Free chapter 路 Read without an account

Chapter 15-16

by Amanarcool 路 RAMIN 茦ARYA...

馃挮 *RAMIN 茦ARYA....* 馃挮




                Story & writing

                         By

     Mrs Muttala (Amanar cool)




       *YOUNG TALENT*
*WRITER'S ASSOCIATION*




Free book鉁嶏笍



Page 15&16





_________Da sauri suka kalli 茩ofar Gwaggo ce da isowarta kenan, ta yi sallama a tsakar gidan ta ji shiru, daga baya kuma sai ta ji ana magana a 蓷akinsu Afnan, shi ne ta zo da niyyar zazzaga musu masifar suna ji tana sallama suka yi banza da ita, sai dai ta na zuwa ta ji Maryam na wannan maganar.

Shigowa ciki tayi, tana bin Afnan da kallo, gaba 蓷aya ta fita hayyacinta, cikin 茩an茩anin lokaci, ri茩e baki tayi ta na salati ta ce "Yanzu ke saboda lalacewa, da sangarta, maganar auren ce ki ke wa wannan haukar? to wai ke '拼ar nan idan ba a aurar da ke ba ji茩a ki ki ke so a yi a sha ki me ki ke nufi? ko kuma kin fi so ki zauna a gida ki na gwada girma ke da uwarki?".


Har Maryam za ta yi magana sai kuma ta yi shiru, sakamakon ganin Afnan na dafe kanta, ta na wani gunjin kuka, ita ma Maryam kukan ta fara ta na fa蓷in "Aunty ki yi ha茩uri in sha Allah, Allah yana tare dake, duk mai son 茩untatawa rayuwarki, da son ganin kin shiga damuwa, Allah ba zai ba shi iko ba, ko da sun yi nasara na 蓷an lokaci ce". Tayi maganar tare da kwantar da Afnan 蓷in a kan katifa.

Baba ya shigo 蓷akin yana fa蓷in "Hayaniyar me na ke ji a 蓷akin?"

Gwaggo ta ce "Shafafiyya da mai 蓷in ku ce, take 茩o茩arin kashe kanta, saboda da an yi mata zance aure, to ki sani komai za ki yi aure dai ba fashi, matu茩ar ina raye".  

Gaba 蓷aya jikin Baba ya yi sanyi, har cikin zuciyarsa yana jin babu da蓷i, ganin halin da Afnan take ciki, ga Maryam sai kuka take, abin da ya tsana kenan, ganin iyalinsa cikin damuwa, sai dai bai san abin da yasa yake yawan jin haushinsu ba.

Cikin sanyin jiki ya 茩arasa inda Afnan ke kwance, ya ce "Ke lafiya? me ye ki ke yi haka? ba na son shashanci. Ke sake ta".
Ya cewa Maryam, cikin damuwa. ta ce "Baba dan girman Allah ka yi ha茩uri, ka da ka yi wa aunty Afnan irin wannan auren, wallahi na yi maka al茩awarin za ta fito da miji idan aka yi mata haka ba a kyauta mata ba".

Shiru ya yi, ya zuba musu ido, ganin hakan yasa Gwaggo cewa "Lallai 蓷an ladi ban 茩ara tabbatar da kai solo蓳iyone ba sai yau, yanzu tsabar an raina ka, an mayar da kai jelar ra茩umi, sai yanda aka yi da kai, '拼arka ce zata dubi tsabar idonka ta gaya maka wannan maganar, to bari na gani umarninta zaka bi ko nawa" tana gama fa蓷ar haka, ta bar 蓷akin, abin da ya kawota ma bata tsaya yi ba. 

Shima fita ya yi daga 蓷akin, Maryam ta dubi Mama da tayi jugum, ta ce "Mama yanzu ba wani abin da zamu yi ne, ki duba halin da take ciki fa".

"Maryam ki rufawa kan ki asiri, ki 茩yale su duk abin da za su yi su je su yi, in sha Allah, Allah yana tare da ita" daga haka ita ma ta bar 蓷akin, rarrashin Afnan Maryam ta ce gaba da yi, ta re da bata ha茩uri.

Bayan fitar Gwaggo daga 蓷akin, cikin takaici ta nufi sashenta, a hanya ta ci karo da kawu Sanusi, ta umarce da ya biyo ta 蓷aki, bayan sun isa ne take gaya masa irin kalar rashin kunyar da su Maryam suka yi mata, sannan kuma da hukuncin da ta yanke. Kawu Sanusi ya ce "Yawwa Gwaggo kin yi mini dai-dai, dama hakan shi ya fi, tun farko yakamata a yi wannan tunanin, amma ko yanzu bata 蓳aci ba, in sha Allah gobe ko bai yi magana ba ni zan yi".

"Yawwa 蓷an albarka, shi wancan bita zai-zai 蓷in bai kira ka bane?"

"A'a 蓷azu ma mun yi waya da shi har ya ce in ha蓷aku, to lokacin bana gida na ce masa ya bari sai na koma gida zan kira shi, yanzu kuma dare ya yi sai da safe zan kira miki shi".

"To ya yi Allah ya kaimu safiyar lafiya, sai na ji idan shi ne ya bawa matarsa damar tafiya tayi zamanta, kamar an aiki bawa garinsu".

Sallama kawu ya yi mata sannan ya bar gurin.



WASHE GARI

Bayan an idar da sallar asuba, Baba tunani yake ta ina zai fara yin wannan bayanin, yana wannan tunanin ne ya ji kawu Sanusi na cewa "Jama'a. Assalamu alaikum ina yi wa kowa barka da asuba, kamar yadda kuka sani cewar a gidanmu muna da yara '拼an mata kusan su hu蓷u, kuma ko wacce a cikinsu ta kai mizalin aure, to daga cikinsu muna so zamu aurar da babbarsu, wato A'isha 拼ar gidan yayana Abbakar, inda mai bu茩ata ya yi magana, sai ya ba da sadaki a 蓷aura musu aure ko nan da kwana biyu ne".

Shiru jama'a suka yi ana kallon kallon. Liman ya yi gyaran murya ya ce "To jama'a kun ji abin da Malam Sanusi ya zo da shi, dan haka inda mai ra'a yi sai ya yi magana, a taru a rufawa juna asiri. Sannan ba abin kunya ba ne, dan uba ya nema wa 'yar sa miji, mutuncinta yake son karewa".

Nan fa kowa ya ce a'a, a wannan yanayin da ake ciki wa zai 蓷auko zancen aure, duk da ya kasance auren sadaka ne, amma ai muhallin da mutum zai zauna shima ba 茩aramin jidali bane, shi kuma wani cewa ya yi "Inda cikin 茩annenta ne da yana so" haka dai kowa ya din ga fadar albarkacin bakinsa, daga 茩arshe aka bawa kawu Sanusi ha茩uri, tare da addu'ar Allah ya fito musu da mijin aure.

Baba wani irin takaici ne ya kama shi, ya ji gaba 蓷aya ya muzanta, wai 拼arsa Afnan ce kowa ya ce baya so, sai ka ce mai wata ba茩ar kama, yarinyar dake da farin jini, ga ta kyakyawa, tsananin damuwa yasa ya tashi ya riga Kowa fita daga masallacin, ko hu蓷ubar da ake yi bai tsaya saurara ba.


 Bayan kawu Sanusi ya dawo daga masallaci, ya je gaishe da Gwaggo, sannan ya fa蓷a mata duk yanda aka yi, shiru tayi ta na nazari sannan ta ce "Anya Sanusi wannan abin ba shiryawa kuka yi ba kai da 蓷an ladi ba? tukunna ma ina 蓷an ladin yake?" . Kawu ya ce "Ai ya riga ni dawowa, tun 蓷azu shi ya dawo" .

"Au ya dawo amma shi ne ya gagara biyo wa ya gaishe ni? eh lallai ya nuna mini bai ji da蓷in abin da na yi ba, kai kuma Sanusi ka fa蓷a mini gaskiya anya babu wata 茩ullaliya ko? saboda na yi mamakin abin, wai kun fa蓷i yarinyar kuwa?" .


"Haba Gwaggo ta ya ki ke tunanin za a ha蓷a kai da ni a munafunceki, wallahi na yi maganar, kuma Ai'sha na ce musu".

Gwaggo ta ce "Ikon Allah ina ga dai yarinyar nan 茩auye zamu aurar da ita, kowa ma ya huta" .



*******


茦arfe takwas da rabi Hudah tayi shirin zuwa school, 茩awarta Nusee ta kira bayan ta 蓷aga babu sallama ba komai ta ce "Sis ki na gida ne?" Nusee ta ce "Eh lafiya dai?" "Ina fa lafiya ganinan zuwa yanzu" "Ok sai kin zo". Ko da Mami ta ga Hudah ta shirya, mamaki ne ya kama ta, saboda Hudah ba ta son zuwa makaranta a kan lokaci, amma wai yau ita ce ta shirya tun lokacin zuwan su bai yi ba, saboda ta ce mata sai 茩arfe tara da rabi zata je, dubanta Mami tayi ta ce "Daughter yau ke ce da shirin makaranta tun lokacin zuwan na ki bai yi?". 

"Eh Mamina kin san yau zamu fara jarabawa ne, sannan kuma akwai abubuwan da muke son dubawa ne ni da Nusaiba, kin san ita 蓷in she is brilliant shiyasa na shirya da wuri". 


Mami ta ce "Haka ne to Allah ya ba da sa'a ya taimaka" 

 Ta ce "Amin Mamina ni dai, zan yi missing 蓷inki sosai, kafin na dawo, i feel sad with out you".


Murmushi Mami tayi ta ce "Haba daughter, sai ka ce wadda za ta yi tafiyar kwanaki, yanzu dai ki tashi ki karya, sai ki wuce". "To Mami".


******


Tunda Baba ya dawo daga masallaci, ya shige 蓷aki bai fito ba sai yanzu, Mama ta so tambayarsa akan maganar Afnan, sai kuma tayi shiru gudun kar ya rufeta da fa蓷a, ta san koma me ye za ta ji.


Kawu sanusi ne ya shigo da kansa, ya ce masa "Ya zo Gwaggo ta na kiransa" sai a lokacin ya tuna da bai je gaisheta ba, da sauri ya bi bayansa.


Cikin ladabi Baba ya ce "Gwaggo barka da safiya ina fatan kinsha lafiya?" "Lafiya 茩alau, wato inda ban aika a kirawo mini kai ba kenan ba zuwa zaka yi ka gaisheni ba?" . Ba haka ba ne Gwaggo 蓷azun raina ne a 蓳ace shiyasa" "Me ye zai 蓳ata maka rai? bayan dama haka kuke so, kai da iyalin na ka, to bari ka ji tunda na yi niyyar sai an yi wa yarinyar nan aure a yanzu, wallahi ba wanda ya isa ya hana sai Ubangiji da ya halicce ni. Dan haka zan yi waya da 拼an uwana na can 茩auye, su bincika cikin dangi a samu wanda za a ha蓷a su aure".


Baba ya ce "To Gwaggo ba ni da ja akan umarninki, duk abin da ki ka ce haka za a yi, Allah yasa hakan shi yafi alkhairi".

Kawu Sanusi zai yi magana kenan ya ji ana kiran wayarsa, duba wa ya yi yaga 茩anensa ne Umar, 蓷auka ya yi bayan sun gaisa ya mi茩awa Gwaggo wayar, kar蓳a ta yi ta ce "Yau ka ga damar kirana, tun yaushe rabon da ka yi magana da ni, amma na san ita waccan shashashar matar taka ka na kiranta, saboda ka na gudun zuciyarta, na rasa me yake damunku kaida 蓷an ladi, gaba 蓷aya kun susuce akan mata sai yanda suka yi daku".


"A'a Gwaggo wallahi ba haka bane, ina yawan kiran su Yaya akan su ha蓷a ni da ke, lokacin kuma basa gida, ke kuma gashi ba wace dake ba, an ce a siya miki waya kin ce a'a, ba za ki ri茩eta ba ta saka ki yin 茩arya ba, amma ki yi ha茩uri in sha Allah za a ki ya ye" .


"Na ji ai dama haka ka ke kullum, tukunna ma kai ka bawa matarka damar tafiya tayi zamanta? daga zuwa biki".


"Gwaggo ba zamanta tayi ba, ba ta da lafiya ne, shiya hana mata dawowa, amma in sha Allah yau za ta dawo".


"Ai dama kun iya kare matanku kamar me, haka dai Gwaggo tayi ta yi musu mita, idan ta ce wannan, ta wancan, sai da ta yi mai isarta sannan suka bar gurin.


*******


Bayan Hudah ta gama karyawa, sallama tayi wa Mami ta fita, kai tsaye gidansu Nusee ta wuce, a 蓷aki ta sameta, zama tayi ta na fa蓷in "Wash! Allahna". Nusee ta ce "Sis lafiya na ganki haka a birkice? ni duk kin 蓷aga mini hankali, tunda na ji kin ce ba lafiya. What is problem?".


"Sis ki bari kawai ina cikin wani hali ne".

"Me yake damun ki?" wane irin hali ne ki ke ciki haka, Sis kin gan ki kuwa hadda rama na ga kin yi fa".


"Ai zaki iya ganin abin da yafi rama a tattare da ni, Sis wai kin san cewar ya Mudan aure za a yi masa, kuma abin ba茩in cikin da takaicin a rasa wadda za a ha蓷a shi da ita sai wannan yarinyar 拼ar rainin hankalin Sharifa 拼ar gidan Alhaji Munir, abokin Abbanmu".


Da 茩arfi Nusee ta wuntsilo daga saman gado ta ce "What wa ki ka ce?. Do you mind repeating that".

Hudah ta ce "Wai Sharifa".


*Sai Monday kuma in Allah ya kai muna rai da lafiya, a yi week lafiya* 


Amanar cool ce 鉁嶏笍
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol