Free chapter · Read without an account

Page 40

by Sumayya Usman · JADEEDA

PAGE    40. ❤🔥

"Wallahi Nurain ka matsa ka bani wuri ,tun kafin in bud'e idanuna in sa ka a cikin su,a yi Yaro sai fitinanniyar rigama d'an barcin safen ma ba zaka barni in yi ba haba dan Allah....", sautin muryar da ta ji ne ya sa ta tashi a firgice ba tare da ta shirya ma hakan ba,ta sake fad'awa cikin kogin tunani a lokacin da tai Arba' da shi zaune a kusa da ita,sake murza idanuwanta ta yi ,ilai kuwa shine zaune a gabanta ba gizo Zuciyarta ta ke mata ba," Good Morning Ummu,yau Abbunah yai min wanka da wuri kuma ya had'a min breakfast na ci na k'oshi, ke ma ga naki nan mun taho maki da shi",Nurain ya kai k'arshen zancen ya na mai kinkimo farantin da breakfast d'in ya ke akai da sauri Imam Jaheed ya tarbo shi don gudun kar ya zubar,shi ko sai faman washe baki ya ke.
    Su duka biyun ta bi da kallo ji ta ke kamar ba wa'inda ta sani kuma ta saba rayuwa da su ba ne a gabanta,sanya suke su duka da fararan kaya masu taushi,sai raba idanu take a tsakanin su kar ma Nurain da ta ke ganin fatarsa har wani glowing ta ke,tamkar an musanya ma ta shi,shar da su kamar ba su ba,ko kad'an bata ga alamar fushi ko damuwar abinda ta aikata ma shi a daren jiya a fuskarsa.
    Hankalin ta ya koma akan k'amshin abincin da ya aje mata nan da nan ta ji cikin ta ya fara kuwwa ba tare da ta jira komi ba ta duma hannu ta fara cin duk abinda ya tare mata gaba,ba ta tsaya ba har sai da tashi komi da ke jikin farantin, sai a lokacin ta mai da kallonta kan Jaheed da ya zaro idanunsa waje ya na binta da kallo.
    "Kin cinye komi ba tare da Kin tuna Cewar na ci ko ban ci ba, ga shi ko hannu da baki ba wanda ki wanke ".
    Wata irin kunya ce from no way ta ji ta lullu'beta,kafin ta san me ya kamata ta yi ,saurin muryarsa ya sake ratsa kunnuwanta da kuma gangar jikinta," Yau a Gidannan gasar wanda yafi kowa kyau za ai,ki tashi ga ruwa can na had'a miki a bathroom,ni da Nurain mun shirya ke mu ke jira",jikinta ta bi da kallo sai dai tun kafin aje ko ina tai saurin kauda kanta,zani ne d'aurin k'irjin,gashin kanta kuwa ba a ganin tsagar kitsonta duk ya bi ya susuce.
   "Tashi mana kar lokaci ya k'ure mana da", ya kai zancen tana mai sauke tiren da ta ci abinci tare da tai maka mata don ta mik'e,jikinta duk ya mutu har wani sanyi ta ke jin ya na ratsata ba tare da ta san daga ina ya ke fitowa ba, bai barta ba har sai da ya tabbatar da ta shiga wankan kafin ya koma wajen Nurain ya bashi kayan wasa yanda za su d'auke masa hankali.
     Tun shigar ta bayin kasa ta'buka komi tai Zuciyarta sai faman kai kawo ta ke gami da sak'a mata wasi-wasi kala da kala," Duk da kaancewarsa mutum mara rik'o da saurin fushi,Amma  abun da ta aikata masa jiya ya yi wuri a ce har ya manta abinda ya faru a tsakanin su jiya da daddare,me hakan ya ke nufi,wannan sabuwar kulawar kuma ta me ye,Allah ya sa ba wani tarkon ba ne ya ke yunk'urin d'ana mata ba", da sauri ta kawar da wannan tunanin tare da cewa,"Aa shi ba haka ya ke ba mutum ne mai saurin yafiya,sannan baya rama cuta da cuta,eh tabbas haka ne yana yi min wannan kyautatawar duk dan in gane kuskurena da na aikata",ta kai zancen ta na mai tabbatar ma kan ta game da abin da Zuciyarta ta ke kitsamata,tun shigarta ba abinda ta aikata ta dai d'auki sponch da soap ta rik'e a hannunta daga nan fa ta tafi duniyar tunanin.
      Baya taja a d'an tsorace sakamakon d'agowa da tai ta ganshi tsaye a gabanta ya yi folding d'in hannayensa ya zuba mata kaifafan idanunsa ma su sanya mata mutuwar jiki,takowa yai har inda ta ke ya amshi sponch da soap d'in da ke rik'e a hannunta ba tare da ya ce da ita komi ba,hannu ya sa ya sa'bule zanin jikinta, da kan shi ya wanke ta tsab,tun tana kauce-kauce har ta gaji ta daina,har shaving cream sai da yai mata amfani da shi,kitson kanta da bai fi guda shidda ba ya tsefe su ya sa Shampoo mai k'amshi ya wanke kan,ita kanta jin kanta ta rik'a yi tamkar a wata sabuwar duniyar ko kuma wacce aka sabuntawa gangar jikinta.
    Bayan ya shafe ta da lotion, ya ciro mata wata pich d'in half     da da k'adan ta wuce gwuiwarta,kanta kuma ya sanya mata Vanderner wacce ta bayyanar da gashin kanta daga baya,daga nan kuma yai mata 'barin Brut perfums mai dad'in k'amshi ,cikin jikinta kuwa ya fito rad'au sai ma ya k'ara fitar da kyawun kwalliyar ta ta, ita kanta sake baki tayi ta na kallon kanta.
    "Anya kuwa za ai wannan gasar kuwa,tun yanzu na fara karaya", shine furcin da ya fito daga bakin sa tun shigowarsa.
    Rasa me ma za ta ce da shi tai sai binsa da tarin mamakin da yake bata tun safiyar yau,ba ma a Maganar tarin kunyar da ta kwasa,rabon ta da irinta tun farkon Auren su.
    " Shikenan an gama mataki na farko na gasa,saura na biyu",Zanin gadon da ke kan gadon ya yaye Wanda yai cud'u-cud'u da daud'a,har ma ba a iya banbance asalin colour d'in sa,sannan ya fara shifid'a wani,ganin hakan da tayi ne ya sa tai saurin kama ma shi suka shifid'a a tare,nan fa suka zage gyaran Gidan kowanne lungu da sak'o na Gidan ,wasu kayan ma in ya fitto da su sai ta ji inama k'asa za ta tsage ta shige cikinta ,hatta da Kitchen, Room d'in Nurain duk sai da suka bi suka gyara shi tsab,duk wani un use da kuma wanda ba zai wanku ko ya gyarubu sai da suka fitar da shi,tamkar sun sabunta komi,kayan wanki kuwa guri guda suka tara su da zumar kiran mai yi masu wanki ta zo ta zo ta wanke, sun gama sun zauna suna maida numfashin tarin aikin da suka sha,Yaron su Nurain sai kara kaina ya ke a tsakanin su wata magana da ya fad'i duk sai da ta sa su kai shock,"Ummu yau kin yi kyau,kin yi kwalliya ta yi maki kyau sosai ban ta'ba ganin kin yi kyau irin haka ba, ko dai unguwa za mu ne ?",ya k'are zancen da sigar tambaya.
    Da wayo su ka samu su ka kaudar da batun,ringing d'in wayarsa ne ya katse shi, ya d'auka ya na fara gaishe ta cikin girmamawa,kafin ya bata amsar abinda ta ce mi shi,"Eh Momynah yanzu na ke son in shirya na je can babban Gidan,in ga Ummie da kuma su Baba Malam "," Okay daganan sai ka biyo ina son mu tattaunawa akan wani abu mai muhimmanci ",Hibba ta fad'a daga wancan side d'in,da haka suka gama wayar ya mai da kallon shi kanta yanda ya ga tana yamutsa fuska gami da dafe bayanta ya sa ya fara jin tausayina,hanunshi ya kai yana mai tayata har zuwa k'afafunta kafin ya ce," I'm sorry na wahalar da ke da yawa ko,ki yafe ni ba nufina kenan ba"......hannunta  ta kai da sauri ta rufe bakinsa tare da cewa,"Ba ka wahalar da ni ba ko kad'an,hasalima sai dai in ce ka taimake ni ne na sauke responsibility na da na kasa saukewa na tsawon wani dogon lokaci,thanks for being by my side,thanks you a lot My Husband, sannan kuma ina mai baka hak'uri akan abinda ya faru a jiya,ba zan kuma ,kuma na janye furucin da na yi  mara dad'i,kuma ina tuba akan haka".
    Murmushi ya sakar mata yace,"Komi ya wuce a gare ni,ko kin manta ke d'in Sarauniyar Imam Jaheed ce,kuma kin san Sarauniya ba ta laifi,dan haka ki manta da komi,yanzu dai zanje Momynah na Kira kafinnan zan he wajen Baba Malam,ki kula da Gidan zan tafi da Nurain ko za ki samu ki huta".
    "To shikenan Allah ya tsare a dawo lafiya in ka je ka ce duk ina gaishe su".
    Nan ya tafi ya sake yin wanka shi da Nurain ya shirya su,su ka fito,saitin ta ya tsaya ya duk'a gami da kamo hannayenta ya rik'e ya na mai cewa da ita,"Zan tafi dan Allah kafin in dawo ki yi mana lunch domin na yi kewar abincin ki,zan so in tuna baya,ki sani har gobe har jibi kina nan a raina ina jin son ki a cikin raina ban ta'ba yunk'urin sauya ki da wata ba,ko wacce mace za ta shiga rayuwata sai dai ta biyo bayan ki,ke ce ta fari a gare ni,ina yi maki so mai yankan shakku,zan rayu da ke a cikin kowanne lokaci, dan Allah ki koma kamar Zeenat d'in da na sani bana son cigaba da gudanar da irin wannan rayuwar a tsakaninmu,ina cutuwa da hakan ,Nurain ma na cutuwa,hatta kan ki kina cutar da kan ki ba tare da kin farga da hakan ba,zan so mu cigaba da shinfid'a rayuwar mu kamar yanda muka fara tun farko kafin sauyi ya shigo tsakanin mu".
    Daskarewa Zeenat ta yi a zaunen da ta ke,ta riga da ta zama speechless,kafin ta samu damar da zata ce da shi wani abu ya kama hannun Nurain su bar mata Gidan cike da k'amshin turaensu.
     Zuciyar ta ce ta fara gaya mata gaskiya har ta kai ga fara fidda zance zuci a fili, "Wai dama da gaske har yanzu Abu Nurain ya na so Na ,to ya akai na I saka ki da damata ,tabbas Na d'aura d'amara can za duk wani abu mara kyau da na ke aikatawa ko dan dawo da martaba da k'ima ta a idon sa, ke kuma da ki ka shiga ki ka fita ki ka raba ni da Mijina ganinan gare ki ko ni ko ke mu zuba mu gani"...
    Bai kai ga fita ba sai da ya sake zuwa ya gano jikin Gimbiya Ayush ya ga da sauk'i kafin ya nufi can Babban Gidan.
    Lokacin da suka isa bai iske su Malam K'arami  ba sun tafi wani taro hakan ya sa kai tsaye cikin Gidan ya nufa,bayan yai parking d'in motar sa a parking space Gidan gabad'aya an gyara shi  an k'awarta shi da kayan zama ni dai-dai gwargwado,sashen Ummie Maryam ya nufa a zaune ya iske ta cikin ladabi ya zauna a gabanta tare da fara gaishe ta,"Jiya na dawo na biyu tanan aka ce ba kunan ke da Mama",ya ce da ita bayan sun gama gaisawa.
    "Eh mun d'n fita ne an yi rasuwa nan bayan layi,ya can gurin aikin Na ka komi dai lafiya ko,kuma Na Hibba ta sanar min Na ce wata k'ila gajiya ce ta hanaka ka tsaya ka jira mu?"," Alhmdllh Ummie,ina cikin shirin zuwa in gaishe ku sai ga kiran Momy ta na son gani na","Tooooo Allah ya sa dai lafiya ,ya mutanen Gidan,ina Nurain d'an rikici?",murmushi ya yi kafin ya bata amsa da cewa,"Tare fa da shi Na taho amma tunda mu ka shigo ya saki hannuna yai gaba ban san ina ya shiga ba".
"Too Yana can ya shiga wajen yaraka tashi ka tafi wajen nata ,Na San yanzu tana can ta na jiran ka,amma kafin ka tafi ka zo ka amshi wani sallahu da gare ni,ka kai ma mara Lafiyar ",da to ya amsa kafin ya nufi hanyar da za ta kaishi Part d'in Momynta shi..
    A tsaye ya iske ta sai faman kai da kawo ta ke, wanda hakan. Yasa ya  ya ida sa kusa da ita da d'an saurinsa tare da cewa," Momynah lafiya dai ko ,ya jikin Uncle,, ina fatan ba abinda ya same shi ko ?".duk ya jero mata wad'annan tambayoyin ba tare da ya tsaya ba.
    Sai da ta dafa shi kafin tace da shi"Ka ga Yarona kwantar da hankalin ka ba abinda ya faru, zo zauna ka ji komi ".
    " Am ina Maganar taron k'aramar juna sanin da na ke ta ce maka za a yi a Canada to yau sun fidda nan da two days za a fara hakan ne ya sa na nira ka domin ka zo mu tattaunawa yanda komi zai tafi,Na Kira Yayah Nasir ya ce min zai shigo ko da zuwa yamma ne,daga yanzu sai ka kasance cikin shiri ,domin kai ne za ka je taron". Hankalin shi ya maido kanta ya na mai mamakin abinda ta ce ,"Momy ni kuma dama can tun tuni ni ki ke ma wannan shieye-shiryen tafiyar? ".
    " To AI dama kai ya kamata ka je ba ni ba,kai ne dubbunan al'uma su ke amfana da iliminka amma ba ni da kaina kawai na ke amfanawa ba".
    "Amma....Momy".....ta katse shi da cewa,"Ya isa haka tashi ka tafi Gidan ka fara shiri,ka sallami iyalan ka ,ni dama tuni Na riga da Na sanar ma da Baba K'arami, don har Na fara k'ok'arin yi maka booking d'in flight, amma dai na ga da yiwuwar sai dai ka bi jirgin yawo domin kamar akwai k'arancin tashin jirage a wannan satin sakamakon sauyin weather da mu ke a  ciki".
Ba tare da ya yi mata mu su ba ya amin ce da barinta nan ya zauna suka cigaba da tsara yanda komi zai tafi,kusan tare da Ummie Maryam su ka tsara komi ,har su Baba K'arami su ka dawo bai tafi ba ,kowa sai murna da farin cikin samun wannan babbar damar suke gani suke kamar hanyar ko damar samun sauk'in Abubakar ta zo,sai gab da la'asar ya bar Gidan.


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol