Free chapter · Read without an account

3

by Amina Abubakar Yandoma · BAYAN AURENA

DAGA AURENA

 

©️MEENAT A 'YANDOMA

 

DEDICATED TO

ASMA'U ABUBAKAR MUSA     (JASMINE)

 

GARGAƊI

HARAMUN NE A SARRAFA MIN LITTAFI TA KO WACE HANYA, BA TARE DA IZININA  BA. 'YAN YOUTUBE KU KIYAYE.

 

 

MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION (M.W.A)

Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu masu nazari da aiki da ilimi burin kungiyar a koda Yaushe shine ta faɗakar ta kuma wa'azantar ta nishaɗantar da masoyanta

____________________

PAID BOOK, FREE PAGE

 

ZAKU TURO 300 TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 2294023532 UBA BANK AMINA ABUBAKAR, KU TURO SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER *** WANDA BASU DA ACCOUNT SU TURO HOTON KATIN 300 TA WANNAN NUMBER ***

 

 

PAGE 03

...Kuka Umma ta ke ganin an shafa ma Huda ruwa sai firfita ake mata amma shuru, lambar Alhaji ta lalubo zata kirashi sai jin Muryar Kubra ta yi, a guje ta koma falon ta na tunanin ko dai ta farka. "Yaya wannan fa ina tunanin Mayu ne suka kamata ya kamata a samo magani a yi mata hayaki." Rufe bakin ta ke da wuya Huda ta ja dogon numfashi tare da buɗe idota ta na mai sakin ihu. Umma ki taimake ni mage zata kashe ni ku fidda ta a gidan nan wallahi in ta hau ni mutuwa zanyi. Nan fa aka fa ta kallon-kallo cike da mamaki da kuma tsoro, zaune suke a falon ba su ga shigar mage ba shin ina ma ake da mage da har zata shiga dakinta. "Gaskiya lamarin nan akwai sa hannun jinnu Yaya ki dage akan ta in ba haka ba muna gani za a kashe mana 'ya" " Kubra na tsorata da lamarin nan ku kama Mani ita muje daki." Jin sun ambaci za su mayar da ni ɗaki zumbur na yi zan zabga da gudu amma ina haka matan nan suka min kamun kazar kuku ta yadda ko yatsana ban iya motsawa, ina ji ina gani aka dannani cikin dakin tare da yimin wasu hayaki da suka ƙara firgita ni. Abin mamaki babu mage bare alamarta a dakin nan kaina ya sake kullewa, shigowar Zainura da ta dawo daga amso mana dinki ce ta fara tambayar abinda ya faru. Nan umma ta bayyana mata abinda ya faru, "Anya ba jinnu ba suka shafeta, lafiya ƙalau fa muka dawo gidan nan" nan fa daki ya hargitse kowa ya hau tofa albarkacin bakinsa.

 

Ni dai jinsu kawai na ke don tun bayan shigowa ta dakin na rasa natsuwata, wata hayaniya na ke ji a cikin kaina kukan jarirai ga kuma wani irin sauti mai kama da iskan maƙabarta yayin da dare ya yi. Daren ranar gidanmu cike ya ke don haka a dakina muka kwanta ni da Zainura da ke ta faman ja na da surutu ina amsa mata da kyar. Karfe dayan dare aka ciremin dilka wanka nayi duk da har yanzu a tsorace na ke, Zainura na hango har tayi barci don haka nima bayanta na kwanta tare da danne kaina da fillow. Dare ya tsala baka kiyo sautin komi sai kukan karnuka da karar harbin bindiga, juyi na yi tare da sauke idona akan wani bakin abu da ya nufo inda nake. A gigice na fara kiran sunan Zainura ina bubbugata cikin tashin hankali, fitilar da ke gefenta ta kunna abin mamaki wayam! Abin ya bace "lafiya kuwa ki ke faman tayar dani cikin daren nan" ta karasa maganar ta na hamma. Rasa abinda zan fada na yi nan fa na hau kame-kame ina tsoron fada mata gaskiyar abinda na gani. Washe gashi ranar daren bikin kenan tashi na yi jikina duk babu kwari duk da kasancewar muna da event (Mothers day) ficewa muka yi daga gidan muka nufi gidan mai kwalliya. Gudu muke tsalawa a saman titi karaf idona ya sauka akan wata halitta da na ke da tabbacin mace ce, amma ina hannunsa da kafarta ina kuma idanuwanta ? Na jefa ma kaina tambayar. Tambayar da Zainura ke min shin munyi waya da Bilal ita ta sakani dauke idona akan matar sai dai yayin da na sake kallon wurin watan ba bu kowa. Bayan isarmu gidan ji na yi damuwata duk ta kau, kasancewar gidan cike ya ke da ƙawayena. Ba mu baro gidan ba sai karfe uku wato lokacin da za a gabatar da shagalin. Kiran wayar Bilal na ke amma a kashe, to mi ya ke nufi da ka she waya. "Ke ki fita harkar shi gobe za ki ganshi har ki gaji, wa ma ya sani ko masifaffiyar uwarshi ta hana shi zuwa" Ce War Anti Kubra

 

Ba muka bar Hall din ba sai karfe goma da wani abu, bayan dawowarsa gida jikin kowa ya yi liƙis don haka kowa makwancinshi ya hau nema. In da a bangarena damuwa tare da masifaffen kunci suka ziyarce ni tun bayan tsoma kafata a cikin gidan, wani irin bacci na ji ya fara fizgata dole na kwanta gefen Zainura. Dare mahutar bawa yayin da kowa ke bacci a daidai lokacin ne wasu ke neman ta su duniyar ido rufe. Baƙaƙen kaya ne a jikinta ta rufe fuskarta ta yadda baka ganin ko da tafin hannunta, a tsakiyar dajin ta fiddo wani abu mai kama da mazubin turaren wuta tare da barbada wani garin magani, hayaki ya hau tashi sama tamkar gobara ta tashi. Kururuwa gami da iface-iface ne suka gauraye jejin kafin daga bisani a kyalkyale da mahaukaciyar dariya, "Burinki ya cika, ki saurara za ki ga sakamako" a hankali dariyar ta fara lafawa kafin komi ya koma yadda yake. Kwance ta ke ta na sharar bacci ji da tayi kamar ana lasar kafarta ne ya sakata miƙewa a firgice. Duk da duhun da ke cikin dakin hakan bai hakanata hango tsaleliyar  budurwa da bakaken kaya ta juya mata baya. Murtsuke idonta ta hau yi don tabbatarwa sai dai ta bace bata ga komi ba sai Zainura da ke bacci. Tsoki ta yi ta koma ta kwanta cike da jin haushin kanta don ta lura ita ke firgita kanta. Rana bata ƙwarya sai dai uwar ɗaya ta ji kunya, a yau ne daddazon jama'a suka shaida auren Bilal Badamasi da amaryar shi Huda Abdulhadi. Ta ko wane bangare hidima ake gabatarwa ba kama hannun yaro, musamman gidansu Huda bikin farko ne kuma na karshe domin ba ta da yaya bare kuma ƙani. Amarya ta ci ado a cikin farin leshi cike da farin ciki Zainura ta kamo hannunta zasu fita a yi hotuna da ango, abinda ban taba ji ba shi na fara ji yau ko ido bani so mu hada da Bilal ganinshi na ke ya budemin ido. Nan da aka gama hotuna muka koma gida. Abokan wasa suka fara ja na nan fa na ji jikina yayi luɓus! Gabana ya na tsananta faɗuwa, ganin anti Kubra ta zo dauka ta za amin nasiha wasu hawaye Masu zafi suka fara gudu a kan kumatuna. Nasiha mai ratsa zuciya mahaifina ya yi min kuka nake tamkar raina zai fita, nan aka wuce da ni wurin Umma. "Mahaifin ki ya gama duk wata nasiha, amma yanzu zan ɗora da tawa. Kada ki ragawa duk wanda ya ce bazai daga miki ba, bance kiji tsoron daya daga cikinsu ba domin ba su na aura ma ke ba. In sun so ayi zaman lafiya kuyi in kuma sunki ki nuna musu kin fisu zama tijararriya, Allah ya yi albarka." A haka aka saka ni mota. Gida ne madaidaici wanda duk abinka ba zaka rena shi ba, tun daga bakin get din gidan muka ci karo da su Hawwa suna aika mana kallon banza. "Alhamdulillah amarya ta iso gidanta mai farin ciki da mai akasin haka sai hakuri, wa ya isa ya ja da lamarin Allah jama'a kuyi min guɗa" Anti Kubra ta karasa maganar tare da sakin guɗa. Kai tsaye dakina aka wuce da ni.

 

A wulakance Murja suka shigo mana da kulolin abinci, abin mamaki sa'i daya fuskarsu ta canza suna dariya tamkar ba su ba. "Sannu fa amarya, an sha hanya ko. To ga abinci nan ku fara da shi don kunsa 'yan magana sunce baƙonka annabinka." Cike da mamaki suke kallon Murja da ta canza lokaci ɗaya. Ba su sake da lamarinta ba sai da suka ga ta jera da amarya anata daukar hoto. Bayan fitar ta nan fa kowa ya fara tofa albarkacin bakinsu, Anti Kubra ta ce ita dai bata yadda da su ba akwai abinda suke kullawa. Murja bata zarce ko ina ba sai wurin su Hawwa. "Anti na shiga uku, shikenan Bilal ya auri wannan mayyar nasan bazai taba aurena ba" Hawwa ta ƙarasa maganar tare da fashewa da kuka. "Share hawayenki, aurenki da Bilal tamkar an gama. Yanzu dai ina shirin da muka kulla." Jidda ce ta saka hannunta cikin jikka sai ga shi ta fito da barkono. Tuntsurewa suka yi da dariya tare da watsa barkonan cikin garwashin da suka tanada. A guje kaf ahalinsu suka fice daga cikin gidan tare da kulle get ta waje. Anti Kubra ce ta fara sakin atishawa "Mi ye wannan haka maƙaƙinshi har cikin maƙoshi." Rufe bakinta keda wuya dakin kowa ya hau atishawa numfashi su na neman tsayawa. Gaba dayansu waje suka yo, nan fa suka ga gida ya turnuƙe da hayaki. "Wallahi hayakin barkono suka mana" Zainura ta karasa maganar idanun ta sunyo waje tsabar azaba "Na fasa auren ku maidani gidan Ubana, wayyo Umma zan mutu" amarya ta faɗa hawaye da majina sun wanke mata fuska. A gigice suka yi bakin get, jin kofar da suka yi a rufe nan fa suka fara ihu suna neman taimako amma shuru...

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol