Free chapter · Read without an account

02

by JamilaUmarJanafty · SAIFUDEEN

SAIFUDDEEN

(Ba mutum ba ne)

Wattpad:JamilaUmar315

Mallakar:Janafty♥️

🅿️2

GRA:Zaria

8:50am.

Misalin karfe takwas da Mintina hamsin na wannan ranar ta litini monday tushen aiki,awani katafaran gida ginin zamani Dake GRA cikin Rantsatsiyar anguwanan Dake cikin zaria.

Kai tsaye daga cikin gidan Cikin wani Katafaran babban Bedroom wanda ya kunshi Kalan baki da Fari Kama Daga gadon har Wardrope din Dake D'akin,Labulayan duka Farare ne tas har ta Cafet din Daya malale Dakin mai kalan Baki da Fari ne gwanin ban sha"awa Domin harta Blanket din Dake kan gadon fari ne tare da Zanin gadon da Filolinka duka Masu kalan Farare ne tas suna kyali suna tashin wani Sanyayyan kamshi mai shiga Jiki da zuciya gabadaya.

Kofar Tiolet din Dake cikin bedroom din ta Bude wani kakkarfa Namiji ya bayyana yana sanye da Rigar wanka Fara tas sai karamin towel Dayake Tsane kansa dashi domin akwai alamun Digan ruwa ajikinsa.

Gaban Katon Dressing mirror din dake D'akin ya karisa yana cigaba da Tsane kansa Kyakyawan kafafunsa masu cike da garsasa suna tsinewa Cikin Italiyan Cafet din Dake shimfide abakin madubin karami da shi kalan Fari shima da baki baki ajikinsa.

Kansa na Duke ne yana Goge kansa sai da ya gama sannan ya Dago bayan ya Cire karamin Towel din dake kansa,kyakyawan Doguwar Fuskarsa ta bayyana wanda kallo daya zakayi mai kaga kammaninsa da diban jini da yake yi da larabawan Sanjaha da suka fara samun matsugguni agarin na Lere dake Jahar kaduna.

Dogo ne sannan kakkarfa ne Daya samu Inganci Ruwa biyu na Fulani acikin jikinsa shi ya bashi Daman zama murjajjan jiki kamar wani Bakin Bature,Ba fari bane sannan kuma ba baki ba ne, yana Tsaka tsaki ne Doguwar Fuska garesa mai Dauke da Hanci har baka sai Faffadan Tattausan Lebunansa wadanda suke a cure Daga gashin giransa dana idonsa zaka gasgastan ya Hada jini da fulani ko labarawa Saboda yadda yake mai Santsi da kuma murdewa kamar yana Relezzer.

*DR.SAIFUDDEEN CONEL.SALAHUDEEN LERE* kenan,D'a ga marigayi Conel. Salahuddeen Inuwa Lere da Metron Zaliha Bungudu asalinsu Fulanin Bunkuri ce dake Jahar zamfara,rashin zaman lafiya da tashe tashen hankulan na yan Bindiga da yan Boko Haram yasa suka baro garinsu ita da kanwarta Zuwaira da yayansu Sunusi suka yada Zango a Gayan kano Nageria.

Ba Dr. Bane a bangaran Likitanci Dr ne a bangaran karatu,Saifuddeen mutum ne mai kwakwalwa,da Tarin ilimin boko da na addini,Yana da Tarin Degree a bangarori da Dama har guda shidda Inda dai yafi kwarewa shi ne yana da shaidar Degree biyu kan Karatun B.A English,sannan Akan Letriture yayi phd dinsa a standford University,Sannan ahalin yanzu haka Shekaru biyar da suka gabata ya fara Laccaring a Abu samaru a bangaran Department din B.A English,Sannan Shekarun biyun da suka gabata da Sauya sabon gwamnati gwamna mai ci a yanzu Abdulhadi Shitu ya zana sunansa a matsayin Kwamishinan ilimi na Jahar kaduna Saifuddeen bai taba Siyasa ba ballatana mafarkinsa sai kuma rana Tsaka yaji sunansa a matsayin kwamishinan ilimi ta Jaharsa,sai dai yasan Nasaran sa daga Allah ne,sannan shima akwai Jajircewan sa da kokarinsa Tunda tun yana Secondary sochool dinsa na federal Science and Tecnical Collage(FSTC)KAFANCHAN,An san sa wajen Hazaka zai ya iya cewa da Taimakon gwamnatin Jahar kaduna ya samu Shedar Degree dinsa na biyu bayan ya gama karatun Degree din sa na farko a BUK KANO, kafin ya tafi Stanford Universty yayi Master dinsa duk da Tallafin gwamnatin Jahar kaduna a wanchan Lokacin Datake bama Hazikan yaran da suke da kokari Socholarship.

Shiri yake a gaggauce saboda yasan Lokaci ya tafi barcin daya kwashe shi ne mai bai mai adalci ba,Yasan za"a rina Saboda jiya sai D'aya na Dare ya iso Zaria wannan gidan nashi da ba wanda yasan inda yake sai Mujaheed da Ummi sun san ya mallaki gida a zaria ammh acikin su ba wanda yasan inda gidan yake ballatana har su taba Takowa yaji Dadin haka ko bakomai yaji Dadin haka Saboda a wannan gabar wannan gidan ya zame masa mafaka Daga Laifin da su Ummi suke ganin ya aikata musu wanda a wurinsa ba laifi bane saboda riko da wannan kalmar tasa na ba biyayyah ga abokin Halitta wajen sabama mahallaci.

Agogon Dake kafe a Dakin ya Daga kansa yana gani Lokaci ya tafi yau in bai manta ba suna da Meeting da Gwamna Saboda tun last week Sakataransa Michel ya turomai Gabadaya Jadawalin aikinsa na satin nan daya shiga.

Tashin Hankalin abunda ya tunkaraesa ne yasa ma ya manta da komai a gurguje ya shafa Lotion cikin wani irin sauri ya taje suman kansa ya shafa mayukan daya saba shafama kansa,Wardrope din dake kafe a Bangon Dakin ya nufa ya wangale sai ga suit a jere iya kallon ka iya zaban ka Kala kala na kamfanoni da Dadama masu ruwan toka da bakake.

Baki da Fari ya ciro Cikin abun da bai yi minti goma ba, ya tsuke cikin Suit baki da Fari Lokaci Daya yana kokarin matse wuyansa da Tie din Daya Dauko baki,Wajen ma"ajiyar takalmansa ya nufa gasu nan kala kala bakake da Farare da masu ruwan toka da duhuwa,Masu iya baki ya Dauko wani Rufaffe mai kama da Fatar Damisa ya saka bayan ya dawo gaban madubin yana Feshe jikinsa da Turare mai kamshi sai alokacin naga Tabon sallah a saman goshinsa sannan in ka duba sosai Wandonsa bai Sauka kasa sosai ba Har kana ma Hango bakar safar daya sanya ma Kafarsa Daga yanayin kamewarsa kai Tsaye sai ka iya kiran Saifuddeen din da Ustaz saboda yanayinsa da yanayin Shigarsa.

Komai bai Kauda ba ya fita Daga D'akin sai gashi ya bayyana a wani Falo mai Fadi da girma da Tsaruwa shima kamar ciki ne kalan Fari da Baki ne bai Tsaya ba Wayoyinsa guda Biyu da tun jiya ya zube su saman Center Table din Dake falon ya kwashe Tab dinsa tana mota chan ya barta wayoyin nasa duka suna kashe ne tun jiya da ya baro Lere ya Datse su sai wata yar karamar Kirar Samsumg daya barta a Bude saboda sako kawai itama ta wajen aiki ce Daga chan gida ba wanda yasan shi da wannan layin personal ce saboda yanayin aikinsa..

Key din motarsa ma yana Hannun Excort dinsa jiyanan a Firgice ko nace a gaggauce ya iso zaria shiyasa bakomai ya tsaya ya Duba yadda ya kamata ba Cikinsa yana ta Kiran Ciroma ammh sanin ka"idansa na rashin son Cika alkawari da kuma Sabama Dokar aikinsa yasa ya maze ko a Fuska Yunwa ko jigata bai bayyana a yanayinsa ba,da Wani irin Takun Sarsarfa ya fice Daga falon batare da yayi waige ba.

Yana fitowa wasu Samudawa dake tsare bakin kofar Falon suna Sanye da suit suma bakake da wasu manyan gilasai na ba mutumci su ka nufesa Cikin Harshen Turanci suke gaisheshi ya amsa yana mikama Daya Daga Cikinsu tarkacen kayan Hannunsa kafin ya Kallesu yadda suka natsu agabansa suna Jiran Umarni.

