Free chapter · Read without an account
02
*SHANTYTY💃💕*
_The Little Sister of Manga_
*_(ƘANWAR MANGA)_*
A charming cinematic Hausa comedy-drama that celebrates family, friendship, mischief, and the unforgettable journey of a spirited young girl whose presence changes everyone's life.
(Labarin wata fitinanniyar yarinya 'yar ƙauye wacce take amfani da sunan yayanta, Manga, wanda ya kasance riƙaƙƙen ɗan daba, domin ta ci karenta babu babbaka. Duk inda ta shiga sai ta haddasa rigima da tashin hankali har ma da abin dariya...)
Page 2
Washegari kam zuwa ƙarfe goma na safe ma tuni har Shantyty ta gama shiryawa tsaf cikin zumuɗi ta fito saɓe da jakar kayanta tana washe baki ta isa ga Umma tana faɗin.
"Umma zan tafi ina sakon da kika ce zaki bayar na kai ma Kaka?"
Ta faɗa daga tsayen da take bakin kicin ɗin da Umma ke ciki tana tuyar waina kasancewar tana siyarwa da safe waina da miya ko da ƙuli, kuma sosai Allah ya sama sana'ar nata albarka tana kwasar ciniki domin kullum sai ta yi wainar shinkafa mudu hudu zuwa biyar kuma ta kare tass.
"Aw saboda ana yankan naman jikinki shi ne zaki kama hanya kice zaki koma tun sassafen nan ko? Ai dama nasan sati ɗayan ma da kikayi a takure kike?"
Jin abin da Umma ta faɗa tana harararta ya sa Shantyty yin ƙasa da kanta kamar zatayi shiru sai kuma ta ce
"Allah Umma ba haka ba ne kawai dai nayi kewar Kaka ne sosai shi ya sa nake zumuɗin ganinta har na gaza hakuri anjima ta yi...."
"Ba wani nan ko kuma kin kosa kije ki ci gaba da neman tsiwa da rashin ji ba."
Umma ta katse ta da faɗin hakan. "Ai kuwa dai Umma kamar kin sani domin alla-alla nake na koma naci ƙaniyar Karime wacce bata san ta nemi inda nake ba tsawon sati guda da zuwana nan"
Ta faɗa hakan ƙasa-ƙasa yadda Umma ba zataji ba yayin da kanta ke a ƙasa ta sunkuyar kamar wata ta Allah.
Umma dakeyi mata kallon tsaf ta sake faɗin. "Ko karyawa bakiyi ba shi ne ki ke maganar tafiya salon ace uzzara miki nake ko?"
"Hmmm Umma ke nan ai abin da kike min yafi uzzurawa ah to tun da baki barina nayi rawar gaban hantsi ai gaba daya a takure nake jina indai nazo gidanki shi ya sa ma bana son zuwa kawai idan na tuna kayan daɗin da Babanmu yake bani ne sai na kasa hakuri...."
"Me kike cewa ne?"
Umma ta tambaya jin kamar tana magana da sauri ta ce.
"A'a a'a lala-lala in kin ganni a lahira kaini akai aradu Umma ban ce komai ba."
Girgiza kai Umma ta yi a Zuciyarta tana yi ma ta addu'ar shiriya ita kam zata so ganin ranar da Shantyty zata nutsu kamar sauran yara.
"Ki koma ki aje kayan nan sannan ki dauko min wayata."
Umma ta bata umarni ba dan taso ba ta juya tana dira-diren ƙafa tama manta a gidan Umma take ba'a wurin Kaka mai ji da ita ba sai da ta ɗaura hannu aka zata fasa ihun shagwaɓa irin an takura mata ɗin nan sannan ta tuna a'ina take ai tuni ta nemo nutsuwa ta yafa ma kanta.
"Allah ya sa Umma bata ga abin da nayi ba."
Ta faɗa a fili ƙasa-ƙasa tana zaro ido dan tasan kaɗan ne daga aikin Umma ta rufe ido ta nakaɗa mata na jaki.
Waiwayawa ta yi a hankali domin taga ko Umma taga abin da ta yi ai kuwa da sakon hararar da Umma ke antaya mata taci karo dariya ta yi tana mai fadawa dakin Umma lokaci guda kuma take faɗin.
"Yi hakuri Umma nah ai saboda naji dadi ne ya sa na bubbuga ƙafafuna."
Dariya kawai Umma ta yi tana girgiza kai domin ta fahimci nema Shantyty take ta mayar da ita abokiyar wasanta ko ma ace kakanta a fili ta ce.
"Allah ya shiryeki."
Daidai lokacin kuma mai gidanta dake fitowa daga bandaki kuma yaji duk abin da ya wakana tsakaninta da Shantyty hakan ya sa ya magantu da faɗin.
"Ai dama addu'ar ya kamata kike bin ta da shi wannan takurar da kike mata a har kullum ina faɗa miki ba shi ne zai saka ta canza hali ba fa ce addu'a ita kaɗai ne abin da zaki riƙe amma kin kasa ganewa."
Ya ƙare maganar da mai da kallonsa gareta bayan ya zauna saman dutse ɗan nesa da madafar da Umma ke zaune.
Umma ta ɗan taɓe baki tana sallamar yaron da ya zo siyan waina sannan ta ce, "Babansu ba zaka gane bane kawai amma yara irin A'isha in ba ana takurawa da haɗa musu da zana bane wasu lokutan Allah ba zata dena wannan halin nata na tsiwa ba da neman faɗa da rigima yanzu ka duba duk garin nan waye mara ta idon da yake amfani da sunan wannan yaron yana cin karensa babu babbaka idan ba ita ba?"
Baba ya yi dariya yayin da yake kokarin fara alwala ya ce.
"Ai Yayanta ne saboda haka ba laifi bane dan ta yi amfani da sunansa."
"Kana wani bin bayanta kamar ita da yayan nata abin kirki suke yanzu Dan Allah har wani abin alfahari ne dan mutum yana da ɗan uwa ɗan daba yake alfahari da hakan har da bazawa a gari dan ma dai bakaga abin da takeyi a gari ba ne gaba daya ba wanda bata faɗa wa ba cewa Yayanta ɗan daba ya tafi Legas ko tsoron bakin mutane ma bata yi."
Baba ya sauke ajiyar zuciya idanunsa akan matar nasa da ɗan murmushi a fuskarsa ya furta.
"Shi ya sa a koda yaushe nace ki dinga bin ta da addu'a domin ƙuruciya ce wata rana in aka ce ta yi wani abin koda kuɗi ne ba zata iya ba."
Kau da kai kawai Umma ta yi ba tare da ta ce komai ba daidai lokacin ita kuma Shantyty ta fito daga Dakin Umman hannunta ɗauke da wayar Umman kuma har zuwa lokacin bata aje jakan kayan nata ba.
"Babanmu masallaci zakaje tun yanzu naga kana alwala?"
Shantyty ta tambaya tana washe baki bayan ta mika wa Umma wayar.
“Mamana, ai kina nan, sai kace yau ne kika fara ganin ina alwala? To ba masallaci zan je ba. Kamar yadda na saba, na yi alwala ne domin in kasance cikin tsarki a kowane lokaci. Kasancewa da alwala a kullum yana daga cikin kyawawan sunnonin Ma'aikin Allah, ﷺ, kuma abin so ne mutum ya yawaita kasancewa cikin tsarki idan ya samu dama.”
Cewar Baba yana shafa kan Shantyty lokacin da ya mike tsaye bayan ya idar da alwalan, da yake sunan mahaifiyarsa gareta wato A'isha shi ya sa yake kiranta da Mamana.
Ta yi murmushi zata yi magana sai ga Idrissa ya fito daga ɓangaren mahaifiyarsa cikin girmamawa ya gaida Umma sannan ya ƙari sa ga mahaifin nasa yana sanar dashi sakon da mahaifiyarsa ta aikosa karba.
Kallon harara tare da gargadi na zamu hadu domin ban manta abin da kayi min jiya ba Shantyty take ta aika masa shi kuwa da yake ya san ya mata laifi koda wasa bai kalla inda take ba.
Kuɗi Baba ya zaro a aljihu ya miƙa masa ya karba tare da nufar kofar fita.
"Ina zaka je ne? ba kai mata kudin zakayi ba?"
Baba ya tambaya. Yaron ya juyo tare da faɗin. "Ai dama ta aikeni ne kuma da kudin zan yi siyayyar."
"Okay, kayi sauri ka dawo yau na makara ba zan tsaya jiran ka ba mu haɗu a shago kawai."
Baba ya ƙare maganar yana nufar ɓangaren mahaifiyar Idrissa.
"Af na manta..."
Ya faɗa yana juyowa ga Shantyty ganin hakan ya sa ta maida hankalinta garesa.
"Yau zaki koma ko?"
Ya tambaya.
Da "Eh." Ta amsa masa sannan ya ci gaba. "Okay tun da kin nace ba zaki dawo wurin mu da zama ba gaba daya ai shikenan yanzu dai idan kin fito kafin ki wuce kizo shago ki karba sako."
Amsa masa ta yi har da godiya ganin duban da Umma ke yi mata duk da bata san sakon na miye ba amma ta san wata kila ma ba zai wuce kuɗi zai bata ba domin kuwa mijin Umma akwai hannun kyauta shi ya sa ko dan shi take hakura tazo gidan ta yi musu kwanaki.
"Kije shagon Saminu ki siyo min kati ina so na kira Yayanki."
Cewar Umma tana mika mata kuɗi. Ta ƙari sa tare da karba sannan ta nufa kofar fita ke nan taji kuma ta kwala mata kira tana faɗin.
"Aw da jakar kayan zakije aiken ke nan?"
Ganin yadda Umma ta yi maganar tana riƙe haɓa ne abin ya bata dariya amma sai ta danne tare da aje jakar a ƙofar daki tana jin sadda Umma taja tsaki ita dai ta fice ta bar gidan cike da murnar zasuyi waya da Yayanta Manga tun da Umma ta ce shi zata kira.
Idan kaga yadda take tafe tana tsallake-tsallake har da rausaya wasu lokutan abin zai baka mamaki domin ba zakayi zaton budurwar da ta kai shekarunta goma sha biyar zata yi wannan abu ba sai dai ita ko'a jikinta kuma ba ruwanta da kallon da mutane ke yi mata harkar gabanta kawai takeyi.
"Ƙanwar Manga ahalin bala'i da yan daba masu saran mutane."
Shi ne abin da taji an faɗa ta bayanta da ƙarfi mamaki ne ya kamata hakan ya sa ta juyo ai kuwa taga wata yarinyar makwaftan su Umma tsaye a kofar gidansu ganin ta juyo ne ya sa Yarinyar ƙara yi mata kwalo tana faɗin.
"E dake nake Ahalin bala'i ɗan daba ai bala'i ne haka Mamana ta ce."
Dakatawa ta yi da tafiyar tana kallon Yarinyar yayin da yarinyar ta ci gaba da faɗin kalaman dake ƙara tunzura zuciyarta ai kuwa batasan lokacin da ta ƙari sa wurin tare da kwashe Yarinyar da mari ba tana faɗin.
"Dan abu ta kaza-kazanki ni kike kira da ahalin bala'i ban kula ki ba shi ne kin ci gaba ai kuwa ba ruwana cin kaniyarki zan yi la'ada waje yo ni ba'a taɓoni bama na saka kudina na siya faɗa bare kuma ina zaman zamana an tsokalo ni."
Ta yi maganar tana kama ƙugu bayan ta sake kifa ma yarinyar mari lafiyayye sai dai hakan bai saka yarinyar ta yi shiru ba domin ci gaba da ta yi da faɗin.
"Allah ya isa muguwa kawai e ɗin na faɗa Ƙanwar ɗan daba masu kashe mutane.."
Ai tun kafin ta rufe baki Shantyty ta kai hannu tare da kwabe bakin nata ji kake pappp harshen yarinyar ya datse labbanta hakan ya sa ɗan jini kaɗan ya fito.
Ai tuni yara sun fara taruwa ana kallon ikon Allah yayin da Shantyty bata kyaleta ba sai da ta yi ma ta tass daga ƙarshe aka sama wani yaro ya lallaba yaje ya sanar da mahaifiyar Yarinyar abin da yake faruwa zuwa lokacin ita kam Shantyty ta yi gaba abin ta taje siyo katin da aka aike ta bayan ta rarrankwasheta tare kuma da gargadi akan sunan da ta kira Yayanta da shi.
"Wallahi ba zan yarda ba hukuma ce zata rabani da wannan yarinyar ba Shantyty Ƙanwar Manga ba ko shi kansa Manga ɗin ne aradu ba zan yarda ba sai kace ita ta haifa min yarinyar da zata kama ta ta jibga kamar Allah ya aikota ai kuwa muje wurin uwanta yau koni ko ita wallahi dan ba zan yarda da wannan wulak'ancin ba ai ba tsoronsu akeji ba dan Yayanta ya kasance ɗan daba kuma ai ba karya aka yi masa ba ai kashe mutane yake yi a harkar dabancin in ba hakan ba mene ne zai kai shi Legas wata da watanni ya je ya shantake."
Mahaifiyar Aminatu yarinyar da SHANTYTY ta daka ne ke wannan kurarin yayin da ta kama hannun d'iyarta suka nufa gidansu Umma domin kai ƙarar Shantyty na abin da ta yi ma yarta.
Ita kam uwar gayyar hankali kwance ta ci gaba da tafiyarta tana tafe tana sababi faɗi take.
"Lallai yarinya kin ma ga gadon baccina wallahi da har kike faɗa min wannan maganganun wai me ya sa ma ban kakkarya yar banza ba, komai ma ta fanjama-fanjam har Yaya Manga zata kira da mai kashe mutane saboda ta raina mutane."
Ta kare maganar ita ɗaya tana jan kwafa ji take kamar ta juya ta koma sannan ta sake nadama yarinyar shegen duka na tashi kaci tuwo amma ta daure ma zuciyarta bata juya ba a haka ta ƙari sa shagon ta siyo katin acan ma sai da ta mammare wani yaro wai acewarta ya yi ma ta rashin kunya dan kawai ya ce ya riga ta zuwa siyayya amma an fara sallamarta, bata tsaya nan ba sai da ta tsokane wani mutumi mai suyan kifi da yake bako ne a garin bai san wacece ita ba domin tsaban neman faɗa irin nata ya daura mansa a wuta yana jira ya yi zafi sannan ya fara soya kifin, ita kuwa Shantyty ta lallaba tare da daukar danyen kifi wanda ko wanke wa ba'ayi ba ta tsunduma cikin man tare da rugawa da gudu bata tafi ba ta tsaya lokacin da mai suyan kifin ya dawo yaga aika-aikar da ta yi masa da ya fara tafa hannu yana neman wanda ya yi masa sai ma ta fito daga buyan da ta yi tana faɗin.
"Kai bakon Inyamuri ni ce nan Shantyty wacce na saka maka kifi a cikin mai gani nayi kabar man zai kone ka tafi yin fitsari kuma ko tsarki ma baka yi ba."
Mamaki ya hana mai kifi magana yayin da ɓacin rai ya cika zuciyarsa na abin da ta yi masa mutane kuwa waɗan da suka santa da halinta basa mamaki sai ma girgiza kai da wasu keyi kowa da irin abin da yake faɗa akai.
"Sai anjima ɗan Inyamuri moaaa..."
Ta yi maganar hankali kwance har da tura masa sumba ta iska tare da arcewa a guje tana dariya sai a lokacin kuma mamaki ya saki Inyamurin ya shiga masifa yana faɗin ta rainashi kuma abin da ta yi masa ba zai tafi a banza ba dole sai ya rama sai daukar alwashi yake cikin zafin zuciya.
Wata Bakar mota ƙirar BMW ce ke tafe cikin nutsuwa bada gajare ba tana bin layi a hankali cikin ƙauyen daga cikin motar yana zaune a mazaunin Driver kamilalliyar fuskarsa a kame baka iya ganin kwayar idonsa saboda glass ɗin da ya makala yayin da yana sanye ne cikin black slim-fit trouser da fitted black T-shirt mai matuƙar kyau. A ƙafafunsa kuwa fararen leather sneakers masu tsabta ne sababbi ƙyal. A wuyan hannunsa kuma wani baƙin leather wristwatch ne mai tsada dake ta faman kyalli, yayin da ƙamshin luxury oud perfume ɗinsa ya bazu a ko'ina na cikin motar yayin da ya haɗe da sanyin Ac na motar ga Ƙamshin dake ciki sai ya bada wani daddaɗan kamshi mai sanyin dad'i, Salon shigarsa ba hayaniya ba ne, amma yana bayyana cewa ya san sirrin gayu kwarai kuma sannan ba ƙaramin mutum ba ne.
Ya mutsa fuska ya ɗan yi ganin map ɗin da yakebi gaba daya ya rikice sai faman shan wahala yake bai gane inda zai dosa ba.
Hakan ne ya sa shi fara 'yan waige-waigen ta inda zai ga wani da zai tambaya address ɗin da yake nema sai dai bai ga kowa ba ya ɗan ɓata fuska yana sake ya mutsa fuska tare da tunanin mafita a fili ya furta.
"What should I do?"
Ya tambaya kansa ba tare da ya san abin yi ba daidai lokacin da ya ɗago kansa caraf kuwa ya hango ta tana tafe a gefen hanya a nutse.
Nutsuwar da ya gani a tare da ita ya sa shi ɗan sauke ajiyar zuciya tare da buga horn na motar sai dai bata juyo ba hakan ya sa shi sakeyin wani horn ɗin still bata juyo ba rasa abin yi ya sa shi yin fi to (whistle) ai kuwa sai gashi ta juyo kallo ɗaya ta yi ma motar ganin zata dauke kai ta ci gaba da tafiya ne ya sa shi saurin sauke tinting glass ɗin tare da dubanta fuska a ɗan sake ba da murmushi ba ya furta.
"Hi girl wani kwatance nake nema na bata hanya."
Sai da ta yi masa kallon tsaf sannan kamar bata so ta buɗe baki ta ce.
"Ina ne?"
Da sauri ya faɗa mata inda yake son zuwa.
Gyara tsayuwa ta yi tana ɗan murmushi ta ce. "Aw kace gidan mai gari kake nema."
Jinjina ma ta kai ya yi alamar tabbatar wa.
Ta saki wani malalacin murmushin rainin hankali tana wani gyara tsayuwa da ƙare masa kallo a sace bayan ta nuna masa wata hanya ta ce.
"Ka bi nan kai tsaye. Idan ka ga tsohuwar bishiyar mangwaro sai ka juya dama. Daga nan idan ka ga rijiya mara ruwa, kada ka tsaya. Ka ci gaba har ka ga wani gida mai ƙofa shuɗi. Amma kada ka shiga. Ka wuce shi. Sai ka juya hagu inda babu hanya... daga nan za ka isa."
Mutumin ya ɗan lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya na samun nutsuwa sannan ya furta, "Kin tabbata?"
Ta ɗaga gira tana yi masa wani duba ta ce. "Ni ɗin nan da kake gani 'yar garin nan ce saboda haka ba zan taɓa saɓa lamba a kwatance ba."
Ya girgiza kai. "Nagode." Sannan ya ja motarsa ya tafi.
Sai da taga ya yi nisa sannan ta fashe da dariya a fili ta ce. "Wato kai gaka ɗan birni kazo da wata ƙatuwar motarka zaka mana iyayi har kake wani yi min fi to (whistle) kamar kaga karya to wallahi kaje wahala ma zaka sha domin ba daidai na faɗa maka adireshin ba."
Ta kare maganar tana sake kwashe wa da dariya abin ta cikin nishaɗi sai kuma ta kai hannu ta dafe saitin Zuciyarta a fili ta ce. "Amma fa ya haɗu... To ina ruwana ma yaje can da kyansa ai nima Kyakkyawa ce..."
Ta faɗa a fili tana ci gaba da tafiya bata farga cewa ta yar da katin wayar da ta siyo ba har sai da ta karya kwanar gidan mijin Umma sannan ta duba hannunta taga wayam ba katin waya ba alamarsa. Ta zaro ido hankali tashe ta ce.
"Ina yake...? InnaLillahi ina Katin ya tafi...? Shikenan kuma kaɗe daga ni har ganye na yau Umma farfesuna kawai zatayi ta huce takaici."
Ta ƙare maganar tana daura hannu aka ji take kamar ta zunduma ihu saboda tashin hankali!
‼️ Hmmm lallai Shantyty kina ruwa da alama kuli-kulin kubra Umma zata yi dake😂mu haɗu a next page domin ganin yadda zata kaya🤍
💞✨😍
They all feared Manga's name... but it was his little sister who turned the whole village upside down.😂💃
SHANTYTY (ƘANWAR MANGA) is more than a comedy. it's the unforgettable story of a fearless village girl whose mischievous adventures, endless trouble, and unstoppable spirit make her the heartbeat of her community.
But everything changes when a mysterious CID officer arrives in the village on a secret mission.
She sees him as another enemy. He sees her as nothing but trouble.
Yet sometimes... the greatest love stories begin with the loudest arguments. ❤️🥹
One fearless girl. One secret investigation. One unforgettable journey of laughter, chaos... and love. 💕
Nainarh KD ✍️
***