Free chapter 路 Read without an account
page 11
by Gimbiya Ayshu 路 馃尰馃尰MATSALAR GIDAN MIJI馃尰馃尰(GIDAN AURENA) BOOK 1.
馃尰馃尰MATSALAR GIDAN MIJI馃尰馃尰
(GIDAN AURENA)
STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU馃挒馃挒馃挒
ELEGANT ONLINE WRITER'S馃摎
BOOK 1:CHAPTER 21&22
___________________________"Kuluwa!",mai ya sami kafar ki?.
Shagwabe fuska Hauwa tayi tace"Mama turmi nazo ajewa shine na daura kan kafata",ta karasa maganar kanta a kasa,gaban ta sai bugun tara-tara yake,Allah-Allah take kar Mama ta ranfo ta.
Allah Sarki Maman Abban ta,bana ce miki ki dinga kula kafin ki ajiye turmi ba,kinsan in kikayi irin haka kafar na kwana biyu kafin ya warke.
"Ajiyar zuciya Hauwa ta sauke tana godewa Allah".
Rike hannun ta Mama tayi ta kaita har daki ta zaunar da ita,duba kafar tayi taga yayi jawur.
Anya kuwa kulu turmi ne ya miki wannan aiki.
"Saura kadan zuciyar Hauwa ya fashe tsabar firgice".
matsar kwalla ta farayi tace"da na bige kafar sai nazo ina aiki shine ruwan zafi ya dan zubar min,a haka ma ya sauka,dan Mami ta shafa min rub da wani magani",ta karasa maganar ta tana matsar kwalla.
Kwantar da kanta Mama tayi a kan cinyarta tana bata hakuri tace"ki bar kuka kinji zai bari insha Allah".
Kwalawa Ummi kira Mama tayi,bayan tazo tace"ta miko mata kankara daga cikin fridge".
Daukowa tayi tace"mai zakiyi da shi Mama".
"In kin sa ido zaki gani".
Turo baki tayi tana jiran taga mai Mama za tayi.
Sauko ki kwanta a kasa dan karki kifo in na fara danna kafar.
Kankarar Mama tasa ta matsa kafar.
"I da sauri Hauwa ta dauke kafar tana ihu sabida wani irin sanyin daya ratsa ta,ga sanyi ga zafi".
Matse min ita Ummi na matsa kafar nan,dan yanda naga kafar nan ya kunbura in na barta da shi har ni sai na ji jiki.
"Babu irin kukan da Hauwa ba tayi ba,har Abban ta daya rasu sai da ta kira shi".
Paracetamol Mama ta bata tasha,tasa Ummi ta dibo ruwa a buta da roba ta kawo Hauwa tayi Alwala.
A zaune tayi sallah,bata tashi ba sai da tayi isha'i da shafa'i da wutiri.
Abinci Mama ta saka mata,tana gama ci Mama ta rike ta ta kaita dakin su.
Da zazzabi sossai Hauwa ta tashi washe gari,dan kafar yayi tsami sossai ko taka shi bata iyayi sossai,Ummi ce ta zama sandar ta dan ita ke taimaka mata wurin yin komi.
"Allah ya isa ko Jalal ya sha shi ya fi a kirga".
Ummi dauko min wayata na kira Hajiyar ta na sanar mata kar taji shiru.
"Toh Mama".
Kiran Hajiya Mama tayi,har wayar ta katse bata daga ba,bata kaiga kira ba Mami ta kira,sai da kiran ya kusa katsewa Mama ta dauka tayi sallama.
Bayan sun gama gaisawa Mama tace"mahaifiyar Hauwa ce".
Ayyyah Hajiya na gane ya gida ya Hauwa da kafa.
Alhmd wlh,kinji shiru kohh!,wlh kafar ne ya kumbura sossai ko taka shi bata iya yi,gashi ya saukar mata da zazzabi shiyasa na kira na gaya miki ba zata samu zuwa ba.
"Allah sarki diyata,ashe dai kafar bai sauka ba,kuma sai dana shafa mata man zafi".
Insha Allah zanzo in dubata zuwa anjima.
"Zaune Jalal yake a parlor bayan ya dawo daga sallan asuba,tun yana zaune,ya kishingida,karshema barci barawo ya dauke shi a kan kujera".
Ba shi ya tashi ba sai karfe goma da minti biyu.
"Da sauri ya tashi ya zauna da Addu'a a bakin shi,duba agogon dake parlor yayi yaga goma da minti uku,zaro ido yayi yana mamakin barcin da yayi kuma akan kujera".
"Kallan dining yayi yaga coolers,motsin da yaji a kitchen ne yasa shi mayar da hankalin shi kofar".
"Ba jimawa dayar mai aikin mai suna zulai ta fito".
"Binta da kallo yayi yana mamaki,kasa shiru yayi har sai da ya tanbaye ta inda Hauwa take".
Wlh yau batazo ba,Hajiya tace"ba tada lfy shine na chanjeta".
Shiru yayi yana kallan ta kaman Tv.
"Toh mai ya same ta?,mai ke damun ta?,rasa mai bashi amsa ne yasa shi yin shiru".
Yafi karfin minti Biyar yana zaune,daga karshe kuma ya tashi ya nufi dakin shi.
Bayan an gama breakfast Mami taje ta shirya.
Sha biyu dai-dai ta gama shiri ta fito hannun ta daya rike da jaka dayan kuma rike da waya.
Jalal dake zaune a parlor ya kurawa Tv ido amman baya gane komi,kamshin tularan Mami da yaji ne yasa shi kallan stairs.
"Ganin taci kurus ne yasa shi fadin Mamina ina zaki haka da safen nan"
Murmushi Mami tayi tace"zanje duba diyata ne".
Hannu yasa yana sosa kai yace"toh Mamina nazo na rakaki,ya fada yana sunnar da kai".
Wani irin kallo Mami ta mai tace"kai dawa?",ba dani ba wlh,sam bazai yu ba,salan ka bini kaje ka mata wani muguntar,ni bansan inda ka gado mugun hali ba,kai bari na tafi lokaci na tafiya.........................................
By Gimbiya Ayshu馃挒馃挒馃挒.