Free chapter · Read without an account
Page 30
by Sumayya Usman · JADEEDA
Part 30
"Asiya wai ke ce tunda wannan uwar safiyar",Ummu Nurain ta ce tana mai buɗe mata door ɗin shigowar,"Kai Aunty yanzu ne safiyar yanzu da wajen goma da wani abu","Ke haba har goma ta yi,Ni ban ma san garin har rana ta fito haka ba",",Ai ko dai rana ta yi yanzu haka ma Mamanmu ce ta ce inzo in jiye mata kanun zancen da ake ta yawo da shi a cikin Gida",tsaki Ummu Nurain ta saki kafin ta juyo su ka shigo a tare, Ummu Nurain hamma ta saki gami da yin miƙa tare da cewa "Waɗanne maganganu ne ke ta faman yawo a cikin Gidan?",Ya mutsa fuska Asiya ta yi tare da cewa,"Wai cewa su kai saboda tsabar baƙin kishin ki kin ƙona ƴar Sarki da ruwan zafi".
"Munafukan banza a haka za su ƙare ba wani a cikin su da yasan gaskiyar abinda ya faru sai yaɗa gutsiri tsoma","Kenan da gaske kin ƙona ta kamar yanda ake faɗa ?","Mtssssss na ƙona ta mana amma wallahi ba intentionally na ƙona ta ba,kawai tsautsayi ne,kin san ni bana shiga harkarta na je kare martabar Aurena gami da kwatar haƙƙina takawomin wargi nqi kuma na hankaɗar da ita cikin tsautsayi ta ɗora ruwan zafi ya sheƙo mata a ƙafarta".
Wata irin dariya Asiya ta kwashe da ita,har ta na tafa hannayenta tare da cewa,"Maganinta kenan uwar kinibibi da iyayi,ai yanzu sai muga da ƙafar da za a nunama mutane isa da gadara,ai ni na so ace ruwan zafin da ya tashi ya saɓule har fatarta muga ta tsiya".
"Ba zaki gane ba Asiya amma ina zaman baƙin ciki da takaici a cikin Gidannan kuma duk a saboda wannan munafukar,kan wannan lamarin har marina Yah Jaheed yai wanda irin haka bata taɓa shiga tsakanin mu ba",maganar ba ƙaramin kaɗuwa ta jefa ma Asiya ba,"Mari fa Aunty Zeenat akan wancan shashashar matar tasa ?, wallahi in ni ce da ba iya nan abun zai tsaya ba".
"Hmmmmm ai ba ayi komi ba Asiya ,barshi ba dai yau zai dawo nan Part ɗin ba na rantse sai na tada ma shi hankali fiye da yanda ya ke zato da tsammani,kuma ko ɗaya a yanzu bana danasanin ƙonewar da ta yi ko ba komi na zaunar da ita guri ɗaya kuma daga yanzu za ta san ruwa ba tsarar gwando ba ne ba ".
"Hehehe ana yi muna jin daɗi,ai babu nadama don kin illata ko raunana kishiyar ki,a ai ba a jira,ba a sanya ki sani in itace ta samu wannan damar ba jira ba sanya za ta aikata miki fiye da haka,gobe ma in ta ƙara kawo maki wargi kome ke kusa dake ki ɗauka ki buga mata a ka in ya so kome ye ya biyo baya",dariya Ummu Nurain ta saki gami dakai mata duka tare da cewa,"Shegiya Asiya ƴar ƙarama dake amma kin iya tuggu,ke wannan in aka yi maki kishiya ai tabani ta lalace"......"a'a a'a bar yi min mugun baki,Ni ko zuwa nai na iske na ci alwashi sai na fidda ta balle kuma a zo a iske ni,Aunty ni fa kwata-kwata na tsani kishi ,Ni fa zan iya aikata abinda za a ƙulle kaf ahalin mu indai akan kishiya ne","A'a Ni kin fi ƙarfina bar ni dai zan aikata abinda shi kan shi mijin ba zai tsira ba,ba shi ba kwanciyar hankali da natsuwa,yanda zan yi rayuwa cikin baƙin ciki haka shima zai rayu cikin rashin kwanciyar hankali".
"Ai ko in ki kai haka kin kyauta yauwa wai Nurain da sanin ki aka maida shi,can Gidan na ji ma ance ya koma kenan wai da yiwuwar ma an bar ma Momy Hibba shi",a kiɗime Ummu Nurain ta wai go tare da cewa,"Me ne an bada kyautar ɗana ba tare da na sani ba,duk ikon da ake nuna min a cikin Gidana bai isa ba har sai an raba ni da ɗana da na haifa da cikina,ba fa tsinto shi nai ba ni na haife shi da cikina","To aiko haka muka samu wannan labarin don da Mama da kanta zata zo ta ji ba'asi sai Baba Asabe ta hana ta ce abun magana zai zama gara ni in zo in ji gaskiyar zance ba sai ta zo ba","Wallahi ba zan iya cigaba da irin wannan rayuwar ba na rasa wa yake Aurena cikin Mahaifiyar Uncle Jaheed da kuma Momy Hibba,umarni da hukuncin su ne kawai ke gudana a cikin wannan Gidan ba zan iya ba dole in ma abun tufkar hanci tunkafin a wayi gari in rasa tudun dadafawa a cikin rayuwata".
"Da kin kyauta inji kin aikata abinda zai haukata mutanen cikin babban gida, in ki kai haka ba Mama ba hatta da Baba Asabe sai ta ƙara yin alfahari da ke,mudun ki ka aikata abinda ki ka ce","Tabbas ki shaida ma su haka zata faru,zan fara daga waccan sakarar mai ƙaryar Sarauta,sai na nuna mata ita ba bakin komi ta ke ba,daganan in samu hanyar da zan yi waje da ita,babban fata na a yanzu in rabu da wannan cikin da ke jikina duk shine ke hana ni aikata duk abinda ya tare min gaba".
"Sai dake ƴar ƙunar baƙin wake ban ce ki raga ma kowa ba,kar ki manta ko ke wace ce ƴa gurin Mama Zaliha kuma jika gurin Baba Asabe,tijara ba sai an koya maki ba,kin gada kuma kin iya,bari in tashi in tafi da wannan".
"A'a Asiya ki tsaya ko ruwan shayi ne in haɗa maki bai kamata ki tafi ba ki ci komi a gidana ba","Wa ni a'a na ƙoshi kin san Mama bata wasa indai maganar girki ne,sai da na cika cikina kafin in fito","To Shikenan ba damuwa mu je in raka ki",wani daddauɗan zanin na ta ta ɗauka ta yafa a madadin mayafi suka nufi harabar Gidan,suna tafe Asiya na ƙara famfata,gami da sake tunzurata,wani irin daskarewa wuri guda Ummu Nurain ta yi sakamakon abinda ta gani,tafe su ke cikin nishaɗi da kwanciyar hankali janye da trolys,sai briefcase dinsa sagale akan shoulder ɗin Gimbiya Ayush,ba Zeenat ba hatta da ita kanta Asiyar ta girgiza,sai da tai ƙarfin zuciya kafin ta iya cewa
"Kan uba Aunty Zeenat mai na ke shirin gani haka,na ga kamar unguwa za su tare",kasa iya cewa komi Zeenat ta yi sai,zuciyarta ke ta faman bugawa da sauri ta ke,gudun jininta ya ruɓanya da wajen kashi uku,ta kasa iya hassala komi, su ko da alama ba abinda ya dame su,Imam Jaheed sai faman murmushi yake akan labarin da Gimbiya Ayush take ba shi,ko nuna alamun sun gansu ba su yi ba, ganin da gaske tafiyar za su yi Ummu Nurain ta nufi inda suke ta sha gaban su,sai faman huci ta ke kamar wacce ta yi dambe,ko nauyin cikin da ke jikin ta ba ta yi ji,cike da masifa da bala'i ta fara magana da cewa,"Me ye ya ke shirin faruwa anan,na ga kun kwaso trolys kamar kuna shirin barin gari a'a kar ka ce min fita za kai tare da ita,idan ma haka neka sani hakan ba mai yiwuwa ba ne".
Waige-waige Jaheed ya fara yana son ya tabbatar da shi ta ke ko-ko da wani daban take,"Wai da wa ta ke,wace ce ita ,nan a wurin dai banga wani ƙaramin yaro da zai dai-dai da ɗan ta ko sa'an ɗan ta ba balle in yi tunani shi take bama wannan umarnin",ya kai zancen yana mai zagaye ta ya buɗe but ya shigar da kayan da suka fito da su,"Kar ka nemi ka raina min hankali Yayah ,Ni ɗin ce ba ka gane ba,ko dai ka fara samun matsala a cikin tunanin ka ne,ka samu juyewar ƙwaƙwalwa ne kome ?".
Da fushi ya saki murfin but ya fuskance ta da cewa,"A'a ban samu juyewar tunani ko ta hankali ba,kamar yanda ke ki ka samu,kuma da gaske ban san ki ba,domin ni ban Auro mahaukaciya mara tunani kamar ki ba,ban aje ballagaza kuma mara tunanin irin ki ba,da kuma ki ke tambayar ina zamu ko tafiya za mu yi?, Eh tafiya zamu yi domin ba zan bar maki ita ki kashe ko ki naƙasa min ita ba,ita ɗin mata ta ce,ina samun natsuwar hankali da kwanciyar hankali a tare da ita fiye da ke,ki sani a duk randa ki ka shirya zama mace ta gari ki ka koyi ɗaukar nauye-nauyen da su ke a kan ki ,to daga ranar ni kuma zan cigaba da kallon ki a matsayin Mata ta,amma ba a yanzu da ki ke rayuwar da ko dabbobi ba sa irin ta ba".
Cikin rawar baki Ummu Nurain ta tari numfashin sa da cewa,",Me waɗannan munanan kalaman na ka su ke nufi,shin kana nufin na zama sakakkiya,to ka sani wallahi ba ka isa ka maida ni bazawara ba, ina so ka sani ba wata mace da ta isa ta zo har cikin Gidana ta ci ni da yaƙi ta fidda ni daga cikin sa,Aurena da kai mutu ka raba,babu wata da ta isa ta shiga tsakanin mu,ba a haife ta ba,daga kai har ita ku rubuta wannan a cikin ran ku,ba zan yafema cutar da ku ke min ba, sannan ke kuma".ta mai da kallonta kan Gimbiya Ayush,"Kar ki yi farin ciki ko murna domin zato da tsammanin da ki ke karen ki ya kama kura to ba kura ya kama ba damisa ya kama,Ni da kaina zan kawo ƙarshen zaman ki a cikin Gidannan",tun kafin ta gama fadar abinda ta ke cewa Jaheed ya shigar da Gimbiya Ayush cikin Mota ya barta sai ɓaɓatu ta ke,ganin da gaske tada Motar zai yi su tafi ya sa ta shiga gaban Motar ta tsaya ta babbake ko ina gami da ɗaga muryar tare da cewa,"Wallahi in ka ga ka fita da Motarnan to ba na raye,sai dai in gawata za ka taka ka bi ka wuce,amma babu inda za ni inanan",kan shi ya leƙo ta wurin glass yana mai cewa da ita"Au haukan na ki har ya kai haka,to ki tsaya zan nuna mi ki naki lissafin gajere ne,in ya so in ki ka je can lahirar sai ki samu wanda za ki nunama wannan kalar hauka da baƙin kishin na ki", gadan-gadan ya taka mota gami da nufo ta, Gimbiya Ayush runtse idanunta tayi gami da kama shi ta cukwuikuye sai faman salati ta ke gami da ba shi haƙuri akan ya daka ta kar ya bi takanta ,in badan wani tsalle da Asiya tai ta janye ta gefe da yanzu ba wannan labarin ake ba,kai tsaye yai ficewar shi ba tare da ya ko waigo ya ga halin da ta ke a ciki ba.
"Aunty Zeenat wannsn wanne irin abu ne haka ta ya za ki sa rayuwar ki da ta abinda ke cikin ki cikin hatsari ko ba ki dubi kan ki ba ai kya yi duba da shi ai ","Asiya ki bar ni.....Asiya me yasa ma ki ka janye ni da kan hanyar da kin bari ya bi ta kaina in ya so sai haddin kisa ya hau kan shi, wallahi Jaheed ka cuce ni kuma Allah ya isa ban yafe maka ba,innan ina jiran ka za ka dawo sai ka yi mamakin bala'in da za ka zo ka iske a cikin Gidannan,ke kin ga wuce mu tafi Gida domin ban ga abinda cigaba da zama cikin Gidansa zai amfanin ba",takai zancen tana mai kama hannun Asiya ta fara ja,su ka nufi hanyar barin Gidan,ko ta kan Gate Man dake ta faman ba su haƙuri ba su bi ba.
"Wai lafiya duk kun bi kun ishe mu, wannan sai faman kuka ta ke, wannan kuma sai faman cika ta ke ta na batsewa sai ka ce wacce ake yi ma fanfo",cewar Baba Asabe bayan shigowar su wacce ta ke daga zaune.
"Hmmmmm Baba Asabe akwai matsala wai yau Yayah Jaheed ne ke shirin bi takan Aunty Zeenat da Motar don kawai ta ce ba ta yarda ya fita da wancan shashashar matar ta sa ba".
"Kamar ya ban gane ba,shi Jaheed ɗin ya fara shaye-shaye ne,ko-ko ya ci kan kare ne ?",Cewar Mama,"Wallahi lafiyar shi lau,babu abinda ya same shi,kawai tsabar balaja'un ɗa Namiji ce",nan fa su ka kwashe ƙarya da gaskiya su ka gaya ma su.
"Abun Mamaki wai Jaheed ɗin ne ya aikata duk wannan abun anya kuwa",Mama ta faɗa cike da mamaki,"Yo ban da abunki Zaliha ai fiye da haka ma zai aikata jika ne fa wurin Hadiza,wanne irin baƙin hali ne ba zai gada da ga gare ta ba,saboda tsabar munafunci da iya ƙulla makirci sai da ta raba ni da ɗan'uwana ciki ɗaya,ki bar mutum in ya kasance ya na gadon mugun tsatso,sai da ta ga na baro Gidan sannan hankalin ta ya kwanta"....."Kai Baba Asabe wannan da kamar kin yi ihu ne kin daɓama kan ki wuƙa,ko kin manta nan Gidan ma da ki ke zaune Gidan ɗantane ",Cewar Nabila Yayar Asiya.
"A'a meye haɗin fura da kashi,don me ki ke ƙoƙarin danganta koko da giya,ai shi kwata-kwata ba irin halin su ya biyo ba shi wannan sak ɗan'uwana ne Malam Ibrahim Mai sai da fata hafizin Malami,hanya natsuwar sa ce ta a na bashi Auren Uwarku gatanan a zaune,kuma ni dalilin ta na ke zaune anan ba dan wani ba,ato dan ki ji, yo ni Allah na tuba in badan haka ba me zai sa in zo in zauna anan ai da daki".
"Ta na kasa ta na dabo,ko kin mata shima Abbanmu shima ita ce ta haife shi,ba fa zai ji daɗi in yaji kuna aibata masa uwa ba".....Asiya ta katse ta da cewa, "Ke dalla ki rufa mana baki waya ce aibata ta ake ba halin ta ba ne ba,ai dole a faɗa ni na rasa wacce irin Zuciya ce da ke Nabilah duk irin cin mutuncin ƴar'uwarki da akayi ba ki gani sai ƙoƙarin kare wasu a banza a wofi da ki ke,mutanen da ba su san ma kina yi ba,in kin ji ba za ki iya goya mata baya ta rama abinda aka yi mata ba ki ja baki ki yi wa mutane shiru "..."Ke Asiya ki yi min shiru domin ba dake na ke ba",....."Ke ce dai za ki yi ma mutane shiru sakaryar banza mara zuciya kawai wacce ba ta san ta taya ƴar'uwarta kare martaba,ƙima da mutuncin ta ba", Ummu Nurain ta katse ta cike da tsiwa muryarta dauke da sheshshekar kuka.
Sallallami Baba Asabe ta saka gami da ɗorawa da cewa,"Ni na rasa ina wannan talasurar yarinyar ta samo wannan soloɓiyo ɗin wannan zuciya ta ta ba, kwata-kwata ba ki taya ƴan'uwanki jimamin halin da su ke a ciki","Baba banni da ita da kusa da ni ta ke da tuni na kai ma ta duka a baki wata ƙila daganan sai ta gane ta yi kuskure".Kamar ta ce ta na zaune bakin murhu.
Miƙewa tsaye tai gami da cewa da su,"Allah ya ba ku haƙuri amma duk da haka ba zan daina faɗa ba ku bi duniya a hankali, Gimbiya Ayush dai matar shi ce,tafiya kuma ya tafi da ita ba yanda za ku yi sai dai ku ɗauki haƙuri da dangana"......tun kafin ta ƙarasa ta zura da gudu ganin yanda Zeenat ta biyo ta,Baba Asabe ce ta riƙota ta na mai cewa,"A'a kyale ta banni da ita Ni da kaina zan yi maganin,ko kin manta halin da ki ke a ciki ne","Baba dan Allah ki bar ni in je in huce haushina akan wannan yariyar, Allah da sai ta yi dana sanin sani na","Na ce ki kyale ta ki bar ni da ita na wallahi wani lokacin in na kalleta ita da Alƙasim sai in yi tunanin ko musayarsu akayi min ba ni na haife su ba".
"Dawo zauna ƴarnan ai yanzu ba ita yakamata ki sa a gaba ba zo mu san yanda za mu yi da wannan babban lamarin da ya tunkaro mu".cewar Baba Asabe.
"Yauwa Baba Asabe don wallahi har yanzu ina jin maganganunsa suna min yawo a cikin kai,karma maganganun sa da suke nuni da kamar ya sake ni","Haba shi ɗin banza ya isa ya ce ya ya sake ki,ke ko kuskuren sakin ki yai sai dai ki koma zama ɗakin Mahaifiyarsa,Uban shi fa ƙanin Mahaifin ki ne, sannan da kakanshi Namiji da kakar ki ni ki Mace tsatson su guda,kin ga kuwa kusan ta yi kusan da bai isa ya iya sakin ki ba,shi ɗin banza,waye shi".
Wata irin dariya suka saki su duka har Asiya na cewa,"Ina yin ki ƴar tsohuwa,hakan ya sa na ke ƙara ji da ke Allah yakaro nisan kwana mu ƙara yin degree a wurin ki,na tabbatar da ke ce za ki yi mana maganinsu",nan fa ta miƙa mata hannu su ka tafa kafin kuma su cigaba da tsara faruwar duk abinda su je so.