Free chapter 路 Read without an account

Chapter 7-8

by Amanarcool 路 RAMIN 茦ARYA...

馃挮 *RAMIN 茦ARYA....* 馃挮


         Story & writing 

                    By

Mrs Muttala (Amanar cool) 



        *YOUNG TALENT*
*WRITER'S ASSOCIATION*



Sadaukarwa ne ga Aysharcool 



Free book 鉁嶏笍



Page 7&8



______Baki bu蓷e Maryam take bin Inna Hajara da kallo, tunani take wane irin turare ne haka da rana tsaka, gashi kuma da shegen 茩arni, anya ma Inna Hajara na da gaskiya.?

Zagin da Inna Hajara ke yi mata ne ya dawo da ita hayyacinta, cikin mamaki Maryam ta ce "Me na yi miki ne da ki ke mini wannan zagin? salon na yi magana ki ce na miki rashin kunya".

Cikin tsananin ba茩in ciki, da takaicin ganin da Maryam ta yi mata, ta ce "Na zage ki shegiyar yarinya, uban me ki ka fito yi, tun 蓷azu baki tashi fitowa ba sai yanzu, saboda tsabar jaraba da son 茩untatawa rayuwata" Maryam ta ce "Ikon Allah amma dai Inna Hajara baki da gaskiya wallahi ina ro茩on Allah ya shiga tsakaninmu dake, kuma ta Allah ba taki ba, muguwar mata, duk sharrin da zaki yi sai dai ya makara ga kanki dake da wannan figagar 拼ar taki, mai shegen kai yanda ka san an bugi diron".

Tana gama fa蓷ar haka ta yi wucewarta, ta bar Inna Hajara na 蓳a蓳atu ita ka蓷ai.
Da sauri Hajara,  ta koma ciki, ta 蓷auki waya Larai ta kira, bugu 蓷aya ta 蓷auka tana fa蓷in 茩awata lafiya dai? ko kin yi mantuwa ne? cikin jin haushi Inna Hajara ta ce "Ina lafiya wannan tijararriyar yarinyar ce ta ganni ina turaren nan. Ni dama na san shara蓷in nan, yayi tsauri".

Larai ta ce "Wai ki na nufin Maryam taga lokacin da ki ke turarenne? ke ma dai Hajara akwai ki da a zar蓳a蓳i, me yasa ki ka 茩i bari sai cikin dare ki yi".

Ta ce "Tsautayi mana, sannan kuma kin san halin wannan tsohuwar da jarabar tsiya, tsaf zata iya 蓳ata mini aiki ita ma. Sai aka yi sa'a da na dawo ba ta nan, ashe ita wannan ba茩ar Jarababbiyar tana nan". 

Larai ta ce "Idan ita bata 蓳ata aikin ba ai jikarta ta 蓳ata, kin ga yanzu dai babu Maryam a cikin wannan sabgar". Tsaki Inna Hajara tayi tare da kashe wayar saboda  蓳acin rai.

Ko da Maryam ta fita 茩ofar gidan, kicibis tayi da Haidar, kallonsa tayi da mamaki ta ce "Laa kaine yaushe ka zo"? ya ce "Ai na da蓷e tsaye a gurin ban samu yaron da zan aika ba ne".

"Me yasa baka kira ni a waya ba?"

Ya ce "Wayar na gurin chaji ne ina Auntyn ki fatan tana lafiya? shekaran jiya na zo. Aka ce bata nan". 

Murmushi tayi ta ce "Dama  wajanta ka zo kenan, yanzu kuma tana nan bari na kirawo maka ita"

Komawa tayi cikin gidan, 蓷akin su ta shiga da rawar jiki a kwance taga Afnan, ta dafe kanta dake sara mata. Maryam ta ce "Aunty Afnan lafiya na ga kin da fe kai, me yake damunki?".

Bata amsa ba sai ma 茩ara dafe kan tayi ta kuma cewa "Aunty Afnan baki da lafiya ne?"  Da 茩yar Afnan ta bu蓷e baki ta ce "Maryam kaina ji na ke kamar, zai fashe" dafa kan Maryam tayi ta na tofa mata addu'a sannan ta ce "Ya Haidar mai napep 蓷in nan ne ya zo gurin ki yana waje, gashi kuma ba kya jin da蓷i".

Runtse ido Afnan tayi jin an ambaci sunan Haidar, wani irin abu ta ji ya dira acikin ziciyarta, lokaci 蓷aya ta ji wata mummunar fa蓷uwar gaba, sam ba ta ji tayi maraba da zuwan nasa ba, take ta ji, wata irin matsananciyar tsanarsa, tsana mafi muni, da 茩yar ta ce "Maryam ki je ki ce masa ya tafi, babu in da zani.

Maryam ta ce " Aunty  me yasa ki ke haka ne wai? Yanzu shikenan haka za mu zauna, kowa ya zo ki ce ba kya son sa ya tafi, ke duk gori da wula茩ancin da ake yi miki baya damunki? Yanzu menene aibunsa fisabilillahi?".

Cikin rauni Afnan ta ce "Maryam baza ki gane ba, ni ka蓷ai na san me nake ji a zuciyata, ni kaina abin yana damuna, ba na jin da蓷in hakan, ban san dalilin da ya sa da mutum ya ce yana so na, nake jin muguwar tsanarsa ba".

Shiru Maryam tayi, kafin ta ce "Ina zuwa"
 Fita tayi a 蓷akin,  gurin Haidar ta koma ta ce "Yi ha茩uri na barka ka na jira, Auntyn ce ba lafiya, ba zata samu fitowa ba, ka yi ha茩uri, idan ta ji sau茩i zan kira ka, tun da ina da lambarka".

Cikin damuwa Haidar ya ce "Me ke damunta?. Tun yaushe ta fara rashin lafiyar?" ya jero wa maryam tambayar.

 Ta 蓷an ka蓷a kai ta ce "Kanta ne ke ciwo sosai"

Take damuwa ta bayyana a fuskarsa, ya ce "To ko asibiti Za mu je ne" 

"A'a, ba sai munje asibiti ba, ta sha magani, na san da zarar ta samu bacci zata samu sau茩i, in sha Allah".

Ba dan Haidar yaso ba, haka ya ha茩ura ya ce, yana mata sannu da jiki, zai sake dawowa ya duba jikinta. Gaba 蓷aya sai ya ji shi ma ciwon kan ya kama shi, ya so ganin Afnan ba ka蓷an ba, amma gashi ha茩ansa bai cimma ruwa ba, wancan karon ya zo bata nan, yau kuma bata da lafiya.

Suka yi sallama, Maryam ta koma cikin gida Shi kuma ya shiga babur 蓷insa.
Har zai kunna babur 蓷in ya tafi, ya zauna yayi shiru yana nazari, ya da蓷e a zaune yana tunanin abin da ya gani a gidan su Afnan, abin ya tsaya masa a rai, to me hakan yake nufi? ganin ba shida amsar tambayar, kuma babu mai ba shi amsarta, yasa tayar da babur 蓷insa ya bar wajen.

******

Hudah ce kwance a kan makeken gadonta, sai juyi take, wani irin feeling take jin yana taso mata, burin kasancewa da Ya Mudan na 茩ara bijiro mata, dafe mararta tayi tare da runtse idanuwanta, a fili ta ce "Ya Mudan ka kassarani, ya zan yi da wannan jarabar, bazan iya ci gaba da aikata abin da muke yi ba". Ta furta a hankali cikin damuwa. Wani irin juyi mararta ta kuma yi, a hankali ta bu蓷e idanunta. Duk yadda ta so ta jure, domin tayi ingantaccen tuba ta kasa, fitinar son kasancewa da shi, ta cigaba da damunta.
Da 茩yar ta iya mi茩a hannu ta 蓷aukko wayarta  ji take idan har bata samu abin da take bu茩ata ba akwai matsala, number shi ta kira, yana 蓷auka ta ce "Yaya kana gida ne?

Wani shi'umin murmushi ya saki, kafin ya ce "Eh yanzu na shigo gidan, akwai wata matsala ne?" 

茦ala bata ce ba, ta kashe wayar sauka ta yi daga kan gadon, ta fita daga 蓷akin ta nufi kitchen, wata 茩aramar 茩ofa tabi wadda zata Sada ta da bayan gidan, zagayawa ta yi ta shige sashinsa, a bu蓷e ta samu 茩ofar zaune ta ganshi akan kujera, yana kallon tv. Babu tunanin komai, ta fa蓷a jikin shi tana rumgume shi, shima rumgumar ta ya yi yana shafa ta, daga baya ya 蓷aga ta cak ya yi bedroom da ita.

Kallon 蓳angaren Mudan Hajiya Zainab take, tana mamakin me Hudah ta je yi a wannan lokacin, sannan me ye dalilin biyowa ta hanyar kitchen, ta da蓷e zaune a lambun gidan, tana jiran fitowar Hudah, amma shiru cikin Yanayin damuwa, ta mi茩e tabar wajan, tana addu'ar Allah ya tsaresu  daga mugun ji da mugun gani.

Sun da蓷e suna she茩e ayarsu, sannan tabar bangaren.

Ko da ta bu蓷e kofar kitchen 蓷in ido biyu suka yi da Mami, kallon ta Mami ta yi, ta ce "Daga ina ki ke?" cikin yana yi na rashin gaskiya ta ce "Dama Ya Mudan ne yace na zo na gyara masa 蓷akinsa". 

Babu tunanin komai Mami ta ce "Ok kin kyauta zo ki 茩arasa Ha蓷a mini kayan nan" ta yi maganar tare da fita daga kitchen 蓷in, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, ganin mami bata gane ba.

*****

Inna Hajara har maraice masifa take, ta ji ba茩in ciki sosai a kan ganin da Maryam ta yi mata, 茩wafa ta yi ta ce "Zaki gane baki da wayo"

Bayan Gwaggo ta dawo ne, 

Inna Hajara ta same ta ta ce "Gwaggon dan Allah a ja wa Amina da 拼a'拼anta kunne"

Ta ce "Wani abin Suka yi miki ne?"

Ta karkace baki ta ce "Kin san ni duk abin da zai zubar da mutuncin gidan nan, ba so nake yi ba, kuma ba na fatansa, ko dan saboda gudun lalacewar sunan zuriyar gidan nan.
Afnan fa maza take tarawa a 茩ofar gidan nan.
Kuma wallahi mutanen banza ne, dan ba ki ga 蓷an iskan da ya zo wurinta ba, yayi sallama da ita ba, da gajeren wando ya zo. Ga wani 蓷an iskan aski, irin na 'yan iska yayi, wallahi Gwaggo ki saka ido, tun kafin a wayi gari a ga abin kunya a gidan nan. Dan na yi wa uwarta magana, ta ce babu ruwana".

Ran Gwaggo ba 茩aramin 蓳aciya yi ba, ta ce "Yi ha茩uri Hajara bari 蓷anladin ya zo, zan yi maganinsu, Dole ya 蓷auki matakin da ya dace, ai shiyasa na 茩ara amincewa da su dawo nan, idan shi an asirce shi, ni ba a isa ba wallahi ". 

Hajara ta ce "Ya dai fi Gwaggo, dan yadda uwarsu ke da shegen son abin duniyar nan, wallahi bari za ta yi su lalace a banza"

Gwaggo ta ce "Wallahi haka ne, zan 蓷auki matakin da ya dace ai".

Ko da Hajara ta fita daga wurin Gwaggo, ta kwashe da dariya ta ce "Wai aure, na ga ta gidan uban wanda za ta yi auren, ita da aure har abada, kuma in Allah ya yarda, sai ta lalace ta fi 茩arfin kowa a gidan nan, muddin ina raye sai yaran nan sun ajiye abin kunya"

Bayan Baba ya dawo, ya je gaida Gwaggo, titseyeshi ta yi, inda take shiga, ba nan take fita ba, sai da ta yi masa ta-tas, sannan ta ce "Tana bashi Umarnin, ko Afnan ta fitar da miji, ko kuma a aura mata duk wanda aka samu".

Cikin 蓳acin rai Baba ya bar gurin, 

Mama da Maryam na zaune ya shigo, ko sallama babu, kallon juna suka yi, suna mamakin me ya tunzura shi haka, saboda kallo 蓷aya  zaka yi masa, kasan a hasale yake, aikuwa ya hausu da masifa ba ji ba gani, fa蓷a yake sosai.

Fa蓷an Baba ne ya tashi Afnan daga bacci, fitowa ta yi tsakar gidan, Baba ta gani yana  masifa, Maryam na ge gefe tana 茩un茩uni, tare da tsinewa Gwaggo da Inna Hajara, sai Mama dake kallon shi kamar yau ta fara ganinsa, tunani take me yasa mu Baban Afnan,  Ita ma Afnan cike da mamaki take bin shin da kallo abin da bata ta蓳a ganin Baba ya yi ba kenan.

"To me aka yi masa da zai yi irin wannan hasala?"

Ji ta yi  yana fa蓷in "Na gaji da wannan halin naku, me yasa ba Kwa son a zuna lafiya, sai dana garga蓷e ku akan ba ruwanku da shiga sabgar Hajara.To na gaji, aurar daku zan yi, ba zaku ha蓷ani da mahaifiyata ba, musanman ma ke, da aka ce kin fara kawo samarin banza a gidan"

Ya nuna Afnan data fito yanzu

Ya ce "Dole ki fito da miji na aurar dake ko kuma na aurar dake ga duk wanda naga dama, na bayar da sadakar ki" runtse ido Afnan ta yi, saboda jin abin da baba ya ce, 

Mama dake kallon ikon Allah ta ce  "Baban Afnan wai me yake faruwa ne?" ka zo ka rufe mu da fa蓷a ba tare da munsan laifin da muka yi ba".

Cikin jin haushi ya ce "Rufe min baki ai duk abin da suka yi wa Hajara da Sanin ki, akan me zasu zage ta sa'arsu ce, daga ta fa蓷a musu gaskiya". 

Maryam ta ce "Wallahi Baba 茩arya take, Inna Hajara munafukace, ba haka aka yi ba, Aunty bata san komai ba".

Duban Maryam Mama ta yi ta ce "Me ya ha蓷a ku da ita Maryam ba kya jin magana ko, kinga abin da ki ka jamana ko".

"Mama ni fa ba wani rashin kunyar dana yi mata" nan ta kwashe komai ta gaya musu, tsaki Baba ya yi, tare da 蓷aukar buta ya yi alwalar magariba, ya  bar gidan. 

Fa蓷a sosai Mama ta yi wa Maryam, akan komai Hajara zata yi, kar ta 茩ara kulata.

Afnan tsayuwa ta yi, guri 蓷aya, ta kasa motsi, sai da Mama ta yi magana kafin ta 蓷auki buta zuwa alwala.

****


Haidar cikin damuwa yayi wunin yau gaba 蓷aya, daga baya ma ha茩ura yayi da 蓷aukar fastoinja ya koma gida.

Mamaki ne ya kama ummansa, ganinsa a gida, ba lokacin dawowarsa ba.
Kasa 蓳oye mamakinta tayi ta ce "Ya na ganka a gida ne, lafiya dai ko?"

Ya jinjina mata kai, ya ce "Lafiya 茩alau" ya bu蓷e 蓷akinsa ya shige.

Wuri ya nema ya zauna, a gefen katifarsa, ya 蓷aukko wayarsa, ya duba number da Maryam kira shi da ita, ya kira sai dai aka ce a kashe guntun tsaki yayi, ya ajiye wayar a gefe.

*****

Abba ne ke waya da Alhaji munir, bayan sun gama magana akan harkokin kasuwancisu, Alhaji munir ya ce "Abokina ina muka tsaya ne akan maganar yaran nan" Abba ya ce "Dama ina son yima maganar, to bari nayi in shedawa uwar yaron, na ji ta bakinta" Alhaji munir ya ce to ba damuwa Allah ya tabbatar mana da alkhairi" Abba ya amsa da Amin, sannan suka yi sallama.

Duban Hajiya Zainab dake zaune a gefen sa ya yi, ya ce "Madam ya ne? kwana biyu nan kin sauya" ko dai baby ne ya sauya mini ke" murmushi ta yi ta ce "Wani irin baby, a ina ka ga babyn" . "A cikin matata mana, amma naga 蓳oye mini ake yi, ban san dalilin hakan ba".

"Ni fa ba ni da komai" ta fa蓷a tana dariya" shi ma dariyar ya yi, ya ce "Wai sai yaushe zaki dai na jin kunyata ace mata da mijin ta ba zata iya gaya masa tana da juna biyu ba" idan ba a fa蓷a mini ba, waza'a fa蓷ama".

Hannu tasa ta rufe fuska tana dariya, tsokanarta ya dinga yi, sannan ya ce "Allah ya inganta mana, yasa babyn nan rabonmu ne " da amin ta amsa.

"Ya ce bu蓷e fuskar mana
magana zamu yi" bu蓷ewa ta yi tana kallon shi,
Abba ya ce "Dama Alhaji munir ne yake son a ha蓷a auren Sharifa da Mudan, me ye shawarar ki a kai".

Kafin ta yi magana, suka ji 茩arar fa蓷uwar abu, da sauri suka dubi 茩ofa, Hudah ce wayar hannuta ta subuce, sakamako jin furucin da Abba ya yi.

Amanar cool ce鉁嶏笍
***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.