Free chapter · Read without an account

page 17

by Gimbiya Ayshu · 🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻

               (GIDAN AURENA)

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU💞💞💞

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚

BOOK 1:CHAPTER 33&34

__________________________"Kitchen ta nufa kai tsaye ba bata lokaci".

Bakwai da rabi ta gama komai harda raban abinci da gyaran kitchen.

A parlor ta zauna ta kunna Tv tana kallo.

"Gaba daya kallon da take ya dauke mata hankali wanda har yasa ba taji alamun saukowar mutun ba".

"Ji kawai tayi an dungure mata kai",dagowa tayi a razane sabida ba tayi tsanmani ba,ba taji alamun saukowar mutun ba zunguri kawai taji.

Tana ganin Jameela ce ta dan risina tace"ina kwana Anty".

Wani arnan kallo Jameela ta aika mata da shi tace"ta ina na zama Antyn ki dan ubanki".

"Dagowa Hauwa tayi da sauri jin tace uban ta",a fili ta furta ubana da alamun mamaki a fuskar ta.

"Ohhh! tantama kike koh mehh!,Uban ki nace,Uban ki,ko shi Uban naki waye ne da baza a zage shi ba ehhhh! yar matsiyata,wa ya sani ma koh".............

"Ji kake tasssss!",Hauwa ta dauke ta da wani razanannan mari.

Tana haki tace"wlh ko da wasa kika kuskura kika kara zagin Ubana dake kwance a kabari,na rantse da Allah sai naga Uban daya tsaya miki".

"Ni kika mara",Jameela ta fada hannun ta rike da kuncin ta.

"A an mareki din,ko akwai abinda zaki iyayi ne",ta fada tana nuna ta da yatsa ranta a bace.

Hannu Jameela ta daga da zumman ramawa Mami dake tsaye a sama ta daka mata tsawa.

Fashewa da kuka Jameela tayi sabida tsabar takaicin rashin rama marin da bata yi ba.

Saukowa Mami tayi tace"maike faruwa a nan?".

"Hauwa bata san lokacin data fashe da kuka ba tsabar takaicin zagin data mata,ga kuma kukan munafurcin da take".

Wuri Mami ta samu ta zauna tace"idan kun koshi da kukan zaku min bayani".

"Sossai kukan Hauwa ke damun ta amma babu yanda za'ayi ta lallashe ta,tabbas tasan ba laifin Hauwa bane,duk yanda akayi Jameela ce ta haddasa wannan husumar".

"Upstairs Jameela ta nufa fuuuuuu! kamar zata tashi sama".

Tabe baki Mami tayi tace"Allah ya kara,  tamin dai-dai,maganin mara kunya kenan".ta karasa maganar ta tare da daga hanci sama.

"Hannu tayiwa Hauwa alamun tazo".

"Da rarrafe Hauwa ta karasa kusa da Mami".

Kwantar da kanta Mami tayi kan cinyarta tana lallashin ta.

"Da kyar ta samu tayi shiru".

"Tanbayar ta abinda ya hada su Mami tayi".

"Nan Hauwa ta gaya mata ba tare da ta boye mata komi ba",ta karasa maganar ta hawaye mai zafi na zuba daga idan ta.

"Yi shiru Jiddah ta,yi shiru kinji zanyi maganin ta".

Zaune Mama take a parlor hannun ta rike da waya tana tunanin wanda ya dace ta kira ta shaida mai hukuncin data yanke ba tare da sanin su ba,kuma tasan ba ita ya dace tayi ba.

"Daga karshe dai ta yanke shawarar kiran kawu lado dan yafi dama-dama a cikin su".

Bugu biyu ya daga,bayan sun gaisa ta mai bayanin abinda tayi.

"Ahhh! Mairo ya za kiyi haka,i ba wurin mace ake naiman izini ba shima yaran yayi wauta i".

"A'a ba haka abin ya faru ba,dama Abban su yazo naima shine nace i Allah ya mai rasuwa,sai nace mai yasa yake naiman shi,nan ya sanar min da abinda ke tafe da shi,ni kuma na yaba da hankalin shi da natsuwar shi,hakan yasa na amince da batun shi".

Wannan satin zaizo in babu damuwa kazo kawu.

Amman kayi hakuri nasan nayi ba dai-dai ba hakan yasa na kira na gaya maka.

"Toh shikenan Mairo bakomi na fahimce ki,insha Allah zanzo".

Shikenan kawu nagode,Allah ya kara girma da daukaka,nagode sossai daka fahimce ni,ina godiya.

"Ya su Maman Hamida da sauran yaran".

"Alhmd lfy su lau"

"Toh  a gaida su".

"Madallah za suji insha Allah,sai naji kiran ki".

"Shikenan kawu nagode sossai".

A nan kan cinyar Mami Hauwa tayi barci.

"Murmushi Mami tayi ta dagata ta kwantar da ita akan kushin".

"Uku da kwata Jalal ya dawo daga Office a gajiye,direct dakin Mami ya nufa ya tura kofar dakin ba tare da sallama ba tsayawa yayi a bakin kofar ya kasa gaba balle baya".

"Kwance Hauwa take akan gadon Mami ta kwanta da damarta taba kofa baya tana barci hankalinta kwance". 

"Shiga dakin yayi yana tafiya kamar wanda kwai ya fashewa a ciki har ya karasa bakin gadon da take kwance".

"Tsayawa yayi a kanta yana kallon ta tun daga gashin kanta dake bude duk ya barbaje a kan gadon,kallan fuskar ta yayi,a fili yace"she look innocent and dam cute(sleeping beauty)"daga nan kuma ya tsallaka,sai daya kare mata kallo tas".

"Barin wurin  yayi da sauri sabida alamun bude kofar da yaji".

Fitowa Mami tayi daga bayi daure da towel,kallan tuguma tamai tace"wani muguntar ka mata".

Hada rai Jalal yayi yace"mugunta kuma Mami,mai tamin da zan mata mugunta".

Harara Mami ta dalla mishi tace"oho wannan kuma kai ka sani,ni dai fitar min a daki zan saka kaya".

"Sossai Jalal yaji ran shi yayi mugun baci,kwana biyu da bata gidan bai sami matsala da Mami ba,amman daga dawowar ta yau har ta fara ruguza mai farin ciki mtsswww"............

"Ni kaja ma tsaki?,"

Saurin girgizawa Mami kai yayi yace"no Mami,wlh ba dake nake ba".

"Oho dai tafi ka bani wuri".

"Fita yayi daga dakin ranshi a mugun bace".

Sai bayan la'asar Hauwa ta tashi tayi sallah,tana idarwa ta sauka down stairs,ba tako lura da mutun a parlor ba,daga kan da za tayi kawai tayi ido hudu da Jalal,sai da gaban ta ya fadi,dauke kai tayi kamar bata ganshi ba ta nufi hayar kitchen.......................

By Gimbiya Ayshu💞💞💞.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol