, cikin kame-kame na ke bata labari.
Kaka kallona takeyi maganganu Sarki tsafin Yankin Tudu na amsa kuwa a cikin kunnenta "Naila zata warke amma akwai jarabawar da ya fi wannan ra蓷a蓷i a gaba, domin zata isa Babban Birnin Abyad, da 茩arfin ikon Allah! Amma daga lokacin 茩ullin shekarun da aka kasa warwaresa zai fara warwarewa da kansa, arzi茩in da Sufyan ya yi gajen ha茩urin ya riskesa zai bayyana, wannan yana 蓷aya daga cikin abinda Mahaifiyarsa take kwa蓷aitar masa ya gaza fahimtarta, da ya yi ha茩uri da zai zama wankakke abisa laifin da Kakannin-kakanninsa suka jima su na aikatawa aban 茩asa, ko da Naila ta warke ta koma Birnin Abyad, Birnin Abyad ba mazaunin Naila ba ne. Ba lallai ki yarda da maganganuna ba, amma daga ranar da sanadi ya kai Naila Babban Birnin Abyad, zaki gasgata batuna" furucin Sarkin Tsafin Yankin Tudu kenan lokacin da ya zo duba Naila, amma Kaka ta茩i basa damar yiwa Naila magani acewarta Boka 茒an uwan sha蓷ai ne, ita kuma magani mai tsarki take nemawa jikarta.
"Wallahi ban amince ba Naila, kinsan abinda kike fa蓷a kuwa? Babban Birnin Abyad har abada ba wajen zuwanki ba ne, karma ki 茩ara tambayata don bazan lamince ba na gayamiki" Kaka ta fa蓷a cikin masifa! Tsabar masifa har rufe idanuwanta take yi.
Birkicewar Kaka lokaci 蓷aya da yadda take magana har da su fashewa da kuka ba 茩aramin tsoron abin ya bani ba, cikin haushin yadda ta hantare ni har da su kuka na ce;
"Kaka kukan me kike yi, ni fa kawai shawararki na nema, bance dole sai na je ba, sannan ke kika ce na gayamiki kar na ji nauyin komai zaki fahimce ni, amma gashi akan kawai na fa蓷a miki gaskiya shine kike masifa har da su kuka, dama can dai haushina kike ji, daga dawowata zaki sanyani cikin damuwa, na fara ciwo kuma kiyimin sharrin Yankin Tudu nake son komawa, gaba 蓷aya kin canza Kaka." Tsit ta yi tana kamo hannuna. 茒an fizgewa na yi ina cewa " ki 茩yale ni Kaka, tunda kin fara jin haushina a 蓳oye bansani ba, ni ma daga yau babu ruwana da ke"
Hawayenta ta share still ba ta saki hannuna ba, da sanyi jiki ta ce
" to zauna na fa蓷a miki gaskiya ina fatan kema za ki fahimceni, ki janye batun zuwanki Babban Birnin Abyad"
Son labari irin nawa yasa na zauna da sauri jikin mu na gogar na juna.
Abinda Sarkin tsafin Yankin Tudu ya fa蓷a ta maimatamin sannan ta 蓷ora da;
" Naila bawai na gazgata maganganun sa bane 蓷ari bisa 蓷ari, amma a yanzu a jikina nake jin ko dukka maganganunsa ba su zama Gaskiya ba, to baza'a rasa gaskiya ko da yaya bane ciki, duba da yadda su Hindu suke fafutukar dole sai kin koma cikin rayuwar 蓷ansu, Naila inajin tsoron matsalar da zai 茩ara kunnowa rayuwarmu kai a yanzu, ki gafarceni"
"Saboda iya wannan dalilin zaki haramtamin samun ku蓷in da zai sauya rayuwar Yankina? Kinsan nawa za'a biyani Kaka?. Rayuwarmu bazai ta蓳a cigaba da tafiya a haka ba, dole sai da gwagwarmaya tare da 茩alubale Kaka, ba茩in ciki da farin ciki basa dawwama a rayuwar Bawa, idan warware 茩ullin ne zai zama cigaban Yankinmu mai zai hana mu tunkari warwareshi ko da hakan zaisa mu rasa rayukanmu, tun da dai dole zamu mutu wata rana. Kaka kiyi tunani tunda na ki tunanin yafi nawa zurfi, ba kuma zanyi yin kaina ba dole zan jira umarnin ki, amma Kaka ki tuna gina kanmu da Yankinmu wajibunne, saboda Yasar shine 茩arfin gwiwar zamanmu a Birnin Abyad, to idan ya mutu fa? ko ya gaji damu fa? Jira zamu yi tayi sai dai wani yayimana gwagwarmaya muji da蓷i mu ba za muyi da Kanmu ba? Saboda muna tsoron mutuwa?
Kaka kiyi tunani a nutse, kuma karki ji shakkar sanar da ni duk abinda kika yanke, In Shaa Allah zan yi miki biyayya kin ji."
na 茩arasa fa蓷a ina rungumeta bayan na sumbaci goshinta.
Tun a lokacin bugun zuciyata ya sauya daga tsoro zuwa 茩arfin gwiwa.
SUFYAN
Da ya farka ya ganshi a gadon Asibiti baiyi mamaki ba.
Sumaya tana ganin ya farka ta ajjiye wayar hannunta tana matsowa kusa da shi, sannu take ta maimatamai tana kamo hannunsa. La茩was Sufyan ya yi. A hankali ya bu蓷e bakinsa ya zaro harshensa.
"Sumaya kina ganin harshena, yana cikin bakina?" Ya yi tambayar yana karka蓷a harshensa.
Da mamaki Sumaya ta ce; "gashinan kana karka蓷awa, maiyasa zaka yimin irin wannan tambayar Baby, relax har yanzu zafin ciwon bai gama sakinka ba, bari na kira Doctor" ta 茩arasa fa蓷a tana sakin hannunsa ha蓷e mi茩ewa ta bar 蓷akin.
Ajiyar zuciya Sufyan ya sauke, sai dai kafin ya yi relax 蓷in da Sumaya ta ce, asalin fuskar Malik da babu Tabarau babu komai sai 茩asumbar da shima an ragesa sosai sa蓳anin jiya da ya cikemai rabin fuska ya bayyana a 蓷akin, mai kamannin Salman sak na biye da shi a baya.
Jikin Sufyan ne ya saki, tabon tsoron Malik da ya kwana da shi washe gari ya 蓳ace na dawowa sabo fil, idanuwansa ya kulle gam kamar mai barci.
Ido Malik ya lumshe kafin ya saki murmushin da sam bai masa kyau ba saboda bai saba ba, da iya ganin fuskarsa ka蓷ai zai iya kawar da Sufyan a doron 茩asa ta hanyar bugawar zuciyarsa. Amma Yaron tausayi yake bashi bai san komai ba sai abinda suka 蓷orasa akai, ya jima da karantar Sufyan shi ba fa蓷an kawar da wani ne a gabansa ba, shi dai burinsa ya zama kyakkyawa ya tara ku蓷i shima ya zama Dhahab 蓷in kansa kamar yadda suke sauraran duk wa su hirarrakinsa ta offishinsa har ma da Gidan da yake kwana.
Da bu蓷a蓷蓷en muryarsa mai nauyin dake amsa amo da ya dace da kalar siffarsa Malik ya ce "sannu da Jiki Sufyan 茒ayyib Jalal, Allah Ya 茩ara afuwa, ga colleague 蓷ina Uzair ku gaisa" ya 茩arasa fa蓷a yana nuna Uzair.
Sufyan daya kasa gaishesu da sunan ya na barci, kuka ya fasa idanuwansa a kulle, kansa a can gefe. Hannuwansa biyu ya ha蓷a waje 蓷aya ya 蓷agashi can sama dai-dai saitin su alamar ro茩o. Tsabar kukan da yakeyi kafa蓷unsa da ko ina nasa rawa yakeyi.
Malik mi茩ewa yayi zai fita sa蓳anin Uzair da ya tsaya kallon Sufyan da mamaki. Ds taushin Muryar da sam baya kama da na Salman yake tambayarsa da yaren Abyad
"maiyasa kake kuka?"
Damacan Sufyan ba wani sanin Murya Salman ya yi ba balle ya tantance.
Sufyan bai amsa ba still ya茩i kallon gefen da Malik ya bar Uzair a tsaye.
Sufyan na jin Muryar likita ya 蓷an saki ajjiyar zuciya sai dai 茩ara jin Muryar Malik a bayansa ya sa ya sume kansa ya karyo kamar zai fa蓷o daga kan gadon.
Hannun Malik Uzair ya ja suka fito waje.
Da fuskar tausayi Uzair yake tambayar Malik wanene Sufyan? Maiyasa yake jin tsoron da ya ke sashi sumewa idan ya gansu?
"Yankin Tudu, Babban 茒a namijin 茒ayyib Jalal" Malik ya fa蓷a yana kallon diamond wristlet 蓷in hannunsa.
Wayar Uzair ne ya fa蓷i kasa a take gilashin baya da na gaba yayi kwatsa-kwatsa.
Dariyar muguntar da ba kasafai Malik ya fiye yi ba yasa ya na kama hannun Uzair da ya san茩ame a tsaye. Wayarsa ya sunkuya ya 蓷aukarmai suka bar wajen.
Sufyan sai da ya yi kwana biyu yana fama da zazzafan zazza蓳i jininsa har hawa ya yi, baya iya 蓷aga kiran kowa, da zarar ya ji motsin 茩ofa gabansa yake fa蓷uwa, hankalisa baya dawowa jikinsa har sai yaga wanda zai shigo.
Likita ne ya zaunar da shi yayi mai fa蓷an yana so ne ya kashe kanshi? Ko wani abun ake yi mai a Asibitin da yake sashi yawan fargaba?
Hannu likita Sufyan ya kamo yana kuka yana bashi labarin su Malik ne suke basa tsoro. A wannan ranar da茩yar Sufyan ya nutsu ya kwantar da hankalinsa tunda likita ya yi masa al茩awarin su Malik ba zasu 茩ara dawowa ba.
Da yammaci ya dannawa Mahaifiyarsa kira, bayan Sumaya ta tafi Gida ta 蓷an huta.
Kamar tayi shekaru tana jinya haka Sufyan ya tsinkayi Muryar Mahaifiyarsa. Saitin zuciyarsa da bugunsa yake fita da 茩arfi ya dafe kafin ya ce;
"Menene yake damunki Ummeena? Kwanana biyar bani da lafiya babu wanda ya nemeni a cikinku, ashe idan ba bu茩atar ku蓷i ba, ba ni da wani amfani a gareku"
Murmushi tayi kafin ta ce;
"Sufyan 蓷ana na fika shiga halin jinya, domin ciwona ba irin naka bane" gyara zama Sufyan ya yi yana yi mata sannu cikin tausayawa. Kamar daga sama ya ji tace;
"Ina ka jefar da makarin sirihin jikin Naila Sufyan?" Kame-kame ya farayi, sau茩in dole na zuwarmai lokaci 蓷aya.
"Sufyan! Malik zai iya riskarka a koda yaushe, amma kafin na baka labari, inaso duk halin da kake ciki karka 蓷ara kwana biyu baka isa Birnin Abyad wajen Naila ba, duk iya yadda za kayi karka bar Naila ta isa Babban Birnin Abyad ba tare da ta amincewa komen aurenku ba, ko kwanciya ne kayi a 茩asa ka ro茩i yafiyarsu, domin Naila itace Makamin tsirarka daga su Malik Sufyan albarkacin matsayin da take da shi a Dhabah. Karkayi watsi da umarnina kamar yadda kayi watsi da shi ka cigaba da zama da Sumaya, idan ka isa Birnin Abyad duk abinda ka riska ka yi gaggawar kirana domin na baka wasiyyata ta 茩arshe." Tana gama fa蓷a ta datse kiranta.
Shi dai Sufyan bai san abinda ya samesa bayan katse wayar Mahaifiyarsa ba, sai da ya wayi gari yaga Sumaya tsaye a kansa tana kuka..
Da茩yar Sufyan ya daure ya 茩ara kwana 蓷aya a Asibiti. A gaggauce ya sanar da Sumaya ta shirya kayanta, a kwai aikin da zaiyi a Birnin Abyad.
NAILA
Muna zaune da Kaka kiran Customernta ya shigo wayata. Domin Kaka taji komai a sarari na saka wayar.
Da zumu蓷i take sanar dani kitsona ya yi matu茩ar jan ra'ayinsu kuma sunyi al茩awarin biyana ku蓷i masu nauyin gaske. Zanzo nayi kwana biyu sannan tayi musu bayanin ina da Kaka sun ce zasu turo tikiti da komai mu taho tare. Kallon Kaka nayi ina jiran umarninta.
A hankali ta 蓷aga kai alamun ta amince!!!!.....馃槃
Shin Sufyan zai riski Naila.???