Motarsa ya kallah Baka Kirar prado wanda Daman da ita yaje lere duk tayi kura alamun tasha gwagwarmaya sam ya manta bai ce su kai wanki ba Dayar Motar tasa tana Gidansa na Kaduna Sauran kuma suna da Muhalli ne agidan Ummi Dake Abuja.

Megadin Dake kulamai da gidan tun da ya siyeshi ya fito da hanzari ya Rugo ya zo ya zube gabansa yana kwasansa gaisuwa Matashi ne mai jini ajika shima..

Cikin irin mganarsa ta koyaushe yace"Junaidu ka kula da gidan nankamar yadda ka saba zan koma kaduna.."

Da ido kawai yayi mgana naga Daya Daga Cikin Escort dinsa ya nufi motar ya Bude ya Dauko Kudi bandir Daya yan Dubii ya mikama Saifudeen shi kuma ya bama Megadi ya karba kamar zai mai Sujjada Saif yayi kayattacen mirmishi jin Sanda Junaidu ke fadin"Nagode Yallabai Allah ya Tsare gabanka da bayanka..Allah yasa ka gama da Mahaifiyarka Lafiya.."

Cikin Farimcikin dayake ji in akayi masa addu"an gamawa da Ummi Lafiya yace"Ameem Junaidu ka kara kayi Cefane kafin na dawo..

Bama muje.."

Yafada yana yin gaba suka bisa a baya Junaidu kuma na Durkushe kamar zai yi kwallah Saboda godiya.

Daya Daga cikin su ya Bude mai bayan Mota ya shiga,Dayan kuma ya shiga bangaran Direba,wanda kuma ya Bude mai motar ya kame agaba.

Cikin Lokaci kankani suka saki Hon junaidu ya mike jiki na rawa ya wangale bakin karkakkafan bakin get din suka Sulale suka Fice Daga gidan yana Daga musu hannu tare da Fatan alheri Domin har ga Allah bazai iya kwatatan girman Alherin Yallabai garess ba,ba domin yana masa aikin gadi ba abunda yake biyansa yafi karfin aikin da yake masa Allah dai yasa ya gama lafiya.

Sai da suka Hau shimfidad'den Titin Dake Gra sannan ya karbi wayoyinsa bai kunna ko Daya ba Tab din ya kunna kamar ana jiransa sakonnin suka Fara Tururuwan shigowa na Michel kawai ya fara Dubawa ajiyar rai ya Sauke ganin an Daga ganawar su da gwamna sai karfe goma na Safe,jin haka yasa yayi amfani da karamar wayarsa ya Tura ma parmanet Secatary Sakon dayake son ya turamai yana da Tabbacin ya nemesa bai same sa ba.

Jingina bayansa yayi a jikin kujeran motan,lokaci Daya ya Rufe Tab din batare da ya bi ta kan sauran Sakonnin Dake shigowa duk da yasan har da na bangaran karatunsa dayake yi a kasar California,Unites State University,San-Diego,California

domin samun kwarewa kan abunda ya shafi Na"ura mai kwakwalwa.

Tunani ne birjit suka shiga kansa Daya sa saida ya Dafe kansa ya gangaro da Hannunsa yana Shafa Zagayenyen Sajensa zuwa gemunsa daya Ragesa kadan bai yi yawa ba kuma sannan bai yi kadan ba.

Yasan Ummi nachan ta cika dashi Ya kuma sani ana chan ana ta Uban cigiyarsa,Mujaheed yasamu labarin yanzu sai dai ko ya nemesa bazai samesa ba sai dai in ya shiga kaduna yau,mganan su Baffa Hashimu da Iya kuma tunda ba Dukansa zasu yi ba Hakuri ne Zai shiga tsakaninsu Ummi ce babbar Damuwansa yasan Halinta kan abubuwan da suka Faru zatayi Fushi mai Tsanani dashi.

Ammh bakomai yasan Lagonta zasu gyarota Tsakaninsu ammh bazai yarda su hadu ba sai komai ya lafa zuwa Sati mai zuwa in ta koma Abuja.

Dadinsa Daya ma Addarsa Sadiya gidan mijinta zata koma Sauran yaran nan munafukai su kuma suna ganinsa ai baza su iya motsi ba,ba Raini a Tsakaninsu,sai dai su gaji da zuga Ummi bayan idonsa Daya bayyana yayi amfani da kalaman bakinsa komai zai zama kamar bai Faru ba.

Da ace yayi auran da Hakki zai hau kansa Allah ya kamasa da Rashin Sauke hakkin yar yarinyar nan ai gwara Allah yayi fushi dashi Saboda yayi Saki sannan gwara Fushin Ummi na dan Lokaci da Fushin Ubangiji,sanman gwara Fushinsu Baffa na dan Lokaci da girmam Hakki da zai Daukan ma kansa.

Shifa ahakan ma yana ganin bai yi wani Laifi ba,gwara sabama Mutum sama da Sabama Allah.

Yana kwance a bayan Mota,Sai sharara gudu suke akan Hanyar Zaria zuwa Kaduna zuciyarsa ta cunkushe waje daya babu wani karsashi ko kadan.

*******

A garin lere har alokacin Ranar Safiyar Litinin din da sukayi wayi gari Cikin wannan Alhinin,Ummi tayi kuka har bata san ina adadin hawayenta ba, Mama zuwaira da Adda Sadiya sun gaji da bata baki sun hakura ganin yadda wannan karon Lamarin Hamman yafi koyaushe Tabata abu kadan sai ta Dago kanta ta Share hawaye tana fadin"Ba dai ni yaro zai ma haka ba Zuwaira..?

Yaje bani yayi ma wa ba kansa yayi mawa..Tijaran Dangin Ubansa ne yake so yajamin kuma Burinsa ya cika Nagode..!

Sai kuma ta saka kuka Adda Sadiya da tayi Tagumi abun Duniya ya isheta tace"Ummi don Allah ki daina wannan kukan mana.

Kada jininka ya hau kin fa san baki da Ishaahiyar lafiya.."

Ummi ko Sauraranta batayi sai sharan kwallah take yi su kadai ne adakin Sadiya ta kora su Laala Dayan Bedroom din ganin zasu kara ma Ummi Damuwa.

Mama Zuwaira data fito Daga Tiolet Dake cikin Dakin Fuskarta da Ruwa alamun alwala tayi ta kalle yayar tata Da tun data koma ta zauna Saman Darduman nan bata tashi ba sai Sharan kwallah take faman yi da mganar burin yaro ya cika ya jawo mata Tozarci.

Sadiya ta koma ta kalla da Duka Damuwa ya bayyana Saman Fuskarta Allah yasa Nihad na wajensu Sauda Dayake bata ma da Rigima.

Cikin kulawa tace"Addan su Mujaheed din ya same sa..?

Sadiya ta Dago tana kallonta Cikin wani yanayi kafin tace"Mama yace duka wayoyinsa daya sani suna kashe ne..Sannan yaje Office dinsa Sakataransa ya tabbatar mai da cewa Rabon sa da Office tun Ranar Laraba sannan bai samesa a waya ba.."

Mama Zuwaira ta jinjina kai kafin ta wuce wajen wani karamin jaka ta Dauko Hijabinta tana Fadin"Uhm..Daman nasan baza"a same sa nan kusa ba.."

Sadiya tace"Ammh yace suna da Meeting da gwamna yau din da Safe kuma yana da Tabbacin zai hallata so yace min zai je office in ya gama abunda yake yi zai koma chan ya gani ko za"a dace su hadun.."

Mama zuwaira tace"Allah yasa ya bari su hadunn Addansu.."

Sadiya ta amsa da Ameen kafin tayi mgana Mama zuwaira tace"Dubamin Lokacin Walha ya tafi ne..?

Sadiya ta Duba agogon Wayarta kafin tace"A"a mama zaki iya yi yanzu goma tayi.."

Ba musu ta isa gefen yar"uwanta ta kaikata ta tada sallah bayan ta saka Dogon bakin Hijabinta kamar ana Jira Tana Tada sallah Sadiya ta jiyo Hayaniya da Sababin Iya sannan kuma Lokaci Daya da Muryan Baffa Hashimu na kwalama Ummi kira Cikin Cikakken sunanta.

"Zaliha.."

Ina zalihar take.."

Ummi ta Dago Jajayen Idanuwanta ta Sauke kan Sadiya wacce itama ta Kalleta Cikin wani yanayi kafin ta samu Zarafin mgana Ummin ta mike tana Fadin"Ga su chan sun iso..Abunda nake jira ne bari naje na same su.."

Mama zuwaira na sallah tana ta umh uhm da gyaran Murya Ummi bata Saurareta ba kafin Sadiya tayi wani yunkuri Ummi ta Fice da Dogon Hijabinta Dauke da Carbi a Hannunta Fuskarta har ta kumbura Saboda kuka.

Sadiya ta Dafe kanta daya fara sara mata,Daman tasan ai hakan zai Faru,Iya bazata yi shuru ba koda kuwa wannan karon Baffa Hashimu bai yi mgana Majeeda wajenta ta girma duk cikin jikokinta tafi sonta kamar yadda Baffa Hashimun yake Dan lele awajenta.

Bata yi kasa a gwiwa ba ta bi bayan Ummi mama zuwaira kuma sai Allah Allah take ta idar ta je Falo saboda tasan Yayar nata nachan duke Dangin Uban Saifuddeen suna kare mata Tanadin da suka saba.

Koda Sadiya ta fito Falon karaf Daidai Lokacin da Inna Atika ke nuna Ummi Tana fadin"Karya take yi iya..Wlh ko Rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba Tasan inda D'an iskan yaron nan yake..Tasani ai itace uwarsa sannan in akwai wacce ke zuga Saifuddeen wajen Bijiremana ai itace.

Kada ku yarda da Magiyarta da wannan kukan munafuncin data saba Rudar ku dashi"

Tafada tana jin kamar ta kai ma Ummi Duka wacce ke duke a kasan Saman Cafet din Dake falon inda Iya ke zaune ranta bace tana Faman jijjiga Jiki Baffa Hashimu na gefe ya kasa mgana Baffa Hayatu na zaune kan Hannun Kujeran da Iya ke Zaunee goggo Atika da Daman bata bar komai na Tijaram iya ba, tsaye take ta kasa zama tana Faman auna ma Ummi Dake duke tana sharan kwallah gaban Iya harara.

Kafin Sadiya tace wani abu Laala Dasuke leke a Dakin da suke tayi Zaraf ta fito Tana Fadin"Iya mganar gaskiya Ummi fa batasan ina Hamma yake ba..Muma nemansa muke yi.."

Tafada idonta kar domin bata da Tsoro.

Ran Iya ya baci ta Dago tana kallonta kafin tayi kyaci Lokaci Daya tana Fadin"Su cin Danko har da su kaza..?

Ke kuma miye naki aciki..?

Da zaki sakomin baki ina mgana..

Kaji min ja"irar yarinya mara kunya.?

Tafada tana kumfar baki ko Tsufanta bata Duba ba,Domin ta tsufa kawai jin Dadi me ya lullubeta Ammh zata bama Saba"in baya sai dai ganin yanayinta zakasan tun tana matashiyarta ta iya tijara da bala"i.

Goggo Atika ce ta rike Haba kafin tace"Iya abunda aka kitsa mata ta Fada mana fa.

Ke yarinya ki kama bakin ki kafin yanzu ki shiga hannuna ki raina kanki.."

Laala ta juya ido zatayi mgana Ummi ta Dago Cikin kwallah kafin tace"Shema"u koma ciki nace.."

Kin tafiya tayi ganin Ummi na Hawaye ta kasa mgana sai Zeeha ta fito kamar tayi kuka tana Fadin"Ummi..!

Kafin Ummi Tayi mgana Adda Sadiya ta shigo Tsakiyar Falon tana Fadin"baku ji me Ummi tace bane..?

Ku wuce ku koma Daki kada wacce ta Sake fitowa."

Ba su isa suyi musu ba yasa Zeeha ta kama Hannun Laala suka koma dakin da suka fito suka Hada kai suka Fashe da kuka aduniya basu da kamar Ummi Shiyasa basa son zuwa lere saboda babu Alheri kwata kwata a zuwansu kowani Lokaci Ummi tazo da kuka take komawa..

Bayan fitan su Laala Falon Sadiya ta kalli Iya tana fadin"Ina kwanaku iya..?

Dukkansu ba wanda ya amsa sai Baffa Hayatu,kadai ya amsa sai jikinta yayi sanyi Bayan Ummi tabi ta Duka Tana Fadin"Dom Allah kuyi hakuri..Ba Laifin Ummi banee..Wlh batasan Hamma..!

"Ke rufe ma mutane baki..ai kema munafukar ce.."

Baffa Hashimu ya tareta tun kafin ta karisa kawai sai ta saka musu kuka Tana Fadin"Wlh gaskiya na ke fada muku..Bamu san me yasa Hamma yayi haka ba kuma bamu da masaniya.."

Iya tayi wani Dariyar rainin Hankali kafin tace"Ai ko jikina duka kunne ne bazan yarda ba Sanin Zaliha yaron nan ya Tozartamu ba..Komai yake Faruwa tana sane ita ke saka shi..Haka yayi ma Amira kuma ita ta sakashi Saboda ba Dangin ki ya Dauko ba ko Zaliha..?

Shiyasa kika saka shi Daki jiya kika basa Umarnin Sakin Majeeda,yarinya karama da batasan komai ba,an maida ita bazawara Gida nachan ya koma kamar gidan makoki uwarta da Danginta sai koke koke suke yi Hashimu sai kiran yaron nan ya ke yi bai same sa ke kika ce wayar ma ya kashe ko Zaliha..?

To gamu acikin gidan nan ko mu ko ke Zaliha"

Goggo Atika ta karbe da Fadin"Sai Saifu yazo gabammu ya Fada mana Dalilinsa na Tozartamu muji ko ya Sauya wasu Dangin ne damu.."

Ummi na kuka ta kasa mgana Sadiya ma Nayi iya ta gaji da jin kukan su ta Daka ma Sadiya Tsawa tana Fadin"Ki rufemin baki munafuka kema ai duk Daya kuke ba, man ta saka kika yi d'an uwanki Shitu ba..?

Ta aura miki D'an kanwarta ko..?Danginta sune Dangi mu kuma duk yan iska ta saka kuka Daukemu..?

Rufemin baki Kafin na saka Atika ta Nada miki Dukan tsiya.."

Sadiya tayi tsit sanin Halin Iya ada suna shiri ammh tun mganar auranta suka samu matsala Saboda taki Shitu yaron wajen Baffa Hayatu ne shine harda shi Haushin da suke ji na Ummi Iya ita adole sai sun dawo gida sun Auri Dangi Kada Ummi ta Karbesu Gabadaya duk da kuwa Hamma a wajensu ya tashi bayan rasuwar mahaifinsu kwace su sukayi Hannun Ummi ita kadai suka bar mata ta koma gaya inda yayansu yake da zama da iyalansa Kafin ta sake yin wani aure ta koma Abuja da zama.

Baffa Hashimu ne yana Huci yace"Mufa ba kuka muka ce ki Tsamu kina mana ba Zaliha baki zaki Bude ki Fadama ina yaron nan Saifu yake..?

Nayi rantsuwa bazan yi kaffara bai isa ya maida min y'a karamar bazawara ba karyansa tasha karya wannan karon.."

Ummi na kuka tace"Wlh bansani ba sau nawa zan rantse muku..bansan inda yake ba.."

Atika tace"To ke baki san ina yake ba wa kike so ya sani..?

"Ku zaku san inda yake mana..Tunda kuka makala masa auran da baya so.."

Atare dukkansu suka waigo suna kallon Mama Zuwaira tsaye kikam da Hijabinta Data gama sallah Fuskarta ahade suna ganinta suka kara Hade rai sanin Halinta mai zafi ce bata Daukan raini ba kamar Ummi bace

Atika ce tace"To ta ya ya kuma mu zamu san inda yake..?

Kudai kukasan inda kuka Boyesa Tunda abun naku rashin mutumci ne."

Ko kallonta Mama Zuwaira batayi ba,Ta isa ga Ummi tana Fadin"Yaya zulai ki daina wannan kukan don Allah..Taya ya zaki zo su tasaki suna Fada miki mganganu haka kiyi shuru..?

Ko baki yi musu bayanin kema baki san me ya aikata ba ballatana ya gayamiki inda yake ba..?

Ummi na kuka tace"Zuwaira na Fada musu basu yarda bane..Tayani kara Fada musu wlh bansan ina yaro yake ba."

Mama Zuwaira tace"To ba kin gaya musu ba..?

Zaman me kike yi taso muje Daki kiyi wanka na kira yaya sunusi yace yana Hanya yau zai Taho.."

Ummi ta Dago tana Fadin"Jiya fa ya koma Zuwaira..?

Mama zuwaira na Hararan su iya tace"To ai ta kama ne..Gani nayi zasu yi miki Taron Dangi gwara yazo su san kema kina da gata.."

Atika ta tsoma baki da Fadin"Ina gatan yake..?

Nace ina gatan yake yar kanzagi..?

Mama Zuwaira ta Daga mata Hannu Tana Fadin"Ke Atika ki iya bakin ki Domin ban saka Dake ba.."

Tafada cikin Kaushinta sanin Halin Zuwaira yasa bata kara mgana ta koma tana wani zare ido.

Baffa Hashimu ne ya kalleta sanda ta tada Ummi Tsaye tana rike da Hannunta ya kada kai kafin yace"Ke zuwaira har yanzu bazaki Daina Rashin Da"arki ba. Ko..?

Iya ce ke mata mgana kika D'agata me kike nufi..?

Ta kallesa wani Shekeke batayi mgana ba illah Hannun Ummi data Damke tama Fadin"Muje kiyi wanka Yaya zulai don Allah.."

Ummi bataso tafiya ba Mama Zuwaira ta jata tana Fadin"Sadiya saka su Laala su Dafa mana ko Ruwan zafi ne mu sha Tea in yaya sunusi ya iso yau gaya zamu wuce domin banga amfanin zaman mu anan ba.."

Sadiya murya dishe ta amsa mata su Iya suka bi Mama Zuwaira da kallo har ta Shige da Ummi Ciki Atika tace"Kan bala"i Iya..!

Iya ta Daga mata Hannu Tana Fadin"Kada kice komai Atika..Ai zuwaira daman bata da mutumci ko na Miskala zarratin..ki bar su muna nan sai dan"uwan nasu yazo ayi ta kare..Wlh Tallahi wannan karo ko ni ko Zaliha..Kuma Auran Majeeda kamar Saifu ya maidashi ya gama zai gane ni nayi Nagudar Ubansa yazo Duniya Tunda ya zama d'an jakar Uba.."

Atika sai kara zuga iya take Baffa Hashimi kuma sai Huci yake saki ga waya a Hannunsa yana ta kara kiran lambar Saifu bata shiga Baffa Hayatu dai na zaune shi dan cewa abi komai a Sannu ne.

Sadiya kuma sai da tayi aikin Lallashin kannen nata kana suka shiga Kitchen suka Dafa ruwan zafi suka soya Dankali Saboda sha"anin nan da kayan abincin su suka zo Duk da daga Babbar gidan su Adda Sadiya din ake aiki musu da abinci n suka zo garin, gidan da suka sauka Gidan da Hamma da Sadiya suka gada ne nq mahaifinsu suka Bugesa suka falala ya koma na zamani nan suke sauka indai suka shigo Lere kamar koda yaushe.

Su Iya kuwa basu jirga ba sun yi Rantsuwa sai an yita ta kare duk suna zaune su Laala suka gama Hada Breakfast,Sadiya ta kawo musu goggo Atika ta mata tsawa tace ta kwashesu hakanan ta kwashe jikinta a sanyaye.

Ummi kuwa tana ciki tayi wanka Mama zuwaira ta lallabata tasha Tea ta bata panadol Mganinta na Hawan jini ya mata karfi tasha shi yanzu sai zuwa Dare.

Banza da su iya Sukayi Mama zuwaira ko kara lekosu batayi ba itama ta gaji kan Damuwar yar"uwanta itama ta amince yau ko so ko dangim Saifuddeen

Har ta su Laala sun yi wanka itama Adda Sadiya tayi wanka ita da yarta Nihad sannan tana jiran kiran Mujaheed ne ya sanar mata agidan gwamnati Su Saifudeen suka Shiga meeting din ammh zai jira ya gani in sun fito ko Shi Saifun din ya Hallacin Taron..?

Da haka dai suka rabu tana jiran kiransa ita kuma Mama Zuwaira jiran zuwan yayan nasu suke wanda ya zame musu kamar Uba da uwa yaya Sunusi domin ayi wacce za"ayi yau su da su iya Tunda basu san mutumci ba.

Littafin Saifuddeen na kudi ne pay N500 via 0552179550 Jamila umar Gt bank,sai a turo evidence of payment ta wannan Lambar *** ko kuma katin waya na Mtn sai adauki Hoton katin a tura ta wannan Layin kai Tsaye *** mutanen mu na Niger kuma zasu tuntubi Kausar aglan Nissa ta wannan lambar domin karin bayani +22796562223 Ina maraba da masoya na a duk inda suke

Janafty

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol