Free chapter 路 Read without an account
page 28
by Gimbiya Ayshu 路 馃尰馃尰MATSALAR GIDAN MIJI馃尰馃尰(GIDAN AURENA) BOOK 1.
馃尰馃尰MATSALAR GIDAN MIJI馃尰馃尰
(GIDAN AURENA)
STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU馃挒馃挒馃挒
ELEGANT ONLINE WRITER'S馃摎
Godiya ta musamman ga itz Bash ne,ina godiya sossai ga yanda kake jajircewa wajen posting a Facebook.
Allah ya biya ka da mafificin Alkhairi.
Inawa dukkan yan uwa musulmai barka da sallah,fatan an yi sallah lafiya.
馃帄馃帄馃帄EID MUBARAK馃帄馃帄馃帄
To all my readers and followers on Facebook,WhatsApp,wattpad and Arewabooks Ina godiya da kaunar ku a gare ni,ina godiya sossai da yanda kuka amshi novel din nan Allah yayi muku Albarka ya sa muna cikin yantantun bayi Ameeeeen.
Barkan mu da dawowa,ba tare da bata lokaci ba zamu daura daga inda muka tsaya......
21/04/2023:Friday
BOOK 1:CHAPTER 55&56
___________________________Bayan tafiyar Sani Mama ta jingina da kujera tana tunani,ringing din wayar ta ne ya katse mata tunanin da take.
Daukar wayar tayi bakin ta dauke da sallama tace"ina wuni Kawu Lado ya gida da iyalai da ayyuka,dama kai nake shirin kira sai ka riga ni".
"Ayyyahhh!,Alhmd duk suna lafiya".
Akan zancen yaron nan dana ce ki bari sai nazo zan miki bayani sai gashi ban samu zuwa ba shi yasa na kira na sanar miki.
Toh nayi bincike kuma Alhmd komai yayi kyau dan ba'a sami matsala ko cikas daga ko wani bangare ba,tun daga kan yaron har iyayen yaro.
Girgiza kai Mama tayi tace"shikenan Allah ya tabbatar da Alkhairi Ameeen"
"Yauwa masha Allah,hakan kawai za kice sai kuma ki taya ta da Addu'a".
Yauwa Kawu ya ce yana naiman izinin turo wakilai,kuma na ce ya turo su zo su gana da kai juma'an nan mai zuwa,kayi hakuri na yanke hukunci kafin na gaya maka.
"A'a babu komai hakan ma yayi,Allah ya kaimu ya tabbatar da Alkhairi".
"Ameen Ameeen kawu a gaida gida",da haka su kayi sallama.
Shiru Mama tayi ta buka tagumi,ta yanke dukkan hukunci wanda bai kamata ace ita ta yi shi ba,ta yi karyar da bai kamata ace ta yi shi ba,"ya Allah ga ni gare ka ka yafe min,Allah kai kadai kasan dalili na,kai kadai ka san gaibu da zahiri,kai kadai kasan halin da nake ciki,ya Allah ka tabbatar da Alkhairi kasa gidan zaman ta ne".Ameeeen.
Washe gari da wuri Hauwa ta gama break sabida ta iso gidan da wuri,ko da ta shiga gidan biyar da minti hamsin.
Tana duba time taga seven thirty,zaro ido tayi tace"wai yau na gama da wuri,ko da yake da wuri nazo".
Parlor ta dawo ta kunna Tv ta kwanta kan doguwar jujera tana kallo,a haka barci ya dauke ta.
Takwas da minti ashirin Jalal ya sauko jikin shi sanye da farin three quater da farin riga harmless an rubuta i love u da bakin color.
Yana sauka stairs dining area ya kalla,ganin ta jera coolers yayi murmushi yace"mutuniyar kenan har an gama".
Kitchen ya nufa yaga ba ta ciki,tsayawa yayi yace"toh ina ta je?,ko dai tana dakin ta?",karan Tv da ya ji ne yasa shi kallon bangaren,yasan dai ya bar Jameela a daki tana barci,Mami kuma tana wanka,toh wa ya kunna Tv,kuma ga dukkan alamu babu mutun zaune a kan kujera,karasowa parlor yayi yana tunanin inda take,ko dai naje na dubo ta a daki,wani bangare na zuciyar shi yace"kai dai ka bari tukunna minti nawa ya rage ta sauko,kila bata jima da gama girkin ba ta haura dan ta huta".
Duba agogon hannun shi yayi yaga takwas da minti talatin,zama yayi kan kujera idan shi akan agogon shi,lumshe ido yayi ya jinginar da kanshi da kujera ba tare da ya karewa parlor kallo ba ya daura kafar shi a hannun doguwar kujerar dake kusa da shi.
Bude ido daya yayi jin kaman ya bige abu,da sauri ya sauke kafar shi kasa ganin mutum ne kwance,zaro ido yayi murya ciki-ciki yace"Happiness ",ya fada yana sakin wani lallausan murmushi mai tattare da ma'anoni kala-kala.
Tashi yayi ya nufi inda take kwance ya duka dai-dai saitin fuskar ta,yatsar shi daya yasa ya gyara mata gashin kanta dake kokarin rufe mata fuska,kiris ya rage dan kwalin ta ya zame,zai iya rantsuwa cewa bai taba ganin ta da kitso ba,kullun gashin ta a tsefe sai kace................
Ganin tana motsi yasa shi mikewa da sauri ya zauna kan kujerar dake kusa da shi.
Dagowa yayi ya kalli stairs jin alamun saukowar mutun,ido biyu yayi da Mami.
Kallan da Mami ta aiko mishi da shi ne yasa shi dukar da kanshi kasa yana sosa keyar shi yace"ina kwana Mamina,sannu da saukowa".
"Yauwa lafiya lau ya kake ya jikin naka?".
"Alhmd Mami naji sauki sossai".
"Na tashe ta Mami tunda kin sauko".
Harara Mami ta dalla mai tace"na sa ka,idan ka tashe ta aikin meh za ta maka?".
"Shiru Jalal yayi kaman wanda ruwa ya cinye shi".
Dining Mami ta nufa tace"idan ka gama tunanin ka zo ka same ni".
Tashi yayi ya bi bayan ta fuskar shi babu walwala,sam baya san abin da Mami ke mai akan Jiddah,ya san yayi kuskure a baya amman yanzu ya gyara ya daina takura mata,ya bar yi mata mugunta,hasalima yanz..................
Katse mishi zancen zuci Mami tayi da fadin"ka zo kayi serving dina yunwa nake ji".
Zaro ido Jalal yayi yace"niiiii Mami!?",ya fada yana nuna kan shi da yatsa.
Harara Mami ta dalla mai tace"a'a ba kai ba ni".
Shiru Jalal yayi yace"ayyaaahhhh! Mami shi yasa fa nace bari na tashe ta in yaso idan mun gama break sai ta koma barci".
Toh baza'a tashe ta ba,nace baza'a tashe ta ba,da matar ka na da anfani i da baka yi ba,ba ta da maraba da babu,i ka ga dole ka dau responsibilities din ta,da kai da gwauro banbancin ku kadan ne wlh,kai ni kar ka bata min rai da safen nan do as i say.
Shiru Jalal yayi ya bude cooler farko yace"mai za'a sa miki Mami".
Mami na hura hanci tace"duk abin da kaga dama.
Bude sauran coolers din yayi kafin yayi serving din ta,bayan ya gama ya hadawa Mami tea,yana cikin motsa sugar da ya zuba ya ji Mami tace"Daughter har kin tashi".
Dagowa yayi da sauri yana kallan bangaren da take fuskan shi dauke da murmushi.
Stairs Hauwa ta nufa.
"Ina zaki daughter?"
"Da hannu tayi mata alamun brush za tayi".
Har Hauwa ta gama hawa stairs Jalal bai bar kallan ta ba,sam ya manta da abin da yake,muryar Mami daya ji ne yasa shi dawowa hayyacin shi.
Bata fi minti biyar ba ta fito fuskar ta da alamun laiman ruwa wanda hakan ya karawa fuskar ta kyau da sheki.
Kura mata ido Jalal yayi yana kare mata kallo,a zuciyar shi ko tasbihi yakewa Allah daya kagi wannan halittan mai daukar hankali...................
Ku yi hakuri da wannan sai mun hadu a next page.
By Gimbiya Ayshu馃挒馃挒馃挒.