Free chapter · Read without an account
06
*SAIFUDDEEN*
_(Ba mutum ba ne)_
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*♥️
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*🅿️6*
Maganar su Inna kan Saifuddeen ba Mutum ba ne zan iya cewa na Aminta dasu bisa tarin Hujjojin da ni kaina nasan haka din ne sai dai zuciya ta bata Aminta da mganar ya aureni bazan taba aure ba, abu daya na sani nayi zaman Aminci da Saifudeen bani da masaniyar Mutum ne ko aljani ne duk da alokacin ina da karancin shekaru kuma wannan Aminci na rikesa a zuciyata yayi min Tasiri da nike Tunanin ko da muna da bambamci wajen Halita Saifudeen bazai taba cutar dani ba.
Na dogara ga Allah sannan na san shi ke yi alokacin da ya so da kuma sanda yaga dama,ammh ina shan magani ko da yaushe saboda Inna yadda take damuwa da al"amarin mganani na sai kaji Tsausayinta bata da wargi tana da Fada in nace ma bazan sha ba sai an ji mu ni da ita shiyasa bakina alekum nake karba nasha wani Lokacin ma daya kare da kanta take zuwa gidan mallam Haruna ta karbo min wani Tunda gidansa bashi da nisa da namu.
Inna ta fara gasgasta mganar wannan Bafulllatanin na Bakori Daga Sanda Girma ya kamani na zama Cikakkiyar Budurwa duk da dai ni Muhibba bani da wani kyau na azo agani ammh ni kaina nasan ina da Farinjini duk inda na shiga sai na samu masu sona ba ga matan ba ba ga mazan ba,Sannan ina samun makiya Saboda Sanyin Halina da Hakurina yakan siyamin soyayyar Mutanen da nike zaune dasu haka nayi Rayuwata a makaranta bani takamammiyar kawa sai abokan arziki da ake gaisawa dasu kuma har na kamallah nayi Service ban tantance wata Aminiyata ba sai dai ana mutumci sannan akan gaisa ta waya Lokaci bayan Lokaci..
Ko fita nayi Inna ta aikeni bana Dawowa sai wani ya tareni yace yana sona ammh duk wannan Rubibin da ake yi akaina wani namiji bai taba Dadani da kasa ba,ban taba jin wadanda ke sona suna Burgeni ba,Babani ta na nan araye a garin Bakori agidansu Inna ita ke kara Fadama Inna tunda taga bana son kula masu sona Ta tabbata Aljanin ya aure ni kenan ita kuma Inna sai ta yarda da mganarta Sau tari Ya Habiba bai cika yarda ba In inna ta zaunar dashi tana Fadamai sai an mike Tsaye abubuwana suna ta karayin gaba shi dai Sai dai yace koma da wata matsala Inna mu cigaba da gayama Allah Lokaci ne Watarana sai Labari..In yace Haka Inna haushi take ji sai ta kallesa tace"Lokaci ne ammh ai kasan Akwai aure tsakanin mutum da Aljan..Sannan kana da ilimi kasan Akwai junnul Ashiq ko..?
Bai kara mata mgana sai dai ya bata Hakuri Sani ne yafi biye mata in tana irin wad'andan mganganu shima Saboda ya Tsokane ni Sani har suna ya Taba samin wai matar Aljani Tun ina Tankasa muyi ta Hayaniya watarana Inna ta tankamu watarana kuma Tayi banza damu ta cigaba da aikin gabanta,Danagaji ne na kai karar sa wajen Ya Habibu shine ya taka mai Burki ya daina Kirana da wannan sunan..
Sau tari na fi kaunar zuwa Gaya babban gidansu Babanmu akan Bakori Saboda Babani har tafi Inna Zafi gata da Mitar Tsiya in naje garin nan ta rika yawo dani gidajen masu mganguna har fa gidan wani Boka tataba kaini to boka Mana tun da Yana kallona yana Zare ido nan take yace ai Saifudeen ya Dade da aurena ya"yan mu goma ma dashi kaji karya goma kamar wata akuya har tambaya yayi wai bana mafarkin ina shayar da Jarirai na tura baki nace ni banayi Babani ta Dunguremai kai tace ai ko" ki nayi bazata Fadi gaskiya ba abunda yasa nace Boka ne cewa yayi Babani zata bada kudin yanka ni kuma ina da Ilimi na daidai gwargwardo duk da ban yi sauka ba Ammh ai ba inda bazan karanta ba acikin Alqur"ani ba sannan Sauran Littafai ina da sani a kansu har yau har Gobe ban daina Neman ilimi ba Domin shine ado da kyalkyalin ya mace bayan Hallaya mai kyau.
Shiyasa muna Dawowa bata sani ba na kwashe kayana na Gudu Gaya daman Lokacin nagama Bautar kasa kafin na samu aiki ina gida.
Achan Gaya wajen Goggo Naja nake Sauka in naje saboda itace kawar innamu,Duk da suma su Inna Firdausi girma yasa sun sauya Hallayansu ammh kuma nafi sakewa a bangaranta Saboda diyarta Sa"atace Asma"u ammh an yi mata aure shekarar data gabata tunda su basa zurfi a ilimi,Sannan ina zuwa gaida Goggo Barira duk in naje garin da kuma gidan Baba Sunusi shi ba kasafai nake zuwa ba Saboda nafi zuwa In tare da Inna muka zo garin.
Aikin koyarwa bashi ya zaabeni ba ni na zabesa da kaina domin yana Burgeni,Ita Inna Burinta nayi aure bata so ma nayi B.Ed dina ba ammh Ya Habibu da Anty Habiba da megidanta suka Lallashi Inna nacigaba har nakai matakin da nike ayau zuwa Lokacin kuma bansan adadin Samari masu abun hannunsu da suka nuna suna so na ba naki su,Har da'n Baba Surajo Aminu daya gama karatunsa a zaria nan Nuhu bamalli yayi Nd dinsa da H.N.D Dinsa gidanmu ya zauna ma kafin ya koma cikin makaranta shima har Baba Surajo ya sanar mawa yana sona ammh naki sa Ya Habibu yace kada a matsamin,Ran Inna sai da ya baci ahakan ba to gwara ma shi tafi jin Haushin yadda naki wani abokin kasuwancin Ya Habibu Alhaji Maude,Shagonsu suna kusa da juna ne a Sabon gari sannan suna Aminta sosai,ya so ni sosai matarsa ce ta rasu ya"yansa uku tun wani zuwa da yayi gaida Inna ya ganni shi kenan ya Rude sannan Ya Habibu na Fadin kirkinsa da Hallayarsa na gari aiko Fir naki sa shi kanshi da Bakina na Fadamai yayi Hakuri Inna dataji sai da tamin Dundu Sani na Zugata wai Bani da mutumci ne babbar Mutum kamar Alhaji Maude na wulakantasa Shi kuma Ya Habibu yana da Zafi ammh kuma awajena ruwan sanyi ne Baya taba Tsamanin in nace bana son abu to shima ya barshi kenan Da Inna ta Fara Fadan yana Daure min gindin Iskanci ya zaunar da ita ya Fadamata Cewa kamar Amana ne ni a wajensu Baba ya bar gidan duniya dani aransa Bai kamata domin kasa ta rufemai ido kuma sai a tursasani yin abunda ban yi niyya ba ballatana sha"anin auren wannan zamanin kada ayi kuma Daga baya azo ana jin zafin juna da wadanan kalaman Inna ta dan Sausautamin ammh a kwanakin Inna In na mata mgana Dakyar take amsani ballatana Lokacin Sani yazo Hutu ya dinga Hura wuta..Kai Sani karshe ne wajen Hada husuma baya Raba Fada sai dai ya hada dackaifin Bakinsa...
Sani Bello maiRago,Dan gaye ne sannan dan Fafane sani yafi ni kyau kamar yadda yake fadi saboda yafini Dogon Hanci sannan dogo ne burin kowacce Macen zamani ya iya Tsara Zence gaskiya kuma ya iya Turanci wannan Zamanin ta wannan bangaran sai dai mu goga in Wulakancinsa ya tashi sai yace bazai yi mgana da Hausa ba duk yinin Ranar,Ni wani lokacin bana tankasa saboda nasan So yake yaga ya sakani kuka ko kuma na kulasa mun yi tsiya ammh shi kanshi ya sani ni Muhibba a Karatu bai isa yamin zarra ba sai dai banbamcin inda kowa ke karatun nasa..
Sani tun ba yau ba ya sha sakani kuka,aTun ban gane ba har na gane nima na fara kwatan kaina yana gayamin zan fadamai sai ya Bige da na Rainasa namai rashin kunya ai shi Yayana ne ga Sani da Saurin Hannu Abu kadam in ina kusa dashi sai yace zai kaimin Mari wannan kuma Inna ta takamai Burgi tace bata son iskanci shi ai bata Dakesa ba da zai rika Dukana Shikenan sai ya koma in ya kamani sai kusa sumar dani ni kuma nace in ya Fasa in ya Biyoni sai na shige Shashen Ya Habibu to yana jin kunyar Anty Zeenatu baya bina chan Saboda yana son kanwarta duk da na yaudaran daya saba yi ne sannan Sani yana bala"in Shakkar ya Habibu ni kuma ya Habibu da Anty Habiba basa taba kwaremin baya har gwarama Anty Habiba muna yar Tsiya da ita wani Lokacin.
Ban kara shiga uku da Lamarin Sani ba Sai da abokinsa Abbati yace yana sona Abbati makotanmu ne,Babansa yana da gareji na gyaran mota achan bakin Titi,Abbati shi ke kula da wajen Sannan shima ya iya kanikancin,Sai dai bai yi karatu ba iyakarsa Secondary school,Abokin Sani ne Tun Dawowarmu anguwan,Tun suna yara Bashi da wani aboki kaf anguwan nan sai shi Tare sukayi islamiya dashi ajinsu Daya har makaranta secondary ma tare.
Ni ban raina Abbati ba ammh ni bai taba kwantamin araina ba kuma bazan Boye abunda ke raina na cutu ba,Tunda Sani yaga na nuna bana son ya kara matsanin Lamba ko baya gida sai ya Kirani a waya yana gayamin mgana kan abokinsa ni kuma na tankasa muyi Rabuwar tsiya a baya muna Fada ammh bana kwana bamu Nemi juna ba ammh Dalilin mganar Abbati muna gabar wata Daya da Sani Saboda ko baya gida muna Haduwa a Chart Tunda ina da babbar Waya Infinix Hot 12 da Ya Habibu ya siyamin Sai muyi wata bai kirani ba nima haka sannan a chart bayamin mgana nima nayi kamar ban gansa ba Sai dai muyi View Status din juna kuma ko Dawowa yayi muka Hadu kowa zai Dauke kai ne ammh shi kam sai ya samu mganar daya Chabamin.
Akwai tsiyar da muka tabayi wanda bamu taba irinta ba kan ya bama Abbati Nombar waya ta kuma sai da nace Kada ya basa Abbati na kirana na Gane muryansa na kashe Sani baya Gida yaje Bakori gaidaa Babani ya kwana Daya ya Dawo yana Dawowa na Taresa da bacin rai meyasa ya bada Nombana yace ya bada ko zan dake sa ne..raina ya baci nace bana son haka Sani kada ka karamin haka shima ya tasomin na Raina sa ni kuma naki guduwa ya mammareni da girmana fa har Bautar kasa nagama alokacin aiko ranar naci kuka Inna tana jin mu taki tankamu tayi banza Damu sai da Ya Habibu ya Dawo na tafi Shashensa ina kuka na Fadamai ya Kira Sani yamai Fatafata yace kuma Abbati ya kyaleni Tunda bana so Watarana Wanda nake son Allah zai kawosa Tunda ga Lokacin Sani kamar ya Hadiye rai da an yi mgana Sai yace Ni ai Sauran Aljani ne sai ma wanda yaga Allah ne zai taimakamai yasha sani kuka ba Tun yau ba sai dai abun tambaya anan Suna da Sheda ko Hujjan Saifudeen ya aureni..? In suna da Hujjan shi ba Mutum bane ammh basu da Hujjan Mganar karyan malaman da suke Fadin ya aure kawai dai shi Namiji ai sai kana Ra"ayinsa zaka auresa ni abunda na yarda dashi har yau ban samu wanda yayi daidai da Ra"ayina bane In na sameshi zan karbesa kuma nina zan yi aure ko don na Numa su Inna Ni SAIFUDEEN bai aureni ba.
Na fara aiki da makarantar Saifudeeen Acadamy shekara daya da wattani a online naga Tallar sabuwar makarantar sannan kuma suna Neman Sabbin malamai,alokacin makarantar shekararta Biyar ne da Budeta ammh Saboda Tsaruwarta da yanayin Tsarinta yasa take da Dalibai kamar tsohuwar makaranta Tsakani ga Allah Sunan makaranta ne yafi jan Hankali na domin har Gobe ko a ina aka Kira sunan Saifudeeen sai gaba na ya amsa,Ta online muka cike Form da bayanan mu sannan Daga baya suka Neme mu mukaje cikin makaratar mukayi Exam ta Computer sai alokacin na kara raina kaina Dana ga makarantar da irin malamanta da wadanda suka jagoranci jarabar duka Drs na ilimi,sannan malamansu Very Educated kai daga gani kasan wajen ba wajen marasa ilimi ba ne waje ne na wadanda suka san me suke yi ban Taba Zaton bazam ci ba saboda nasan kaina ba cika baki ba Bayan wani Lokaci aka turomana Sakon muje Interview,anan ne kuma na Hadu da Anty Khadija da Anty Usaina da Uncle Hafiz duk tare aka Dauke mu.
Kuma cikin ikon Allah mun ci sannan aka Daukemu aiki a matsayin parmanet, malamai a makaranta sannan A Teacher per class ne ni primary 4 nake Dauka Shashen primary,Da albashinsu mai Tsoka sai dai sai fa ka Dage domin basa Shiri da Malamai wadanda basu san abunda suke yi ba ganin haka na kama jikina sosai na rike aikina da Hannu Biyu ba ni da Ranar hutu sai Weekend a cikin makaranta kuma ko Zaman Staff room da sauran malaman kan yi ba na yi ina ajina saman kujeranta ina Duba Darasin gaba da zan yi ma yara sam bani da wasa kowa ya sani shiyasa sauran malaman ke kallona ni ba kyau ba yar masu kudi ba sai uban girman kai Duk ba dai ba na mugun shiga ba Koda yaushe Anty Habiba da Ya Habibu Cikin dinkamin kaya suke nima ina yima kaina saboda Dole Zirga zirgan zuwa makaranta sai da Kaya da wadatttun Hijabai.
Ban damuwa da mganar da ake yi akainq abu daya tn sani ba na gaba da kowa ina gaisawar mutumci da mutane sai dai bani da Sakewa ne da kuma irin shanshanci na wasu matan uwa uba kuma ba ni da Hayaniya surutuna ba na cika sakinsa a ko"ina Shiyasa Anty Khadija da Anty Usaina ke adawa da ni barin ma da suka ga Har Deractor musa Dake Rike da Ragamar makarantar yana yabama min sosai,Kuma har yau basu san waye mai mallakin wannan makaranta ba Director Musa ya ce Kila wannan Speech din da za'a yi in mai makaratar nada Lokaci zai yi kokari yaga ya matsamai ya samu zuwa.
Wannan kenan.
*********
Tunda Muhibba ta shige cikin Daki bata kara ko lekowa waje ba batasan ma Tafiyar su sani ba sai dare da Baban Walid ya Dawo yana Tambayata Siyama ta shigo ta kirata ta Zumbuda katon hijabin Anty Habiba ta fita fuskarta Duk ta Kumbura Saboda kuka ta zauna a kasa suka gaisa
Yana Zaune yana cin abinci ya kalli Anty Habiba yana Fadin"Waya taba mana Auta ne..?
Anty Habiba na kallon Muhibba da tana wani Hade rai tace"Kaima ka sani..Ita da Sani ne.
Yace"Sani..? Ya dawo garin ne..?
Ya Habiba tace"Eh ya dawo yau yazo shi da abokin nan nasa mai son Auta..To dai akansa ne ya gayamata mganata ita kuma ta shiga Daki tana kuka."
Baban Walid ya kalli Muhibba yana Fadin"Gaskiya sani bai kyauta ba..Kiyi Hakuri kin ji Auta.
Muhibba tayi shuru batace komai ba Anty Habiba tace"Nima Haushi na take ji kila domin ban ma sani mgana ba.."
Baban Walid yace"Kema ai baki kyauta ba sai ki Tsawarta masa ai ba"a so Dole ko..?
Anty Habiba tace"Ko Innar Habibu bata shiga fadan Sani da Auta..gwarama Ya Habibu..Kyalesu sun fi kusa sanda zasu shirya kansu bansani ba.
Muhibba tace"Allah ya kyauta.
Tafada ranta bace Anty Habiba da Baban Walid sukayi Dariya Dakyar ya Lallasheta ta saki ranta sukaci abinci da yaran sun Dade afalon suna kallon Arewa24, Anty Habiba suna ciki ita da Mijinta goma nayi ta kashe ta tarkata Walid ta ja siyama zuwa Daki sukayi Shirin barci Daman khalipa bai cika kallo ba shi yana Daki tunda suka gama cin abinci.
Har washegari Lahadi Muhibba batayi shirin komawa gidan Inna ba da Anty Habiba ta mata mgana sai ta Tabe baki tace"Sai wannan d'an rainin wayau ya tafi zan koma ammh matukar yana gidan nan na bar mai..
Anty Habiba tayi ta Dariya kafin tace"Innarki da yayan ki zasu yi Cigiyarki nasani.
Ita dai Muhibba ta yanke shawaran Daina zama kusa da sani Tunda ta Lura rainin wayau nashi ya kaita Bango gwara uban kowa yayi ta kansa kawaai.
******
*LERE*
10:30AM
Saifuddeen ne Durkushe gaban Iya acikin Falonta da jikokinta irin su Saifuddeen suka gyara mata shi babu Abunda babu na alatun Rayuwa isowar sa garin kenan Jiya bai samu zuwa ba Gajiya ta saukarmai yayi ta barci har Rana tayi shiyasa bai Taho ajiyan ba sai yau da Safe.
Kansa na Duke kamar zai musu sujjuda yana Sanye Cikin Shadda Fara dinkin zamani da bakar Hula Zanna akansa,kafarsa sanye da bakar Safa da alamun bakin sawu cikin Dake kofar Falon Iya nashi ne.
Baffa Hashimu na gefen Iya sai Fama yake da Zuciyarsa sai Baffa Hayatu da Fuskarsa bata bayyana komai ba Goggo Atika kuwa sai karkada kafa take kamar wacce take jiran ace kyat ta fara Feshin hayakin Bala"i.
Falon yayi shuru bakajin komai sai Mganar Iya cikin Fada da bacin rai Fadi take"Idon ka kenan Saifu..?
Nace kuma Idon ka kenan..? zaliha taga Dama ta baka izinin zuwa kenan..?
Kansa na kasa bai ce Uffan ba Goggo Atika tace"Iya ki kira mai yarinyar nan Majeeda yaga yarda yarinyar nan ta koma Cikin Sati daya da yayi mata sakin Wulakanci..Tun da abun nan ya Faru take kuka abinci bata iya ci Ita da uwarta sun shaki bakinciki wlh Tsakaninmu da Zaliha sai Allah ya isa..!
Sai alokacin yadan Dago kansa yana kallon Goggo Atika tako Hararesa tana Fadin"Eh nace Allah ya isa mu a tsakaninmu da ita ko zaka rama mata ne..?
Saifudeen ya maida kansa kasa bai ce komai ba Baffa Hayatu yace"Iya duk ba wannan ba ke Atika ki bar Zagin Zaliha hakanan kada ku manta d'anta ne ko bai nuna ba yana jin zafin Abun..Yanzu abunda ke gabammu muji Dadinsa na aikata abunda ya aikata kawai."
Iya ta sauke ajiyar rai kafin tace"Hakane Hayatu..Kai Saifu dago ka kalle nan..
Dole ya Dago yana kallonta nuna kanta tayi tana Fadin"Wacece ni a wajenka..?
Cikin yanayin muryansa yace"Ke Kaka tace.."
Iya tace"Ba haka ba..Ni kakar ka zakace..Sannan ni na yi nagudar Ubanka Salahadeen bayan nayi Dakon Cikinsa na wata tara kafin ya fito Duniya."
Saifudeeen ya gyada kai kafin yace"Hakane Iya."
Ta nuna Baffa Hashimu kafin tace"Wannan fa shi waye a wajenka..?
Saifuddeen ya kallesa kafin ya maida kansa kasa yace"Baffa Hashimu Baba na ne, kani yake wajen mahaifina."
Iya tace"Dakyau..Wannan fa..?
Tafada Tana nuna Baffa Hayatu Saifudeen ya kaskastan da kansa kafin yace"Shima Kani yake wajen mahafina.."
Iya ta sake nuna Goggo Atika tana Fadin"Ita kuma wannan fa..?
Kansa na kasa ya kara fadin"Tana Matsayin goggo na ce..Kanwar mahaifina."
Iya ta gyara zama tana Fadin"Nagode Allah ma da kasan babu abokin wasanka anan wajen.To kada ka nemi ka raina mana wayau kamar yadda kayi abaya Lokacin auran Amira wannan karon ba Ragowa a tsakaninmu mune Dangin Mahaifinka kuma mune Dolenka muke da Cikakken iko akan ka ba Zaliha da Danginta ba..Saifudeen Dago ka Fadamin me Majeeda tayi maka ka Saketa a washegarin auranku..?
Saifuddeen kansa na kasa bai Dago ba kuma bai yi mgana ba Baffa Hashimu da ya kasa mgana Tun dazu a fusace yace"Bakaji ana maka mgana ne kayi mana mutane banza."
Saifudeen ya kara sauke kansa kafin yace"Na kasa mgana ne..Ina kokarin Harhada kalmar hakurin da zan baku tayi tasiri a zuciyarku ne..Iya don Allah kuyimin aikin Gafara kwata kwata ba'a son Raina hakan ta faru ba..Ko da kuka ga na tafi ban yi sallama da kowa ba kunyarku nake ji bazan iya tsayawa na hada ido daku ba bayan abunda ya faru..Shiyasa na tafi ba wanda ya sani ammh don Allah kuyi hakuri hakan bazata kara faruwa.
Ya karishe fada Cikin Taushin murya da iya tsara Zence sai falon yayi shuru Domin kalamansa sun kashe musu Jiki Baffa Hashimu ya gyara zama kafin yace"Mun ji min yafemaka..Ammh me ye dalilin dayasa kace ba Laifinka bane.?
Saifudeen na sosa kunnensa da Hannunsa na Hagu yace"Baffa bazan iya gaddama da ku ba..Kun isa har kun yi yawan da zaku bani Umarni nabi..Ko alokacin da kuka auramin Amira ai ban yi gaddama daku ba..Bana son ina gaddama daku shiyasa hakan take faruwa.
Cikin mamaki Baffa Hayatu yace"Kamar ya bamu gane ba..?
Sai da ya Dago ya kallesa kafin ya Sadda kansa yace"To baffa da ku zaunar dani kuce ga aure zakuyimin nace bazam karba ba..ai gwara na karba na sauwake ma yarinyar saboda kada na shiga Hakkinta.
Sai sukayi shuru suka kasa mgana shi kuma ya cigaba da Fadin"Wlh Tallahi ba ruwan Ummi a wannan mganar ko ita kanta bata kara ganina ba..Lere na fara zuwa sai nagama da nan zan wuce Abujan..Iya mganar gaskiya bana son Hakki ko kankani ne ya zauna akaina..Nasam kun auramin Majeeda cike da kauna kamar yadda kukayi na Amira,sai dai duka ban iya Biyan ku bashin kaunarku ba..Ba kuma Laifina bane Iya da su Baffa Da ka sabama Ubangiji ko kuma ka Sabama mutum Dan"uwanka wanne yake da Saukin Dauka..?
Sukayi shuru suka kasa mgana sai Iya ce tace"Sabama wani mutum ai kuwa bai kamata ka hadasa da Sabama Ubangiji ba Saifudeeen."
Saifudeen yace"To kamar haka ne Iya in na Faranta maku rai ni kuma zan Sabama ma Ubangiji na.saboda bazan iya Sauke Nauyin matar da kuka auramin da ya rataya a wuyana ba..Bazan iya ba ni kuma da in Farantamuku na sabama Ubangiji na gwara na bata muku sannan na tsira da Lada ranar gobe kiyama."
Gabadaya sai da jikinsu yayi sanyi Safuddeen Harshensa nada wani kaifin da in yana mgana duk yadda ka kai da jin Haushinsa sai kaji ka sauka harta Baffa Hashimu da ya zuciya ya fara Saukowa.
Iya ce ta kada kai kafin tace"Bangane bazaka iya sauke Hakkinta ba..?
Baka da muhallin ijiyeta ne..?
Ko sana"ar da zaka riketa ne baka dashi..? Kai da kake da aiki yafi uku ma da zaka iya rike mata hudu bama Daya ba.
Baffa Hayatu yace"to ko dai wata matsalan ce ta Dabam.
Goggo Atika ta kurama Saifudeen ido tana kallonsa kafin tace"Kodai gaskiyar ne kai ma Aljanar ta aureka kamar yadda ta auri musan gidan Alhaji isuhu shekararsa Sitti bai yi aure ba..
Sai iya ta Rude ta fara Salati Tana Fadin"Saifuddeen kardai mganar Atika gaskiya ne..?
Kana da lafiya kuwa..?
Kansa na kasa bai yi mgana ba kadan ya Rage bai yi dariya ba wai Aljanna ta auress ba bazai manta ba har Ummi tasha tambayansa bai da wannan amsar,amsar kuma da zai gayamusu bai shirya fadinta ba bazai iys sanar dasu acikin mafarki ne kadai zai iya Saduwa da mace ammh ba"a Zahiri ba mace ko Tsirara zata yi agabansa bazai taba jin komai akanta ba.
Gajiya sukayi da Tambayansa yayi musu shuru yaki mgana Iya ta Fashe da kuka tana Fadin"Allah Sarki muna ta Zargin baiwar Allah Zaliha ashe shi lafiya ce bai da ita..Mun shige su.
Baffa Hashimu yace"Iya to menene mafita..?zamu maida masa da auran majeedan ne yanzu..?
Iya tace"Wani aure Hashimu..? Ana neman Lafiya ai in muka maida masa ita mun kwareta..Sannan yaron nan yafi mu hankali..Muna ta kokarin yi masa aure bamu taba tambayarsa yanayinsa ba da sai aure yayi nisa ayi ta samun mtsala..Ai yanzu mganar maida aure bata Hashimu sai dai ayi mganar Lafiyarsa kawai.
Baffa Hashimu yayi shuru bai yi mgana ba goggo Atika tace"Tab Iya abun fa ba sauki Domin in suka aureka har Abada mutum bashi ba aure."
Iya ta zaro ido Kafin tace"Uban Aljana tayi kad'am ta auremin jika ta hanashi aure..Bata isa ba."
Baffa Hayatu yace"Iya indai wannan matsalan ne akwai wani mai bada irin wannan laluran a Marabas jos yake,nan ai Alhaji isuhun ke kai Musa kuma ana da Tabbacin zai yi aure nan da Lokaci kadan.
Iya tace"To to aiko chan zamu je yanzu..Kai Saifu ba mganar zuwa Habujan nan sai munje wajen mai mgani.
Saifudeen kansa na kasa yace"Ban ki mganarki ba Iya Ummi ma kinsan tana Fushi dani kimin alfarman naje na ganta nayi miki alkwarin sati mai zuwa zan dawo sai muje.
Iya zatayi mgana Baffa Hashimu yace"Yana da gaskiya Iya ki bar shi yaje din."
Baffa Hayatu yace"To ai ko bashi zamu iya zuwa mu masa bayani mu karbo mai mangunguna..
Iya tace"To ai shikenan zamu je dakai Hayatu yau ko gobe duk abunda kenan zakaji Saifu Allah dai ya Dubeka ya warware maka ita kuma wannan Aljanar data aureka sai an yi mana Hisabi da ita Ranar gobe kiyama Tunda ta zama azzaaluma banda zalunci ina ta taba jin Aure Tsakanin Mutum da jinsu aljanu."
Ba wanda dai yace ma Iya komai sai Fada take Saifuddeen ya karkace ya Zaro Sabbin kudi yan Dubu Bandir Biyu a aljihun sa ya sauke ma iya a gabanta sannan ya kara zaro Wasu Biyu ya sauke mata sannan ya karo Daya duka ya Sauke agabanta yana Fadin"Gashi nan iya naku ne..Wannan kuma in kunje wajen mai mganin sai ku basa.."
Iya tana ta saka albarka har da Goggo Atka da addu"an albarka ta bisa domin Saifuddeen ba daga nan ba baya zuwa ya barsu haka ita kuwa Iya Fadi take"Allah sarki shi kanshi Laluran ta Dameshi Zaliha ce ba wayau ita da ya kamata ma ta fara sani."
Sai jin dadi take ganin ya bada kudi har da na wajen mallam nan kuwa bata san bagarda tunaninsu yayi na kada a kara acusamai auran yarinyar nan.
Bai jima ba yayi musu sallama ya Fito Daga Dakin gabda zai bar gidan Daga shashen Baffa Hashimu ya hango yarinya tana lekensa tana kuka yana ji wata mata tana fadin"Ke dai majeeda anyi mara zuciya..Yaron da yayi miki sakin wulakanci kike leke kina kuka..?
Sai ya kara kallonta domin shi ko kashe shi za"ayi ai bazai taba nuna Majeeda ba, yana gani uwar ta janye ta tana Fada Dariya ta kamasa sai dai ya kanne bai bar gidan ba sai da yabi yaran gidam da kudi har matan su Baffa ma sun samu rabonsu.
Chan waje ma mutane suna ta Jiransa nan dai ya bata Lokaci sai wajen 12 ya bar garin na lere,Sau da Dama Iya tasha Fadamai Mahaifinsa ya gado shima in yazo Lere mutane basa yankewa a kofar gidansu mutum ne mai kyauta da kyawawan zuciya shiyasa shima yake kokarin kwatatanwa
Bai sauke numfashi ba sai da suka bar garin Lere suka Dauki hanyar Abuja Tim ke tuka Motar Bama na zaune gefen Direba shi kuma yana gidan baya yana Sauke Numfashi sai alokacin ya murmusa.
Afili ya furta"Nagama da wannan yaki ..Saura guda daya dake jira na a Abuja.
Littafin Saifuddeen na kudi ne pay N500 via 0552179550 Jamila umar Gt bank,sai a turo evidence of payment ta wannan Lambar *** ko kuma katin waya na Mtn sai adauki Hoton katin a tura ta wannan Layin kai Tsaye *** mutanen mu na Niger kuma zasu tuntubi Kausar aglan Nissa ta wannan lambar domin karin bayani +22796562223 Ina maraba da masoya na a duk inda suke
*Janafty*